Showing 75001 words to 78000 words out of 355604 words
zauna, wannan ita ce Halimar sai ku gaisa, ki yi sauri mu wuce ɗaki dan na ga ji ina son in yi wanka"
Wani shu'umin murmushi Rufee ta yi wadda ya sanya Aunty tantama a kan ta.
Kusa da Aafia tazo ta zauna tana faɗin "Ke Aafia ba ki da kunya yanzu matar Abbin ne kike kiran sunan ta kai tsaye haka? Gaskiya baki kyauta ba"
Mamaki ya hana Aafia magana, tunani ta fara yi "ko dai basaja Rufee ke yi wa Aunty ne, amma in ba haka ba ai ita ce ta ce mu rinƙa kiran Aunty da sunan ta Halima, shine kuma yau dan a gaban Aunty ne zata wani ce min bani da kunya, lallai Rufee anyi yar duniya"
Aafia tana can duniyar tunanin makirci irin na Rufee, ita kuma Rufee ta zamo kasa daga saman kujera, ta zube gwiwowinta a kasa ta ce
"Mummy ina wuni? Ya jiki?"
Tashin hankali zaro ido waje Aafia ta yi, tamkar idanun nata za su faɗi kasa, ta fara tsorata da lamarin Rufee, har da zubewa kasa tana gaishe da Aunty anya kuwa.
Aunty kuwa tun da ta karanta addu'ar nan sai ta ji karfin gwiwa, kuma ta ji bata shakkan komai, dan haka sai ta ce da Rufee
"Lafiya lou Alhadulillah, jiki kuma da sauƙi"
Shiru Rufee ta yi ta kasa magana kuma ta kasa mikewa ta koma saman sofar, kamar wadda ta yi sumar zaune, da alama dai Akwai wani abin da ta shirya wa Aunty ne, Allah kuma bai nufa zai kama ta ba, shine ya sanya jikinta ya mutu.
Ta ɗan jima a wajen ta kasa tashi, har sai da Aafia ta taɓa tare da kiran sunan ta, sannan ne ta ɗan firgita ta miƙe ta koma saman sofa ta zauna.
"Rufee ba zama za ki yi ba, mu wuce ɗaki kawai, dan na je na yi wanka"
Aafia bata gama Rufee baki ba, suka ji shigowar motar Abbi cikin gidan.
Da murna Aafia ta miƙe tana faɗin "Ga Abbi nan ya dawo ki tsaya ku gaisa sai mu wuce"
Wani kululun bakin ciki ne ya tokarewa Aunty maƙoshi, har ga Allah bata son Abbi ya kalli Rufee, tana ki shin mijinta sosai, to amma ba yadda ta iya, bata isa ta yi wa Aafia wata magana ba, ga shi kuma ba lafiya ke gareta ba, yanzu idan ta yi wata magana suna iya samun matsala da Aafia, hakan ya sa ta ɗaure, ta danne, ta cije, har wa su siraran hawaye ya fara bin gefe da gefen idonta, kasan cewar tana kwance ne hakan yasa hawayen ke gangarawa ta kunnanta.
Ita kuwa Rufee lokacin da ta ji abin da Aafia ta ce, sai ta ji wani mugun sanyi ya dira mata a zuciyar ta, har da wani sauƙe nauyayyar ajiyar zuciya, sai wani kara fari da ido ta ke yi.
Suna wannan hali Abbi ta shigo bakin sa ɗauke da sallama, duk da cewa ya rame saboda damuwa, hakan bai hana shi yin kyau ba, ya sha dakakkiyar shaddasa sky blue, ɗin kin ya masa kyau sosai.
Tun da Rufee ta ɗaura idon ta a kan shi take ta haɗiyar yawu, kamar wata mayya, cikin sauri ta zura hannun ta a cikin jakarta, cikin dabara ta lakuto wani abu kamar mai, ta shammaci su Aafia ta shafa a idanuwanta.
Abbi na karisowa cikin falon Rufee ta yi saurin karisawa in da yake, ta sanya hannu ta karɓi jakar computer dake hannunsa, tana faɗin "Sannu da dawowa Abbi"
Galala Aafia ta wangale baki tana kallon ikon Allah, Aunty kuwa, tsabar shiga tashin hankali bata san lokacin da ta miƙa zaune ba.
