Showing 189001 words to 192000 words out of 355604 words
magana ba.
Yana ƙoƙarin juyawa izuwa wajen labulen kawai idanuwansa suka sauƙa saman mirror dake a cikin ɗakin, gaba ɗaya Mirror shaƙe yake da mayunka Lion da ya saba shafawa, ga su perfume nasa air freshener da sauransu, mamaki ne ya kama Imran daga ina wayan nan abubuwa kuma suka fito.
Bai gama rikicewa da mamaki ba ma, sai da ya buɗe wannan kyakkyawar labule fari tas da Lion ya nuna mashi, yana yaye labulen wani irin kyakkyawan dressing room ne ya bayyana a wajen, da glass aka yi dressing room ɗin, kusan dai irin dressing room nasa na Washington DC, cike da mamaki ya karisa ciki, abin mamaki kaya ne shaƙe a cikin, duk kuma kayan sabbine bama a ciresu a ledarsu ba, kenan saya ya yi? Ko dai daga Usa aka zuba su a jirgi ta kawo mashi? Abin mamaki dai baya karewa a tattare da Lion, kullum cikin saka mutane mamaki yake yi.
Dadduma ya zaro sai tashin fitinannen daddaɗar kamshi kayan cikin drawer suke yi, da alama sun sha perfume sun ƙoshi, shi ma daddumar sai kamshi yake yi sosai, ga shi da laushi kamar jikin bargo, fari tas, komai na Lion fari ne tas, yana son white color over.
Shifiɗa daddumar ya yi tare da gyara tsayuwa ya tada kabbara ya fara sallah.
Lion na zaune yana ganinsa har ya idar, ya zauna a saman daddumar ya yi askar tare da addu'ar Allah ya dawo mashi da jelly sa, Allah kuma yasa kada Lion ya yi wa James hukunci mai tsanani. Da haka ya shafa addu'ar tasa ya miƙe yana faɗin "Saif zan je hospital daga nan zan wuce gida sai da daddare zan shigo mu gaisa, amma kafin nan zan kawo maka kayan sawan ka". Ya karisa maganar yana jiran amsar Lion ɗin.
"No Professor I want you to stay with me here before na koma" ya yi maganar a nutse kuma ba tare da ya kalli Imran ɗin ba. Dama already Imran yasan hakan zata faru domin Triplets a tare suka saba rayuwa, duk da cewa Lion baya wani shigarsu sosai, ma'ana baya zama da su sosai su yi hira, amma fa ko ina da wuya ka ga ɗaya baka ga ɗaya ba, ba zai iya zama a cikin wannan gida shi kaɗai ba, ba Michael ba kuma James, abin ya mashi yawa, akwai wuyar zama, sannan kuma ba kasar su ba, zama ba tare da su Michael ba zai mashi matukar wahala.
"Saif i can't stay here without my Sister, ita ɗin amana ta ce, Ammie ba ta son ta zauna a gidan mu, kuma bata da kowa, ni kaɗai ke a gareta, kuma yanzu haka da nake maka magana ita zan je dubawa a hospital bata da lifiya, Dr ya ce tana buƙatar kulawata sosai, ba zan iya yin nisa da ita ko na minti ashirin ba, idan zan zauna a nan to dole da ita zan zauna....." Bai kai karshen maganar ba ya Katse shi ta hanyar ɗaga mashi hannun, sannan gently ya ce "Idan kuma na ce ina son ka zauna a nan ɗin ba tare da ita ɗin ba fa?".
Wani dum-dum Imran ya ji gaban sa ta faɗi domin ya san halin Lion tsab zai iya sawa dole ya baro Rimsha a gidansu, shi kuma ya zo nan su zauna, idan hakan ta faru kuma to ba zai taɓa samun kwanciyar hankali ba, babban abin da ya kara ɗaga mashi hankali shime Dr ya ce Rimsha na matuƙar buƙatar kulawa, kada a barta ita kaɗai a gida, cos abin ya taɓa shi sosai. Tsabar shiga damuwa da tashin hankali har wani zufa ne ya fara tsastsafo mashi daga gefe da gefen fuskarsa, yana son ramawa daddyn Rimsha alkhari da ya yi masu ta hanyar kula da Rimsha da dukkannin lokacinsa, amma Lion na ƙoƙarin dakatar da shi.
