Showing 63001 words to 66000 words out of 355604 words
fita ta can, ga cikin wajen ta sama kankarane kasan kuma normal ruwa, da kallo ɗaya zaka yi wa wajen kasan tsara shi a kayi, an tsara shine ya kasan ce hakan, da alama wani abin suke sakawa ruwan yake mugun sanyi haka, har ya zama kankara ta sama, kasa kuma normal ruwa, ta yadda idan ka shiga ba zaka iya ɗagowa sama ba, saboda kankaran.
Ba tare da lion ya ce musu su shiga ba suka yi saurin fara shiga dan already sun san da wayan nan kalar mugunta na Romeo kuma sun san idan suka kuskura suka bari ya musu magana sai ransu ya yi mugun ɓaci, sai na lahira ya fi su jin daɗi, shiyasa suka yi saurin shigewa.
Kasancewar Tga yana da training ɗin sojoji hakan yasa ya yi saurin iyo a cikin ruwan ya fito ta ɗayan kofar, sai dai kuma sanyin cikin ruwan mai bala'i mugun kama kashi ne, dan kuwa yana fitowa ya zube kasa yana riƙe da kafafunsa al'amar suna masa zogi.
John da Jay kuwa sai da suka ɗauki minti 5 kafin su iya fitowa. Idon nan nasu ya kaɗa ya yi jawur kamar jini, harta fuskarsu sai da ta yi ja sosai alamar sun wahala iya wahala, kuma daman kun san farar fata bata jure wuya, sun sha ruwa sun koshi, dan ga cikinsu nan kamar zai fashe.
A tunanin su tun da sun jigata lion zai kyalesu sai su kaga akasin haka, domin kuwa suna fitowa lion ya wuce ya nufi wasu tanki masu kama da drom na manja.
An jera su layi a wajen ɗaya da ruwa ɗaya ba ruwa haka a ka jere tankunan a wajen, suna da yawa a kalla za su kai kwara 20 haka suka tafi layi har karshe.
Kuka sosai John ke yi, kuma da ka ji kukan kasa na gabalaita da a zaba ne, duk wanda ya gansu a halin da suke ciki sai ya zubar mu su da kwalla, wannan ma a haka lion ya mu su da sauƙi.
Tashin hankali to idan ba da sauki ya mu su ba kuma sai yaya kenan? Ina ga sai mutuwa kawai, Jinjina mai girma lion, wannan dole a baka jinjina wai.🤔
Shi kuwa Michael sai wani kara lafewa yake a jikin lion, shi ma lion ɗin yana biye masa, dan yana son a yan kwanakin nan Michael ya samu farinciki over saboda ciwon nasa.
Duk in da lion ya je sai Michael ya bi shi ya kwantar da kansa a saman bayan lion ɗin yana turo baki yana yamutse fuska.
Lion na isa wajen wadannan tankuna zaratan sojojin biyar suka karaso wajen da gudun gaske, haka zalika suma su Tga jan kafafunsu suka yi zuwa wajen dan gara musu su lallaɓa su kai kansu idan su ka bari lion ya ce a ɗaukosu ba zai mu su da kyauba.
Cikin siririyar murya lion ya ce, "Uncle T, you and John go and rest." Cike da murna suka zube kasa a wajen suna mayar da numfashi da kyar da kyar. Shi kuma Jay sojojin da su ka zo wajen suka damko shi suka tsayar da shi gaban ɗaya daga cikin tankunan da ke wajen suka ɗauko ɗan cokali suka miƙa masa sanna suka umarce shi da ya ɗaga kafarsa ɗaya ya ɗora saman ɗayan, ma'ana ya tsaya da kafa ɗaya ke nan.
Haka sai layi yake ya tsaya da kafa ɗaya suka miƙa masa wannan cokalin tare da ba shi umarni a kan ya rinƙa ɗebar ruwan wannan tanki mai ruwan yana zubawa a cikin mara ruwa har ya kwashe ruwan gabaɗaya kuma da wannan cokalin, sannan kuma ko da ya kusa gamawa idan ya kuskura kafarsa ɗayan da ya ɗagan nan ta taka kasa to za a sako lissafi daga farko.
