Showing 318001 words to 321000 words out of 355604 words
kyautar makudan kuɗaɗe, sosai su ka yi farinciki fiye da tunanin mai tunani, su kuma sauran sai nazari da tunani suke yi akan addin.
Da haka Aseef ya ce suma waƴan da basu musultar ba su bashi account number bari ya yi masu kyauta domin yau ranar sadaka ce, yau duk sadakar da zai yi yana fatan Allah ya bawa Musharraf ladan, uncle Musharraf zai yi wa sadaka.
Haka kuwa akayi, dukkansu saura goma da basu musultar nan ba sai da Aseef ya sanya masu kuɗi a cikin account nasu, sannan ya ce huɗu su tsaya a wajen table saura takwas ɗin kuma suje su huta wa ransu sai da rana.
Da haka suka yi sallama Aseef ya ciro wayarsa ya kira number Lion.
Yau karo na farko a duk rayuwar da Aseef ya yi da Lion yau ita ce rana ta farko da ya kira Lion kira ta farko ya ɗauka, wannan shine zai nuna maka Lion yana cikin damuwa, domin dama ya faɗa maku Aseef ne kawai mai ɗebe mashi kewa da kuma rage mashi damuwar da yake a cikinta, mutane sun kasa ganewa duk tarin makudan dukiya da kake da shi ba zata iya yi maka komai ba idan kana cikin wata matsala ko jarabawa ta Ubangiji, amma sai mutane su dage sai sun yi kuɗi ta ko wace hanya, su dai kuɗi kuɗi kawai, suna ganin kamar shi ne kwanciyar hankali da farinciki, tabbas kuɗi yana sanya farinciki kuma yana maganin wata damuwar, amma fa ba kowanne ba, kuma idan ta hanyar da bata dace ba aka sami kuɗin sai ma karawa mutun azaba da zai yi a maimakon maganin matsala, kuɗi bata isa ta warware maka kaddarar da Ubangiji ya ɗaura maka ba, yanzu tambaya a nan shine wani irin kuɗi ne su Lion basu da shi? Ga kuɗi ga mulki isa da duk wani abin da bawa yake ganin shine jin daɗin duniya, sune ke mulkar kasar baki ɗaya tun da kakansu ke a kan kujerar president, ga Lion da babbar muƙamin da babu biyunsa, sannan ga jarumta na iya tunkarar komai da zai kawo masu matsala, uwa uba ga makudan kuɗaɗe da su kansu basu san iya kan shi ba, amma kuma sai me, ga shi dai kullun suna cikin damuwa, daga Lion har James ɗin kullun suna cikin damuwa, Aseef ne kawai bawan Allah wadda bai san komai ba sai kaunar mutane, shine kawai yake cikin farincikin da har yake sanya ƴan uwan nasa farinciki, yanzu wani idan ya ga mutun irin Lion ko ya ji labarinsa sai ya ce shikenan su kam ba zasu taɓa shiga damuwa ba, dan suna da kuɗi, to ga dai shi nan kullun cikin binciko wani matsalar suke yi suna shiga damuwa.
"Hello Lion" kamar dai kullun wannan halin tasa tana nan idan aka yi mashi magana sai ya jima kafin ya amsa.
"Aseef what is going on?" Shine abin da Lion ya tambaya bayan ƴan mintoci kenan.
"Lion please ina son kasa Tyrone ya tura wa duk wani maaikacin da muke biya albashi a gidan nan sadaka, tun da shine dama mai biyansu albashi, a hannunsa komai yake, to ya sanya masu kuɗi a account nasu da nufin Allah ya bawa uncle Musharraf lada ka ji ko?" Shiru Lion ya ɗan yi na ƴan mintoci da ba za su wuci 5 ba.
Can kuma sai ya ce "Okey what about your Exams?" Nan Aseef ya gaya mashi e next week zai fara exam ɗin yanzu ma school zai ta fi, to Lion ya amsa da shi tare da ce mashi ya kula da kansa, daga nan suka yi sallama.
Yana ajiye wayar suka fara cin abinci shi da Musharraf a cikin plate ɗaya saboda tsananin kaunar juna da suke yi, sauri sauri suka ci abincin dan karfe takwas ta kusa.
