Showing 303001 words to 306000 words out of 355604 words
jinin a can ta yadda zan biya buƙata ta hankalina a kwance, amma kin zo kin fara jini a nan wadda ya zamar mani dole yau na aiwatar da kuɗirina a kanki idan ba haka ba ina cikin bala'i, ga shi gidan nan cike yake da jama'a ban kuma isa in tsallake yau ba tun da jinin ranar farko muke buƙata, gaskiya baki yi mani adalci ba amma ba komai zaki ɗanɗani kuɗarki wlh, sai kin zama dake da gawa duk ɗaya ne, banbancin kawai dai ke zaki kasance kina numfashi ne, ita kuma gawa bata numfashin bacin haka ba wani banbanci, wlh sai kin yi danasanin zuwarki duniya".
Sai sambatu yake yi shi kaɗai da alama ya fara zaucewa ya fara fita hanyyacinsa.
A ɓangaren Rimsha kuwa data ga ji da zama sai ta koma cikin gida ta fara dube dube a cikin kitchen ɗin ko Allah zai sanya ta sami wani abin da zata iya ci kada yunwa ya hallakata.
Ta yi rashin sa'a domin kuwa babu komai a cikin kitchen ɗin wadda ya yi daidai dana kasarmu idan ba nama da kwai ba sai dankali, bata daddara ba domin bata da wani zaɓi tana jin yunwa, haka ta sake ɗibar nama ta dafa tare da soyawa, a wannan karon ta yi sa'a Mark bai zubar mata da abincin ba domin iya nama ne kawai bai yi masu wari ba.
Bayan ta gama ta zuba a plate ta ɗauka ta wuce ɗakinta. Saman bedside drawer ta ajiye plate ɗin tare da fitowa dan ta ɗauki lemon ko ruwa da zata haɗa da shi.
Har zata sauƙa palon kasa sai kuma ta ɗan hango cikin ɗakin Lion domin kofar a buɗe, a hankali ta lallaɓa izuwa bakin kofar ɗakin, kamar wata ɓaraubiya haka ta leƙa cikin ɗakin, ganin ba kowa ne yasa ta shige ciki, dama kuma tasan basu nan kawai dai dan tabbatar da tsarone yasa ta fara leƙawa.
Tana shiga ta fata kalle kalle, ko'ina tsab kamar ba'a taɓa amfani da komai na ɗakin ba saboda gyara, sai tashin kamshi yake yi, tsalle ta buga tare da direwa a saman katafaren bed nasa tana dariya kamar zautaciya, da ɗan karfi ta furta "Yau ni ce GAR na gidan nan dole kowa ya bani respect" ta kai karshen maganar tare da kwashewa da dariya ta mirgina ta kara muginowa, yarinta ta ji gado mai daɗi har wani lumshe idanu take yi alamar barci take ji.
Ta jima kwance a gadon nasa tana surutai kafin ta miƙe ta gyara mashi gadon tsab kamar yadda ta samu sannan ta wuce dressing nasa, nan ma ta yi iya taɓe taɓen abin da take so kafin ta fito izuwa wajen mirror sa. Duk wasu drawers dake a ɗakin sai da ta buɗe su ta leƙa me a ciki, a wajen drawers na mirror ne ta ga wani pistol gun, tsabar rashin ji irin tata sai da ta ɗauki gun ɗin nan ta gani sannan ta maida, tana ƙoƙarin rufe drawer kuma idanunta suka sauƙa akan wannan ɗan akwatin na mum ɗin su wato Josephine, hannu tasa ta ɗauko akwatin ta fitar tare da fara ƙoƙarin buɗewa, sai dai ina ta kasa domin Lion ya sanyawa akwatin matakan tsaro sosai.
Ba dan ta so ba ta mayar da akwatin ta ajiye sannan ta cigaba da taɓa mashi abubuwansa, bata taɓa tunanin ko zai gane ba, ita dai duk abin da ya yi mata kyau sai ta taɓa shi.
Harta kayan sawarsa sai da ta taɓa, takalmarsa, watch's nasa komai dake a cikin ɗakin sai da ta bi ta taɓa sannan ta shiga toilet, nan fa taga duniya, dan toilet basa duniya ne guda, irin su shower gel da yake amfani da su ma kawai abin kallone, mayukan wanke gashin nan nasa duniya ne guda, yana kaunar gashin nan nasa sosai hakan yasa yake kashe mashi makudan kuɗaɗe dan gyaranta.