Tashin hankali lallai Lion ka kware yanzu na san dalilin da ya sa sojojinka ke kashe kansu idan har aka ce kai za ka musu hukunci, yanzu na gano dalilin da ya sa tsawarka kawai takan sa zuciyar mutun ta buga ya mutu, irin wannan azabtarwa haka wannan ma dan yan gida ne, to da na waje ne kuma sai yaya? A haka kuma dan ba wani laifi mai girma suka aikata ba, wayyo Jay soyayya ba ta maka adalci ba ga shi kana cikin ha ula'i😭😭
Haka Jay ya fara wannan aikin bakar wahala. Yana farawa Romeo ya sa kai ya wuce cikin gida, ya bar shi da wayan nan sojoji marasa imani wadda basa taɓa saɓa umarnin sa ko kaɗan, ina da tabbacin ko daddy lion ya kawo ya ce su hukunta shi tofa babu makawa sai sun hukunta shi, dan ba su da imani ko kaɗan da sun karɓi umarni shikenan kuma, aiki ba kama hannun yaro, ko shekara za su yi a tsaye sai sun kammala aikin da ya umurce su, ba su da wasa ko kaɗan.
Lion na wucewa cikin sauri Michael ya bi bayansa, John da Tga kuma suna zaune a wajen suna hutawa tukunnan.
Dad na kokarin ceto rayuwarsu Jennifer da uncle Herry, a wanna hali lion ya same shi, wucewa ya yi ya haura sama ba tare da ya ce da daddy upan ba, kamar ma bai san da zaman dad a wajen ba. Haka shi ma Michael ya zo ya wuce bai tanka dad ba, ya bi bayan Romeo.
Romeo na shiga bedroom nasa bai fi da 3mins ba sai ga jibga-jibgan sojoji su shida sun shigo palon, daidai lokacin yaron Jennifer ya tashi ya fara kuka, ɗaukan yaron dad ya yi yana rarrashin sa. Wayan nan sojoji da suka shigo kuma zuwa suka yi suka ɗauki Jennifer da uncle Herry suka fice da su daga palon suka nufi babban hospital, shi kuma dad ya ɗauki yaron su ka koma sama dan ya je ya ba shi madara ko zai dai na kuka.
A ɓangaren lion kuwa yana shiga bedroom nasa ya ɗauki hand gloves ya sanya tare da cire jacket ɗin jikinsa ya fito ya nufi wani ɗan siririn hanya dake tsakanin part nasa dana James. Michael bai ga fitar sa ba ya yi tunanin ko toilet ya shiga, shiyasa da ya shigo ɗakin ya hanye saman gado ya kwanta.
Wani waje mai kyau da ɗan girma lion ya shiga, wajen gaba ɗaya ɗaure yake da buhun masge, rai a matukar ɓace ya fara chaskale da buhu ɗaya, da karfi-karfi yake kai wa buhun nan duka da hannunsa, yana yi yana kara ɗaure fusataccen fuskar nan tasa, yadda yake kai wa buhun naushi yasa damtsen hannun sa suka kara kunbura har wasu jijiyo green suka bayyana a damatsan hannun nasa, gaba ɗaya jikinsa ya fara haɗa zufar, sai cizan lallausan red lips nasa yake da karfi-karfi. Lokacin guda ko me ya tuna ya kara ɗaure fuska sosai tare da damke lips nasa na kasa da karfi gaske, a fusace ya dunkule hannun sa ya kai wa buhun naushi da karfin gaske har sai da buhun ta fashe duk karfin da take da shi. Kai da gani kasan yau lion na cikin damuwa, sai Allah kaɗai ya san meke damun shi.
Damke buhun ya yi da hannayensa ya kifa goshinsa a saman buhun yana sauke numfashi tare da furzar da iska mai bala'i zafi daga bakinsa.
Ya ɗan ɗauki tsawon lokaci a haka kafin nan ya saki wani nauyayyar numfashi tare da sakin buhun masgen ya juya ya nufi waje, kai daga ganin yadda lion ke tafiya a yau kasan baya cikin kwanciyar hankali, yau wani irin tafiya yake yana kara bubbuɗe faffaɗar kirjinsa duk da cewa daman kirjin nasa a buɗe take, amma yana kara buɗe wa, alamar baya cikin kwanciyar hankali.
