Showing 12001 words to 15000 words out of 355604 words

Chapter 5 - Triplets Book 2 Hausa Novel Complete

10 Dec 2024

2735

da gaske, dan haka ba musu tabi bayan sa, tana turo baki.

Allah sarki Akila baiwar Allah mai kaunar yan uwan ta, taso su fahimci Juna da Aafia amma abun bai samu ba, Aafia akoi ta da ji da kai, da nuna isa da izza.

Kai tsaye gida Akil ya kai ta da motar sa, kuma da kan sa ya tuka, sai dai ko da suka je gate ɗin gidan, shi bai shiga ba, a kofar gida ya sauƙe ta, ya juya kan motar sa zuwa gida.

Cikin gida ta wuce tana rakuɓe rakuɓe, tana addu'ar Allah yasa daddyn Jelly baya palo, dan idan ya kalle ta da kayan jikin tan nan akoi matsala ba kaɗan ba.

Tayi Sa'a kuwa daddy baya palon, cikin sauri ta wuce ta haye sama ta nufi bedroom nasu.Tana shiga ta cire kayan jikin ta ta faɗa toilet dan yin wanka.

Bayan tayi wanka ta fito, ta shirya cikin atamfa riga da skit kayan sun kama ta sosai, ta ɗauki after dress ta ɗaura saman kayan nata, ta fito palon kasa hannun ta riƙe da maganin da Rufee ta bata, dan ta zubawa Aunty a abinci, taci cikin jikin ta ya zube.

Shiru palon kasan babu kowa, ga kuma abinci saman table an geresu, sauri sauri ta nufi table ɗin, kulan miya ta buɗe ta zuba maganin a ciki tare da gauraya miyar sannan ta rufe, tana tunanin anya idan su Abbi suka ci maganain nan ba zai musu illa ba kuwa, gashi kuma bata da wata hanya da zata sa Aunty taci maganain nan dole dai sai dai ta zuba a kulan miyar gaba ɗaya, shiyasa ta zuba, kuma ta dawo tana danasani kar su Abbi suci maganin ya zamo musu illah.

Tayi nisa cikin tunanin da take, sai ji tayi Aunty nace mata "Aafia lafiya?" Yar firgigit tayi irin na marasa gaskiya.
Ganin Aunty ne yasa taja dogon tsaki tare da wuce wa, ta bar wajen, ta koma saman sofa ta zauna, Aunty kuwa baiwar Allah bata kawo komai a ran taba, tayi tunanin ma ko yinwa Aafia take ji ne yasa tazo wajen table ɗin, shiyasa ma ta tambaye ta ko lafiya.

Dai dai lokacin daddyn Jelly ya shigo palon shirye cikin wata dakakkiyar shadda fara tas ɗinkin full jompa, yayi kyau sosai, ɗan zaman sa a gidan har ya fara murmurewa.

Har kasa Aunty ta tsuguna ta gaishe shi, da fara'a ya amsa tare da ce mata "Zan fita kila yaya ya rigani dawowa, idan ya dawo ki sanar da shi na fita, ganin gari shine abun da ya shigo dani part naku" cikin girmamawa Aunty ta amsa masa da to, ita kuwa Aafia ko ajikin ta kamar bata gan shi ba, sai faman tura baki take, wucewa yayi ya fice daga palon, dan tun da suka nuna masa basa son shi a gidan ya daina shiga harkan su, idan sun masa magana fine ya amsa, idan kuma basu masa magana ba shima baya kula su, dan baya son raini ko kaɗan, ko part nasu bai cika shigowa ba, sai dai idan Abbi yana nan, sai ya shigo palo suyi hira, Abbi na fita shima zai fice ya koma part na shi, wato ɓangaren Irfan kenan.

