Showing 285001 words to 288000 words out of 355604 words

Chapter 96 - Triplets Book 2 Hausa Novel Complete

10 Dec 2024

2838

hakuri ki sha ko?".

Idanunta a runtse ta girgiza mashi kai alamar a'a ba zata sha ba, da kyar ya fara lallaɓata har da yi mata kukan shagwaɓa sannan ya samu ta buɗe bakin nata wadda yanzu ya yi mata mugun nauyi, ga shi kwata kwata bata jin daɗin komai ya shiga bakin nan nata.

A hankali ya fara zuba mata a ɗan bakin nata, haka ta daure ta rinƙa sha sakamakon taga hankalinsa ya tashi sosai, ya shiga damuwa, sai rarrashinta yake yi, har da yi mata kukan shagwaɓa, hakan yasa ta jure ta sha mai ɗan yawa.

Sosai ya ji daɗin shan da ta yi, sai da ya tabbatar cikin ta ya ɗan cika sannan ya ajiye cup ɗin tare da kwantar da ita ya diro kasa daga saman bed ɗin.

Kananan kayan da suka sawo shekaran jiya ya fitar mata da guda ɗaya, doguwar riga ce tana da ɗan kauri kaɗan.

Dawowa saman bed ɗin ya yi ya sanya mata rigar, bayan ya saka mata ne ya ɗauketa cak.

Bai direta ko'ina ba sai tsakiyar carpet ɗin, har lokacin taki buɗe idanunta, wani irin mugun tausayin daddyn nata ne ta ji yana shigarta, sai hidima yake yi da ita, sannan gabanta zafi yake yi mata kamar me, duk jikinta ciwo yake yi mata, dan ma Allah ya sa ya gasata da ruwan zafi sosai, da ba dan haka ba ai ko motsi ba zata iya ba.

Taɓa wuyarta ya yi yana faɗin "Baby har yanzu akwai zazzaɓi ajikin ki fa, ki gama cin abincin nan mu je hospital". Yana magana yana zuba mata wani haɗaɗɗen ferfesu wadda Aunty ta shirya masu, ya ji kayan kamshi da kuma ya ji, sai tashin kamshi yake kamar me.

Ɗaukar spoon ɗin ya yi tare da fara ɗebo ferfesun yana kai mata shi a bakinta, har lokacin taki buɗe idanunta, haka zalika taki buɗe baki ta karɓi ferfesun.

Kasa kasa cikin sigar rarrashi ya ce "Babyn daddy ki yi hakuri ki ci abincin ko? Ko dai kina son daddy ya yi maki kuka ne?".

Idanu a rufe ta girgiza mashi kai alamar bata so ya yi kuka. "To idan baki son daddy ya yi kuka buɗe baki daddy ya baki abinci ko?"

A hankali baiwar Allah ta buɗe bakinta, zuba mata ya yi tare da mai da spoon ɗin cikin plate dan ya ɗebo wani.

Haka ya rinƙa bata tare da lallaɓata, har ta ci sosai ba tare da ta sani ba, sai da ya tabbatar cikinta ya cika sannan ya kyaleta tare da mayar da plate ɗin cikin trya ya ajiye.

Kusa da ita ya zauna tare da rungumota a jikinsa yana gaya mata kalamai masu daɗi tare da rarrashin ta yana faɗa mata ya tuba ba zai kara ba. Saboda daɗin kalaman da yake yi mata yasa har ta mance da abin da ya faru ta buɗe idanunta.

"Daddy kai baka ci abinci ba ai to". Ta faɗa tana ƙoƙarin ɗagowa daga jikin nasa.

Ihu ta saki lokacin da ta yi yunkurin tashi tare da koma ta lafe a jikin nasa tana hawaye. "Subhanallah baby me ya faru kuma?" Ya tambaya yana ɗago haɓarta.