Duk wasu gel da suka burgeta da mayukan goge baki masu kamshi da tsada sai da ta taɓa, wani irin kwalbar turaren baki ta gani mai siffar sojoji ya ɗaga hannu irin jaruman sojijin nan, haka akayi design na kwalbar, ɗaga kwalbar ta yi tare da ɗaga hannunta kamar yadda aka kera kwalbar sannan ta ce "Kai nima fa soja ce jaruma mai jini a jika kuma kakkarfa" ta kwashe da dariya tare da mayar da kwalbar ta ajiye sannan ta fito waje
Bayan ta gama duk taɓa mashi abin da zata taɓa ne ta buɗe fridge nasa dake a cikin ɗakin kuma ta ɗauka mashi abin shansa guda ɗaya ta koma bedroom nata.
(Shin kuna ganin duk da ta gyara komai Lion ba zai gane an shigo ɗakin ba kuwa? MY MUM KIN KI JAWA ƳAR NAN TAKI KUNNE KO? TO GA SHI DAI YAU TANA GAƁA KUNA RUWA SAI KU KAWO ƊAUKI IDAN DA RABO KU RAGE DA RAI IDAN KUMA BABU ALLAH YA JIƘAN RAI😭. Amsa na gare ku ni dai na koma gidan Abbo.)
Misalin karfe 12 na dare abin mamaki gaba ɗaya ƴan bikin nan sun yi barci mai nauyi kamar waƴen da aka zubawa maganin barci, harta Nawid da Ummi sun yi barci mai nauyi, a takaice dai babu wata halitta mai rai a cikin gidan wadda bata yi barci mai nauyi ba sai Abbo, harta Jelly ta yi barci mai nauyin gaske.
Fitowa Abbo ya yi daga ɗakinsa jikinsa na sanye da wasu kaya kamar na matsafa launin ja kalar wuta, abin mamaki shine kansa da dogon gashi har kafaɗa sannan kwayar idanunsa sun sauya launi izuwa dark purple kamar ba shi ba, hannunsa na ruƙe da wani ɗan karamin kwarya bakinkirin kamar zunubi. Kai tsaye ɗakin jelly ya nufa yana taku cike da isa da izza kai daga gani kasan akwai abin da ya yi wa ƴan gidan shiyasa yake tafiya haka dan yasan ba za su tashi daga barci ba.
Yana shiga ya tura kofar tare da wuce wa ya haye saman bed ɗin jelly dake kwance kamar gawa saboda barci, wata zabgegiyar wuƙa ya zaro daga ta cikinsa, wuƙace mai kaifi sai kyalli take yi kamar madubi, a gefe ya ajiye wuƙar tare da kwaryar tasa sannan ya cire mata kayan jikinta tas ya mata tsirara haihuwar uwarta, sannan ya buɗe mata kafafunta da kyau kamar yadda ake yi wa maza kaciya............. Ya ilahi ya lillihi😭😌 sai dai mun haɗu gobe idan mai dukka ya kai mu
💖💖TRIPLETS💖💖
E79-80💖
Yana shiga ya tura kofar tare da wuce wa ya haye saman bed ɗin jelly dake kwance kamar gawa saboda barci, wata zabgegiyar wuƙa ya zaro daga ta cikinsa, wuƙace mai kaifi sai kyalli take yi kamar madubi, a gefe ya ajiye wuƙar tare da kwaryar tasa sannan ya cire mata kayan jikinta tas ya mata tsirara haihuwar uwarta.
Bayan ya gama sai ya buɗe mata kafafunta da kyau kamar yadda ake yi wa maza kaciya, ɗaukar wannan zabgegiyar wuƙar ya yi yana ƙoƙarin tura mata a tsakiya gabanta dan wuƙar gabaɗaya ta shafi jinin period da take yi.
