Showing 255001 words to 258000 words out of 355604 words
yawan kallonsa, amma ta kasa ɗauke idanunta daga kanshi, sai kallonsa take yi sosai, ji take tamkar ace ya zama nata, shi kuwa yana fuskartar gefe bai ma san suna yi ba, ya dai san mutane sun shigo palon, amma bai nemi sanin koma su waye bane.
Kasa kasa Imra ya ce mata ta je ta yi sallama da Areef yana zuwa bari su yi magana da Lion, to ta amsa mashi da shi sannan ya nufi ɗakin Areef ɗin, tana tafiya tana waigo Lion, ba ƙaramin tafiya da imanin ta ya kara yi ba, ya ruɗa mata kwakwalwa yau ɗin nan sosai da sosai.
Tana shiga ta sami Areef ya gama magana da Aseef yana latse latse a wayar Lion ɗin, daga ɗan gefa ta tsaya tana gaya mashi zata tafi school, dawo da kallonsa kanta ya yi kafin ya ce "Okey waye zai kai ki?" "Yaya Imran" ta bashi amsa.
Shiru ya ɗan yi kafin ya ce "Idan ya kai ki dawowa yake yi ko?" Jinjina mashi kai ta yi alamar e, girgiza kai ya yi kafin ya ce "Haka ba zai yi wu ba gaskiya, dole ki samu tsaro sosai, saboda yanzu ke ba kamar sauran mata bane, nasan ba za'a rasa maza masu karan kwana da zaku yi maki magana ba, ni bana son haka, komai namu saboda ne wadda mu kaɗai muke fara amfani da shi, dan haka Lion ma sabuwar mace za mu sama mashi wadda ba wanda ya isa ko da sunan wasa ya yi gigin yunkurin tinkarar ta bare ma har ya ce yana sonta, bari Prof ya zo, sojan dake bakin gate ya kai ki school, Prof ya je ya nuna mashi school ɗin, kuma ya yi gadin ki sai an tashi ya dawo da ke, zan gayawa Lion ya karo wasu sojojin guda biyu wadda za su rinƙa tsaron bakin gate ɗin, daga yau wancan ya zama mai tsaron ki, kuma nasan a wannan gaɓar Lion zai yarda, domin ya sani cewa duk wanda yake tare da mu, idan bamu ba shi tsaro ba mun ɗauki alhakinsa, kuma ma yasan wannan dokar mu ce, kuddin mutun yana a karkashin mu to yana cikin tsaro".
To ta amsa mashi da shi tare da yi mashi godiya. Tana rufe baki sai ga Imran ya shigo bakinsa ɗauke da sallama.
Kusan a tare ita da Areef suka amsa sallamar, kamar yadda ya gayawa Rimsha haka ya gayawa Imran, haka kuwa akayi, da sojan suka tafi, sai bayan sun tafi ne da Lion ya shigo karɓar wayarsa a hannun Areef ɗin, a nan ne yake sanar da Lion alfarman da yake nema, yana son abar wancan sojan ya rinƙa bawa sister Imran tsaro, shiru Lion ya yi bai yi magana ba, har ya gama abin da zai yi, zai fita ne sai ya ce "Idan sojan ya dawo ka sanar da shi nan da leƙa waje ban yarda ya sake yi ba, nan ba kasar su Prof bane? Before sister tasa ta zo nan waye ya ke bata tsaro? Ko a ƙarƙashin mu take ne? Idan ka sake yi mani irin wannan ranka zai ɓaci, ai ba a karkashin mu suke ba bare mu basu tsaro" Ya kai karshen maganar tare da ficewa abinsa.