Runtse idanunta ta yi tana hawaye ta ce "Daddy zafi zafi nake ji, zafi sosai". Nisawa ya yi har ga Allah yana matuƙar jin tausayinta domin yasan waye shi, kuma har cikin zuciyarsa bai so kusantar ta a yanzu ba, yasan idan ya yi gigin yin hakan zasu iya samin gagarumar matsala, ba zata iya jure bukatarsa a yanzu ba, ta yi karama, ba wai kawar da budurcinta yake cewa ta yi karama ba, no abin da zan biyo baya bayan sun yi kwanciya ta farko shi yake gudun mata, tabbas ba zata iya ɗaukar karfin sha'awarsa ba, saboda kananun shekarunta sannan kuma raguwace ajin farko, ga saurin kuka, daga ita har shi kuma muddin aka fara to fa ba za su iya hakuri da juna ba, sai dai nashi jarabar ta ninka tata sau ba adadi, yana daga cikin dalilin da yasa ya ki yin wani aure ya zauna yake fama da azumi da sallar dare, itama mummyn jelly ba karamin kwakwa ta ci a hannunsa ba, bawan Allah shi yasan waye shi.

Rarrashinta ya fara yi tare da zuba mata kalamai da nasihohi har ta hakura ta yi shiru, rungumeta sosai ya yi a jikinsa yana ɗan bubbuga mata bayanta.

"Daddy bayana kafafuna duk suna yi mani ciwo sosai". Ta yi maganar kamar zata yi kuka.

Miƙewa ya yi tare da kwantar da ita a saman bed ɗin, tattare kayan abincin ya yi tare da fitarwa izuwa Palo, bayan ya dawo ne ya haye saman bed ɗin, bawan Allah kwata kwata tausayinta ya hana shi cin abinci, yana jin yunwa amma ya kasa samun sukunin da zai iya natsuwa ya ci abincin, dan gaskiya yana da zuciyar tausayi sosai.

A hankali ya fara yi mata tausa yana matsa mata cinyoyin nata zuwa bayanta, sai sauke numfashi mai kama da nishi take yi a hankali hankali, har cikin ranta take jin matukar daɗin matsa mata jikin da yake yi, lumshe idanuwanta ta yi tana ta faɗin wash a cikin zuciyarta.

Ya jima yana yi mata tausa ba tare da gajiya wa ba, sai da ita da kanta ta ce ya bari sannan ya bari tare da komawa kusa da ita ya kwanta yana kara yi mata sannu.

Mirginowa ta yi ta shige cikin jikinsa tana kankame shi. "Daddy jikinka yana yi mani daɗin kwanciya" ta faɗa a shagwaɓe.

Kara kankameta ya yi sosai, sai sokinsa breast ɗinta suke yi a kirjinsa, hakan ba ƙaramin daɗi yake yi mashi ba.

"Baby jikin daddy ai mallakin ki ne ke kaɗai, dan haka ki yi kwanciyar ki yadda kike so".

Cikin sauri ta ce "Daddy ni kaɗai kuma? Jelly fa idan ta dawo? Ai itama zata kwanta a jikinka".

Girgiza kai ya yi yana faɗin "Ai ko karfe biyun dare aka gane jelly ba zan kara minti gomaba za'a ɗaura mata aure da Imran ta kuma bi mijinta ko zan sami kwanciyar hankali, tun tana ƴar shekara 13 Imran ya so na aura mashi ita, na ki yarda a lokacin nace sai ta girma, sai ta kammala secondary school, yanzu kuwa na yafe karatun ta je gidan mijinta ta yi kawai, hakan zai fi mani kwanciyar hankali, dan haka jikin daddy naki ne ke kaɗai".

Kankame shi ta yi tana goga kanta a kirjinsa, wani irin azababben kaunarsa ne yake kara ratsata, tana matukar kaunar mijin nata kamar yadda shima ya mace mata.

Haka suka kasance manne da juna suna hira cike da so da kuma kauna, sai lallaɓata yake yi yana rarrashinta, da zarar ta ɗan motsa zai tambayeta menene, ko ta ce mashi babu komai baya yarda sai ya bincika da kansa.

A ɓangaren su Imran kuwa, suna isa gida kai tsaye ɗakin Areef suka fara shiga, yau dai yana zaune ne saman bed ɗin nasa, ya jingina kansa da jikin headboard na gadon yana latsa wayarsa.