Yana shiga bedroom nasa ya wuce balcony. Zubur Michael ya miƙe zaune yana mamakin wai daman lion baya ɗakin ne, cikin sauri ya diro kasa daga saman gadon ya nufi balcony ɗin dan ya ga me lion ya ke yi.
Cikin ɗan karamin pool dake wajen Michael ya isko lion kwance a ciki, gaba ɗaya jikinsa na cikin ruwa, daga kansa zuwa wuyarsa ne kawai a waje, ya lumshe dara-daran idon nan nasa ya ɗaga kai sama kamar mai tunanin wani abin, zara-zaran dogayen eyelashes nasa nan sun jiƙe da ruwa, da alama ya wanke fuskar tasa.
Bakin pool ɗin Michael ya zo ya zauna yana faɗin "My lion ina son shan Ice cream" ya yi maganar a shagwaɓe, shiru lion ya yi bai tanka shi ba, amma har cikin ransa ya yi mamakin wai yau Michael ne zai sha ice cream, su da ko tea basa sha da sugar, ɗan garama James amma Michael kwata-kwata baya son zaki a rayuwarsa.
Ganin lion bai tanka shi bane yasa ya fara kukan shagwaɓa yana turo baki. Banza da shi lion ya yi kamar bai san da zamansa a wajen ba.
Tsawon minti goma suna haka sannan Michael ya miƙe ya zai nufi hanyar komawa cikin ɗakin. "come here Michael". A nitse lion ya yi maganar.
Komawa Michael ya yi ya zauna yana faɗin "My lion na ce maka zan sha Ice cream amma ki min shiru". Slowly ya waro dara-daran blue eyes na sa da suka kara kirma sosai saboda yar rama da fuskarsa ta yi alamar baya samun isasshen barci.
Sosai Michael ya tsorata da ganin yadda idon Lion ɗin nasa ya zama, zaro dara-daran brown eyes nasa ya yi yana faɗin "My Lion what happened to your eyes? What is wrong with you? And where is James?" Ya jero masa tambayoyi ne yana kara zaro ido waje.
"Which kind of ice cream you want?" Shine abin da lion ya faɗa a maimakon ya amsa masa tambayoyin da ya masa. Make kafaɗa Michael ya yi kaman karamin yaro yana girgiza kai ya ce "No need of ice cream again, please my lion amsa me what is wrong with you?" Slowly ya mai da idon sa ya lumshe ba tare da ya sake cewa Michael ko uppan ba.
Kwafa Michael ya yi yana kallon kyakkyawar fuskar Lion da yanzu ya ƙara haske da kuma kyau, sai sheki fuskar nasa yake yi kamar fatar jariri, ga gashin sa sun bazun masa har saman fuskar tasa, ba karamin burgesu Lion yake yi ba, duk da suke Triplets basa kama da shi, sai dai kama ta jini, amma duk ya fi su kyau, dan shi da dad yake kama, har kwayar idonsa na dad ya ɗauko tsawo da komai duka na dad ne, sai dai yafi dad ɗin ma kyau sosai.
Ganin ya jima a zaune Lion bai ce masa komai bane yasa ya kai hannunsa ya ja dogon hancin lion yana faɗin "Wake up and answer me" shiru Lion ya masa kamar baya jin shi. Hakan yasa Michael ya miƙe ya bar wajen yana turo baki.
Lion ya jima sosai a wajen kafin ya fito ya ɗauki towel ɗaya daga cikin towels dake jere a wajen, ya ɗaura a jikinsa sannan ya nufi cikin ɗaki jikinsa na ɗigar da ruwa.
Lokacin da ya koma bedroom nasa Micheal ya yi barci, kallo ɗaya Lion ya masa ya kauda kai tare da wucewa dressing room nasa.
Jim kaɗan ya fito sanye da wando jeans three quarter fari tas da kuma riga mai ƙaramin hannu mara nauyi launin sky blue mai haske. Gaban mirror ya zo ya tsaya ya fara shefe-shafen lotion nasa masu bala'i kamshi da kyau da tsada.
