Showing 234001 words to 237000 words out of 355604 words
na yi aure amma bani da wanda zan gaya mawa, kafin su Abbi ke kaɗai nake da shi a duniyar nan, ina kika shiga, dan Allah ki zo ki taya ni murna kin ji ko?". Abin tausayi haka ta zauna ta rinƙa kuka har karfe 5, sai da ta tuna daddynta ya ce ta kawo mashi abinci, sannan ne ta miƙe da sauri ta faɗa toilet dan yin wanka.
Su Aunty kuma suna palo suna hira suna dariya, while ita kuma Hajiya Hadiza tana can tana zuba barcinta dan ita bata takurawa kanta.
A ɓangaren Lion kuwa.
Zaune yake gefen Areef (James) yana ƙoƙarin haɗa wasu alluran da zai yi mashi, amma sai ya farfaɗo zai yi mashi, abin da kuma yasa yake haɗa alluran yanzu shine abinciken irin alluran da suka mashi da ya yi lokacin farkawarsa ta yi.
Imran kuma yana ɗakinsa yana wanka.
Bayan wasu mintoci da ba za su wuci 30 zuwa 40 ba. A hankali ya fara motsawa tare da fara yin sambatu kasa-kasa.
"Is time for praying, i want to pray, Sallaht!! Sallaht!! Sallaht!!" Kalmar da James ya farka da ita keman abakinsa. Ko kallon in da yake Lion bai yi ba, shi kuma sai kara cigaba da sambatu akan Sallah yake yi.
Sun kwashi good 10mins a haka kafin Lion ya miƙe tsaye tare da goya hannunsa a saman kirjinsa yana karewa jikin James ɗin kallo.
Lokaci guda James ya kurma wani irin razanannen ihu mai tarwatsa kwakwalwa mai sauraro, ko motsawa Lion bai yi ba.
Bayan ya yi ihun kuma, a zafafe ya yunkura zai miƙe, da alama bai dawo cikin hayyacinsa ba, bawan Allah yaci bakar wuya a hannun mutanen nan.
Hannu Lion ya sa ya mai da shi ya kwantar, sake ƙoƙarin miƙewa ya yi, a karo na biyu ma mai da shi Lion ya yi ya kwantar, da ya ji ana mai da shi, sai ya saka karfi da gaske yana son miƙewa, kuma idanunsa a rufe, gently Lion ya ce "Areef you are saved now, you are together with your Triplets, open your eyes and see" ya kai karshen maganar tare da same hannunsa dake a saman kafaɗun James ɗin.
Jin sexy voice na ɗan uwan nasa ya sa ya natsu ya kwanta shiru tare da waro idanunsa a hankali, kai tsaye sai saman kyakkyawar fuskar Lion ɗin, while shima Lion ɗin shi yake kallo.
Wani irin nauyayyar ajiyar zuciya James ya sauƙe, can kasa-kasa ya furta "Please my blood I want to pray". Zuba mashi ido Lion ya yi na yan mintoci kafin ya kawar da kallonsa izuwa saman diamond watch dake a hannunsa, dan duba time, 8:30 pm, already anma yi sallar isha, ba tare da ya yi magana ba, ya wuce izuwa cikin toilet dake a cikin ɗakin, lumshe ido James ya yi yana sauke ajiyar zuciya, daga ta cikin zuciyarsa kuma yana yi wa Allah godiya da ya kuɓutar da shi, lokaci guda kuma wani tunani ya faɗo mashi a ransa wadda ta sanya idanuwansa suka cika da kwalla tab, har suna gangarowa, zafin da zuciyarsa ke yi mashi tana ratsa dukkanin ilahirin jikinsa, abubuwa da dama suna mashi yawo a ƙwaƙwalwarsa, nadama da dana sani da dama suna gudana a cikin kansa.
A wannan hali Lion ya fito ya same shi, hannunsa ɗauke da ruwa a cikin roba mai ɗan faɗi, bai damu ba dan ganin James ɗin yana hawaye, dama ya san za'ayi hakan, kuma yasan me James ɗin yake yi wa hawayen.
Saman bedside drawer ya ɗaura ruwan tare da fara yi mashi alwala yar shafa.
