Showing 330001 words to 333000 words out of 355604 words

Chapter 111 - Triplets Book 2 Hausa Novel Complete

10 Dec 2024

2791

sauke kafin nan ya ɗauki kiran. Yau karo na farko daya ɗan zaro ido lokacin da ya ɗauki kira Aseef. Kayatatcen murmushi ne ɗauka akan fuskar Aseef ɗin yayin da kuma ya zaro brown eyes nasa tamkar yana kallon wani abin, Lion ya san me yake yi mawa, shiyasa shima ya zare mashi ido sai su zama iri ɗaya kawai.

Shiru Lion bai yi magana ba yayin da shi kuma Aseef yake zaune a saman bed nasa daga shi sai shot jikinsa babu riga, wata iriyar gashi ne mai bala'i kyau ga tsantsi kwance a saman faffaɗar kirjin nasa, shima dai breast ɗin nasa tamkar na ƴan uwan nasa ne, bul bul da su.

Kallo ɗaya Lion ya yi mashi sannan ya kawar da kansa gefe yana tunanin shi kuma Aseef me ya je ya jajuɓo masu, domin daga ganinsa akwai wata a ƙasa, dama kuma shi ɗan nema ne, ya iya rigima idan aka taɓa shi.

"Lion please and please smile now, smile for me even for one time in my life". Ya faɗa yana kara faɗaɗa murmushin nasa.

Lion yana ƙoƙarin kunna laptop nasa, ba tare da kalli Aseef ɗin ba ya ce "What is smile?". Aseef bai yi mamaki ba dan Lion ya ce bai san menene murmushi ba, domin kuwa tun da suka girma suka yi wayo, bai taɓa ganin koda makamancin murmushi komai kankantarta akan fuskar Lion ba, kullun fuskarsa a yanayi ɗaya take, wato a fusace, a ɗaure kamar hadari.

"My lion look at my face, look at the way am smiling, to haka zaka yi, I'm very sure idan ka yi murmushi or dariya idan a kusa da mutane kake to ba za'a rasa waƴan da za su suma ba saboda kyan ka, please maybe ma nima zan iya suma saboda kyanka, ni nama rasa ya zanyi, kwata kwata even your teeth ban taɓa gani a waje ba, idan zaka yi magana baka buɗe baki sosai bare mutun ya ga hakwaranka, sai dai ka yi maganar da wani ma zai ce baka motsa Lips naka ba, anya kuwa ma kana da hakwara kuwa? Sannan anya kana da harshe ma kuwa?". Ya kai karshen maganar tare da ɗaga kai sama kamar mai tunani.

A zahirin gaskiya wannan magana da Aseef ya yi ta karshe na cewa ko Lion yana da hakwara da harshe, ya yi tane da sa ran ko Lion zai yi murmushi, da gangan ya yi, amma ina sai ya ga akasin haka, kuma gaskiyar Aseef ne ko hakwaran Lion ba su gani a waje, domin idan zai yi magana ba zaka taɓa cewa ma yana motsa lips nasa ba, saboda kasa kasa yake fitar da words, hakwara ma ba su gani bare kuma murmushi, da girmansu da wayonsu dai bai taɓa makamancin murmushi ba, wata kila da suna yara sun yi, kun dai ji yanzu shi bai ma san me murmushi ba. Lion duniya ne gaskiya wai

"Aseef what is going on on your side?" Shi ne abin da Lion ya faɗa, "Lion wai yanzu da gaske ba zaka yi murmushi ba? Wlh ina matukar so na ga murmushi kane fa".

Sai lokacin ya dawo da kallonsa kan wayar tasa. "Aseef i said what is smile?".

Ɗan turo baki ya yi yau ya tuna da shagwaɓa ta baya, "Kai Lion ai na ce maka ga shi nan akan face na ina yi ko?, to kamar haka zaka yi mani".

"Aseef i don't know how to do this nonsense, cox idan ba ka kyaleni da shirmen nan naka ba i will going to block your number, because I don't have time for nonsense, ko wani 1 second in my life yana cikin lissafi, so ka kyaleni".