Bayan daddy ya fitane Aunty ta duɓi Aafia tace "Aafia me yasa zaku rinƙa yiwa kanin mahaifin ku haka? Babu kyau abun da kuke yi fa, ya kamata ku gyara kuyiwa kan ku faɗa domin baku san me gobe zata haifar ba, kuma kuna sane da tashin hankali da bawan Allah nan yake ciki, kamata yayi ku jashi a jiki dan ku ɗebe masa kewar rashin Jalila a tattare da shi, sannan kuma shima fa a matsayin mahaifi yake a gare ku ida.... Bata kai karshen maganar ba Aafia ta daga mata tsawa "Ke dallah kima mutane shiru, ina ruwan ki da rayuwar mu? Ba dai kanin mahaifin mu bane? Ai ba kanin tsohon ki bane, to dan haka ki shiga hankalin ki, ina buga miki last warning da babban murya, idan kika sake shiga harkana, wlh sai na miki illa, wawuya kawai yar datti!!" rai a matukar ɓace Aunty tace "Ke Aafia ina son ki shiga hankalin ki, ya issheki haka nan, ya isheki cin mutunci na a gidan nan in kyaleki, na gaji, wlh idan kika sake faɗa min wata maganar banza idan ranki yayi dubu sai na ɓata miki shi"

Miƙewa tsaye Aafia tayi tana faɗin "Eyee a lallai yar talakawa kin sha jar miya, har ni kike wa last warning kenan, to wlh baki isa ba, in dai ni Aafia na haifu sai kin bar gidan nan yau!!" guntun tsaki Aunty taja kafin tace "To sai me? Dan na bar gidan ku sai me? Mutuwa zan yi ne dan na bargidan, ko kuma a'a aljanna ce ba zan samu ba idan na bar gidan, ai wlh da zaman wannan gidan naku gara mutun ya tabbata a gidan uban sa, yan iskan yara mara sa hankali, marasa tarbiyya, ku daga gani wlh uwarku ba hausa fulani bace , dan wanna bakin halin naku bayyi kala da na mu ba, amma ni ina mai baku shawara wlh kubi duniya a sannu, idan ba haka ba, watara na sai kunyi nadamar zuwan ta, ku mata ne, baku san ina aure zai kai ku ba"

Rai a matukar ɓace Aafia ta nufi Aunty da niyar ta mare ta, cak Aunty ta riƙe hannun ta, yau fa hakurin mai hakuri ya kare, daman ance mai hakuri bai iya fushi ba, to wanna ma hake ne

Wanke ta da wawan mari Aunty tayi a fuska, tare da daka mata tsawa "Dan baki da hankali sai kiyi yunkurin saka hannun ki a jikin mahaifiyar ki, matar baban ki?!!" tashin hankali Aunty fa ta fusata.
Kokarin kwace hannun ta Aafia take daga riƙon da Aunty ta mata dan ta rama marin ta da aunty tayi, tureta aunty tayi ta faɗa sama sofa, sanna ta wuce da sauri ta haye sama abun ta, dan bata son tsayawa tayi faɗa da Aafia, yin hakan zubar da kai ne, sai dai kuma Aafia tana da burin hakan ko dan ta daki Aunty a ciki.

Da gudu Aafia ta miƙe tabi aunty sama, sai dai kafin ta iso Aunty ta shige bedroom nata tare da murzawa kofar ta key, haushi kamar Aafia ta fasa ihu, kafa tasa ta shuri kofar da karfi sannan tace "Zaki fito ai, wlh sai kin yabawa aya zaƙin ta a gidan nan" hayewa saman gadon ta aunty tayi abun ta, ta kwanta tana mai jin bakin cikin abun da yake faruwa a gidan nan, Aafia ta kureta, ta kai ta bango, taso suyi zaman lafiya amma abun ya faskara, ba yadda za tayi dole ta fito ta karɓawa kan ta yanci kawai dan ta samu zaman lafiya kuma ta samawa ɗan da zata haifa ko ƴa yancin kan su a gidan baban su.

Aafi kuwa palo ta koma tana ta surfa ruwan bala'i a kan aunty zata fito ta same ta, ba zata kyale taɓa.

A ɓangaren Umaisha kuma, da zazzaɓi mai zafi ta tashi tare da kuka, lokacin ana kiraye kirayen sallar mangariba, Akil baya nan, ya tafi kai Aafia gida bai kai ga dawowa ba, ya wuce masallaci daga nan.