Shi kuwa Abbi yana kokarin janye jakar computer sa kada Rufee ta karɓa, a nan ne aka yi rashin sa'a idanunsa suka sauƙa a cikin tata.
Wani irin zirr ya ji a jikinsa kamar wadda aka yi wa allura, lokaci guda ya ji wani irin yanayi, ji yake duk duniya ita kaɗai yake so.
Ya kasa ɗauke idonsa daga kallonta, har ta karɓi jakar nasa tana faɗin "Abbi ina ne ɗakin ka na kai maka jakar" tana magana tana kara fari da ido.
Da hannu ya nuna mata sama, ya kasa magana, kallonta kawai yake, yana jin tamkar ya riƙota, zuciyarsa na azalzalansa da so da kuma kaunar ta, lokaci guda Abbi ya zama kamar wawa kawai binta da ido ya ke yi.
Aunty da Aafia yau sun ga duniyanci, sun ga abin da ya fi karfinsu, dukkansu an rasa mai bakin magana, sun yi mutuwar tsaye, ba abin da Aafia ke kallon fa ce yadda Rufee ke ta faman yi wa Abbi rakwarkwasa, da karairaya, Abbi ya sake baki kamar wawa yana bin ta da ido, har wani fari take masa da ido, abin ma gwanin ban haushi, ba kyan gani.
Ita kuma Aunty yadda Abbi ke bin Rufee da ido kawai take gani, ji take tamkar ta haɗiyi zuciya ta mutu dan haushi, Allah sarki.
Wucewa ta yi tana wani yauƙi ta nufi sama, hannunta riƙe da jakar, shima Abbi wucewa ya yi, ya bi bayanta, ko kallon in da Aunty da Aafia suke bai yi ba.
Tsabar bakin ciki Aunty bata san lokacin da ta ce "Ke dan uban ki zoki wuce ki bar gidan nan"
Tamkar ba da ita ake ba ta wuce abinta ta haye sama, shima Abbi bai kula Aunty ba, Aafia kam babu bakin magana.
Sai bayan Abbi da Rufee sun haye sama ne Aunty ta dawo da kallonta kan Aafia.
"Kin cuceni Aafia, kin cuci rayuwata, ki rasa wa zaki kawo mini gidan nan sai wancan tsinanniya, mai kama da yan kwalta ɗin, Allah ya isa tsakanina da ke Aafia, Allah ya isa mini" tana magana tana hawaye, ga shi ba damar ta tashi.
A wulakance Aafia ta ce "Ke Halima wlh ki iya bakin ki, idan ba haka ba, sai na tattaka ki a nan wajen banza kawai" Aunty za ta yi magana mamanta ta shigo falon bakin ta ɗauke da sallama.
Wucewa Aafia ta yi ta haura sama ta barsu a nan. Tana kokarin shiga bedroom nata Rufee ta fito daga bedroom na Abbi, sai wani washe baki take yi. Aafia na son yi mata magana amma ta kasa, har ga Allah abin da Rufee ta yi sam bai yi wa Aafia daɗi ba, ta ji haushin hakan, sai dai ba zata iya ce mata komai ba, already Rufee ta riga ta kai sunan su wajen Malam, ba wanda zai iya mata gardama ko ya ja da maganar ta acikinsu.
"Ke Aafia me ki ke wani kallona haka, kamar na ce ina son Abbin ki? Ni fa kawai jakarsa na agaza mi shi da shi, na kai mi shi ɗakinsa, ko na yi laifi yin hakan? Kuma ai nafa ita Halima bata iya kula da miji bane, shiyasa nake nuna mata example".
Girgiza kai Aafia ta yi, kamar wata wawiya, a sanyaye ta ce "A'a baki yi laifi ba, mu je ɗakina bari na yi wanka" girgiza kai ita ma Rufee ta yi kafin ta ce "A'a zan wuce sai mun haɗu kawai"
(Shegiya kin gama aikin da ya kawo ta, dole kice zaki wuce ai)
Tana kai karshen maganar bata jira amsar Aafia ba ta wuce ta nufi kasa, rai a ɓace Aafia ta wuce cikin bedroom nata.