Sai lokacin Areef ya tuna ashe ba kasar su ba ne, kuma ashe basu cike takardan zama a karkashin su ba, tunani ya fara yi ta yadda zai samawa Rimsha wannan takarda ta cike, idan ta cike shikenan tana karkashin kulawar Lion, ba zai bari wani abin ya same ta ba, addu'a ya fara yi Allah yasa Lion ya zo da takardan, idan ya zo da takardan wlh sai ya ɗauko mata ta sanya hannu ko me zai faru, lokaci guda kuma wani tunani ya faɗo mashi, ina maman su Prof take da har ta bar sister Prof a nan, da ya ke kuma su yin hakan ma ba wani abu bane a wajen su, sai bai wani damu ba, bai kuma kawo komai a ransa ba, ya san su a wajen su ma yarinya tana iya barin gidan iyayen ta koma gidan saurayinta ta zauna, kuma iyayen suna gani ba wani action da za su ɗauka akan hakan.
Tunani cike fal ransa har barci ya yi awon gaba da shi.
Imran kuwa suna fita sai da suka sayawa Rimsha abin da zata yi breakfast da shi, sannan ya bata 1k lokaci ya kure sun zauna hira da Areef bata yi girki abin da zata ci ba, tun da bata iya cin nasu ba.
Bayan sun je school ɗin Imran ya dawo ya barsu ita da wannan sojan a school ɗin, kowa sai kallonta yake yi, kowa yana son sanin wace ce ita, da soja yake gadin ta, sojan ma kuma Bature ga shi fari tas da shi kyakkyawa mai kirar jarumai, daga student har malamai sai kallonsu suke yi.
Da lokacin shiga class ya yi, har cikin class ɗin sojan ya shiga, ya zauna a kujeran da malami yake zama yana fuskartar ɗaliban, fuskar nan tasa babu alamar wasa ko kaɗan, shiyasa gaba ɗaya ɗaliban suka razana, class ɗin ya yi tsit tamkar babu kowa, ga Rimsha yar firitu agab shi, dan bata kai kirjinsa tsawo ba, da kaɗan ta ɗara cikinsa tsawo, amma a haka yake bata tsaro, duk in da ta je yana biye da ita, kai Allah ka bamu arziki mai albarka.
A ɓangaren su Ayla kuwa, yau zata fara zuwa school, sosai mijinta ya shirya ta, kamar yadda yake shirya jelly ta tafi school haka ya shirya ta ita ma, ta yi kyau sosai, shima ya shirya cikin wata haɗaɗɗiyar yadi ash color, ya yi mashi kyau sosai da yake yana da haske.
Da farko ma cewa ya yi shi zai yi mata girki tayi breakfast, dan akwai kitchen a part ɗin nasu, amma sai Aunty ta rigashi ta aiko masu da abinci, ba dan ya so ba, ya zuba mata girkin Auntyn tayi breakfast sannan suka fito suka nufi cikin gida, sun jero kamar wasu taurari.
A bakin kofar shiga palon su Abbi suka yi karo da Irfan yana fitowa, har wani faɗuwar gaba ya ji ganin su da ya yi a tare, bawan Allah har yar rama ya yi, kakalo mirmishi dole ya yi tare da miƙawa daddy hannu yana faɗin "Barka da safiya bappa".
Da fara'a daddy ya miƙa mashi hannu yana faɗin "Irfan baka da lafiya ne?" Girgiza kai ya yi kafin ya ce "A'a bappa lafiya ta lou, yanzu shiga na ciki ma sai da Sadiya ta tambaye ni ko bani da lafiya ne, wai me kuka gani kuke tambaya tane?".
Ayla ce ta caɓe zancen da cewa "Yaya Irfan ka rame ne mana, ina kwana?" Dogon numfashi ya ja tare da sauke wa a hankali kafin ya ce "Lafiya lou Aliya kin tashi lafiya?".
Lafiya ta amsa mashi da shi, sai wani kauce masu yake yi, baya son ganin fuskar Ayla, shi kuma daddyn jelly ya tsai da shi akan lallai sai ya gaya mashi menene yake damun sa, kafewa ya yi akan lallai shi ba abin da ke damun sa, haka suka hakura suka kyale shi ya wuce su kuma suka shige cikin palon.