Tsab ya yi mashi ya kammala sannan ya ce mashi, zai iya fare yin sallar sa daga kwance.
Yunkurawa ya yi, ya miƙe zaune tare da jingina da jikin headboard na gadon, sai bin Lion da ido ya ke yi, shi kuma Lion ya ki yarda su haɗa ido, dan ba abin da zai hana shi hukunta James matukar ya mashi wasu tambayoyi wadda ya bashi amsar abin da yake zargi akansa, to sai ya yi mashi hukunci mai tsanani. BABBAR MAGANA MENENE WANNAN? AKWAI SAURAN RINA A KABA KEMAN.
A haka James ya ɗan fuskanci gabas ya gabatar da sallar sa, bayan ya kammala ya koma ya ɗan kishin giɗa.
Alluran da ya haɗa ya ɗauko tare da fara yi mashi a hannunsa, bayan ya ɗaure hannun ya nemi jiniya kenan.
Bayan ya yi mashi alluran ya gama ne ya fara yan bincike a jikin James ɗin, dan ya gano me da me CIA suka sanya mashi a jikinsa, ko ya tambaye shi ma, ba zai sani ba, saboda kafin su sawa mutun abubuwan nasu, sai sun mashi alluran fita hayyaci, so James ba zai san me da me ne a jikinsa ba.
"Da wani face ka shiga CIA?" Shine tambayar da Lion ya fara yi mashi. Ajiyar zuciya ya sauƙe kafin ya ce "Fake face".
Wani nauyayyar ajiyar zuciya shima Lion ɗin ya sauke, kuma har cikin ransa ya ji matukar daɗin amsar, kenan CIA ba su san ainahin kamannin James ba? Zai iya fita cikinsu kuma ba za su iya gane shi ba, sai dai idan sun tsawaita bincike sosai, dan suma ba baya ba wajen aiki da ƙwaƙwalwa da zallar basira, amma dai dukka haka abin ya zo da sauki tun da basu san asalin face nasa, kuma idan suka sa kafar wando ɗaya da Lion a bincike da rufe sirrin gidansu ya ceto James, to fa sai ya kai su kasa, wanan shine wasan kwakwalwa za'ayi bana karfin dantse ba. AKWAI KALLO
"Me yasa idan zaka kashe rai ka ke yin video da asalin face naka?". Shiru ya ɗan yi kafin ya ce "Ina son ajiye tarihi ne, bana son ya zamana nayi amfani da fake face wajen ajiye tarihina, kuma kafin na kashe mutun sai na nuna mashi asalin face na, dan ya san waye ya kashe shi".
Jinjina kai Lion ya yi tare da komawa gefen bed ɗin ya zauna yana faɗin "Ka huta zuwa da safe sai ka gaya mani me ya haɗa ka da G.M.A". Wani irin muguwar faɗuwar gaba James ya ji lokaci guda, abin ma ya bashi mamaki, ya akayi Lion ya iya bankaɗo duka wayan nan abubuwa haka. NI KUWA NA CE KA MANCE MATSAYINSA KENAN THE GENERAL OF THE ARMY.
Yana tsaka da tunani bai ma san time da Lion ya fice daga cikin ɗakin ba.
Yana shiga bedroom nasa ya isko Imran wadda ya shigo a lokacin dan duba shi.
Toilet ya nufa yana faɗin "Prof ba ri na yi wanka sai ka raka ni, akwai wasu magunguna da neke buƙatar sayawa James, wadda bamu da su a nan" To Imran ya ce tare da komawa saman bedside drawer ya zauna yana sauke ajiyar zuciya, shi kuma Lion ya shige wanka.
A ɓangaren Jehan kuwa
Suna zaune shiru saman bed ɗin nan na Adiva, duk jininsu a sake, Adiva tana ji kamar ta je ta kwace Maryam a hannun Mutumin nan, amma ba hali, ita kuma Jehan ta yi shiru tana ambato sunan Allah a zuciyarta, kuma da alama ta fara nasara, dan kamar turaren Zinariya ya fara sakinta, yayin da shi kuma wancan ɗan iskan Alhajin ya shiga da Maryam cikin ɗaya daga cikin ɗakuna uku dake a cikin palon, kuma kusa da shi.