Dafe kansa ya yi, ga shi kuma ba halin ya ce da Lion ya yi hakuri, domin baya son kalmar sorry ko kaɗan, idan ma ya ce mashi sorry to suna iya samun babbar matsala.
"30mins sun isheka ka yi anything da kake so, daga gidan ku zuwa nan" ya kai karshen maganar yana ɗago da kallonsa a kan fuskar Imran ɗin, jinjina mashi kai Imran ya yi alamar to, sannan ya ɗaura da ce wa "In Sha Allah".
Shiru Lion bai sake yin magana ba, shi kuma bawan Allah Imran haka ya sa kai ya fice daga cikin ɗakin zuciyarsa cike da ciwo da kuma kunan sosai, yanzu haka zai bar Rimsha a gidansu, wlh ba zan taɓa samun kwanciyar hankali ba, domin Ammie bata son ta, yanzu bata san da zamanta a gidan bane, idan da ta sani ba zata taɓa barinta ta zauna ba, yanzu idan ya dawo wajen Lion wani abin ya faru da ita fa? Ya zai yi kenan? Bai cika amana ba gaskiya, ko dai in kai ta Maiduguri wajen Hajiya Batula ne? Ya tambayi kansa yana ƙoƙarin shiga motarsa, "No ba zan iya kai ta Maiduguri ba gaskiya ya yi nisa, to ko dai na kaita wajen Ummin Dr ne?" Nan ma sake girgiza kai ya yi alamar a'a ba zai iya yin hakan ba saboda baya son ta yi nisa da shi, kuma Dr Nawid yana son ta, zamansu waje ɗaya ba alkhari bane, domin duk yadda namiji ya kai ga son mace, komai hankalinsa da ilimin sa da natsuwarsa zaman su a wajen guda ba'a yi aure ba, ba babbar haɗari ne, kuma ba alkhari bane, saboda akwai shaiɗan yana tsaye daga gefe yana kula da komai, hakan yasa Imran ya fasa shawarar ya kai ta can. Yana ta tuki yana tunani har ya isa asibiti.
Lokacin da ya shiga ɗakin ta farfaɗo ga ruwan da aka sanya mata ma ya kusa karewa, sannu ya yi mata tare da zama gefenta ya riƙo hannunta ɗaya, cikin murya irin wadda ake yiwa yara rarrashi ya fata magana, Akila na zaune saman kujerar dake a wajen tana jinsu.
"Rimsha dan Allah kada ki ɓoye mani, ki faɗa mani menene yake damunki da har ya sanya ki a cikin wannan hali? Kina kewar su mum ne? Ko akwai wani abin bayan hakan?" Kasa ta yi da kanta, cikin natsuwa ta ce "Yaya Imran wlh ni ma ban sani ba" shiru ya yi yana nazarinta, Akila ce ta katse mashi shirun da cewa "Yaya Imran me yake damunta?".
Girgiza kai ya yi yana faɗin "Ba komai heartbeat yanzu dai bari na kila Akil in gaya mashi idan karfe 4 tayi ya zo ya ɗauke ku zuwa gida" To Akila ta ce mashi.
Ciro wayarsa ya yi ya fara kiran layin Akil ɗin, wayar ta yi ringin har ta yanke bai ɗauka ba, sake kira ya yi, wayar na gab da katsewa sannan ya ɗauka.
Muryarsa cike da mayen soyayya da alama a sama yake, yana network, can kasa-kasa ya ce "Hello yaya Imran" "Barci kake yi ne? Ko dai baka da Lafiya ne?" Imran ya tambaya.
