Showing 132001 words to 135000 words out of 355604 words
dawo, ina dawowa na samu wannan aiki wadda ya zama mini dole na yi shi, shine na fara yi" ta kai karshen maganar tana kokarin sakin kuka mai sauti.
Cikin sauri Imran ya miƙe ya riƙo hannunta suka fice daga wajen ɗin zuwa wajen motarsa. Gidan gaba ya buɗe mata ta shiga ta zauna, shi ma ya shiga ɗayar gefen ya zauna yana kallon ta, shi kuma Nawid ya nufi wajen Ibraheem domin tambayar ina Jehan.
"Rimsha ki natsu ki gaya mini menene yake faruwa kin ji? Ni yayan kine, kin sani, ina zuwa har cikin gidan ku, dan haka ki gaya mini ina His Excellency ina su Madam?".
Kasa ta yi da kanta tana hawaye haka ta fara ba shi labari tun daga ranar da aka ɗauki daddynsu har zuwa yau, duk dauriya irin nasa sai da ya matse mata kwalla, ko ɓatar Jelly bai yi kuka ba amma jarabawar da Rimsha ta haɗu da shi ya taɓa mashi zuciya, ya sanya shi hawaye.
Jugum-jugum suka, zauna ba wanda ya iya ce da ɗan uwansa kala, har sai da Nawid ya zo wajen sannan suka dawo cikin hayyacin su, a ruɗe Nawid ya ce "Rimsha Ibraheem ya ce mini ke kanwar Jehan ce, dan Allah a ina take? A ina zan sameta?".
Ɗagowa ta yi ta kalli Imran a yayin da shima ita yake kallo, girgiza mata kai ya yi alamar ta ce bata sani ba, haka kuwa ta yi masa, kuka ne kawai Nawid bai yi ba, sannan ya kuduri niyyar nemanta koma a ina take.
"Dr ka shiga mota mu wuce gida, kada mu ɓata lokaci". Jin abin da Imran ɗin ya ce na Nawid ya shiga mota su tafi, sai ta juya tana kokarin buɗe kofar motar zata fita,
Cikin sauri Imran ya riƙo hannunta yana faɗin "Ina kuma zaki je?" Cikin halin nuna ko in kula ta ce "Wajen aiki na zan koma" girgiza kai ya yi yana faɗin ",Haba muna raye a duniyar nan family Nawazudden su yi rayuwar kunci, kai ina a baya ma da kikaga hakan ta faru bamu san in da za mu same ku bane, yanzu kuma gaki na ganki kuma kice zaki tafi, a'a haba ai ke daga nan sai Kaduna, idan duk wani abin da zan mallaka zai kare a kan family Nawazudden to ba zan taɓa danasani ba, daddynku ya taimakemu a rayuwa, ba zan iya kwatanta miki irin taimakon da ya yi mana ba, yau duk wani kuɗin da Abbana yake tin kaho da shi to Allah ne ya bashi kuma sanadin daddyn ku, dan haka yau rana ta yi da zan ramawa His Excellency abubuwan da ya yi mini, nasan ban isa na biya shi dukka ba, amma In Sha Allah zan yi kokari wajen ganin na baki kulawa, kuma na san cewa His Excellency ya fi son ki sama da komai nasa, yanzu dai abubuwa masu mahimmanci guda uku zan fara yi, na farko zan tafi da ke gidan mu, na biyu zan fara neman family ki ina suke, na uku kuma ki zaɓi duk makarantar da kike so a duk kasar da kike so, sai in kai ki karatu can".
