Showing 36001 words to 39000 words out of 355604 words

Chapter 13 - Triplets Book 2 Hausa Novel Complete

10 Dec 2024

2783

shekaran sa zai kai talatin a Daular Mutuwa, su Mustapha kuma a gabana aka kawo su, ba zan iya misalta muku wahalar rayuwa da na sha ba, don ya wuce misali, sannan har yau da nake yi muku magana ban sake jin ɗuriyar wani da na sani ba, ban sani ba mamana tana raye ko ta mutu, duka ban sani ba!" Ta kai karshen maganar tare da kara sautin kukan da take.

Duk falon ba wanda bai yi wa Ayla kuka ba, musamman Rimsha ta fi kowa kuka a cikinsu, sai jan hanci Iya take.

Haɗuwa suka yi, suna hawaye suna rarrashin Ayla, da kyar suka samu ta yi shiru, hakuri iya ta ba ta tare da yi musu alkawarin baban Kausar na dawowa za ta karɓa musu kuɗi a wajensa, ta je da kanta ta sanya su a mota su koma wajen iyayensu, sosai suka ji daɗi tare da zuba mata ruwan godiya.

After some minutes👌

Falon ya yi shiru, miƙewa Iya ta yi ta nufi kitchen, da sauri Rimsha ta miƙe ta bi bayanta tana faɗin, "Ina son in koyi girki Iya." Miƙe kafafu Kausar ta yi ta gyara ta kwanta saman sofa tana faɗin, "Ba sai ki koya ba, ni me ruwana, abin da na sani dai shi ne a girka a ba ni na ci kawai na sani, ni ce ƴar auta a gidan nan, kuma ni kaɗai ce mace dole ba zan yi aikin komai ba, sai dai su boda Wasiu." Ita dai Ayla shiru ta yi tana son koyon girki ita ma, amma ba yau ba, don yau ta tuna da rayuwarta ta baya, duk jikinta a mace ba za ta iya ko motsa jikinta sosai ba.

Ita kam Rismha zagewa ta yi Iya na nuna mata yadda ake girki tana koya, don tun asalinta da ma tana da sha'awar koyon girki, shi yasa ko lokacin da suke gida tare da daddy tana yawan shiga kitchen wajen masu aiki ta tsaya tana ganin yadda suke aiki, saɓanin Jehan da ko hanyar kitchen ba ta bi bare ma ta shiga, ko abu take buƙata a Kitchen sai dai ta sanya masu aiki su ɗauko mata.

Kwanciya ita ma Ayla ta yi saman sofa ta rintse ido tana jin kanta na sara mata a hankali saboda kukan da ta sha, da haka har barci ya ɗauke ta. Ita kuma Kausar ta ɗaura kafa ɗaya kan ɗaya daga kwance, ta kafe TV da idon tana kallo,
Rimsha na Kitchen abinta tana koyon aiki tare da Iya.

Ni kuma na tattara kaya na, na wuce Kd don na je na ga wani hali Aunty take ciki?

💞💞KADUNA💞💞

Cike da tsananin tashin hankali Aafia ta figi mota zuwa asibiti, gudu take shararawa a kan titin nan kamar ba gobe, ga shi kuma dare ne, don lokaci karfe takwas da rabi za ta yi

Allah ya tsare, Allah ya kai su asibiti lafiya ba tare da wata matsala ba, tana shiga kuma ta yi sa'a likitoci suka karɓi Aunty hannu bibbiyu, suka shiga da ita A&E (Accident and Emergency) ke nan, sai kai komo Aafia take a bakin kofar, tana ta faman share zufar wahala da ke ta karyo mata ta gefe da gefen kunnenta, sai haki take kamar wadda ta ci uban gudu ta ƙoshi, gabaɗaya ta rasa sukuninta, ta yi da-na-sani har ta gaji.

A can gida kuma, Abbi da daddy su ma suna can cikin bedroom nasu, ransu na musu barazanar fita daga jikkunansu, sai fafutuka wajen neman ceton rayukan nasu suke, lokacin guda suka zazzage suka yi wata uwar rama kamar wadanda suka jima cikin ciwo, da ma shi Daddy Jelly akwai shi da dara-daran ido kamar na Jellynsa, ramar da suka yi ya sanya idanun nasa kara fitowa sosai abin gwanin ban tausayi.