Zaune suka isko Aunty saman dining table, cikin zolaya daddy ya ce "Sadiya kina cin ye mani kuɗi sosai fa, yanzu tun ban tashi barci ba kin haye saman table kin fara ciye ciye ko? So kike yi ki ja mani wata matsala ko? Wai ba ance kada ki rinƙa cin abubuwa masu nauyi ba har sai kin kara samun sauki ko? Shine kike ta ɗurawa da sanyin safiya salon ki jamin sake mai daki asibiti na kashe kuɗi na ko?."
Hararar wasa ta wurga mashi kafin ta ce "Kai da nake renonka ɗin ne zaka yi mani wata magana? Ni fa yanzu Aunty babba ce, ka zama kanina Yaya Maik tun da ka kame mani yar kanwata ka shige da ita part naku na zama aunty babba".
Harara shima ya wurga mata da manyan idanun nan nasa yana karisawa wajen table ɗin, "Ina kwana?" Ta faɗa tana murmushi.
"Yanzu kenan kika tuna da gaisuwar ko? To ni dai kin shirya wa matata lunch box nata ne, ko kuma in shiga kitchen da kaina?".
Kai kallonta kan Ayla dake tsaye ta sunnar da kai kasa ta yi, sai wani ƴan kame kame take yi, "Yaya Maik yanzu ni da nake Aunty babbama ni ce zan shirya maku lunch box ko?" Ɗaukar apple ya yi kwara ɗaya ya wuce ya nufi kitchen yana faɗin "Da dai ban iya girkin bane da sai ayi mani rigima, amma tun da na iya matata ta wuci gori".
"Eyeee irin wannan soyayya haka? To ni dai dawo na shirya mata, ai na san yau zata je school, dan haka na shiryawa yar kanwata komai da komai, Ayla wai kame kamen me kike yi ne? Ki je kitchen ki ɗauko box ɗin naki mana".
To ta ce tana ƙoƙarin nufar kitchen ta jiyo voice nasa daga ciki yana faɗin "No bari na ɗauko mata da kai na, sai ma na binciki me a ciki tukun nan, dan ita ba komai zata ci ba yanzu".
Murmushin kawai Aunty ke yi ta ce da Ayla ta zo mana me ya tsai da ta a can, ba musu ta kariso wajen table ɗin cike da kunya suka gaisa, cikin raha kasa kasa dan kar daddy ya ji Aunty ta ce "Ke jiya da kika wani ce mani daddy da zafi baki ji kunya ba sai yau ko? A lallai yarinyar nan". Ta kai karshen maganar tana dariya.
Ita kuma Ayla hannu tasa ta rufe fuska tana tunanin a yaushe ta ce wa Aunty daddy da zafi kuma, bata san cewa a gigin barci ta yi maganar ba.
Lunch box ɗin ya ɗauko ya fito yana faɗin "Ina yaya Deen?" "Yana barci bai tashi ba" Aunty ta bashi amsa.
Hararar ta ya yi kafin ya ce "Ke kuma har kin tashi kin haye saman table ko?" "E mana ka sani ko dalili ya sanya ni hawa saman table ɗin? Kai ma fa yaya maik wlh wasa wasa ka iya sa ido".
Ɗan zaro ido ya yi kafin ya ce "Serious fa abin da nake tunani ne ya saki cin abinci da sassafen nan? Ba likita ya ce ba zaki sake iya ɗaukar ciki ba?".
Guntun tsaki ta ja tana turo baki ta ce "Da farko dai ban san me yasa nake jin yunwa safe da dare daga jiya zuwa yau ba, na biyu kuma likita bai isa ya yanke hukuncin abin da ya shafi Ubangiji ke bayarwa ba, Allah ke bada haihuwa ba wani ba, so babu likitan da ya isa ya ce ba zan haihuba ko zan haihu, wannan hurumi ne na Aarahman".
"Haka ne zancen ki gaskiya, to Allah dai yasa abin da muke tsammani ne, mu dai mun wuce sai na dawo" ya faɗa yana barin wajen table ɗin tare da riƙo hannun Ayla da ɗayar hannunsa ɗayar kuma ya ruƙe mata lunch box ɗin suka fice daga palon, da kallo Aunty ta bisu har suka fita, sai fatan Alkhari take yi masu a zuciyarta.