Jin kukan Umaisha yasa Akila ta tashi ta nufi part ɗin Akil, lokacin Ammie ta bar palon ta koma bedroom nata, shi kuma Abba ya wuce masallaci.

Tana shiga bedroom ɗin ta haye saman gadon kusa da Umaisha tana faɗin "Umaisha lafiya? Me ya same ki kike kuka? Ko dai yaya Akil ya miki wani abu ne? Ko kina son komawa gida ne?" Kuka kawai Umaisha keyi, bata samu damar samun bakin magana ba "Dan Allah akila kiyi shiru kinji? Tun ɗazun fa nake ta murna ina jiran ki tashi daga barci muyi hira, tun da na dawo school yaya Akil ya sanar min ya ɗauko ki, kuma ke yanzu matar sace, sai murna nake tayi, ina fatan ki tashi daga barci muyi hira, amma shi ne kuma zaki tashi kina kuka? Dan Allah ki dai na kuka ki faɗa min, idan ma yaya Akil ne ya miki wani abun to yanzu zan kira yaya Imran a waya na faɗa masa, kuma zai rama miƙi, dan yaya Imran yana da adalci" nan ma Umaisha bata kula taba, ci-gaba da kukan ta tayi kawai, ita ka ɗai tasan me take ji a jikin ta, ganin haka yasa Akila ta sauƙo daga gadon, ta fice daga ɗakin da sauri, ta nufi bedroom ɗin Ammie.

Zaune bakin gado ta samu Ammie, da sauri ta tafi ta faɗa jikin ta tana faɗin "Ammie dan Allah kizo ki lallaɓa Umaisha tayi shiru, sai kuka take taki yin shiru, ban sane me ya same taba" guntun tsaki Ammie taja kafin tace "Kije kice mata, ta tashi ta tafi gidan su tun kafin nazo na same ta a wajen" zaro ido Akila tayi tare da turo baki tace "Haba Ammie yaya Akil fa yace matar sa ce, to ya za'ayi kuma ta tafi gida?" "Waye yace miki matar sace? Ba matar sa bace, shi ba ajin irin wayan nan yaran bane, ki tashi kije ki ce mata ta wuce ta tafi gida tun kafin nazo na karya ta, dan haushin suma nake ji gaba ɗaya" Kukan shagwaɓa Akila tasawa Ammie, tana ɗan bubbuga kafar ta a jikin gadon tana faɗin "Haba Ammie, to ai ko ba matar yaya Akil bane yar uwar mu ce, kinga kuwa zata iya zama a gidan nan" Jin Akila tace yar uwan suce yasa Hajiya ta miƙe a fusace ta fito ta nufi part ɗin Akil. Da sauri Akila ta miƙe tabi bayan ta

Kamar yadda Akila ta bar Umaisha haka Ammie ta shigo ta same ta, tsawa ta daka mata "Ke tashi ki wuce gidan uban ki, ban son munafurcin banza" shiru Umaisha tayi bata amsa mata ba, kukan ta kawai take.

A fusace Ammie ta haye saman gadon tare da yaye bargon da Umaisha ke lulluɓe, ta riƙon ta, ta miƙar da ita tsaye tana faɗin "To wuce a kai kaya ma sauki" kasa tsayuwa Umaisha tayi, Ammie na sake ta, ta zube a kan gadon tare da kara sautin kukan nata, daidai lokacin Akila ta shigo ɗakin, kamar zatayi kuka tace

"Ammie dan Allah kiyi hakuri ki barta kinji?" Ammie bata kula taba, sai ma kara mikar da Umaisha tayi, ta jata, sai kokarin faɗuwa kasa Umaisha take saboda jikin ta ba kwari, kuma ba zata iya taka kafar ta ba, saboda azaban da take ji, sai kukan wahala take abun gwanin ban tausayi.

Kai tsaye waje Ammie ta nufa da ita, tana jan ta kamar wata rago, sai kuka Akila take tana addu'ar Allah ya kawo yaya Akil ko Abba.