Kasa ta yi da kanta tana jin wasu zafafan hawaye na kokarin bin kuncinta, amma haka ta daure ta mai da hawayen nan ta ɗago kanta sama ta fara magana kamar haka "Daddyna ina alfahari da kai, ina mai farincikin kasan cewar ka mutumin kirki, yau ga shi an wayi gari baka duniyar, amma saboda kirkin ka duk in da muka shiga sai an taimakemu, ba wanda za mu zauna da shi kuma mu yi kuka babu, kowa son mu yake yi, saboda kai daddy, saboda kirkin ka da alkharin ka ga mutane, gaskiya zama mutumin kirkima wani babban baiwa ce a duniya da lahira, ko kai baiwar bata taimake ka ba zata taimaki family ka, saboda gaskiyar ka aka kashe ka, aka raba mu da kai, amma ga shi muna cin albarkaci gaskiya da kuma amanar ka, har na koma ga Allah ba zan dai'na yi maka addu'a ba daddy na" ta kai karshen maganar tare da sakin kuka mai tsuma zuciyar mai sauraro, matsowa kusa da ita ya yi, ya ɗan riƙo kafaɗun ta yana ɗan jijjigata alamar rarrashi, a nitse ya ce "Ki yi shiru Rimsha ki dai'na kuka kin ji ko? Yanzu dai ki gaya mini kasar da kike son zuwa karatun sai na fara shirye-shiryen tafiyarki" kuka ya ci karfinta ta kasa magana.
Ganin haka yasa Nawid ya ce "prof ka barta ta huta tukunnan, ka kyaleta zuwa gobe ko anjima sai ayi zancen school". Dawo da kallonsa kan Nawid ɗin ya yi yana faɗin "Dr ba zaka gane bane amma ba danu wa yanzu dai ka shiga muje gida, idan munje sai mu karisa magana a can". To Nawid ya amsa da shi sannan ya shiga gidan baya, ya bar Rimsha a gidan gaban.
Har Imran ya tada mota cikin sauri ta ce "Ba zai yi wu in biku ba, saboda kaga aiki nake yi, sai na gama biyawa Jehan kuɗin da ta karɓa tukunnan". Abin ma dariya ya bawa Imran, cikin zola lace "Ashe first lady ta girma". Sanya kyawawan hannayenta ta yi ta rufe fuskarta tana turo ɗan baki, zuba mata ido Imran ya yi na ɗan lokacin kafin ya ce "Ke dai ba in da kika baro Madam a kamanni," ya kai karshen maganar yana mai do da kallonsa kan Nawid dake gidan baya yana fama da latsa waya.
"Dr fita dan Allah ka karɓi account number Ibraheem ɗin nan ka sanya masa 1m mu samu mu tafi da wuri, kasan First lady mu daman akwai ta da gaskiya da amana kamar His Excellency, idan ba ku biya wannan kuɗin ba ba zata taɓa barinmu mu bar nan ba".
Ita dai shiru ta yi tana binsu da kallo ta kasan ido. Tuna cewa 1 million Imran ya ce a bawa Ibraheem sai ta ce "Kuɗin shi 500k ne ba 1m ba" fuska ɗauke da murmushi ya ce "E na sani amma shima dole yaci albarkacin ya taimaki family Nawazudden, ni abin da ma ya fi bani mamaki ya akayi basu iya gane Jehan ba? Ya akayi ta yi aiki a nan kuma manyan mutane suna zuwa nima ina zuwa kuma bamu taɓa haɗuwa ba?". Nawid ne ya cafki zancen da cewa "Ai yanzu da na san asalin wace ce Jehan sai na gane a baya da fake face take amfani, nima na yi mamaki da kuka ce Jehan Nawazudden ce ta yi aiki a nan, wlh ba dan daga wajen yar uwarta na ji zancen ba, da ba zan taɓa yarda ba, domin ni ba asalin fuskar ta na gani ba, da asalin fuskarta ce ai da tuni na gane ta na ɗauketa in je in haɗa ta da baby uwar dirama, amma kasan abin da ya ke bani mamaki kuwa?"
Girgiza masa kai Imran ya yi alamar a'a bai sani ba "Jehan Nawazudden tun tana primary 6 lokacin da ta fara media lokacin na kamu da son ta, kasan ita ko ka mata dm bata reply, naso yarinyar nan kamar hauka, amma bani da hanyar da zan iya ganinta, hakan yasa na danne na hakura ina dakon so, sai ga shi yau an wayi gari na haɗu da ita a wani irin yanayi da ba zamu ina gane juna ba, kai wannan abu ya mini ciwo sosai, ba zan taɓa mantawa da shi ba".