Suna kammalawa suka wuce izuwa parking space na gidan.
Yau ma dai tare da su Lucky Aseef ya tafi, sai dai kuma yau su Lucky dukkansu a gidan baya suka zauna, uncle Musharraf ya zauna a gidan gaba.
Da gudu Aseef ya figi motar suka hau titin zuwa bakin gate ɗin gidan, basu wani ɓata lokaci ba suka fice daga gidan.
Sai da suka fita Aseef ya tuna bai bawa Brady abinci ba, hakan yasa ya juyo da kan motar ya dawo ya ba shi abincin, dan ya san Brady baya yarda da kowa a gidan idan ba Lion ba sai kuma shi, to ko wani ya kai mashi abinci ma ba zai ci ba.
Bayan ya bashi abincin ne kuma suka wuce Harvard University.
Suna zuwa Aseef ya kai Musharraf office ɗin ɗaya daga cikin malamansu wanda suke shiri da shi sosai, da ya kai shi ma sai da ya gayawa uncle ɗin nasa ya kula mashi da uncle Musharraf sosai da sosai bari ya yi attending lecture yana zuwa.
Da haka suka yi sallama ya bar su Lucky kuma a wajen motarsa suna gadi.
After 2 hours ya dawo ya ɗauki Musharraf suka bar school ɗin zuwa shopping kamar yadda ya faɗa.
Sosai Musharraf ya ɗauki duk kayan da yake so, ciki kuma har da jallabiyas da dama, bayan shi kuma ya kwashi tsaraba yadda yake so, yana ɗauka Aseef yana kara mashi wani, duk abin da ya ɗauki guda ɗaya sai Aseef ya kara mashi uku akansa.
Sun zo daidai wajen sayar da kayan sanyi Aseef ya yi karo da wani black guy, ɗan baya kaɗan Aseef ya yi kafin ya ce sorry, shi kuma guy ɗin sai ya ce kayi hakuri sannan ya wuce, shiru Aseef ya yi yana kallon guy ɗin har ya wuce yana kuma maimai ta kalmar kayi hakuri da guy ɗin ya ce.
Taɓa shi Musharraf ya yi yanan faɗin "Kana mamakine dan ka ji ya yi Hausa?" Juyowa ya yi yana faɗin "Uncle Musharraf what is Hausa?" Nan Musharraf ya gaya mashi Hausa tana ɗaya daga cikin yarukan Nigeria.
Murmushi ya yi yana faɗin lallai sai an koya mashi yaren nan, ko Musharraf ya koma za su rinƙa yin lecture Hausa ta waya, to Musharraf ya ce, kuma ya ji daɗi zai koyawa ɗaya daga cikin TRIPLETS Hausa.
Haka suka kammala sayayyarsu suka wuce zuwa masallaci domin azahar ta yi, ko da suka je Masallaci a mota suka bar su Lucky su kuma suka shiga ciki.
Bayan sun idar da sallah ne suka fito, suna fita suka haɗu da Aryan yana ƙoƙarin shiga Masallaci hannunsa na riƙe da kwalin dabino mai ɗan girma.
Ganinsu yasa ya kariso wajen da sauri dan yanzu ko Aseef yana sanye da face mask Aryan ya riga da ya san shi, yana gane shi, su kuma Triplets dama duk in da zasu je da face mask a fuskarsu.
Yana zuwa Aseef ya miƙa mashi hannu suka gaisa yana tambayar shi akan me bai zo ya yi sallah a cikin jam'i ba? Ya yi maganar kuma yana karɓar dabinon sadaka dake a hannun Aryan ɗin, ko wace rana Aryan yana zuwa da dabino ya raba sadaka yana addu'ar Allah ya kai wa Aseef ladar, dan Aseef ya yi masu komai a rayuwa, yanzu ga shi shagon da Aseef ya buɗe masu ta kara kirman sosai saboda sada da suke yi tare da kyautatawa al'ummar Annabi.