Sai tunani Jehan take yadda zata ceci Maryam, domin zuciyarta ba zata iya jurewa, Maryam ta sha gwagwarmaya wajen kula da mutuncinta, ta wahala sosai yarinyar nan, kamata ya yi ta kai wa mijinta wannan mutuncin nata.
Almost 5mins suna zaune a haka, can kuma kamar an sikari Jehan ta diro kasa daga saman gadon, sauri-sauri ta ce "Adiva where is your phone?" Da sauri Adiva ta miƙa mata wayar, karɓa ta yi ta nufi waje da sauri.
"Jehan where are you going?" Cewar Adiva ɗin, ta yi maganar kusan a tare da A'isha, sai dai ita A'isha da hausa ta yi tambayar.
"Adiva follow me, come and show me the room that you went to". Da sauri Adiva ta diro kasa ita ma, dan tun da ta ji Jehan ta ce hakan sai ta samu karfi, kuma ta san cewa Jehan ɗin ta tuna wata hanya ce da za su ceci Maryam.
A'isha kam gyara kwanciyarta ta yi domin tana tsoron bala'in Hajiyar daɗi, kuma da alama ita turaren Zinariya bai sake ta ba.
Suna shiga Palo Adiva ta ce da Jehan nan ne wajen da suka zo, sun kuma yi sa'a har suka zo ban ba wanda ya gansu a cikin gidan, kowa yana ɗakinsa, haka su Zinariya ma, suna office nasu.
"Adiva there are many rooms in this palour which one have they enter?" Shiru Adiva ta ɗan yi kafin ta ce "I don't know, because mu a nan palon muka barsu". Jinjina kai Jehan ta yi tana faɗin "Okey go back to our room am coming". To Adiva ta amsa da shi, sannan ta nufi bakin kofar Palon.
Har zata fita sai kuma ta juyo, murya a raunace ta ce "Jehan please kada ki yi wani abin da zai sanya a raba ni da ke, ke kaɗai ke gareni yanzu, sannan dan Allah kada ki yi abin da zai ja wo maki wata matsala, ki kula mana da kanki dan Allah ko dan saboda su Rimsha, suna buƙatar ki". Ba tare da ta yi magana ba kawai ta mata alama da hanu akan ta tafi dan ta jiyo shessheƙar kukar Maryam a cikin ɗakin dake bayanta.
Ba musu Adiva ta wuce, tana addu'ar Allah ya sanya kada wani abin ya sami Jehan ɗin.
A zafafe Jehan ta nufi ɗakin da take ji yo kukukan Maryam ɗin kasa-kasa, a bakin kofar ta tsaya ta kunna Cameran wayar Adiva dake a hannunta sannan ta saita video record, tana saitawa kai tsaye ta afka cikin ɗakin ba ko sallama, ta kuwa yi Sa'a kofar a buɗe ba su sanya key ba.
Yau taga tashin hankali iya ganin idonta, amma da yake, dan ceto ta zo sai ta daure ta kawar da kanta, ta ruƙe wayar ta yadda ba zai gane Video take yi mashi ba.
Lokacin da ta kutsa cikin ɗakin, a zafafe Alhajin nan ya ɗago sirara haihuwar uwarsa, ga shi ɗan baki da shi kamar zunubi, wannan shine tashin hankali da Jehan ta gani, babbar nasarar da ta yi kuma shine juyo da face nashi da ya yi dan ya kalli waye ya buɗe mashi kofar, ta yi nasarar ɗaukar fuskarsa karara a jikin wayar Adiva da ta kunnawa Camera, ga shi kuma yana tsirara, abin ya bata yadda take so.
"Ke lafiya kika shigo mana ɗaki?" Ya yi Maganar har lokacin bai sauƙa daga kan Maryam ba, dama Jehan na gaf da shikowa shi kuma ya hau kanta yana kokarin shigarta.