Yar dariya Imran ya yi yana faɗin "Baka sanar da ni bane ai ni dana kai ka har cikin gidan su, His Excellency yana da kirki sosai, yana kuma kaunata fiye da tunaninka, ni bana zama a palon baki ma idan naje, kai tsaye palon gidan nake shigewa kamar ɗan gida, lokacin da na koma school ne abubuwa suka ja baya, amma duk yaran sa ba wanda bai san ni ba, kuma kamar yadda kaga Jehan a Media bata yi wa mutane magana, to haka take ko a gida ma, bata yi wa mutane magana sam, idan naje ga mai yi mini magana nan first lady, daga ita sai Aunty Aisha da Madam, ita kuma wannan mage sarkin son jiki ce, kulkun tana jikin daddynta, ko ba haka akayi ba?" Ya kai karshen maganar yana dariya yana leƙo fuskarta.
Murmushi ta yi har sai da dimple nata ya lotsa, tabbas ta gane Imran amma sai dai lokacin da yake zuwa gidansu tana karama bata kai haka ba.
Fita daga motar Nawid ya yi zuwa cikin restaurant ɗin, kamar yadda Imran ya ce haka ya yi, ya karɓe Account number Ibraheem ya sanya mashi kuɗin, sannan ya juya zai ta fi, cikin sauri Ibraheem ya miƙa mashi wayar Rimsha yana faɗin "ga phone ɗin ta" karɓa Nawid ya yi, sai zuba godiya Ibraheem yake yi, da haka suka yi sallama.
Lokacin da ya dawo mota ya same su, Rimsha ta ɗan saki jiki suna hira da Imran, domin tun abaya ta sanshi, kuma ko ba'a faɗa mata ba tasan mutumin kirki ne, domin daddynta baya alaka da mutanen banza, duk wanda ka gani tare da daddy to yana da kirki sosai, ba mutunne wanda za'a yar ba, ba zata taɓa manta lokacin da Jehan take cewa bata son ganin Imran ba, a lokacin ya zo gidan su, daddyn su ya ce In Sha Allah in dai yana da rai sai ya aura mata Imran tun da ta raina shi, ranar wuni kuka Jehan tayi wai an kaskantar da ita, ko da wasa daddy yake yi bai yi mata adalciba, ya haɗa ta da bawansu.
(Kai Jehan duniya, ka ji wai bawan su🤔)
Kallonta Imran ya yi yana faɗin "First lady zamu iya tafiya?". Cikin girmamawa ta ce "Yaya Imran tun da ka ganni a nan ai kasan dole akwai wayan da nake karkashin kulawar su ko? Amma shine zaka ce mutafi ban sallame su ba?" "Afuwan our first lady yi mana jagora zuwa gidan su mu zuba musu godiya".
Shiru ta ɗan yi tana tunani ko zata iya gane hanyar, dan kwana biyun da ta yi, Sadiq ne yake kawo ta kuma da yamma ya dawo ya ɗauke ta, sai dai ta gaya musu sunan anguwar kawai idan sun kai nan zata iya gane gida, haka yasa ta juya ta sanar da shi sunan anguwar, kallon Nawid ya yi alamar ko ya san anguwar, dan shi ba garinsu bane.
Gyaɗa masa kai Nawid ya yi alamar ya sani, ba ɓata lokaci ya tashi motar, Nawid na nuna musu hanya suka nufi gidan su Sadiq.
Kamar Kullun zaune suka isko Yusuf a kofar gida yana aikin nashi, wato sa wa mutanen da suka zo wucewa ido, ita kuma Hanan tana aikin tuyar awararta, Sadiq na gare ji bawan Allah.
Kusan a tare Rimsha da su Imran suka fito, sai kallon su Yusuf yake yi.
Tun daga ɗan ne sa Rimsha ta ce "Yaya Yusuf ya kake zaune a ranan nan?" Washe baki ya yi dan a tunaninsa Rimsha ba zata kula shi ba, dan ta zo da masu mota, Allah sarki bai san cewa ita Rimsha ba bakuwar arziki bace, a cikinta ta taso dumu-dumu.