A ɓangaren Aunty kuwa, Aafia na wucewa, mamanta ta ce "Sadiya me ya haɗa ki da yar taki? Na ji kamar kuna magana mara daɗi wa junan ku" Goge hawayen fuskar ta Aunty ta yi, dan kada mamanta ta gani, saboda kullun tana mata nasiha a kan hakuri da fawwalawa Allah komai.
"Babu komai Inna kawai naga ta dawo ranta a ɓace ne shine nake tambayar ta".
Wucewa Inna tayi ta nufi wani ɗaki dake kusa da Kitchen tana faɗin "To dai ki rinƙa yi mata a hankali dan kin san yarinya ce, ku zauna lafiya da juna". Kasa amsawa Aunty ta yi saboda azaban bakin ciki da ta ke cikin zuciyarta.
A wannan hali Rufee ta sauƙo ta sameta, a tsakiyar falon ta tsaya, ta fara bin Aunty da kallon banza daga sama har kasa.
A wulakance ta ce "ƴan kwanaki suka rage miki" tana kai karshen maganar ta wuce ta nufi hanyar fita daga falon.
Tana fita daidai lokacin daddy'n Jelly ya fito daga part ɗin Irfan, ya nufo cikin gida, zai zo ya yi wa Aunty ya jiki, dan ya ji Abbi ya dawo, kuma dama idan ba dole ba, baya shigowa part ɗin nasu sai Abbi na nan.
Mutuwar tsaye Rufee ta yi tana kallonsa, ga shi kuma yau shigar kananan kaya ya yi, yar ramar da ya yi ma kyau ta kara masa, daddy'n Jelly ba baya wajen kyau, da shi Jelly ke kama, ga golden eyes nasan nan ba'a magana gasu manya-manya kamar ball, ya fi Abbi kyau nesa ba kusa ba, kuma shi idan ka ganshi zaka ce matashi ne, domin kuwa bai da wani shekaru sosai, kuma yana da karamin jiki, auren wuri ya yi, shiyasa ya haifi Jelly.
Rufee ta kasa motsawa har ya zo ya wuce ta, da yake shima ba mai shiga harkar mutane ba ne, sai bai ce mata ko sannu ba ya shiga cikin falo. A sukwane ta juya ta bi shi da kallo har ya kurewa ganin ta.
Afili ta furta "No ya zama dole na kunce aikin da na yi wa Abbi ya dawo kan wanna saurayin, kai kaga kyau iya kyau, tab dole naje wajen malam gobe".
(Tofa ke Rufee ruwan ido ne zai kashe ki, ke kowa kina so anya kanki ɗaya kuwa?)
Ta ɗan jima tsaye a wajen tana tunanin ya zata ɓullowa lamarin, kafin ta sa kai ta fice daga gidan, ta fita bakin titin ta tari abin hawa zuwa gida, da waje bata zo da motar ta ba.
Shi kuwa daddy'n Jelly ko a jikinsa, ya je ya gaishe da Aunty ya fito ya koma part nasu.
Allah sarki Aunty ji take kamar zata mutu, Abbi ya dawo bai kula ta ba, ko sannu bai ce mata, kamar bai ganta ba, ga shi kuma ya kara mata wani bakin cikin na yarda da Rufee da ya yi ta karɓar masa jaka.
(To Aunty sai dai muce Allah ya fitar da ke, mu dai bari mo leƙo Jelly muga wani hali take ciki)
💖GIDAN ABBO💖
Zaune Nawid ya ke saman sofa a falo, ya yi shiru yana tunanin yadda zai ɓullo wa abin da ke faruwa, domin har cikin ransa yana zargin Abbonsa.
Ya yi nisa cikin tunani Jelly ta watso a guje tana ihu, a sukwane ya miƙe zai gudu dan ta tsorata shi, har wani kaɗawa hantar cikinsa ya yi, dan har ga Allah bai san zata zo ba, wani sufa ya yi ta saman sofa zai yi waje, kamar wani jikan chinawa haka ya yi, bawan Allah.
Ganin ya da ka tsufa ta saman sofa zai yi waje ne yasa Jelly ta ce "Kai yaya Nawid ashe kai ma ɗan China ne, ashe ka iya firewa".