A takaice dai daddy da Abbi zaune suka kwana, sun daina iya tafiya da kafafunsu, karfinsu duk ya kare, tun suna iya shiga bandaki da kafarsu, har suka dawo shiga da rarrafe, daga karshen a kasa wajen bakin gadajensu suka zube kan gwiwowinsu, suka kwantar da kansu a jikin gadon barcin wahala ya ɗauke su, ba su san abin da ke faruwa a cikin gida ba.

Ita ma Aafia kusan a tsaye ta kwana, don ba su ba ta damar ganin Aunty ba, ita kuma ba ta dawo gida ba, a kujerar da ke bakin kofar wajen ta zauna, idan ta jima ta jima sai ta tashi ta fara zarya a wajen tana tunanin ya su Abbi suke? Idan ta gaji da zaryar sai ta koma ta zauna, haka har dare ya tsala, a zaune saman kujerar wajen barcin wahala ya ɗauke ta.

A ɓangaren Umaisha kuma, kuka take sosai lokacin da Akil ya fita, bai kula ta ba yana jiyo kukan nata, amma yayi buris saboda ta raina shi sai wani cika yake yana batsewa, fuuu ya fice kamar wata guguwa.

Ya je ya shiga motarsa da niyyar ya tafi, sai kuma ya kasa kunna motar, a zahirin gaskiya har cikin dodon kunnensa, yake jiyo sautin kukan nata, ya kasa kunna motar tasa, har cikin ransa yake jin zafin kukan da take, sai dai kuma idan ya tuna cewa ta raina shi, sai ya ji ba zai iya komawa ya rarrashe ta ba, kuma ya kasa tafiya, don yana ji a jikinsa ba zai iya tafiya ya bar ta tana kukan nan ba, zuciyarsa ba zacta juri hakan ba. Shiru ya yi ya kasa gaba ya kasa baya, ya jingina kansa da jikin kofar motar yana tunanin ya zai yi?

Daga karshe dai ya yanke shawarar komawa don ya kasa tafiya, buɗe motar ya yi ya fito ya koma cikin gida.

Yadda ya bar ta tana zaune tana kuka, haka ya dawo ya same ta, kusa da ita ya zauna tare da ɗan rungumo ta a jikinsa yana faɗin "Is okey!" Kankame sa ta yi ta ci gaba da kukanta, hannu yasa ya ɗago haɓarta yana kallon cikin idonta, "Ya isa haka kukan nan kin ji?" Shigewa cikin kirjinsa da kyau ta yi ta lafe tana sauke ajiyar zuciya, ta daina kukan nata, shiru suka yi yana ɗan shafa bayanta a hankali, ya jingina kansa da jikin kayin gadon yana sauke numfashin a hankali, yana jin matukar son ta na kara ratsawa har cikin kwakwalwar kansa.

A ɓangaren Jelly kuwa, sosai Nawid ya ke tunanin yadda zai yi da ita, don a zahirin gaskiya ba zai iya auren Jelly ba, kwata-kwata babu son ta ko kaɗan a ran shi, Jehan yake so, ita kaɗai, bai taɓa jin son wata mace a ransa ba sai Jehan, yana ji a jikinsa cewa, ba zai iya rayuwa da ko wace mace ba bayan ita, har ƴar rama ya yi saboda tunanin mafita.

Gefen shi kuma Abbo tunanin yadda zai ɓullo wa lamarin Jelly yake, don a gaskiya ba zai iya haƙura da ita ba, yana bala'i son ta bai san ya zai yi da rayuwarsa ba.

Kamar kullun suna zaune saman table ɗin cin abinci, suna cin abinci dare, Nawid, Ummi, Jelly da kuma Abbo, Ummi sai faman cin abincinta take cikin kwanciyar hankali, tana farin ciki Nawid nata ɗa ɗaya tilo zai yi aure, kuma zai auri yarinyar da take bala'i so bayan shi, wato baby.