Bayan ya kammala ya wuce ya zauna saman chair dake gaban wani kyakkyawan table a cikin ɗakin, tare da fito da wasu chemicals ya fara haɗawa, yana yi yana tunani. Ya yin da shi kuma Jay yake halin kakani kaye, yana tsakanin mutuwa da rayuwa, ga shi kuma da alama lion ya mance da shi, kuma koda Jay ya kammala matikar Lion bai bada umarni sojojin su kyale shi ba, to fa ba za su kyale shi ba, ko da ya gama transferring na ruwan a ɗayan drom ɗin sake sa shi za su yi ya sake transferring na ruwan zuwa drom da ya kwashe da farko, ga shi kuma drom ɗin a kalla zata kai 200lt ma'ana jarkan ruwa takwas kenan.
(Tashin hankali to kai fa Jay sai dai mu ce Allah ya kwace ka kawai, amma in ba haka ba kana cikin gararin rayuwa, ka ga ta kan ka yau idan halinka ne gobe ma ka sake.
Su kuwa su Tga bayan sun gama hutawarsu, da su ka samu kafarsu ya ɗan yi kwari sai su ka miƙe su ka wuce cikin gida. Tga na shiga bedroom na sa wanka ya yi ya haye gado sai barcin wahala, shi kam John ko wankan ma bai yi ba dan wahala da ya sha saboda bai yi training na soja ba shiyasa ya wahala sosai Tga ya fi sa kwari. Bajewa ya yi a saman bed nasa ya hau barcin azaba.
Su kuma uncle Herry da Jennifer an wuce da su hospital, kuma hakan ya faru ne sakamakon umarnin da Lion ya ba wa sojojin nasa a kan su wuce da su asibiti. Daddy kuma yana can ɗakinsa yana fama da renon yaron Jay.
Wanna fa shine cakwakiya. To mu dai bari mu leƙo Rimsha yar amanar mu mu dawo
💞💞Nigeria💞💞
Rimsha!
Zaune take a wani irin waje wadda kamar ba a duniyar mutane ya ke ba, wajen cike yake da furanni masu kyau da kamshi, abin mamaki kuma kamshin wajen sak irin kamshin jikin Lion ne, wajen ya kasance a bakin wani katon teku ne mai matukar girma da baka iya ganin karshensa, saboda girma, daga ɗan jefenta wani irin haɗaɗen ɗakin da Turawa suke a cikin daji ne, mai kama da bukka, duk da a cikin dajine, ɗakin yaji komai da ake bukata kamar ɗakin wata sarauniya, an kawata shi sosai da sosai. Yana yin iskar da dogayen bishiyoyin wajen ke kaɗawa abin gwanin ban sha'awa da ɗaukar hankali, idan iska ta kaɗa sai ruwan tekun nan ya taho da gudu har zuwa bakin gaba kusa da in da take zaune, idan ruwan ya koma sai kaga wasu kananan kifaye suna tsalle abin ba'a cewa komai ya kayatar ba kaɗan ba.
Sanye take da wando guntu zuwa santala-santalan kyawawan cinyoyin ta dake ta sheki ga laushi kamar fatar jariri, daga ta sama kuma tana sanye da riga zuwa cibiyarta, iya tula-tulan ta kawai ya rufe, ga su a tsaitsaye damdam da su Masha Allah, duk wanda ya ganta sai ya kyatsa domin ta cika ta haɗu ta ko ina, komai ya zauna daidai, kamar ba Rimsha ba.
Daddaɗar iskar dake kaɗawa sai kaɗa mata dark black curly hair ta yake, gashin na bazuwa yana rufe mata fuska, sai cizan Pink lips nata take, tare da lumshe dara-daran sleeping eyes nata kamar mai jin barci, hakan yasa zara-zaran dogayen eyelashes nata suka kara bayyana kamar wadda ta yi kari dana kanti, ta yi shiru tana sauraran kukan tsuntsyen dake tashi daga dogayen bishiyoyi dake gefe-gefen tekun.