Jin sallamarsu yasa ya ɗago kansa yana kallonsu, haka kawai yau tun da yaga Rimsha da safe yake jin sha'awar shan jininta, tun lokacin yana ƙoƙarin kawar da kallonsa daga kanta, amma abin yana ba shi wahala sosai.

Hannu ya miƙe mata akan ta zo, daga ita har Imran sun tsorata da ganin yanayinsa a wannan dare, domin su ba a real ash eyes suke ganin idanunsa ba, idanun nasa ya riƙiɗe masu, ganin idanun suke yi kamar glass, da yake darene sai Imran ya yi tunanin ko dai yanzu shima idanunsa sun koma irin na Lion ne, domin idanun Lion suna kara kyalli da daddare, sai dai abin da Imran bai sani ba, ash eyes da blue eyes akwai banbanci nesa ba kusa ba.

Rimsha kam jikinta har kerma ya fara yi saboda tsoro, bata taɓa kallon masu kalar idanunsu ido da ido ba sai akan Areef ɗin dan Lion har yanzu bata sami damar yin ido huɗu da shi ba, kuma yana ɗaya daga cikin abin da yasa ko a mafarki taga idanun Lion tana tsorata, a iya Tv take kallo, to yau sai ga shi ma idanun Areef ɗin ya canza mata launi.

Amma da yake Imran yana nan, sai ta daure ta karisa wajen Areef ɗin tana karanta duk wata addu'a da ta zo bakinta, a gefensa ta zauna tana kallon kasa.

Hannu ya kai ya riƙo hannayenta, ji yake yi ba abin da yake so a duniya da ya wuce ya sha jininta, sai kallon halittar jikinta yake yi, Imran ya kara tsorata da yadda yake mata wani irin mayen kallon nan, ga shi kuma bai san da zancen cewa Areef yana kungiyar shan jini ba, Lion ya ɓoye mashi, idan baku mance ba, shi Lion yana da sirrin da ko Triplets nasa ba kasafai suka cika sanin cikinsa ba, duk yadda suke da mutun ba komai yake gaya mashi ba, idan ka ji yana magana da mutun tofa maganar ta shafe mutumin ne.

Wani irin azaba Areef yake ji a cikin jikinsa sakamakon ingiza shi da suke yi akan ya sha jininta, matse hannunta ya yi cikin nasa da karfi tare da datse harshensa da hakwaransa, sosai Rimsha ta tsorata tare da tsananta adduar da take yi a cikin zuciyarta.

Shi kuma Imran ganin hakan yasa ya ce "Rimsha ta shi ki je ɗaki ki kwanta dare ya yi". Tana son ta tashi ba hali domin ya kankame mata hannu yana wani irin datse harshen sa da karfi.

Lokaci guda kuma ya sake ta da sauri tare da juyo da kallonsa izuwa bakin kofar ɗakin, ba komai bane yasa ya yi saurin sakinta haka face kamshin perfume ɗin Lion da ya ji, Lion bai kai ga shigowa ɗakin Bama, kamshin perfume ɗin ne ta riga shi shigowa, shima Lion ɗin dama baya gidan yanzu ya shigo ne sai ya ce bari ya fara duba ɗan uwan nasa kafin ya wuce sama.

Ita kuwa Rimsha yana sakinta ta miƙe da sauri ya faɗa jikin Imran jikinta na ta ɓari Baiwar Allah.

Karin wani haske akan wannan al'amari, kwata kwata kungiyar da suka kama Areef wato G.M.A basa son Kamshin perfume na Lion, basa son shi ko kaɗan, shiyasa da ya doso su zasu gudu daga jikin Areef ɗin, wannan perfume ɗin na Lion kuma daga kasar Dubai yake sawa a buga mashi, perfume ne mai kyau over.

Da wannan sexy voice ɗin nasa ya yi sallama can kasa kasa, Imran ne ya amsa mashi sallamar yayin da shi kuma Areef ya kwantar da kansa a jikin headboard na gadon tare da runtse idanunsa, da alama bai so ganin Lion a yanzu ba.