Aryan bai taɓa tunanin cewa Aseef zai ci wannan dabino ta sadaka ba, sai kuma ya ga ya deɓi guda shidda ya bawa Musharraf uku ya riƙe uku, duk da yake dabinon a wanke take sai da Aseef ya sake wanketa tas sannan ya sa ɗaya a bakinsa yana yi wa Aryan faɗa akan ko me yake yi kada ya kuskura ya sake bari Sallah ta sake wuce shi, idan ba haka ba zai bashi hukunci mai tsanani domin yanzu a kani na jini Aseef yake ɗaukar Aryan, shiyasa idan ya yi ba daidai ba Aseef ɗin yake cewa zai hukunta shi.
Hakuri Aryan ya bashi tare da yi mashi alkawarin In Sha Allah sallah ba zata taɓa sake wuce shi ba, zai rinƙa ƙoƙari ya zo akan lokaci, yanzu ma toilet ya shigane Shiyasa, amma ya zama dole ya rinƙa bin jam'i matukar yana son cigaba a rayuwarsa.
Jinjina kai Aseef ya yi kafin su sake gaisawa da Aryan ɗin daga nan kuma suka rungumi juna, bayan sun raba jikinsu ne kuma Aryan ya rungumi Musharraf dan shi Aryan a yayan Aseef yake kallon Musharraf, bai damu da cewa Musharraf baki ne akan hasken Aseef ba, shi dai kawai tun da ya gansu a tare kuma kullun suna a tare shikenan, amma fa batun kyau, Musharraf fa kyakkywar gaske ne, shiyasa da farko JAMES ya kira shi da balarabe, kuma yana ɗaya daga cikin dalilin da ya sanya Aryan ya yi tunanin ko dai yayan Aseef ɗin ne dan kyau dake a gare shi shima.
Sallama suka yi Aseef ya ce Aryan ya je ya yi sallah kada lokaci ta kure, to ya amsa tare sa wucewa cikin masallaci, su kuma suka sauƙo kasan stap ɗin zuwa wajen motar su.
Kamar yadda aka saba jama'a ne sosai suka taru a wajen motar suna jiran isowarsu dan Aseef ya saba yi masu sadaka, yana zuwa kuwa ya zaro kuɗi ya fara raba masu kamar ko da yaushe, yau duk sadakar da ya yi yana addu'ar Allah ya bawa Musharraf ladan ne.
Sosai yau ma ya yi sadaka, sai da ya sanya gaba ɗaya mutanen dake a wajen farinciki sannan suka shiga mota zuwa gida.
Suna a kan hanya ne yake gayamawa Musharraf gobe kuma a account ɗin Areef zai ɗebi kuɗi ya zuba a account nasa dan kuɗin sa ya yi kasa, kuma ya ga ji da karɓar kuɗi a wajen Lion, zai bar Lion ya sha iska na kwana biyu, yanzu zai koma account ɗin Areef daga nan kuma sai account na uncle T, duk sai ya kwashi kuɗinsu ya yi ta sadaka ko Allah zai sanya suma su musulta, bare ma uncle T.
Sai dariya Musharraf yake yi mashi tare da yi mashi addu'ar Allah dafa mashi ya gama karatun shi shima ya kama aiki dan ya tara kuɗin kansa, dan ma Allah yasa ƴan uwan nasa suna matukar kaunar junansu, kuma basu damuwa dan wani ya taɓa dukiyarsu ma bare kuma shi da yake cikonsu, wata zubin daddy da kansa yake cewa Aseef ɗin ya zo ya ɗebi kuɗi a account nasa iya yadda zai buƙata, da yake daddy ba abin da yake yi da kuɗin suna zaune, tsawon shekaru yana aiki, ya tara makudan kuɗaɗe, kuma yanzu ma kullun sai kuɗi ta shigo Account nasa saboda babbar hospital ɗin dake Washington DC tasa ce, shi ya gina kayansa da kansa, kullun cikin kuɗi yake ko bai je aiki ba, ga uncle T shima akwai kuɗi sosai, kuma dukkansu Aseef ya san sirrin bankin su, dan shine bashi da aiki sai dai a bashi kuɗin, shiyasa dan ya rage masu wahala suka nuna mashi komai na daga siririn account nasu, ya ciri kuɗi time da yake so dukka ga card nasu a cikin ɗaki.