A hankali ya tako zuwa in da take zaune, shima jikinsa na sanye da short fara tas daga ta samansa kuma ba bu riga, faffaɗar kirjin nan nasa a waje ga wasu kyawawan bakin gashi mai bala'i tsantsi kwance a saman kirjin nasa, breast nasan nan bul'bul gwanin burgewa.
A zahirin gaskiya bayyanar asalin surar jikinsa ba karamin haukata mai kallo zata yi ba, domin akwai wasu sirrika a tattare da shi wadda duk wanda ya gan shi to dole ya faɗa da mahaukacin son shi, sai dai kuma bayyanar asalin halittar tasa ta kara masa bala'i kwarjini wadda babu wanda zai iya tinkararsa ya masa wani magana, ko kallonsa cikin ido ba zaka iya yi ba, saboda baiwar kwarjini da Allah ya masa ga kuma yanayin kirar jikin nasa na manya jarumai sadaukan yaki, damatsan hannun nan nasa kawai ya isa ya firgitar da mai rai, shiyasa mutane ke razana da kallonsa.
Shima kamar ita bai ɗaure gashin kansa ba haka iskan ke kaɗa masa gashin nasa zuwa fuskarsa, abin ba'a cewa komai sai wanda ya gani, domin baki ba zai iya fasalta yadda kawatuwansu ya kasanceba.
Ta bayanta ya duƙa tare zuro kyakkyawan hannunsa ta saman shafaffen flat tummynta. Dogon numfashi ta ja tare da sauƙewa a hankali lokacin da ta ji saukan hannun nasa a saman cikinta. Slowly ya matso da ɗan karamin bakinsa daidai saitin kunnenta, kasa kasa da wata iriyar murya mai kama da mai mayen barci a hankali ya motsa laɓɓansa ya ce "Ke ma kin yi missed ɗi na ne?" Ya kai karshen maganar tare da sanya ɗayan hannunsa ya fara tattare mata gashin kanta dake rufe mata kyakkyawar fuskar ta saboda iska dake kaɗawa.
"Dole zan yi missing naka mana, ka fa san kai ɗin na daban ne a duniya" yana kokarin ɗaure mata gashin nata ne ya matso da ɗan bakinsa sai tin lallausan wuyarta ya manna mata kiss a wajen, gently ya ce "My Rimsha you are special" lokacin da ta ji saukar lausasan laɓɓansa a saman wuyarta wani irin ɗauke wuta ta yi, na yan mintoci kafin ta saki cool murmushi wadda ya sanya dimple nata lotsawa, yatsansa ɗaya ya sanya cikin dimple ɗin nata tare da sakin gashin kanta dan yaki ɗauruwa ya yi tsantsi sosai, a hankali ya kwanto da kansa saman kafaɗar ta yana sauke numfashi a hankali, yana shakan daddaɗar kamshin dake fita daga gashin kanta, sai faman lumshe ido yake kamar mai jin barci.
Numfashi sa dake sauka mata a saman kirjinta a hankali-hankali ba karamin kara gefata cikin yanayi yake ba, yana kara gigitata sosai, shima kuma kamshinta da yake shaƙa ba ƙaramin gigitashi tare da ingiza zuciyarsa take ba.
Ta yi nisa cikin tunanin wadda sai Allah kaɗai yasan tunanin da take. A hankali ta jiyo hannunsa yana shafa mata shafaffen cikinta, sai ajiyar zuciya take sauƙewa a hankali.
Uhmm abin nema ya samu🤣
Cikin salo da kwarewa ya juyo da ita suna fuskantar juna tare da matso da ɗan karamin bakinsa saitin tata yana kokarin kissing nata, ba karamin razanata kyansa ya yi ba, yau yazo mata ba face mask, ta tsorata da kyansa musamman kwayar idonsa da suke ta kwalli sabo zarosu da ya yi, kunsan blue eyes da kyalli. Tsoratar da tayi da ganin kyansa ne yasa ta saki ihu wadda ya yi sanadiyar farkawar ta daga nauyayyar barcin daya ɗauke ta tun bayan sallar asuba. A zahirin gaskiya ko a mafarki kwarjinin Lion ya tsoratata