Gefensa Lion ya zo ya zauna, jikinsa na sanye da wandon jeans navy blue da kuma farar high neck t-shirt yau ya ɗaura wannan jacket ɗin nasu a saman kayan, da alama yau ba shi da lafiya, domin dai duk zafin da ake yi a Nigeria yau ya sanya jacket a saman kayan jikinsa, bugu da kari ga face nasa ta yi wani fayau tare da ƴin wata ƴar rama wadda zai tabbatar maka bashi da lafiya, bawan Allah abubuwa sun yi mashi yawa akansa ba kaɗan ba, mutun ɗaya yake ɗebe mashi kewa tare da rage mashi damuwa shine Asreef, Aseef bawan Allah yana kiran shi video call ya yi ta yi mashi hira yana rage mashi damuwar da yake a cikinta, Areef kuma kullun kara mashi damuwa yake yi, domin kullun kara binciko wasu abubuwa da Areef ɗin ya aikata yake yi, duk kuma abin da ya binciko sai ta sanya shi damuwa, a yanzu ma daya tsananta bincike ya gano cewa, Areef ya sami kansa a wannan kungiyar ne sanadiyyar kashe wannan mutumi da ya yi, bugu da kari kuma tabbas Josephine ta zama hanyar shi garshi kungiyar, sai dai ita ma Josephine ɗin bata a cikin kungiyar wata makusanciyarta ce wadda suka kasance friend ita ce ke a cikin kungiyar, kuma abin da suka yi wa Areef shi suka yi wa Josephine ɗin ita ma, yadda suke control na Areef ita ma haka suke tata, sai yadda suka juyata, ga shi ita ba musulma bare abin ya zo mata da sauƙi, ba addu'a ba sallah ba komai, shiyasa ta fi Areef shan wahala a hannunsu, kuma sune suka bata abin da ta zubawa Areef ɗin a cikin abin sha ya sha ta haka ya shige su, dan su ɗauki fansa mutumin su da ya kashe yasa suka saka shi a kungiyar, sai dai da yake akwai Allah a ransa sun kasa cutar da shi.

Ɗazun Lion ya gama final bincike akan su, a nan ne ya sami waɗan nan amsoshin wadda suka yi mugun ɓata mashi rai, sai dai daɗin abin ya sanya sojoji runduna guda da su shirya zuwa yakar wannan ƙungiya saboda ya gano a in da ƙungiyar take, sannan kuma ya kira Sultan wato limamin babbar masallacin sa da ya gina a kasarsu, ya ce Sultan ɗin ya tara malamai su yi masu addu'a ayi sauƙar Al Qur'ani mai girma domin ƴakar wannan ƙungiya ba abu bane mai sauƙi, kuma ga shi sojojin dukka kafurai ne bare ace za su yi addu'a, dole ne sai su Sultan sun yi masu addu'a dan su sami nasara, Lion ya bawa sojojin umarni akan cewa ranar Friday su tunkari kungiyar, domin a ranar duk wani ɗan kungiyar yana wajen suna taro.

Abin farinciki ɗaya da Lion ya samu a wannan bincike shine mahaifiyarsu dai bata a cikin kunguyar dan ra'ayin kanta, kuma abin da ta bawa Areef ma ya ci, bada saninta bane domin control nata akeyi, hakan yasa ya ce ranar Friday ba zai bari ta je kungiyar ba, domin kada sojojin nan su haɗa da ita su kashe, yana da ƴakinin idan suka ruguza kungiyar to duk wani abin dake a jikin Josephine da kuma Areef zasu mutu.

STORY

Zubawa Areef idanu sosai ya yi tare da miƙawa Imran hannu dan su yi musabaha.

Ɗan sakin Rimsha Imran ya yi tare da miƙo mashi hannu suka gaisa cikin mutunta juna.

"Why ka je ka daɗe Prof?" Ya faɗa cikin sanyin murya yayin da yake kai hannunsa saman goshin Areef ɗin dan yaga sai faman haɗa zufa yake yi, ya zaci ko zazzaɓi yake yi, bai san cewa G.M.A ke bashi bakar wahala ba.