Yau ma kamar daren jiya, da motar Abbi suka fita, tana zaune a front seat ta kwantar da kanta tana kallon hanya.
"Me babyn daddynta take tunani ne?" Ya tambaya yana kallonta ta cikin mirror motar, dawo da kallonta kan shi ta yi tana murmushi, "Daddy kai nake tunani mana".
"Da gaske?" Ya yi maganar cike da jin daɗi, kuma ya yi magar daidai lokacin da ya ɗauki titin makarantar tasu.
"E daddy da gaske kai nake tunani".
Cool murmushi ya saki tare da jawota jikinsa yana kara gudun motar dan su isa da wuri ya samu ya rungumeta da kyau.
A kuwa cikin ƙankanin lokaci suka isa makarantar, yana kashe motar ya rungumeta da kyau a jikinsa yana faɗin "Baby zan yi kewarki sosai wlh, yanzu sai fa karfe ɗaya zaki dawo, kai anya zan iya kuwa?". Tana daga lafe a kirjinsa ta ce "Daddy nima fa ina jin kamar ba zan iya jimawa ban ganka ba".
Wani irin daɗi ya ji burinsa ya fara cika, haƙarsa ta fara cin ma ruwa, ɗago haɓarta ya yi tare da haɗe bakinsu waje guda, nan take suka shiga bawa juna hot kiss.
Sun shagala da kiss na juna agogon dake ɗaure a hannunsa ta buga mashi karfe 8 ya yi, da kyar ya iya zame bakinsa daga nata tare da sake ta yana faɗi "Muje na kai ki". To ta amsa da shi, kusan a tare suka fito suka nufi cikin school ɗin.
Cikin ƴan mintunan da ba su wuci goma ba ya gama komai ya fito ya shiga motarsa zuwa gida ya bar ta a school ɗin, har ga Allah yana kewarta fiye da tunanin mai tunani, haka ya koma gida ya kwanta cike da damuwa.
After some hours 👌
Gidan Lion.
Bayan Rimsha ta dawo daga school, tare da sojan nan, cikin gida ta nufa kafin ta shiga bedroom nata Imran ya dakatar da ita ya ce ta shirya da wuri su je gidan babbansa su yi wa daddyn Jelly murna ya yi aure. To ta amsa da shi, cike da zumuɗi ta shige cikin bedroom nata.
Tsabar murna zata fita anguwa a gurguje ta yi wanka ta shirya cikin wasu riga da wando masu ɗan karen kyau, rigar pink color ce zuwa gwiwarta ya tsaya mata kamar Pakistan, yayin da wandon kuma ya kasance fari tas mai stones a jiki, wandon dai pencil Jeans ne, while shi kuma rigar yana da ɗan faɗi daga ta kasa, da ta saman shi kuma ya kamata, gyalen kayan fari ne tas kalar wando, light make up ta yi ta gyara gashin kanta tare da ɗaure shi a tsakiyar kanta, sai tashin kamshi take yi, zubawa hannunta ido ta yi tana kallon yadda lallen hannun nata ya rage baki yake ƙoƙarin gogewa, da yake tana taɓa ruwa sosai, tunani ta fara yi dole yau ko gobe ta ce yaya Imran ya kai ta ayi mata wani. RIMSHA SARKIN SON LALLE DA GYARAN JIKI
Da wannan tunani ta ɗauko farin hijabi daga cikin trolleynta ta fito Palon.
Babu kowa a palon, haka kawai ta ji cewa tana son ganin ɗakin Lion ɗin nan, ba ko tsoro ta lallaɓa izuwa bakin kofar ɗakin, bata kai ga leƙawa ba ta ji motsin Imran yana ƙoƙarin fitowa daga nasa ɗakin, da yake kusa ne hakan yasa ta ji motsin nasa.