(Ka ji Imran da shisshigi ina ruwanka, mutun ba gwabroba ka ce me, sai ka jiyo abin da zai hana ka barci wata rana, in dai Akil ne🤣 ko da yake ba laifin ka bane, baka san dawar garin bane🤣)
"E...a'a...dai ban yi barcin ba tukunnan" jin irin amsar da ya bashi ne yasa ya yi danasanin tambayarsa, sai ya ji gaba ɗaya kunya ta kama shi, sauri-sauri ya ce "Karfe huɗu daidai ka zo asibitin Dr Nawid ka ɗauki heartbeat da kuma Rimsha zuwa gida, dan Allah akil na baka amanar Rimsha ka kula da ita sosai" ya kai karshen maganar tare da miƙewa ya fice waje kamar ya san da Akil zai tambaye shi me ya same su.
Ai kuwa yana fita Akil ya ce "Yaya Imran menene ya same su kuma?" Ya yi maganar da ɗan ɗaga murya. Ba tare da ɓata lokaci ba Imran ya labarta mashi duk abin dake faruwa, sosai Akil ya tausayawa Rimsha kuma ya yi alkawarin kula da ita sosai har Imran ɗin ya dawo, da haka suka yi sallama Imran ya dawo cikin ɗakin ya kara yi wa Rimsha sannu, sannan ya musu sallama ya fita izuwa office ɗin Nawid.
Zaune ya isko Nawid yana haɗa wasu takardun, saman kujerar da ya zauna ɗazun a nan ya zauna tare da miƙa mashi hannu suka gaisa sannan ya tambayi wani irin magani za'a sayawa Rimsha, ba tare da ɓata lokaci ba Nawid ya rubuta mashi magungunan da zai saya, har ya karɓi takardan sai kuma ya sake miƙawa Nawid ɗin ya miƙe yana faɗin "Na mance akwai in da zanje, Akil zai zo ɗaukar su anjima ka bashi takardan zai sawo mata maganin" To Nawid ya amsa da shi sannan suka sake yin musabaha Imran ya wuce.
Sai sauri yake zubawa saboda ya kusa cin time da Lion ya bashi.
Kai tsaye gida ya wuce, ya na shiga bedroom nasa ya fara haɗa kayan da zai buƙata, sai zuba sauri yake yi, ya ja trolley zuwa cikin motarsa, bayan ya kai ya dawo ya ɗauki na Lion ɗin ma, sannan ya wuce cikin gida ya sanar da Ammie zai ɗan yi tafiya na kwana biyu, zai je Abuja, shine abin da ya gaya mata, dan in ba ce mata ya yi baya nan ya yi tafiya ba, ba zata taɓa yarda baya kwana a gida ba, amma da yake tasan a baya yana zuwa Abuja, wata sain gidan su Rimsha, wata sain kuma Abba na wakilta shi zuwa taro ko wani abin.
To ta amsa mashi da shi sannan ta yi mashi fatan Alkhari. Sauri-sauri ya amsa da amin tare da fitowa ya shiga motarsa.
Sai bayan ya kama hanyar tafiya ne ya kira Abba a waya ya gaya mashi ga in da zai je, bai yi wa Abba karya ba, gaskiya ya gaya mashi, domin baya taɓa yarda karya ta haɗa su, kuma Abba yana da fahimtar sosai, ba kamar ita Ammie ba. Fatan alheri Abba ya yi mashi suka yi sallama.
Yana katse kiran sai ga kiran Lion ya shigo, jikinsa har kerma yake yi wajen ɗaukar kiran tare da kara wayar a kunnansa. "Prof ka je Airport akwai sojojin da zaka taho mani da su" shine abin da Lion ya faɗa, kuma bai jira amsar Imran ɗin ba ya katse kiran.
Juya kan motar Imran ya yi zuwa airport. Sojoji guda biyu ne masu yi masu girki, sai kuma uban kaya da suka zo da shi, carton carton, mamaki Imran ya yi wannan uban cartons ɗin kuma menene a cikinsu, yana tsaka da tunani sai jin fasasshen Muryan sojan yana faɗin suje, gaba ɗaya sojojin basa a cikin kaki, suna sanye ne da kananan kaya, Jeans da T-shirt, sai rigar sanyi da suka ɗaura a kai, sannan sun sanya face mask a fuskarsu, Turawane farare kal da su, gasu da kirar karfi kuma ya haɗu da sun ji training sosai.