Ba tare da ɓata lokaci ba ta yi musu sallama ta fito, mayafi maman Sadiq ta ɗauka ta rakota har wajen motar, gaisawa suka yi da Imran cikin mutunci da girmama juna, sannan ya zuba mata godiya sosai da sosai suka yi sallama, ya ciro 200k ya bata yana kara yi mata godiya. Da farko taki karɓa, amma daga baya daya matsa mata sai ta karɓa ta yi mashi godiya, ita kuma Rimsha ragowar 4k da ya rage a hannunta ta ɗauko ta bawa Yusuf dan shine abokinta.
Ɗan kwana biyun nan da tayi sun yi sabo sosai, dan Yusuf ma yana da hankali. Da haka suka yi sallama, Rimsha ta shiga mota kamar zata yi kuka, Imran ya buɗe gidan baya ya sanya mata trolley ta sannan ya shiga mazaunin driver ya ja motar suka kama hanyar Kaduna, Dr Nawid sai fama da latsar waya yake yi.
(Nima kuma na haɗa kayana na nufi wajen Jehan yar amana)
💖ABUJA💖
Kata faren gida ne mai girman, wadda da kaga gidin kasan arziki ya zauna wa mamallakan wannan gidan. Hawa ɗaya ne, zaka iya saka gidan a jerin gidan manyan masu kuɗi na faɗin Nigeria.
A kofar wannan gidan motar Hajiya da ta ɗauko Jehan ta tsaya tare da danna horn. Horn ɗaya mai gadi ya wangale mata gate ɗin gidan, cikin kwarewa ta danna hancin motar cikin gidan, kallon gidan nan Jehan take yi tana tunanin anya gidan nan ba wani abu kuwa, ace irin wannan haɗaɗen gida kuma azo ayi shi a keɓaɓen waje kamar haka? Dole a dasa mashi ayar tambaya, Jehan akwai kwakwalwa da kaifin basira abin ba'a magana.
Tana tsaka da tunani ta tsinkayo muryar Hajiyar tana faɗin "Jehan mu je ko?" Kallonta Jehan ta yi kafin ta fito daga cikin motar, zuciyarta sai ayyana mata abubuwa da dama dangane da wannan gida take yi, domin wannan gida bai yi kama da gidan masu gaskiya ba, ya fi kama da gidan marasa gaskiya, ita kanta Hajiyar bata yi kalar masu gaskiya ba.
Jehan bata karasa shi ruɗani da tantama a kan wannan gida ba har sai da suka shiga cikin palon gidan, a irin kallon da take yi wa wannan Hajiyar bata yi kala da mace mai aure ba, to waye ya bata wannan gida? Sannan me yasa za'a yi wannan gida a wajen keɓaɓe haka?.
Suna shiga wani ɗan karamin yaro da bai wuci shekara biyar ba, kamaninsa ɗaya da Hajiyar nan, ya taso da gudu ya yi wajen Hajiyar yana faɗin "oyo mummy". Rungume shi ta yi a jikinta, ita ma tana faɗin "Oyoyo ɗan lele na".
Mamakine ya sake kama Jehan, kenan Hajiyar nan ta yi tafiya daga nan Abuja har zuwa Katsina ta bar wannan yaron shi kaɗai a cikin gidan ne? Dan da alama ba wani motsi mutun a cikin gidan, wannan yaron shi kaɗai ne a ciki, sai mai gadi dake bakin gate.
A karo na biyu ta lula duniyar tunani sai tsinkayo muryar Hajiyar ta yi tana faɗin "Jehan ga waje ki zauna mana, ki saki jikin ki fa, zuwa dare zan kai ki wajen aikin kin ji?".
Ba musu ta zauna saman luntsumemen sofar dake wajen, har yanzu zuciyarta bai dai na mamakin dukiyar da aka narka wa gidan nan ba, ta dai zuba ido ta ga me zai faru.
Saman sofa ita ma Hajiyar ta zauna tana sauƙe numfashin a hankali hankali, shi kuma ɗan lele da gudu ya nufi cikin ɗaki ya ɗauko cake ya fito yana faɗin "Mummy i want to play with this cake".