Bai kai ga sa mata wuƙar ba kamar daga sama ya ji an buɗe kofar ɗakin, a razane ya ɗago kansa tare da kai kallonsa izuwa bakin kofar ɗakin, Nawid ne ya turo kofar daga shi sai shot da singlet a jikinsa, mamaki ne ya kama Abbo ya akayi Nawid bai yi barci ba, duk irin tsafe ƴan gidan da ya yi akan ba za su farka ba sai gobe da safe. Ni kuwa nace ai ka makaro domin Nawid dai abokin Imran ne, duk kuma wanda zai zauna da Imran da Akil to ko baya so dole zai koyi yawai ta yin askar da zama da alwala, to dan haka babu wata sharri data isa ta taɓa su.
Abin da ya fito da Nawid kuwa bakar yunwa ce ta tashe shi mai matukar nukurkusan cikin, ya zo zai wuce ɗakin jelly ya shiga wajen Ummi dan ya tashe ta ta bashi wani abin da zai ci dan baya son abincin da ƴan biki suka dafa, to zai wuce ne ya jiyo kamar motsi a ɗakin Jellyn shine ya ce bari ya duba ko dai ita ce idanunta biyu tana zuba rigimar da ta saba, har ma ya tsara yadda idan ya sameta idanunta biyu zasu zauna su sha hira har asuba, ya samu ya lallaɓata har ta hakura ta amshi soyayyarsa.
Ba ƙaramin razana ya yi da ganin Abbo a ɗakin ba, dan ma dai shi a ainahin suffar Abbon yake kallon shi, ba a irin wannan suffa ta su ta matsa fa. Murya na rawa ya ce "Abbo me ya kawo ka ɗakin baby kuma?".
Rai a matuƙar ɓace Abbo ya diro kasa daga saman gadon, Nawid yana yi mashi kallon sanye da jallabiya a jikinsa, ni da ku kuma masu karatu mun san a ainahin suffar da yake a yanzu wato dai wannan shiga ta matsawa.
"Fita a ɗakin nan Nawid!!" Ya faɗa da tsawa tare da nunawa Nawid ɗin hanyar fita, abin mamaki sai ya ga Nawid yana tsaye bai ta fi ba, abin ya ɗaure mashi kai domin a iya saninsa ya san cewa babu wanda ya isa ya yi mashi musu idan yana wannan suffa ta natsafa, sai ga shi Nawid dai tsafin bata yi aiki a kansa ba, kuma hakan ta samo asaline daga askar na safiya da maraice da yake yi wadda Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama ya bamu akan idan mun karanta shi da bayan sallar la'asar to har izuwa sallar asuba washegari kenan Allah zai turo malaika ya kula damu tare da tsaremu babu wata sharri da zata samemu a wannan bayan la'asar ɗin zuwa asuba, bugu da karin annabi ya ce duk wanda ya karanta wannan addua kuma ya rasu kafin asuba to Ubangiji da kansa ya yi ma wannan bawa albishir da gidan aljanna, haka idan ka karanta shi daga asuba zuwa la'asar Allah zai tsareka babu wani abin sharri da zai same ka, kun dai ga Nawid da yamma ya yi askar nasa, da daddare babu abin da ya yi amma Allah ya tsare sa, ga kuma karin ni'ima idan ka rasu bayan karanta wannan askar ɗin Ubangiji da kansa ya yi maka alkawarin gidan aljanna, Allah kasa muna ciki Amin ya Allah, ASKAR ƊIN YANA DA YAWA KUMA AKWAI TSAWO IN SHA ALLAH ZAN SAKA MAKU SU A ƘARSHEN PAGE NAN, KU LIZIMCI YINSU DOMIN SAMUN UBANGIJIN RAHMA YA KARE MU, SAFIYA DA MARAICE, ALLAH YA BAKU DACEWA.
Tsawa Abbo ya sake daga mashi, amma ina Nawid ko kaɗan bai ji tsoro ba tamkar ma ba da shi Abbo yake yi ba, abin ya ɗaure wa Abbo kai sosai.
Wucewa Nawid ɗin ya yi ya nufi gadon, hawaye ne yake zuba a idanunsa sosai da sosai wani na bin wani, wannan abin takaici har ina, zuciyarsa wani irin tafasa take yi mashi, abin kunya yau ya kama Mahaifinsa da hannunsa yana ƙoƙarin ketawa matar da zai aura haddinta, wannan abin babbar bala'i ce ga Nawid.