Ammie tana zuwa bakin kofar Palo, ta tura Umaisha waje tana faɗin "Kar na sake ganin kafar ki a gidan nan" tana turata ta tafi sai saman kirjin Akil ta faɗa, yanzu ya dawo daga masallaci yana kokarin shigowa kenan

Umaisha na kokarin sulalewa kasa daga kirjin nasa, yayi saurin riƙota yana kallon Ammie dake tsaye a bakin kofa tana kallon sa

Kasa tsayuwa Umaisha tayi dan kafar ta babu kwari, sai kerma jikin ta keyi, dawo da kallon sa kan fuskar Umaisha ɗin yayi, kasa kasa yace "I'm so so sorry" ya kai karshen maganar tare da ɗaukan ta cak, ya juya ya bar wajen, ya nufi motar sa da ita ba tare da yace da Ammie ko uppan ba, dan baya son jan magana da ita a kan Umaisha, yasan halinta sarai zata iya yi masa baki a kan hakan, ta raba shi da Umaisha, shiyasa baya son maganar Umaisha ta haɗa su

juyawa ita ma Ammie tayi ta koma cikin Palo, tana jan guntun tsaki, a tunanin ta Akil zai mai da Umaisha gida ne. Ita kuma Akila tana ɗakin Akil tana kukan ta.

Kai tsaye asibiti Akil ya wuce da Umaisha dan yaji jikin ta da zafi sosai, yan gwaje gwaje aka mata, sannan aka basu bagunguna, ya ɗauko ta suka dawo gida.

A palo ya samu Ammie da Akila suna zaune, Abba bai dawo ba, bai yiwa kowa magana ba, ya wuce ya nufi ɗakin sa, "Akil kazo ka ci abinci" cewar Ammie, a takaice yace "Bana ci, na ƙoshi" yayi maganar ba tare da ya tsaya daga tafiyar da yake ba, "Ka fitar da yarinyar nan daga gidan nan nace ko?" Ammie ta sake yi masa magana, shiru yayi bai tanka ba, ya wuce bedroom nasa.

Saman gado ya kwantar da Umaisha, wadda take fitar da numfashi da kyar saboda wahala, bargo yaja ya rufa mata sanna ya fice ya dawo palon

Kusa da Ammie ya zauna yana faɗin "Ammie me yasa yanzu baki son farinciki nane ne? Me na miki? So kike na mutu ne eh Ammie na?" Zaro ido tayi kafin tace "Haba Akil kasan me kake faɗe kuwa? Nice bana son ka? Idan ni bana son farincikin ka waye kake tunanin zai so farincikin ka?" Kallon Akila dake zaune tayi shiru tana tunani, tasha kuka ta koshi, dan ita a tunanin ta Ammie ta kori Umaisha ɗin ce

"Heartbeat tashi kije ɗaki bari muyi magana" Akil ya faɗa yana tsare Akila da ido, tun bai kai karshen maganar ba ta miƙe ta wuce bedroom nasa wajen Umaisha, dan bata da burin da ya wuce ta gan ta tare da yan uwan ta.

Dawo da kallon sa yayi kan Ammie cikin nitsuwa yace "Ammie na faɗa miki ina son matata, kuma ita ce farinciki na, me yasa baki son hakan? Me ta miƙi? Na san bai wuce kice abun da ya faru tsakanin ku da baban ta, da kuma su bappa Husaini bane, to ita me nata a ciki, kinga ai ita bata san komai ba, kuma da wuya ma idan ta san labarin abun da ya faru kafin a haife mu, dan Allah Ammie ina son kiyi min wannan alfarma, ki yafe wa family'n Abbana komai ya wuce kinji ko?" Ya kai karshen maganar tare da riƙo hannun ta yana kallon cikin idon ta "Akil, Akil, Akil, sau nawa na kira sunan ka?" Shiru yayi yana kallon ta