"Go ahead mana my ɗan lele" ta faɗa tana ƙoƙarin fito da wayarya daga cikin jakarta.
Kusa da Jehan ɗan lele ya zo ya zauna, tare da fara ɗaban cake ɗin yana shafa mata a fuska, kamar ta ce mashi ya yi mata hakan.
"Ɗan lele me yasa kake ɓata mata fuska da jikinta haka? Ka bari mana, baka ga bakuwa bace?" turo baki ya yi yana faɗin "A'a mummy ni ina son ɓata mata ko ina a jikinta ne".
Murmushi Hajiya ta yi tana faɗin "To ɗan lele na, amma da ka barta ai".
Wani mugun kallo Jehan tabi Hajiya da shi, a ranta taka maimaita abin da Hajiyar ta faɗa, wato ɗan lele ya ci gaba da ɓata mata jiki, su ga su ƴaƴan masu kuɗi, komai suka yi daidai ne, basa laifi.
Tana tsaka da tunani, ɗan lele ya ɗebo cake yana kokarin cusa mata a cikin hancinta. Wani gigitatcen mari ta sakar mashi, wadda ya sanya shi tafiya ta baya baya, ya buga kai da jikin table, da karfi ya fasa ihu mai raza kwakwalwar mai sauraro, ita kuma Jehan miƙe wa tsaye ta yi, rai a matukar ɓace ta ce
"It seems like you have not been morally train in this house, and I will give you instantly, be get prepare"
(Toh fa ɗan lele ga maganin ka nan ta zo gidan, sai ka shirya.🤣)
A zafafe Hajiya ta miƙe cikin tsawa ta fara magana, da karfi-karfi "Akan me zaki mare shi Jehan? Dan ya saka miki cake a jiki? Baki ganin yaro ne shi?!!".
Ko kallon in da take Jehan ba ta yi ba, shi kuma ɗan lele sai kuka yake yi yana birgima a kasa, irin dai sangartattun yaran nan.
Komawa Jehan ta yi ta zauna saman sofa tana ɗaure fuska, domin a cewar ta bata da lokacin ɓata bakinta wajen bawa Hajiyar nan amsa.
Da kamar Hajiyar zata sake yin magana, amma kome ta tuna sai ta fasa ta ɗauki wayarta da jakarta tare da ɗan lele suka wuce sama bene.
Kallon banza Jehan ta bisu da shi kafin ta dawo da hankalinta kan binciken da tunanin a kan gidan.
Hajiya kuwa tana shiga cikin ɗauki ta rarrashi ɗan lele, bayan ya yi shiru ne sai ta ɗauki wayarta ta danna kira.
Jim kaɗan a kayi picking call ɗin, kamar tana gaban wadda take waya da shi, cikin girmamawa har tana wani yin kasa da kai ta fara magana "Allah ya taimake ki ranki ya daɗe, yau fa Allah ya yi zan cafki kuɗi yadda ya kamata" shiru ta ɗan yi da alama tana sauraron abin da ake faɗe a ɗayar ɓangaren ne, ma'ana tana sauraron abin da wadda ta kira ɗin take faɗe.
Bayan wasu yan sakannin da ba su 30 ba, sai ta cigaba da cewa "Wlh ranki ya daɗe yarinya ce bata san komai ba, kuma idan kin ganta ko ke sai kin ruɗe kyakkywa ce, amma fa nasan idan kika ganta zaki iya gane yar wace ce, yarinyar Nawazudden ce, kin san sun yi haɗarin mota ya rasu, to ashe familynsa suna Katsina dana je duba kanwar kawata ɗin nan da abin ya sha kan taaaaaa, to a nan naga Jehan". Shiru ta sake yi tana sauraron abin da ake faɗe a ɗayar ɓangaren bayan ta kai aya.
Bayan ɗan lokaci kamar minti ɗaya sai ta ce "E da farko da fake face take yawo, nima ban gane taba, sai da na ce zan ɗauketa shine iyayen nata suka gaya mini gaskiya, sai na ce to ta cire fake face ɗin dan yanzu mutane ai sun fara mantawa da ita, wasu ma sun mance