Shiru Aseef ya yi dama ya san Lion ba zai taɓa yin murmushin ba bare kuma dariya, shi haka yake kullun, su kuma suna son ganin ace yau ga shi koda ɗan murmushi ne ya yi wadda zai sanya kyawawan hakwaransa bayyana, amma ina abin ya faskara.

Haka Aseef ba dan ya so ba ya kyale zancen murmushin ya ɗauko wata hirar dan ya sanya ɗan uwan nasa farinciki.

A ɓangaren Imran kuwa, bedroom nasa ya wuce da Rimsha, yau ba dan jinin Hajiya Umaiya ne yake gudu a jikinsa ba, to da tabbas da wuya ya yi rai, dan saboda ba iya wurgi da shi kawai Areef ya yi niyar ya yi ba, sun yi niyar shan nasa jinin shima, Allah dai ya tsare shi ne kawai ta dalilin mamarsa.

Saman bed ya kwantar da Rimshan tare da kwanciya a gefenta yana mai da numfashi.

Kwanciyar 5 mins ya yi kafin ya samu da kyar ya yunkura ya miƙe ya nufi toilet.

A gurguje ya yi wanka dan ya ɗan sami karfi, shiryawa ya yi cikin kananan kaya sannan ya ɗauki Rimsha suka wuce hospital dan a duba lafiyarta.

Sun yi sa'a Baiwar Allah da suka je asibiti ba wata babbar matsala ta samu ba, kawai shakar ne da aka yi mata ta ji wuya, bayan haka ba su taɓa wani abin na daga halittarta ko wani cutar wa ba, sosai Imran ya ji daɗi da jin hakan.

A ɓangaren JELLY kuwa, tana baro part ɗin su Irfan garden ta nufa, da yake garden ɗin yana ta gefen part ɗin su Abbin ne. Saman ɗaya daga cikin kujerun dake a wajen ta yi zaman minti 20 kafin ta miƙe ta nufi cikin gida.

Kamar yadda ta bar su daddy haka ta koma ta samesu, jikin daddy ta je ta haye tare da fara kuka.

Abbi duk ya rikice da ganin kukar tata, nan take ya fara tambayarta me ya faru, waye ya taɓa ta, amma saboda iskanci irin nata ko sannu ba wanda ta ce wa, shi dai daddy yanzu yana nadamar abubuwa da dama da ya rinƙa barinta tana yi time da take karama, bai taɓa zaton zata girma tana yin abin ba, ciki kuma har da shagwaɓa da kuma kuka babu dalili, dan jelly idan tsiyarta ta motsa haka kawai zata zauna ta yi ta kuka kamar wadda ta rasa iyayenta, sai ta yi mai isarta sannan ta yi shiru, ga shi bata jin rarrashi ko kaɗan, idan ta fara to sai ta kai in da take bukatar tsayawa, sannan ta tsaya.

A yanzu ma haka ne, sai tambayarta gaba ɗaya jama'ar palon suke yi, duk sun taru a kanta, amma taki cewa kowa ko sannu, abin ya ɗaga masu hankali sosai, sun rikice kada wani abin ne ya faru, amma saboda iskanci irin na Jelly taki ciresu a duhu, ta kyale su sai bugawa zuciyarsu take yi, Akil kam har da zuwa ya duba waje ko zai ga wani abin da ya sanya ta kuka tun da daga wajen ta fito, kuma dai shima daga wajen ya dawo yanzu ba daɗe wa, shi bai ga komai ba, amma dai ita ta shigo tana kuka.

Sosai daddy ya rinƙa dannarsu akan su je su zauna su kwantar da hankalinsu yana da tabbacin ba wani abin da ya sameta, iya shegene kawai, amma ina sun ki, kowa ya dage sai lallaɓata yake yi tare da yi mata kalamar rarrashi ko zata faɗi abin da akayi mata, Irfan har da zagewa yana rarrashinta, Abbi ma baa magana, Hjy Batula Aunty duk sai kara shagwaɓa ta suke yi.

Daddy dai da ya ga ba su gama sanin halin Jelly ba sai ya barsu ya zuba masu ido domin yanzu su san halinta dan saboda gaba.