"Ba zaka bani amsa ba, nace sau nawa na kira sunan ka?" "Sau uku kika kirani Ammie" ya bata amsa, "To wlh ka fita ido na, karka sake min maganar su Hussaini a gidan nan, ita kuma yarinyar tun da kace ita kake so, kaje kai kasani da ita can, in dai family'n Abban kane da kan ka ma zaka guje su ba sai wani yace ka barsu ba" murmushi yayi kafin yace "Shikenan Ammie in dai kin yarda na zauna da ita shikenan ba damuwa ai" kawar da zancen tayi da cewa "To ka tashi ka ɗauko abinci ka kaci" to kawai ya amsa da shi tare da miƙewa ya nufi saman table ya ɗauki abinci kula ɗaya da plate ɗaya tare da spoon shima ɗaya, ya wuce bedroom na sa, binshi da kallo Ammie tayi, kasa kasa tace "Ba zan taɓa bari ka zauna da yarinyar nan ba, dan bana son ta, kuma bana kaunar iyayen ta, dole ka rabu da ita"

Da sallama ɗauke a bakin sa ya shiga cikin bedroom na sa, Akila na zaune saman gado tana rarrashin Umaisha dake ta faman kuka har lokacin.

"Heartbeat ɗauko min Yoghurt a Palo" turo baki Akila tayi kafin tace "Yaya Akil ba haka zaka ce ba, kace Heartbeat tashi ki fita min a ɗaki" murmushin yayi kafin yace "Ni na isa in ce ki fita min a ɗaki ne? Yoghurt fa kawai nace ki ɗauko min" "Yaya Akil yaushe ka fara shan Yoghurt ban sani ba? Kai da ko tea da madara baka sha saboda karni shine yau zakace na ɗauko maka Yoghurt, na sani ba wani Yoghurt kawai korata kake yi" ɗaga mata gera ɗaya yayi yana faɗin "To tun da kin gane me kika tsaya yi ware da wuri" dariya tayi tana faɗin "Ba damuwa yaya Imran ya kusa dawowa ai, idan ya dawo ba zan sake zuwa nan ba, kuma shi nasan ko ya auri Aunty jelly ba zai koreni a ɗakin saba" "oho dai tashi ki tafi" yayi maganar yana kokarin hawa saman gadon, bayan ya ajiye musu abincin su saman table dake cikin ɗakin,
Da sauri Akila ta diro kasa daga saman gadon tana faɗin "Aunty Umaisha Amarya sai da safe, yaya Akil mun ɓata da kai" shiru ya mata, dan bai son biye mata, so yake ta fita ta basu waje.

Tana fita ya sanya hannun sa ya tallaɓo Umaisha yana faɗin "Sorry tashi kici abinci kisha magani" cikin kuka tace "Na koshi" girgiza kai yayi yana faɗin "a'a ban yarda ba ki tashi kici" ba dan taso ba, haka ya miƙar da ita zaune ya rinƙa ɗura mata abinci tana ci dan dole

Bayan ta gama ya bata ruwa ta sha, sannan ya mai da ita ya kwanta, ya sauƙo ya wuce toilet dan yayi wanka yazo ya gabatar da sallar issha da bai samu yayi ba, sakamakon kai ta asibiti da yayi.

Bayan yayi Sallah ne ya haye gadon kusa da ita ya kwanta, yana faɗin "I'm sorry kinji?" Shiru ta masa ba tayi magana ba na ɗan lokacin kafin tace "Ka mai dani gida kada Abbi ya neme ni" juyo da kallon sa yayi kan fuskar ta "Already na kira bappa a waya na sanar masa da nazo na ɗauke ki daga school kina tare dani" mamaki ne ya kamata tace "Abbi na fa wanda ya haifeni" ya gane me take yiwa mamaki, wato ya za'ayi Abbi ya yerda ya ɗauke ta su tafi su kwana, bayan ba aure sukayi ba, shine abun ya kulle mata kai

"Eh Abbin maki fa, bakin san cewa ke matata bace ko?" Shiru ta zuba masa ido tana kallon sa "To ki rufe idon ki ya isa haka kallon nawa, karki haifa mana baby mai kama dani, zai fi kyau ki haifi mai kama dake, kiyi barci da safe zamuyi magana" ya kai karshen maganar tare da sanya hannun sa ya rufe mata ido, mamaki ya hana ta magana ta kwanta shiru, da haka barci ya ɗauke ta.

Shima shiru y kwanta har barci ya ɗauke sa. Ammi kuma tana can


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login