Cak ya tsaya, a fusace ya juyo dan har ga Allah bai san ita ɗin ba ce.
"Ke ni kam anya ke mutun ce kuwa?" Ya tambaya yana kare mata kallo.
Sanye take da riga da wando, wandon jeans da riga mai dogon hannun, rigar tata kamar bargo haka jikinsa yake da laushi, saboda sanyin da ake yi, sannan rigar a iya kugunta ya tsaya, kayan sun zauna a jikin ta, gata kuma dama da shape sosai, ga shi an fara zama yan mata, komai na daɗa bayyana Masha Allah, kanta babu ɗan kwali, ta saki wannan bakin gashin fulanin nata, ya sha gyara wajen Ummi sai sheki yake yi.
Cikin sauri ya kawar da kansa daga kallonta domin har cikin zuciyarsa ya ji wani yanayi, ganin ta ba dressing mai kyau duk surar jikinta a bayyane ya sanya zuciyarsa wani mummunar tunani a kanta, cikin sauri ya kori sheɗan ya koma ya zauna tare da ɗaure fuska sosai ya ce
"Me ya fito da ke da gudu haka? Ina kuma Ummi?"
Turo ba ki ta yi, kafin a shagwaɓe ta ce "Ummi ba ta nan, ta shiga cikin gida"
"To baki bani amsa ba, me ya fito da ke daga cikin ɗaki da gudu haka, har ma da ihu".
Yar dariya ta yi kafin ta fara bashi labari "Ina zaune ina kallo ne sai naga wata yarinya tana gudu tana ihu wasu maza na binta, suka shiga cikin wani falo, a cikin wani gida, suna shiga falon sai yarinyar ta ɗauko wuka ta fara nuna musu tana faɗin...." Bata karisa maganar ba ta wuce saman table in da aka ajiye wata yar karamar wuƙa cikin kayan fruits.
Yana zaune yana kallonta, da gudu ta yi kansa da wukar tana faɗin "Idan ka matso kusa da ni sai na yanke ka" tana magana tana gyadawa da karfi.
Ganin da gaske wannan zata iya buga masa wukar nan, ta jimi shi ciwo ne ya sanya ya miƙe yana faɗin "Ke baki da hankali ko?"
Turo baki ta yi kafin ta nufi saman table ta mai da wukar tana faɗin "To ai zan nuna maka yadda matar ta yi ne, wai ma yaya Nawid kai komai na yi, ban maka ba, komai na yi sai ka zageni" "Dole na zage ki, yanzu na ce ki nuna mini yadda matar ta yi ne?" Ya yi maganar yana kokarin gyara zaman shi.
"Dama ai ba kai zan nunawa ba, gwada kaya na nake yi ko zan iya nima, kai ne nan ka tsayar da Ni kana tambayata me yasa na fito ina ihu, to abin da na fito gwadawa kenan".
Haushi ma ya hana shi yin magana, dan in ya ce zai biye mata tsab zai karya ta koma ya sumar da ita gaba ɗaya, yarinya kamar sheɗan ya mata fitsari a kai, cewarsa.
Ganin ya mata shiru ne yasa ta juya zata wuce cikin ɗaki, bata kai ga karisa juyawa ba idon ta ya sauƙa kan wani ɗan karamin kwaro dake tafiya a kan ƙafarsa, irin karon nan ne dake bin sanyi.
Da karfi Jelly ta ɗaga kafarta ta sauke masa a kan nasa, har wani kara ya bada, Nawid bai san lokacin da ya saki ihu ba, domin bai lura da lokacin da ta ɗaga kafar tata ba, hankalinsa na kan wayarsa dan ya ce baya son sake ganin ta a irin dressing da taken nan, shiyasa ya ɗauke kansa daga kallonta.
Jin ya yi ihu yasa ta ce "Yaya Nawid kai fa Allah kamar mace kake, kai rago ne, yanzu kashe kwaron ka ke yi wa kuka? Allah sai na maka irin ta Ram Charan yake ko waye, wannan dai na cikin Tv nan, sai kana barci na ɗebo ruwa yana tafasa a wuta na zuba maka, yadda Ram ya yi wa abokinsa a Tv bayan sun ɓata".