Kuma babban abin mamakin shine kukan nata babu hawaye, ta yadda ma zaka san tsagen iskanci ne yake yi mata yawo akai, ko ɗingon hawaye babu, kai bama alamar hawayen a waƴan nan busassanun idanun nata masu gashin ido a tsaitsaye.

Sun kwashi good 30mins a haka sai fama suke yi da ita, Akil dai ya koma gefe ya zauna dan idan ya ce zai biye mata to tsab zai karyata a gaban baban nata, gudun kada ayi hakan ne yasa ya koma gefe kawai ya kyale su.

Sai da ta kara wani minti goma sannan cikin kukan nata ta ce "Daddy bani wayarka".

Daga nan ne fa kowa ya koma mazauninsa ya zauna Aunty kam ta rasa a wani mataki zata ajiye Jelly, shi kuma daddy godiya ya yi ga Allah da ya sa suka ga halin nata a fili, Ayla Baiwar Allah yau ta ga iskanci mai lasisi, mamaki ya sa bakinta ma ya gaza rufuwa, shi kuwa daddy miƙa mata wayar tasa ya yi kamar yadda ta buƙata.

Karɓa ta yi har lokacin bata dai na kukan ba, da yake wayar ma akwai password sai ta rubuta sunan ta, tana rubutawa wayar ta buɗe, dama ta san shine pin na daddyn nata tun a tsohuwar wayarsa.

Contract nasa ta shiga, dealing number Imran ta yi, tana rubutawa sunan sa ya bayyana a yadda daddy ya yi saving, my son, kiran number ta fara yi.

Lokacin da kiran ya shigo kuma suna asibiti shi da Rismha, bata daina kuka ba har ya ɗauki kiran, kuma ya ɗauki kiran ne da tunanin ko dai daddy ne tun da number sane.

A nitse ya ce "Hello Bappa" cikin kuka ta ce "Yaya Imran ina kake?". Jin kukanta ya sa ya ruɗe shima sosai, hankali a tashe ya ce "Jelly menene yake faruwa? Me akayi miki kuma?".

Hannu daddy ta kama ta zura a bakinta tare da gyara kwanciyarta tana mai juya kukan nata izuwa tsantsar na shagwaɓa har da turo baki kamar ba ita ba, gaba ɗaya palo sun mayar da ita Tv harta Akil yau yana ganin ikon Allah, su Aunty kam ba'a magana sun sami Tv ai, Abbi ma dai ta ɗaure mashi kai tare da jefa shi cikin tunanin anya tana da lafiya kuwa.

"Yaya Imran ya naga har yanzu baka shigo palo ba? Ina son ka shigo ne fa na yi maganar akan idon ka" ta faɗa tana tsotsar yatsan daddy da ta sanya a cikin bakinta.

Ɗan dafe kansa Imran ya yi kafin ya ce "My wife please ki rufa mani asiri kada ki faɗa kin ji ko? Na yi maki alkawarin ba zan kara ba, idan kika faɗa wlh zaki ja mani abubuwa da dama, ciki kuma har da raini tsakanina da kanne na, wato su AKILA".

"To ni ba kanwar ka bace? Ai nima raina ka kenan zai yi ko? Tun da ni ka yi wa abin, ni a kaina baka ji kada na raina ka ba? Sai su Akila?, To ni dai gaskiya sai na faɗa ka shigo ko karka shigo yanzu kuwa zan gaya sai anjuma" . Diff ta katse kiran tare da kwashewa da dariya kamar ba ita ba.

Miƙewa Akil ya yi tare da karasowa wajen yana faɗin Irfan ya zo ya riƙe mashi ita bari su yi mata ruƙiya wata kira aljanun kan nata za su tafi.

Cikin sauri daddy ya ce bari ma ya riƙeta da kanshi domin idan aljanun suka tafi sai ya fi kowa murna. Zuba masu ido ta yi tana kallon ikon Allah.

Ai kuwa har Akil ya gama ruƙiyarsa ba bu wani motsin da zai nuna maka da aljanu a kan Jelly, lafiya lou take kawai dai iskanci ne kwando kwando ta tara a kan nata, shiru palon ya yi suna kallon ikon Allah.