Cikin dakiya Jehan ta ce "Magana nake son yi da kai". Ɗaukar bargon da suke ɗaurawa a saman bed ɗin ya yi, ya ɗan rufe jikinsa ya miƙe cikin fushi ya fara masifa "Ke mahaukaciyar ina ce? Kin taɓa gani an shigowa mutun ɗaki haka?..." Katse shi ta yi da cewa "Ɗakin ka ko dai ɗakin gidar Hakiyar daɗi, ko ma dai ace hotel".
Tsawa ya daka mata "Idan ma ɗakin waye ba dai kuɗi na biya dan na biya buƙata ta ba? Dan haka ki fita a ɗakin nan ko kuma na haɗa dake!!" Karo na farko a rayuwar ta da ta saki kayatatcen murmushi, sannan ta ɗago mashi da wayar daga irin riƙon da ta yi mashi na karya gane, tun da ta sami abin da take so, ya amsa da bakinsa cewa e ya zo gidan Hakiyar daɗi biyan buƙatarsa da ƴaƴan mutane, sai ta ɗaga mashi wayar dan ya gani, a sukawane ya fara ɓoye fuska tare da yin yunkurin kamata, a guje ta yi waje.
Cikin matsanancin tashin hankali ya zura jomparsa ya bi yo bayanta, tana tsaye a palon tana jiran fitowarsa, dan suyi ta ta kare a nan.
Yana fitowa ta kara waya a kunne cike da izza ta fara wayar karya "Hello Rimsha akwai Video da na tura maki yanzu, ki yi download na shi ki ɓoye a wajen sirri, idan kin ji wani abin ya same ni to ki saki video wa duniya, kuma kafin nan ki turawa gwaggo ma ta ajiye dan kada mu sami wata matsala, ni yanzu zan goge WhatsApp ɗin gaba ɗaya ki yi maza ki ɗauki video....." Bata kai karshen maganar ba ta watsa da gudu zuwa bayan kujera, ta yi hakan ne kuma sakamakon ganin da ta yi Alhajin ya nufota da nufin ya kwace wayar.
Cire wayar ta yi daga kunnenta, tana yi mashi kallon wulakanci ka fin ta ce "Kai, na fika tantiranci wlh, ko ka tsaya mu yi maganar mutunci ko kuma wlh ka san saura ba sai na gaya naka ba".
Ya shiga tashin hankali iya tashin hankali, ya yi danasanin zuwansa gidan Hajiyar daɗi yau, har wani jiri yake ji, ya ma rasa ya akayi bai kulle kofar ɗakin nasu ba. Ni kuwa nace ikon Allah ne yasa baka kulle ƙofar ba, mugu, Allah ya yi ba zaka lallata yar mutane ba, an gaya maka Ubangijin na barci ne? To idan ma kana tunanin haka sai ka farka yanzu, Allah ne ya ceci Maryam ta sanadiyar Jehan ba kowa ba, bakin azzalumi, ka killace ƴaƴan ka a gida ka lallaɓo nan dan lalata ƴaƴan wasu dan jaraba, da sannu Allah zai yi maganinku gaba ɗaya.
Rai a matukar ɓace ya ce "To me kike so na baki ki goge video nan?" Shiru ta ɗan yi na yan mintoci ka fin ta ce "Na san halinku manyan nan, ina jin daddyna yana faɗa, zaku iya sawa a kashe mutun ko a ɓatar da shi ba? Shiyasa na turawa mutane na video, kuma yanzu a gabanka ma zan goge number kowa dake a wayar, zan yi formating na wayar baki ɗayar ta, amma dai ka sani idan wani abin ya same mu wlh zaka tsinci wannan video a media kamar yadda ka ji da kunnenka na gayawa yan uwana, haka zaka ganshi a Media ka rasa ta ina ya fito, kuma idan ma kayi maganar da wayan dake a gidan nan, ka ce ga abin da na yi maka, nan ma zaka ganka a media tsirara, to gara maka ma ka natsu, ni ba wani abin nake so ba fa ce ka rabu da Maryam ka wuce ka tafi salin alum, kuma kada ka sake dawowa gidan nan, kada na sake yin ido huɗu da kai, idan kuma ka bari muka sake yin ido huɗu, to ba sai na yi magana ba!!!".
Zai yi magana sai ga Zinariya ta zo wucewa "Ke Jehan me kike yi a nan kuma?" Cewar Zinariyar kenan.