A sukawane ta gudu ta koma saman sofa tana sauke ajiyar zuciya, Malika ce ta bayyana a gefenta tana faɗin "Ke Rimsha bakya jin magana ko? Wlh da kin leƙa ɗakin nan da yau kun yi ido huɗu da shi, domin kuwa yana zaune yana fuskantar kofar shigowa, da kuma hakan ta faru..." Bata kai ga karisa maganar ba ta ɓace abinta, dan ta isar da saƙon da take son isarwa, kuma ba sai ta karisawa Rimsha abin da zai iya faruwa ba idan da ta leƙa ɗakin, ta sani ita da kanta. Tana ɓacewa kuma Rimsha ta fara jiyo muryan Imran dake tsaye a ƙanta yana faɗin "Muje mana ina ta yi maki magana kin yi shiru".
Yar firgita ta yi tare da miƙewa tsaye tana faɗin "Kayi hakuri yaya Imran". Ba komai ya ce mata tare da wucewa gaba ta bi bayansa.
Ɗakin Areef suka fara shiga, yana zaune ya jingina da jikin headboard na gadon, yau ya sha wanka, har wani kyau ya kara, hasken fatarsa ta kara bayyana, yana sanye da singlet fara tas da shot, sai dai ya jawo bargo ya rufe cinyoyin sa, ba ƙaramin razana da kallon kyakkyawar surar jikinsa Rimsha ta yi ba (ni ko na ce dan ma baki ga na Lion ba, ai da sai suma!) Ta razana sosai, har wani kerma jikinta yake yi, shi kuwa zuba masu ido ya yi yana kare mata kallo, dan ɗazun yana kwance bai kalleta sosai ba.
A cikin zuciyarsa ya ce kai ashe karama ce sosai, tab akwai aiki a gabansu. Gefensa Imran ya zauna yana tambayar shi ya jiki, da sauki ya amsa, ita ma ta gai da shi, fuska ba ya bo ba fallasa ya amsa.
Sanar mashi da in da za su je Imran ya yi, shiru ya ɗan yi kafin ya ce "Da ina da lafiya ai da munje tare" murmushi Imran ya yi ya ce "Ba komai idan ka samu lafiya zamu je, zai kai ka wajen dukka yan uwana" Sosai ya ji daɗi dan ba ƙaramin so yake yi wa Imran da ƴan uwansa ba, duk da bai san kowa daga cikin su ba, daga Imran ɗin sai Rimsha da yake yi wa ganin kanwar Imran ɗin ce, amma duk da bai san su ba, yana bala'in kaunar su sosai.
Sallama suka yi, suna yi mashi Allah ya kara sauki, shi kuma yana yi masu adawo lafiya, da haka suka wuce.
Da motar Imran ɗin suka tafi, a hanyane ya ce mata "Rimsha kina da farin jini sosai da sosai kowa son ki yake yi, kina burge duk wanda ya zauna dake" murmushi kawai ta yi ba tare da ta yi magana ba. "Kina jin yunwa ko?" Ya tambaya yana sauƙa daga kan titin da suke zuwa na gidan su Abbi ɗin.
Gyaɗa mashi kai tayi alamar e tana jin yunwa "To ki yi hakuri, an shirya mana abin ci a gidan Bappa zamu je mu ci, su Akila ma duk Akil ya kai su tun karfe 12 na rana, yanzu mu kaɗai suke jira".
Wani irin daɗi ta ji, zata haɗu da Akila da Umaisha.
Suna isa gidan tun bai gama kashe motar ba ta fito, dan ita burinta kawai ta ga su Akila. Tsayuwa ta yi tana jiransa har ya kashe motar ya fito suka jera izuwa cikin gida.
Tun a bakin kofar palon suke jiyo hayaniya alamar suna haɗe a palon kenan, Imran ne a gaba tana bin shi a baya.
Da sallama ɗauke a bakinsu suka shiga cikin palon, wani ihu Ayla dake zaune kusa da daddy ta kurma tare da miƙewa ta nufeta tana faɗin "Rimsha!! Rimsha kece?!!" Ita ma Rimsha ihun sunan Ayla ɗin ta yi suka rungumi juna suna dariya kamar zautattu.
Malika dake tsaye a bakin kofar shigowa ba wadda ke ganin ta dan bata bayyana a yadda za'a ganta ba, da ɗan