Miƙewa ta yi daga jikin daddy ta haye sama abinta kamar wadda aka kira hannunta na riƙe da wayar daddynta wadda Imran yake ta kira tun ɗazun, bawan Allah duk ta rikita shi, sai addu'a yake yi Allah yasa kada ta faɗa

Tana shiga ɗakin Hanan ta yi picking na call ɗin tare da hayewa saman gado tana faɗin "Yaya Imran ɗina ina kewar wlh, dan Allah ka dawo cikin palo ka ji?".

Nauyayyar ajiyar zuciya bawan Allah ya sauƙe kafin ya ce "My wife kin faɗa ne ko baki faɗa ba?" Juya waƴan nan dara daran idanun nata ta yi kafin ta ce "E na faɗa kuma daddy ya ce zaka zo ka same shi".

Shiru ya ɗan yi kafin ya ce "To shikenan da daddare zan zo sai na bawa daddyn hakuri kema kuma ki yi hakuri ba zan sake ba".

Shiru itama ta ɗan yi kafin ta ce "Yaya Imran dama idan mutun ya yi wa matarsa kiss sai ya bawa babanta hakuri ne? Ina cewa da zarar an ɗaura aure kun zama mallakin juna".

Imran ya kasa magana, ya rasa ma ta ina zai fara, ya rasa wani amsa zai bawa yarinyar nan, ya rasa me zai ce mata, anya jelly ba zata haukata shi ba wata rana kuwa? Anya kuwa tana lafiya?.

Turo baki ta yi cikin shagwaɓa tare da yin kasa da murya ta ce "Yaya Imran kai fa mijina ne ba zan tona maka asiri ba, amma dai kada ka sake cinye mani bakina haka, ya yi yawa fa, kuma dama ina son yi maka wasan kafin a kai ni gidan kane shiyasa na yi maka haka, na yi karatun islamiyya ai, kuma ina kallon film sosai, sannan daddy da kansa lokacin da zai aura min Muneer ya gaya mani me ake nufi da aure, so ka ga ai na sani, amma dai yaya Imran kana da tsoro dayawa fa, i am the winner a wannan game ɗin". Ta kai karshen maganar tana dariya.

Bawan Allah bai san time da murmushi ta suɓuce mashi ba, cike da so da kuma kaunarta ya ce "Amma dai gaskiya kin gama da ni, kin saka ni na gudu na bar gidan, amma ba komai zan rama ne, bari na damke ki zaki yi bayani da yaren da ke kanki baki san shi ba".

Dariya ta yi ta mirgina ta mirgino kafin ta ce "Yaya Imran ba wani bayanin da zanyi mijina yaya Imran zai kwace ni daga hannunka ai". "Da gaske?" Ya faɗa yana ɗaga gera ɗaya kamar tana a gaban shi.

Jinjina mashi kai ta yi tana faɗin "E da gaske". Jinjina kai shima ya yi kafin ya ce "To Shikenan ina nan zuwa gidan ai, a nan zamu ci abincin dare, wani irin kwalliya zaki yi wa mijinki?" Ƴar dariya ta yi har sai da hakwaranta suka bayyana.

"Wani irin kwalliya kake so Yayana?" Shiru ya yi yana tunani, can kuma sai ya ce "Wando da riga masu kyau sai ki sanya hijabi a sama dan kada kowa ya kalla mani ke" murmushi ta yi kamar ba ita ba, ta nitsu sosai ta ce "Tom an gama amma dai...." Sai kuma ta yi shiru.

"Amma dai me My jelly?" "Ba komai yaya Imran" "Gaskiya ban yarda ba, akwai dai wani abu, gaya mani menene?". Shiru ta ɗan yi kafin ta ce "Amma dai zaka kawo mani chewing gum da kuma ice candy ko?".

Cool murmushi ya saki yana faɗin "Iya shi kaɗai kike so ko dai akwai wani abin?" "Shi kaɗai nake so, sai kuma ganin fuskarka, Allah ina kewarka sosai".