Rimsha kuwa sai kare mashi kallo take yi, yau wuni zumbur bata sami ganin shi ba, tasha kewa sosai da sosai, ba dan tana kunyar Imran bama da ta ce su dawo time da suke gidan Abbi, ba abin da ya fi burgeta sosai a tattare da shi sai laɓɓansa da gashin kansa, sun fi komai burgeta, yana da wasu irin halittar laɓɓa ne masu matukar kyau da jan hankali tare da kayatar da duk wanda ya kalla, duk wanda ya kallesu sai ya ji yana sha'awar ko da ɗan taɓasu da hannunsa ne, ga su da laushi kamar me.

Da kallo ɗaya kuma Rimsha ta yi mashi ta san ya rame, sai mamaki take yi akan me ya same shi ya rame haka, bata san lokacin da ta furta "Bawan Allah ko me yasa me shi ya rame haha? Ko dai bashi da lafiya ne? Allah sarki".

Bata san cewa a bayyane take yin maganar ba har sai da ta kalli Imran da Areef suna kallonta, shi kuwa Lion hankalinsa na akan jikin ɗan uwan nasa, da alama ma bai san da tsayuwarta a ɗakin ba, kuma dama kun san halinsa abin da yake a gabansa kawai yake yi, Allah mai iko kuma da yaren turanci Rimsha ta yi maganar, da yake dama basu damu da yin magana da hausa ba daga ita har Jehan ɗin.

Da gangan Areef ya ce "Rimsha ke da waye kike magana?". Ɗan zaro ido ta yi tare da fara ƴan kame kame, kashe mata ido Areef ya yi yana nuna mata alamar akan ta faɗi gaskiyar da waye take yi, amma ina tsoro ya hana ta faɗe, Areef ya san cewa idan har ta furta cewa magana take akan Lion ya rame to tabbas ko Lion bai ɗago ya kalleta ba, zai sa a ransa cewa koma wacece ita tabbas yana da mahimmanci a wajenta, kuma Areef ya san da cewa tabbas zai ji daɗin hakan a ransa ko da bai nuna ba, kuma dole ma sai ya jita a ransa, saboda ko daddy baya taɓa iya fahimtar halin da Lion yake ciki, amma ita da kallo ɗaya har tasan yana cikin damuwa kuma ya rame, abun da kuma ba samun damar kallonsa kullun take yi ba, duk wanda aka yi wa haka, dole sai ya ji wani abu a zuciyarsa, musamman mutun irin Lion wadda yasan ba kowa ne yake iya fahimtar shi ba, amma rana ɗaya a sami mai fahimtar shi da kallo ɗaya haka, kai abin fa abin duba wane.

Tsoro ya hana Rimsha magana, Areef ya yi iya yinsa akan ta ce da Lion take magana, amma ina ta kasa, daga karshe ma sai ta kawar da kallonta daga kan Areef ɗin, ba ƙaramin haushin hakan Areef ya ji ba, ji ya yi kamar ya mareta dan haushi, shima Imran bai ji daɗin abin da ta yi ba, shi kuwa oga yana ta faman buɗe magumguna da zai bawa Areef ɗin, sai dai kuma da alama akwai abin da yake tunani dan gane da Areef ɗin, domin kwata kwata baya tare da su, hankalinsa ya yi nisa sosai.

Bayan ya gama ɓare magungunan ne ya miƙawa Areef akan ya sha tare da fitar mashi da ruwan sha.

"Jikeki ki kwanta Rimsha, sai da safe". Cewar Imran. To ta amsa da shi tare da wucewa da sauri ta fice daga ɗakin.

Tana fita ba jimawa Lion ya gama abin da yake yi shima ya fita ya nufi bedroom nasa ya bar Imran da Areef ɗin.

Daidai zai shiga bedroom nasa sai ya ji kamar ana magana a ɗakin Imran, tunani ya yi akan ya bar Imran a ɗakin Areef, kamar zai shiga sai kuma ya fasa ya wuce bedroom nasa, domin ba komai ya cika kulawa ba.

Yana shiga bedroom nasa Rimsha ta fito daga ɗakin Imran ɗin ta wuce tata ɗakin hannunta ruƙe da jacket da ta ɗauko a cikin ɗakin.

Bata san jacket ɗin waye ba, ita dai ta yi wanka ta yi shirin kwanciya ne sanyi ya dameta shine ta shiga ta duba ko Imran


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login