Suna zuwa gida ya fara mayar da su Lucky ɗakin su kafin nan ya wuce izuwa part nasa, soja ɗaya ne ya kwasan musu sayyayar da suka sawo izuwa part nasu.
Aseef yana shiga toilet ya wuce ya yi wanka sannan ya zo suka ci abincin rana bayan shima Musharraf ɗin ya yi wanka kenan.
Bayan sun gama cin abinci ne suka zauna Aseef ya ce Musharraf ya fara koya mashi yaren Hausa, to Musharraf ya amsa da shi sannan suka fara da gaisuwa.
Idan Musharraf ya ce ina kwana sai Aseef ya ce innkowa saboda harshen a lanƙwashe take ba ta taɓa furta kalma makamanciyar Hausa ba, abin ma dariya ya rinƙa bawa Musharraf har da hawaye saboda dariya, kunsan idan aka ce yare ba naka ba to fa sai a hankali zaka sha wahala wajen iya furta shi, ai kuwa Aseef dai ya sha bakar wahala har haɗa zufa ya yi wajen dole dole sai ya yi hausa shi.
Wunin ranar dai a haka suka wuni a koyan Hausa, kuma a iya gaisuwa kawai suka tsaya, shima bai zauna daidai ba kawai dai ayi sha'ani. Har lokacin sallar la'asar ya yi sannan suka wuce masallaci, daga masallaci kuma suka wuce yawata gari dan Musharraf ya ga koina kafin ya koma, har white house sai da Aseef ya kai shi, amma fa da suka je white house Musharraf ya ga ikon Allah, domin kuwa ya ga yadda ake nuna kiyayya karara, karara suka nuna mashi kiyayya dan shi bakar fata ce a cikinsu, da Aseef ya lura da haka sai ya ce su tafi kawai dan baya son hayaniya kuma baya son abin da zai ɓatawa Musharraf ɗin rai, shima Musharraf ɗin tafiyar ta fi mashi alkhari.
Suna barin white house suka sake lulawa duniyar yawo har cikin New York basu bari ba.........nu kuma na haɗa kayana zuwa
NIGERIA dan na ga me yake gudana, wata kila kafin mu dawo su Musharraf ma sun dawo.
# GIDAN LION🦁
Yau dai Rimsha ta riga Imran tashin daga barcin safe, ba laifi kafar tata ta ɗan sake ta, ita kuwa jelly ko tashi sallar asuba ta kasa yi, Imran ba dan ya so ba ya kyaleta ta cigaba da barcinta.
Misalin karfe 7 na safe Rimsha ta fito, ta ci wankanta cikin wandon jeans palazo, ta kasa a buɗe ta sama ya matseta, sai ƴar T-shirt da ta sanya a jikinta, ta yi kyau matuka kamar ba ita ba, yanzu da yake tana girma wani sihirtaccen kyau take karawa, ga shape nan kamar me ba'a magana, akwai hips irin mum ɗinta, sannan akwai tula tulan breast irin na gwaggo, ga breast ɗin tata a sama sannan ga su da faɗi sosai alamar ba zasu kwanta ba, komai zamzam tamkar ita ta yi kanta, sai tashin wani fitinannen kamshi take yi, da kyar ta sha bakar wahala ta ɗaure wannan curly hair nata, yana da tsantsi sosai baya ɗauruwa ta daɗi, bayan ta ɗaure shi sai ta sanya turban cap a kanta mai shegen kyau launin blue kalar jeans ɗin jikinta, shi kuma rigar jikinta karine tas kamar yanzu ta ciro shi daga ladarsa.
Tana fito palon sama ta nufi hanyar sauka izuwa palon kasa, har zata wuce sai ta hango bedroom na Lion a buɗe, lallaɓawa ta yi ta nufi wajen da nufin ta leƙa ta ga ko zata samu ganinsa, ai kuwa bata kai ga leƙawa ba ta ji takun manya ta bayanta yana haurowa saman benen, ya je ne dama ya bawa Areef magungunansa da Dr Tyrion ya bada ya rinƙa sha, an samu an yi mashi aiki cikin nasara yanzu sauƙi kawai suke jira.