Ita kuma Jelly tana zaune tana ta yagar cinyar kaza hankalinta kwance, ba ta san me duniya take ciki ba, ba ta san abin da ake shirya mata ba, kun san dai Jelly da masifar kaunar nama, idan tana cin naman nan ba ta ji ba kuma ta gani, gabaɗaya barin duniyar mutane take, ko magana kake mata, ba ta amsawa matukar tana gaban nama. Hmm su Jelly manya.

"Abbon Nawid da ma ina son mu yi magana a kan auren baby da Nawid." Wani irin dum-dum gaban Nawid ya ba da duka, shi kansa Abbo dukan uku-uku jirginsa ya yi, har wani irin duhu ya gani ya gilma masa ta gaban idonsa, lokaci guda ya rasa nutsuwarsa, sai wani ƴan kame-kame ya fara yi kamar wani marar gaskiya

"Abbon Nawid lafiya na ga yanayinka ya canza cikin kankanin lokaci haka?" Cewar Ummi, ta yi maganar cikin kwanciyar hankali, shi ma Nawid ba karamin mamakin ganin Abbonsa ya shiga yanayi marar kyau ya yi ba. Da kyar Abbo ya iya sai ta nutsuwarsa ya ce, "Ina fa lafiya, ai ba lafiya, dole ki ga damuwa a tattare da ni." Zaro ido Ummi ta yi yayin da shi ma Nawid ya bude kunnuwansa yana jiran ya ji me Abbo zai ce? Sai addu'a yake Allah Ya sa Abbo ya ce, wannan haɗin da za a masa shi da jelly, ba ba ya so, bai yarda ba.

Cike da tashin hankali Ummi ta ce "Abbon Nawid ka mini bayani mene ne matsalar?" Ta yi maganar tana kara zaro ido cike da tashin hankali, dogon numfashi Abbo ya ja tare da sauƙewa a hankali kafin ya ce, "Ba na son wannan haɗi na Nawid da wannan yarinya baby?" Wani sanyi Nawid ya ji ya ratsa masa daga tafin kafar sa har izuwa tsakiyar kansa, wani murmushi siririn ne ya bayyana a fuskarsa.

A ɓangaren Ummi kuwa ƙara zaro ido waje ta yi ta ce, "Abbo mene ne ya sa ba ka son haɗin?" A takaice ya ce, "Saboda tsintaciyar mage ce, ba mu san asalinta ba."



_Ni ma na tattare kayana na yi nan wannan dirama ba a nan ba._

Sai mun haɗu gobe idan mai dukka ya kai mu


💞💞TRIPLET'S💞💞





🌹🌹Episode 13-14🌹🌹


A ɓangaren Ummi kuwa ƙara zaro ido waje ta yi ta ce "Abbo mene ne ya sa ba ka son haɗin?" A takaice ya ce "Saboda tsintaciyar mage ce, ba mu san asalinta ba." Ayya Jelly baiwar Allah tana can duniyar kaza ba ta tare da su, ba ta san wainar da ake toyawa ba.

"A'a Abbon Nawid kada mu yi haka da kai, idan muka ce don ba ta da asali ba za mu ba ta ɗanmu ba, to waye kake tun nin zai aure ta? Mu da muka san komai ma mun ki yarda, to waye kake tunani zai so ta, kuma ma ai yanzu mun zama mu ne asalinta iyayenta komai nata." Ɗaure fuska sosai Abbo ya yi kamar da gaske yana son hana Nawid ne don baby ba ta da asali, alhalin kuma kansa yake gyarawa hanya, yana son ya rushe maganar Nawid ne don ya gina tasa, wannan ita ce cakwakiya.

"Ummin Nawid na gama magana, ɗana yaro ne mai asali, don haka ba zai auri wadda ba ta da asali ba." Ya kai karshen maganar tare da cire hannunsa daga abincin ya miƙe ya bar wajen, cike da ɓacin rai a zahiri, amma cikin ransa kuma farinciki kamar ya zuba ruwa a kasa ya sha.