Gidan baya na motar suka shiga, kayan da suka zo da shi kuma, waya Imran ya yi aka nemo mashi mota mai baya ta kwashi kayan, ya shiga gidan gaba ya tada motar suka nufi hanyar gidan Lion.
Duk cikin sojojin ba wanda ya ce da Imran ko sannu, shima bai yi masu magana ba, saboda ba abin da ya haɗa shi da su. A haka kamar gumaka har suka isa gidan, babu mai gadi dan haka sai Imran ya ce da soja ɗaya ya fita ya buɗe masu gate, ba musu ya fita dan suna girmama Imran sosai, saboda sun san tun da Lion ya turo shi, kuma bai ɓoye mashi a kan tafiyar sirri suka yi ba, suka san cewa yasan komai kuma yana da mahimmanci sosai a wajen Lion ɗin, so idan ya basu umarni dole su bi.
Bayan ya buɗe masu gate ɗin ne suka kutsa cikin gidan. Yana kashe motar a parking space, sojan dake a cikin ya fito suka tsaya sai da da motar da ta ɗauko masu kayar ta kariso cikin gidan, sannan suka fara sauƙe kayan, shi kuma Imran yana fitowa, fitar da trolleys nasu ya yi dukka biyu ya ja izuwa cikin gida.
Kai tsaye ɗakin Lion ya nufa, yana kwance saman lallausan bed nasa, ya lafe luf, gaba ɗaya jikinsa na lulluɓe da lallausan bargon mai laushi sosai da sosai kamar audiga fari kal, iya kansa ne kawai a buɗe, shima kan nasa, gaba ɗaya dark black curly hair san nan ya rufe mashi fuska, baka iya ganin komai nasa, sai kyalli gashin nasa yake yi, cikin kwanciyar hankali yake barcin sa, da ga gani yana cikin yanayi mai daɗi, a hankali yake sauƙe numfashi. Uhmm abin sai wanda ya gani, Lion ba'a magana
Kai tsaye wannan kyakkyawan dressing room ɗin Imran ya wuce, a hankali yake jan trolleys ɗin dan kar ya takurawa Lion.
Guda ɗaya a ajiye a cikin dressing room ɗin, wato na Lion, na shi kuma ya ja ta zuwa ɗayar ɗakin dake a kusa da wannan, a nan ya ajiye, kusan komai na cikin ɗakin irin na ɗakin da Lion ke a cikine, colors ne kawai suka banbanta, shi na Lion komai fari ne, wadda Imran ya shiga kuma komai brown ne.
Bayan ya kai ya ajiye ne ya dawo bedroom ɗin Lion, saman bedside drawer ya zauna ya zubawa Lion ɗin ido, wani irin mugun kyau Lion ya ke yi mashi, yana bala'in Kaunarsa sosai, haka kawai wani tunani ya faɗo mashi a ransa, da ace Lion zai so Rimsha ya aureta da ta ji daɗi, ta huta da kuncin da take ci, ko ba komai zata samu sassauci abin da take ji a zuciyarta na rashin yan uwanta. Lokacin guda kuma ya tuntsure da dariya kamar ba lafiya, cikin sauri kuma ya toshe bakin nasa da hannayensa dan kada ya tashi Lion, miƙewa ya yi ya koma balcony ya tsaya, kasa-kasa ya ce "Amma dai tunani ma akwai hauka, yanzu kawai sai tunani ya bani cewa Lion ya auri Rimsha tab, hmmm ga ƴaƴan manya-manyan shuwagabannin manyan kasashe ta duniya, wayen da suka amsa sunayen su mata masu class, kuɗi, mulki, ilimi, kyau, yayan turawa irinsa suna haukar son shi, suna mutuwa a kanshi, amma ko ɗaga ido ya kallesu bai taɓa yi ba, sai wata Rimsha, amma gaskiya tunani baki yi mani adalci ba, anyama shi Lion yasan me so kuwa? To ni dai ban taɓa gani ba ko kusa ko alama wai ya furta wata kalma makamanciyar hakan ko tsakaninsa da James ne".