Jehan na ƙoƙarin yin magana Alhajin ya ce "A'a Zinariya ni na saka aka kirata, magana muke yi" cikin sauri Zinariya ta ce "Haba Alhaji wannan fa ajiyar wani ce, wani ne ya yi bukkin nata, shiyasa Hajiya ta ce abarta sai ya dawo baya nan yana England, dan Allah ka yi hakuri ka bar ta, ba ga wata ka zaɓa ba, ko baka zaɓi ko ɗaya bane?"
"A'a na zaɓa har ma na gama abin da zan yi, ita dai wannan magana kawai muke yi da ita, ba wani abin bane, yanzu kuma zan tafi ma, ke baki ga ma a palo muke yin maganar bane? So ba wani abu kada ki damu" jinjina kai ta yi tana faɗin "To dai ku yi sauri Jehan ta koma ɗaki, dan hanjiya ta ce ko waje kada ta fito, amma idan wani kyauta zaka bata ai kamata ya yi mu zaka kawowa ko? Ko ka mancen yadda tsarin gidan yake ne? Ai kai iyaka kawai ka zaɓi mace, mu gaya maka farashi ka biyamu ka shiga da ita ciki, ka mance ba'a bawa yaran kuɗi a hannunsu ne?"
"Sorry Zinariya na mance ne, kin san yarinyar da na zaɓa ne ta bani labarin wannan ɗin ta ce ai tana da kirki, shine dama ne ce bari na yi mata kyauta akira mani ita, amma ba komai zan kawo maki kyautar office naki kafin na wuce" ta ji kuɗi sai bata tsawaita magana ba sai ta ce to, ta wuce bata kawo komai a ranta ba, dan alhazawan sun saba yin haka, idan sun zo suka ji yarinya ta yi masu daɗi suna yi masu kyauta sosai, kuma ba su kaɗai ba har da sauran yaran dake a ɗakin gaba ɗaya, amma kyautar office ɗin Haniyar daɗi ake kaiwa, idan bata nan kuma zinariya ta karɓa, basa yarda abawa yaran kuɗi, sannan kuma da kuɗin take yin amfani ta sayawa yaran kayan sawa da kuma kayan mata sosai da sosai, ta yi ta ɗirkawa yara abubuwa, idan ta ga yarinya bata cika yadda ake so ba, har alluran shakafashe tana sawa ayi masu, wasu kuma alluran breast or hips, idan alluran ya tashi sai ya yi masu illa a jiki, idan suka sami wata matsala a gefen titi hajiya take sawa a je a jefar da su, idan kuma yarinya aka samu akasi ta yi ciki, zubarwa ake yi, wata daga haka take mutuwa!!.
Zinariya na barin wajen Maryam ta fito sanye da kayanta Baiwar Allah jikinta sai kerma yake yi, da sauri ta nufi wajen da Jehan ke tsaye.
Rungumeta Jehan ta yi tana mai kara yi wa wannan Alhajin kashedi, sosai Alhajin ya sha jinin jikinsa domin kwata-kwata bai ga alamar tsoro a kan fuskar Jehan ba bare ya ce zai zare mata ido ko ya yi mata barazana, idonta a bushe yake tana tsaye cikin dakiya tamkar wata jarumar sojan yaki, amma a zahirin gaskiya a cikin zuciyarta sai tariyo abin da ta gani ƙwaƙwalwar ta ke yi mata, abin ya ɗaya mata hankali sosai, wannan wace iriyar jarabawa ce, Allah ka sa mu cinye wannan jarabawar, abin da take faɗe kenan a cikin zuciyar ta.
Riƙo hannun Maryam ta yi suka bar palon suka nufi ɗakinsu suka barshi a nan tsaye yana tsaka da warwara a cikin zuciyarsa.
Suna shiga cikin ɗakin da gudu Adiva ta taso ta kariso wajen su tana faɗin "Jehan ba abin da ya same ki ko?" Gyaɗa mata kai Jehan ta yi tana faɗin "Babu komai Adiva yanzu dai ki raka Maryam bayi ta yi wanka dan naga jikinta sai kerma yake yi, ba zata iya