Sosai Ummi ta ji babu daɗi, kuma ta kudure a ranta sai Nawid ya auri Jelly don ita ce zaɓinta, ba ta son Nawid da kowace mace fa ce Jelly, ko me zai faru sai dai ya faru, ɓera ya ɓarar da garin kyanwa. Nawid, Jelly zai aura. Rai a matukar ɓace ita ma ta miƙe ta nufi bedroom nata, yau ranta ya ɓaci sosai ba za ta je wajen Abbo ɗin ba, kwanciya ta yi a ɗakinta.

Shi ma Nawid ganin iyayen nasa sun tafi ya sa ya miƙe ya nufi ɗakinsa, ransa fes sai wani murmushi yake saki, Abbonsa ya rushe maganar aurensa da mahaukaciya a cewarsa. Ita kuwa Jelly sai faman cin naman kaza take, kwatakwata ma ba ta san me suke tattaunawa a kanta ba, tana dai jin zancen nasu sama sama haka yana bi ta gefen kunnenta.

Sai da ta cinye kaza guda tas, ko kaɗan ba ta rage ba, kamar wata mai aljanun cin nama. Bayan ta kammala sai ta miƙe ta wuce bedroom nata tana lashe baki kamar wata tsohuwar mayya. Tana shiga ta haye saman gadonta tana sauke ajiyar zuciya, yau ko kayan barci ba ta samu sawa ba, don da ma Ummi ke saka mata kayan barci yau kuma ran Ummi a ɓace yake.

Abbo da Ummi ransu a ɓace barci ya yi awon gaba da su, Nawid kuwa farinciki cike fal ransa ya yi barci. A gefen ita ma Jelly da yake ba ta san me aka kulla ba, sai ta yi barcinta cikin kwanciyar hankali.

A ɓangaren Umaisha kuma, bayan sun ɗan yi shiru na yan mintuna ne, Umaisha ta katse musu shirun da cewa, "Yaya Akil don Allah gobe ka ɗauko Aunty Afi ta zo ta mana kwana biyu ka ji?" Shafa kanta ya yi kafin ya ce "To, na ji kuma zan je na ɗauko ta." Wani daɗi Umaisha ta ji ya rufe ta, da ƙarfi ta matse shi a jikinta, tana murna. "Za ki ɓalla ni ko?" Ya tambaya yana tsare ta da ido, dariya cikin hawaye ta yi tana faɗin, "Kai yaya Akil ni na isa na ɓalla ka ne?" Shiru ya mata don shi ma ba mai son yawan Magana ba ne. Haka suka yi shiru, ta yi luf a jikinsa har barci ya ɗauke ta, shi kuma sai faman kallon fuskarta yake yi.

Mu koma wajen Rimsha.

Bayan sun gama girki ita da Iya, ta fito ta shige cikin bandaki ta sake yin wanka abinta, don Rimsha akwai ta da bala'i son tsafta sosai, ba ta son datti ko kaɗan.

Bayan ta yi wanka ta sake shiryawa cikin wata doguwar riga ta Kausar, ta fito falo, nan ta samu Kausar da Ayla suna cin abinci, amma kowa kwanonsa daban, ma'ana daban-daban Iya ta saka musu abincin. Kusa da su ta zo ta zauna, Ayla ce ta jawo wani kwano da ke rufe a gefen su ta miƙa mata tana faɗin, "Ga naki abincin." Karɓa ta yi ta fara ci tana jin daɗi yau ta iya yadda ake yin miyar Steew da shinkafa.

Suna tsaka da cin abincin ruwan sama mai karfin gaske ya ɓarke, babu hadari babu komai suka ji zubar ruwa kamar da bakin kwarya, mamaki ne ya kama Ayla. Cike da mamaki ta ce, "Da ma wai har yanzu lokacin damina muke ne?" Kausar na fama da kokarin gutsirar ganda ta ce, "E mana, ni ma dai abin ya ba ni mamaki, rabon da na ga ruwan sama yau wajen sati biyu kenan? Tun da muka shiga Daular Mutuwa, kuma da muka fito ma ba a yi ruwa ba har muka iso nan." Juyawa Ayla ta yi tana kokarin yi wa Rimsha magana, sai suka ga, Rimsha ta a jiye kwanon abinci ta miƙe da gudu ta yi waje.