Kayan ta ya ɗauka ya maida mata jikinta da Allah yasa ma green light ne a cikin ɗakin ba white light ba, hakan kuma yasa baka iya ganin mutun sosai. Idan baku manta ba Jelly bata kwana a ɗakin da babu wuta, hakan yasa Ummi ta sanya aka saka mata green light a ɗakin yadda dai zata samu ganin ɗan haske, Ummi bata son barinta da white light a cikin ɗakin domin annabi ya hane mu da yin hakan, ba kyau kwana da wuta a kunne a ɗaki.
Tsab ya mai da mata da kayan ta tare da sanya mata pant nata mai ɗauke da always a jiki. Bayan ya kammala ne ya sauƙo kasa tare da ɗaukarta a saman kafaɗarsa ya nufo hanyar fita, Abbo yana tsaye yana kare mashi kallo sannan kuma yana mamakin ya akayi Nawid ya bijirewa umarninsa duk da a tsaface ya bashi umarnin, abin ba ƙaramin tayar mashi da hankali ya yi ba.
Daidai Nawid zai wuce da ita ne kuma Abbon ya tare shi yana faɗin "Nawid ka ajiye yarinyar nan ka fita a ɗakin nan ko kuma in kashe ka!!".
Ko kallon in da yake Nawid bai yi ba tsabar takaici da bakin ciki, zuciyarsa wani irin azababben raɗaɗin zafi take yi mashi, kai tsaye ya sa kai ya nufi waje abinsa.
Damƙo wuyar singlet ɗinsa ta baya Abbo ya yi tare da daka mashi wani razanannen tsawa sannan ya fito da wuƙar tasa yadda Nawid ɗin zai iya gani ɓaro ɓaro ya ce mashi ko ya sauƙe jelly ya fita a ɗakin ko kuma yanzun nan ya kashe shi.
Rai a matukar ɓace ya ce "Abbo ka kashe ni sai ya fi mani sanyi akan na barka ka lalatawa yarinyar mutane rayuwarta, Abbo why? Why zaka yi mana haka? Me muka yi maka? Wannan wace iriyar bakar bala'in rayuwace, Abbo ka cucemu, Innalillahi wa Inna ilaihir rajiun".
Furta Innalillahi wa Inna ilaihir rajiun da Nawid ya yi ya sanya Abbo sakinsa ba shiri dan kada ya ƙone, cikin sauri Nawid ya fita waje ɗauke da ita a saman kafaɗarsa.
A zafafe Abbo ya bi bayansu akan lallai sai ya hanasu tafiya. Da dai Nawid ya ga da gaske Abbo yake yi hana su tafiya zai yi, sai ya wuce da Jelly waje, kai tsaye cikin motar sa ya kwantar da ita a gidan baya, sannan ya fara ƙoƙarin tare Abbo akan ya rabu da su.
Kusan kokawa suka yi kafin Allah ya bawa Nawid Sa'a ya tura Abbon a cikin ɗakinsa ya rufo kofar ɗakin tare da murza key ta baya.
Bubbuga kofar da karfi Abbo ya fara yi yana ƙoƙarin karya kofar, bai damu ba dan yasan dukka ƴan gidan ba zasu tashi ba sai da safe, hakan yasa ma yake ta faman buga kofar da karfi karfi.
Nawid kuwa cikin sauri ya faɗa ɗakin Ummi, sai barci take zubawa abinta, key ɗin motarta ya ɗauka tare da wayar ta ya fito waje, da yake ya rufe Abbo a ɗakinsa ba halin na ɗauki nasa key ɗin motar Shiyasa ya ɗauko na Ummi kawai.
Yana zuwa ya ɗauki jelly izuwa cikin motar Ummi tare da nufar bakin gate ya buɗe gate ɗin da kansa yayin da shi kuma Abbo yake ƙokarin karya kofar ɗakin ya fito, shima mai gadin gidan yana ta shan barci har da shi Abbo ya tsafe.
Da gudun gaske Nawid ya figi motar suka bar gidan ya kuma bar masu gate a buɗe.
Kai tsaye gidansu Imran ya nufa domin bashi da biyun Imran a duniyar nan bayan iyayensa.