A fusace Nawid ya miƙe zai wanka mata mari Abbo da ya shigo tun ɗazun kyan Jelly da dressing tata sun ja hankalin sa ya kasa magana, kuma ya kasa karisowa cikin falon, ya tsaya kawai ya zubawa Jelly ido, sai da ya ga Nawid zai mare ta sannan ya ce
"Kada ka kuskura ka taɓa ta, baka ganin yarinya ce kuma bata da lafiya".
Sosai Nawid ya kara yin mamaki "wai ba jiya Abbo ya ce yarinyar nan tsintaciyar mage bace, baya son ta baya kaunar ta, me kuma yasa ya dawo bayan fage yana kareta" Nawid ne ya tambayi kansa a cikin zuciyarsa.
Wucewa Jelly ta yi tana turo baki tana kunkuni ciki-ciki, ta shige ɗaki abinta, shima Abbo zuwa ya yi ya wuce zuwa na shi ɗakin.
Nawid kam ya kasa magana tunani kawai yake a kan Abbo, sannan ga in da Jelly ta dakesa ya masa zafi sosai, dan da iya karfinta ta take masa kafar nasa.
Yana zaune a wajen Har Abbo ya sake fitowa, dama Abu yazo ɗauka. Ko sannu bai ce da Nawid ba, ya sa kai ya fice abinsa.
Yana fita ba jimawa Ummi na shigowa bakinta ɗauke da sallama, ka sa amsa mata sallamar Nawid ya yi.
Bata wani damu ba tazo ta zauna kusa da shi tana faɗin "Baka fita zuwa asibiti bane Nawid?"
Da kyar Nawid ya iya ce mata "E Ummi ban fita ba".
"Lafiya Nawid na ganka cikin wani yana yi?" Ta tambaya tana kare masa kallo.
Nauyayyar ajiyar zuciya ya sauƙe kafin ya ce "Ummi dan Allah ki fahince ni ba wai zan miki gyarane dan kin gaza ko wani abu makamancin hakan ba, na san ke mace ce mai hankali, ilimi, addini, da kuma hakuri, to amma a wannan fannin kin kaza, bana ganin laifin ki saboda baki taɓa haihuwar ƴa mace ba, sannan kuma kema ke kaɗai ce mace a wajen kaka, baki taso kinga yadda ake kula da ƴaƴa mata ba, wannan dalili yasa ni bana ganin laifin ki".
Zuba masa ido Ummi ta yi tana kallon cikin kwayar idanuwansa masu ɗauke da damuwa turun.
Ci gaba da magana ya yi "Ummi dan Allah ina so idan zaki fita anguwa, koma ina ne ki fita tare da baby, kada ki barta ita kaɗai a cikin gidan nan, yin hakan babban haɗari ne, wlh ko jiya a asibiti sai da na yi wa yarinya yar shekara 3 ɗinki saboda fyaɗen da wani azzalumi ya mata, kuma kinga gidan ba mu kaɗai bane ga su Sadiq suna nan, ba wai ina zarginsu ko wani abu bane, a'a kawai dai kula ce, ka kula da kayan ka, ya fi kazo kana cikiya, kuskure kaɗan za ka yi a tarbiyar ƴa mace ya zama mata babban illa, kuma zai iya zama sanadiyyar tarwatsewar rayuwar ta gaba ɗaya, sannan Ummi dan Allah wasu dressing ɗin baby ta dai na yin su, kinga yanzu ta fara zama cikakkiyar mace, koda a gida ne ta daina saka su, saboda bamu san wani irin bako za mu yi ba, kuma idan kika duba mai son abinka ya fika dubara".
Sosai Ummi ta ji nasihar Nawid har cikin ranta, dama bata taɓa kawo hakan a ranta ba, kuma dama haka ne wani abin sai an nusassheka ka ke iya gane hakan, ta yi kukan zuci a kan abin da ya faru da yarinyar da Nawid ya yi wa ɗinki jiya, ta kuma kudiri niyyar kula da Jelly sosai fiye da a baya, ta wani ɓangaren kuma ta ji daɗi sosai, domin a tunanin ta Nawid ya fara son Jelly shi