Cikin sauri Ayla ta ajiye cokalin hannunta, ta miƙe ta bi bayanta, don a tunaninta wani abin ne Rimsha ta ji a waje, shi ne ta je leƙowa.

Rimsha na fitowa ta shige cikin ruwan saman nan, tana dariya tana juyi a ciki kamar kifi, mamaki ya hana Ayla magana, ta tsaya kawai daga bakin kofa ta zuba wa Rimsha ido. Ita kam Kausar da ma idan tana cin abinci ba ta taɓa yarda wani abu ya tayar da ita, ba ta tashi har sai ta kai aya a cin abincin da take, sai ta ga karshen kwano take samun nutsuwa, don haka yanzu ma ba ta taso ba, tana zaune tana cin abincinta kawai.

Wani nishaɗi Rimsha ke ji yana ratsata, sai juyi take cikin ruwan saman nan tana dariya, ga ruwan zuba yake sosai kamar da bakin kwarya, ga shi babu iska. Tun tana karama take bala'i son ruwa, ko lokacin da suke gida tare da daddy in dai ba cikin dare aka yi ruwan sama ba, in da rana ne sai ta shiga, tun daddy na hana ta har ya hakura ya dai'na.

"Rimsha kina son ruwan sanyin nan ya saki mura ko?" Daga bayanta ta ji wannan zazzakar murya mai kama da tata, a sukwane ta juya, Malika ce ke tsaye ita ma cikin ruwan tana ta murmushi dimple nata irin na Rimsha na lotsawa.

Yar dariya Rimsha ta yi kafin ta ce "Malika me kika zo yi a nan? Ko dai ke ma yar nan garin ce?" Matsowa kusa da ita Malika ta yi tana ta murmushi ta ce, "A'a ni ba yar nan ba ce, na zo wucewa ne na gan ki kina wasa cikin ruwa na ce bari na zo mu gaisa" Kara faɗaɗa murmushi Rimsha ta yi tana faɗin "Gaskiya kina da kirki sosai, ina godiya." "Duk kirki na ai ban kai ki ba Rimsha" Cewar Malika, shiru Rimsha ta yi tana tunanin wani kirki ita kuma ta yi da har Malika take ce wa tana da kirki.

"Rimsha ki fita a cikin ruwan nan fa, kada mura ta kama ki". Cewar Malika, ta yi maganar tana kara matsowa kusa da ita, "Malika to ai ke ma kin shiga cikin ruwan, ke ma ki fita kada mura ta kama ki".

Jan dogon hanchinta Malika ta yi, kafin ta ce, "Ni kam mura ba za ta kama ni ba, don asalina ma a ruwa nake rayuwa, ke dai ki fita". Rimsha za ta yi magana Ayla dake tsaye a bakin kofa ta cikin falo tana ganin ta ta ce, "Rimsha kan ki ɗaya kuwa?" Juyowa Rimsha ta yi ta kalle ta tana faɗin, "Ban gane kai na ɗaya ba, me na yi kuma?" Ta yi maganar tana zaro dara-daran idanunta alamar mamaki, "Da wa kike magana to?" Cewar Ayla.

A sukawane Rimsha ta sake dawo da kallon ta kan Malika dake tsaye ta goya hannu a kirjinta sai murmushi take tana kallon su, juyawa ta yi ta sake kallon Ayla. A ɗan tsorace ta ce, "Ayla ban gane da wa nake magana ba? Ni da Malika ce mana".

Ɗan sako kai waje Ayla ta yi ta leƙo da kyau ko za ta ga wani ko wata da ke magana da Rimsha, amma sai ta ga wayam ba kowa. A kule ta ce "Wace ce kuma Malika? A ina kuma take? Don ni ban ga kowa a nan ba." Zaro ido sosai Rimsha ta yi ta ɗan ja baya daga kusa da Malika, ta matsa tana faɗin, "Ga ta nan ki gan ta." Zaro ido Ayla ta yi da nufin ya yi tozali da wacce ake nuna mata din amma babu abin da ta gani.

"Ki daina wahalar mini da kanki Rimsha Ayla ba za ta gan ni ba". Cewar Malika, juyo da kallon ta kan Malika ta


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login