Ai kuwa ko ba'a faɗa mata ba tasan cewa tabbas Lion ne mai wannan taku, da wani irin mahaukacin gudu ya watsa ta shiga bedroom nata, tana shiga shi kuma yana shigowa cikin palon, lumshe dara daran blue eyes ɗin nan nasa ya yi, tabbas ya ga geftawar abu kamar mutun ya shiga bedroom nata, sai dai bai san daga ina ta fito bane.
Shiru ya ɗan tsaya, jikinsa na sanye da wasu irin kaya masu haukata kwakwalwar wadda ya kallesu, riga da wando ne dukka iri ɗaya, launin ash color mai ashe ne, sai walwali kayan suke yi, rigar ya yi kamar T-shirt amma ba t-shirt bane, suna da bala'in laushi sosai, da alama kuma kayan barci ne, sai tashin wannan sihirtaccen kamshin nan nasa mai kwantar da hankalin mai shaƙa yake yi, ya ɗaure dark black curly hair nan nasa a bayan wuyarsa, sannan ya bar wannan guntu na gaban goshin, kallo ɗaya zaka yi mashi ka gane jikinsa a mace yake domin kuwa ga shi nan dai sai wani faman lumshe idanu yake yi kamar mai jin barci.
Bedroom nasa ya shige domin kuwa kwakwalwarsa ta gaya mashi wace ce ta gifta ɗin, dan yasan ba Imran bane, bai damu ba saboda yasan ai tana zuwa wajen Imran, so ya yi tunanin daga ɗakin Imran ɗin ta fito.
Ita kuwa tana shiga bedroom nata ta laɓe a bakin kofa tana kallonsa ta mahangar kofar, shi kuma baya ganinta, a yaune ta samu damar kallon fuskarsa sosai a zahiri, ba a camera ba, ba kuma a hoto ba, wani irin sake haukacewa da kaunarsa zuciyarta ta yi, ji take yi kamar ta je ta rungume shi, har wani zogi zuciyarta take yi mata, baiwar Allah.
Ta jima tsaye a wajen tana tunani kafin ta sake fitowa ta nufi palon kasa. Babu kowa a palon dan haka sai ta shiga cikin kitchen ta ɗebi fruits a wani kyakkywar plate mai shegen kyau da tsada ta fito ta nufi waje harabar gidan baki ɗaya.
Tun da ta fito sojan dake tsaron gate ɗin nan ya zuba mata idanu, yana zaune shi da Mark kamar dai jiya, sai hira suke yi. Ganin ya yi shiru yana kallon wani waje ne yasa Mark ya juyo dan ya ga me yake kallo ya ɗauke mashi hankali haka, ganin ita ce kamar wata tauraruwa a tsakiyar duhun dare ne ya sa ya daka mata tsawa akan ina zata je? Jikinta har ya soma karma ta ce garden zata je, daga nan bai sake yi mata magana ba ta wuce ta nufi garden ɗin, shi kuma gate man ya bita da ido kamar wani tsohon maye yana wani lashe baki.
Sai da ta kure wa ganin sa ne ya ce "Mark i really like this girl, she is so cute". Shiru Mark bai yi magana ba kuma bai ɗago ya kalle shi ba, sauƙe ajiyar zuciya ya yi yana mai sake maimai tawa Mark abin da ya faɗa.
Sai lokacin mark ya ɗago kai cikin sanyin murya ya ce "You are not serious, Sister babbar aminin oga ce fa, ban taɓa ganin oga ya tsaya yana magana da wani kamar yadda suke magana da brother ɗin yarinyar can ba, ko tsawar da na daka mata yanzu ma dan na san ba wanda zai ji ne shiyasa, amma ba dan haka ba da ba zan yi mata ba, zan baka shawara kada ka bari idanunka ya sake kallon yarinyar nan, if not lahira zata yi baƙo, kasan dai yadda oga yake kaunar brother ɗinta dole idan abu ya sameta bro ɗin nata ya shiga damuwa, idan kuma ya shiga damuwa dole oga zai tanka maganar dan na lura baya