"Allah sarki muna asibiti ne da Rimsha, amma dai yanzu za mu baro asibitin, idan mun fito sai mu wuto nan kawai".

Ɗan kiƙewa ta yi a zabure tana faɗin "Me ya kai ku asibiti kuma?" Tana magana tana kara zare idanun nan nata sosai, "Ɗan ciwon kai ne yake damun Rimsha, amma dai an bata magani yanzu zamu taho".

Koma wa ta yi ta kwanta tana kara dafe kirjinta domin ta ɗan ji sauƙi jin ba wata matsala ba ce ta faru.

"My jelly zaki bi yaya Imran naki idan na zo ko?" Shiru ta yi mashi bata amsa ba, a can cikin zuciyarta kuma tunanin kalar tsiyar da zata yi mashi shi da daddy take yi, dan ta yi niyar sai ta yi masu tsiya sosai da sosai.

"My jelly baki jina ne?" Ya faɗa daidai lokacin da yake miƙawa Dr hannu suna gaisawa akan za su wuce shi da Rimsha, tun da Allah yasa ta farfaɗo kuma ta dawo cikin hayyacinta, Allah ya takaita abin saboda addu'a da karatun Al Qur'ani mai girma da take yawan yi.

"Yaya Imran ka bari sai ka zo ɗin ka ji ko?". To ya amsa mata da shi sannan suka yi sallama, ta ɗaura wayar a saman bedside drawer tare da gyara kwanciyarta ta kwanta tana tunanin kiss da ya yi mata ɗazun, wani irin yanayi ta ji a jikinta.

A can palo kuma, cigaba da hiransu suka yi, da farko sun yi niyyar bin bayar Jelly ɗin, amma daddy ya dakatar da su a in da yake gaya masu su fita harkarta, domin lafiya lou take, iskanci ne kawai.

Hakan yasa suka kyaleta aka cigaba da hira, miƙewa Akil ya yi ya fice waje dan ya amsa kiran da ake yi Mashi, Umaisha, Akila, Hanan, a tare suka miƙe dan su haura sama su bawa iyayen nasu fili su tattauna.

"Aunty Ayla muje ko?" Cewar Umaisha, ɗan satar kallon daddy ta yi domin ba iya tafiya zata yi ba.

"Umaisha ku je Batula zata zo tare da ita". Shi ne abin da daddy ya faɗa, to suka amsa da shi kafin su wuce sama.

Dawo da kallonsa kan Hjy Batula daddy ya yi yana faɗin "Batula ƴaƴanki nawa ne a yanzu?" Duk kunya ya isheta, ta zubar da ƴan uwanta, shiyasa tun da ta shigo palon ta kasa sakewa saboda kunyarsu da take ji.

"Ƴaƴana uku, biyu maza ɗaya mace, akwai HAROON da HARISH sai ABLA ita ce auta".

Addua sosai Abbi da daddy suka yi wa ƴaƴan nata tare da ita kanta, sannan suka ce ta saki jikinta komai ya wuce ai, ajiyar zuciya ta sauke kafin ta yi masu godiya sosai da sosai.

"Batula taimakawa Ayla ta bi bayan ƴan uwanta zuwa sama". Cewar daddy.

To ta amsa da shi tare da tambayar wace ce Ayla ɗin. A takaice sama sama Abbi ya bata labari, sosai ta yi murna sannan ta yi wa daddy gaisuwar rasuwar mummy jelly kafin ta riƙo hannun Ayla ɗin dan su nufi sama.

Ƴar kara ta saki lokacin da ta miƙe, girgiza kai daddy ya yi Ayla raguwa ce ta karshe, hakan yasa yake cewa tayi yarinya, ba wai shekarun yake dubawa ba, shi yasan me yake dubawa yasa yake kiranta da yarinya.

Ganin abin da ya faru yasa Hjy Batula ta gane me ya wanzu a tsakanin yayan nata da kuma matar tasa, hakan yasa ta kara Kaunar Ayla sosai da sosai, cikin dabara ta taimaka mata suka wuce sama, miƙewa ita ma Aunty ta yi dan ta bi bayansu, shima dai Irfan miƙewa ya yi


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login