Sai gudu yake shararawa yayin da ita kuma Jelly take ta sharara barcinta abinta bata ma san me yake gudana ba.
Yana zuwa kofar gidansu Imran ya tsayar da motar tare da fito da wayar Ummi ya fara kiran layin Imran ɗin da yake ya haddace number.
A lokacin da kiran ta shigo wayar Imran yana kwance saman gadon Lion suna hira shi ko in ce yana yi wa Lion hira yayin da shi kuma Lion yake ta fama da aiki a kan bincin case ɗin Jellyn a laptop nasa, domin kuwa Tyrone ya turo masu akan cewa tabbas Jelly tana Kaduna kusa da su a unguwa kaza gida mai kala kaza, Lion kuma yana kara dubawa ne dan ya tabbatar da hakan ne ita ɗin ce, a daidai lokacin yana bincike a gidan su Nawid ɗin kenan, kuma kusan duk abin da ya faru a gidan ya gani sakamakon wani camera da yake a palon su Abbon, bai kalli abin da ya faru tsakanin Abbo da jelly a ɗaki ba, amma dai ya kalli faɗar Abbo da Nawid ɗin dukka wadda suka yi a Palon, dan a iya palon ne akwai camera, so sun datsi cameran gidan ne, amma kuma da Nawid ya fito da wayar Ummi Lion ɗin ya bibiyi cameran wayar domin yanzu ba technology da ta fi sauƙi kamar ta datsar camerori da kuma wayoyin mutane dan aga halin da suke a ciki, shi kuma Imran yana kwance a gefensa yana jiran ya gama bincike ya gaya mashi in da Jellynsa take ya je ya ɗaukota.
Bari mu koma baya kaɗan kafin mu cigaba, lokacin da Lion da Imran suka dawo gidan karfe uku ne na rana, tun a Palon kasa suka rabu da Imran, Lion ya haura sama shi kuma Imran ya wuce wajen Areef, bayan ya duba shi sai ya wuce wajen Rimsha dake ta famar aikin barci, yau ta ci nama har ta shiga uku, ba komai a gidan na ci da ya wuce nama.
Lion kuwa yana sako kafarsa a cikin bedroom nasa ya gane cewa tabbas an shiga cikin ɗakin, ta yadda akayi ya gane kuwa shine, wani kamshi ya ji saɓanin nasa kamshin, bacin haka kuma yana sako kai a cikin ɗakin dara daran idanunsa suka sauƙa a saman drawer mirror dake rabi a buɗe bai gama rufuwa ba.
Perfume na Lion tana da karfin bala'i wadda zata iya rinjayar ko wace iriyar kamshi, amma kuma duk wannan karfin tata Lion yana iya tsame wata kamshin da ta gifta ta cikin tasa, hakan yasa ya tsame kamshin perfume ɗin Rimsha.
Shiru ya ɗan yi yana tunanin kamshin waye? Ya san tabbas bana Imran bane, ba kuma na Areef bane, kuma ma yasan Areef ba zai zo mashi ɗaki ba duk da cewa yanzu yana iya takawa kaɗan kaɗan amma dai ba zai iya haurawa saman benen nan ya zo ɗakinsa ba, kuma wannan kamshin bana perfume ɗin su Mark bane.
Lumshe dara daran idanunsa ya yi yana tunanin wani mai karan kwanan ne ya shigo mashi ɗaki, shida ko sojojinsa bai yarda su shigo mashi bedroom ba idan ba ƴan uwansa ba, Imran shine bare ba ɗaya daga cikin Triplets nasa ba wadda yake shiga mashi ɗaki, bayan Imran babu wani ɗan adam dake shiga bedroom nan, dan Lion ba shi da yadda da mutun ko kaɗan, in ma mace ko ba miji.
Cikin natsuwa ya karisa cikin ɗakin, abun ku da babban soja yadda kasan a gabansa Rimsha ta yi duk abun da ta yi a ɗakin nan, duk wani abin da ta yi haka yake Imagine a cikin ƙwaƙwalwarsa, duk abin da ta taɓa kwanciya da ta yi a saman bed nasa, bayan ta tashi duk wasu abubuwa da ta taɓa mashi haka yake kallonta gata nan tana yi,