Sai magana yake yi, jin motsi mutun ne yasa ya dakata, cike da tsoron kar dai Lion ne, haka ya juyo a hankali, wani irin dukan uku uku kirjinsa ta yi ganin Lion. Tsaye yake a bakin kofar balcony ɗin, kamar dai ɗazun daga shi sai wannan farar Short ɗin, dan ya ce Nigeria akwai bala'in zafi, lokacin kuma ya taso daga barcin da yake yi, ganin Imran a wajen yasa ya fito wajen dan su zauna su sha iska tare, ko kaɗan bai ji abin da Imran ɗin ya ce ba domin lokacin ya kariso wajen, kuma kasa-kasa Imran ɗin yake magana.
Yan kame-kame Imran ya fara yi, wani irin razana ya yi da ganin kwayar idanun Lion, dan dama haka suke idan ya tashi barci sai ka gansu suna kyalli, bare ma idan ya ɗan zaro su, dama gasu nan dara-dara da su, abin ba'a magana, sai ka gansu suna wani irin haske suna rikita mai kallonsu, ko su James suka yi ido huɗu da shi ya tashi barci kuma ya zaro idon, suna tsorata bare kuma Imran da bai saba ba, bawan Allah yau ya ga ta kanshi.
Wucewa ya yi ya zauna saman ɗaya daga cikin kujerun dake a wajen, shima Imran da ya ga bai kula shi ba sai ya wuce ya zauna gefensa. Kwata-kwata Imran bai san da zancen Lion ya tsani mum ɗin su ba, domin idan baku mance ba Lion ba kowa ya san abin da yake ciki ba, ko ya yake da mutun ba komai yake gaya mashi ba, Tga da yake uncle nasa ma, ba komai yake sanar da shi ba, hakan yasa Imran bai san da wannan zance ba, saboda bai taɓa zuwa gidan su ba, iya haɗuwa a School kawai suke yi, kuma duk cikinsu ba wanda ya taɓa gaya mashi, in ma James or Michael, yana dai mamakin da basu kula mutune, dan ba iya matane kawai basa kulawa ba gaba ɗaya ne, rashin sanin kuma yasa Imran ya aika Rimsha ta kai mashi abinci, da yasan da haka ba zai aikata ba.
A ɓangaren sojojin nan kuwa, bayan sun gama sauƙe kayan ne suka kwashe su zuwa cikin Palo, a nan suka tsaye suka duba Kitchen, bayan sun gani suka zuba kayan a ciki, sannan suka ɓubbuɗe cartons ɗin, abubuwa ne na cimarsu irin kayan girkinsu da ruwan sha da dai sauransu, shirya komai suka yi a muhallinsa, sannan soja ɗaya ya koma bakin gate dan yin gadi, shi kuma soja ɗayan ya fara ƙoƙarin yin girki, ya kunna fridge dake a cikin Kitchen ɗin, dan ruwan da suka zuba a ciki ya yi sanyi.
Wannan kenan a ɓangaren su Lion bari Mu leƙa ɓangaren Aafia muga a wani hali take a ciki.
💔😭BANDITS😭💔
Kwanan zaune Aafia ta yi, ta kasa iya yin barci saboda bata saba kwana a kan siminti ba, ta kasa iya barci saboda bala'in yunwa dake addabama cikinta, sai matsar kwalla take yi, kamar yadda taga rana haka ta ga dare, ita kuwa Rufee doguwar suma ta faɗa saboda azaba kuma ga jinin da ta rasa.
Haka har wayenwan gari, sosai Hanan ta rinƙa yiwa mamanta kuka. Abin da ya kawo Hanan da mamanta wannan waje kuma shine, sun baro katsina ne suna hanyar Kaduna za su je duba kakanta, ta gefen maman kenan, tana asibiti ba lafiya, to za su je dubata kenan yan Kidnaping ɗin suka kamasu a kan hanyarsu ta zuwa Kd, duk da talaucin da suke a cikin, sun gwammaci gidan su akan hannun yan bandits ɗin nan, sun ci bakar wahala a ɗan kwana ɗaya da suka yi.
Sai misalin karfe 8 yan bandits suka zo suka fitar da su, a wannan karon da gudu Aafia ta yi gaba, dan jiya tasha bulala.
Wajen dai da suka zauna jiya, a nan suka zauna