Showing 39001 words to 42000 words out of 355604 words

Chapter 14 - Triplets Book 2 Hausa Novel Complete

10 Dec 2024

2753

yi, kirjinta sai dukan uku-uku yake, ta tsorata sosai, taya za a yi a ce ita tana kallon Malika, amma Ayla ba ta kallon ta.

"Me yasa kike tunani Rimsha?" Malika ce ta katse mata tunanin da take da tambayar ta. Yar firgita ta yi kafin ta ce, "Dole zan yi tunani mana Malika." Tsare ta da ido irin nata Malika ta yi tana faɗin "To tunanin me kike yi?" Ayla dai ta ga ikon Allah, don ba ta ganin Malika sai dai ta ga Rimsha nata surutu ita kaɗai kuma abin mamaki ba ta iya jiyo me Rimsha ke faɗa, sai dai bakinta kawai take gani yana motsawa. Babban magana wannan shine ruɗani!

"Malika me yasa Ayla ba ta ganin ki?". Cewar Rimsha, ta yi maganar a matukar tsorace, "Kina son ta gan ni ne?" Malika ta tambaya tana sanya hannunta a saman tsakiyar kan Rimsha, don ta tare mata ruwan saman dake dukan tsakiyar maɗigarta, don ruwan zuba yake sosai kamar da bakin kwarya.

"Eh mana Malika yana da kyau ai kowa ma ya gan ki, bai kamata ki ɓuya ba sa ganin ki ba, ai sai su yi tunanin da aljana nake magana." girgiza kai Malika ta yi tana faɗin "Yaro, yaro ne, amma dai ke yarinya ce mai zuciyar manya, ki ce Ayla ta kalli cikin ɗaki". Kananun shekarun Rimsha ya hana ta gane in da Malika ta dosa, don haka sai ta juya ta ce, "Ayla ki kalli cikin ɗaki." Ayla kuma ta yi zaton wani abu Rimsha ke nuna mata a cikin ɗakin don haka sai ta juya, ta kai kallonta cikin ɗakin, kafin ta juyo Malika ta bayyana yadda kowa zai iya ganin ta

Ayla ganin babu komai a cikin ɗakin yasa ta juyo tana faɗin, "Rimsha me zan gani a cikin ɗakin? Don na juya ban ga komai... Ba ta ƙarasa maganar ba idon ta ya sauka a kan Malika, a zabure ta ce, "Wace wanna mai bala'in kama da ke ɗin kuma Rimsha?" Juyowa Rimsha ta yi tana kallon Ayla kafin ta yi magana, Ayla ta yanke jiki ta faɗi kasa sumammiya, a sukwane ta dawo da kallon ta kan Malika, sai ta ga wayam babu Malika a wajen, Malika ta tafi, cike da tsoro ta fara waigawa ko za ta ga Malika, amma babu ita babu alamarta, da gudu ta kwasa ta bar cikin ruwan ta nufi wajen Ayla, in da take kwance magashiyan a kasa.

Kanta ta yi ta fara jijjiga ta tana kiran sunanta, hakan ya yi sanadiyar jawo hankalin Iya da kuma Kausar. Da sauri suka karaso wajen a tare, iya tana faɗin "Lafiya Rimsha?" Ganin Ayla kwance magashiyan a kasa yasa Iya ta yi kanta tana kiran sunanta.

Ruwan saman dake zuba daga jikin Rimsha shi ya zubar wa Ayla a fuskarta zuwa wuya. Hakan yasa ta farfaɗo daga suman da ta yi.

Har suna haɗa baki wajen cewa "Ayla lafiya?" Shiru ta ɗan yi kafin ta ce, "Babu komai." Don ta mance komai, a zahirin gaskiya abin da ya sanya ta suma shi ne ta ga lokacin da Malika ta ɓace, kuma kafin ta ɓace sai da ta ɗora hannunta a kan Rimsha dana sakin cool murmushi sannan ta ɓace, lokacin ita kuma Rimsha tana kallon Ayla ɗin abin ya faru. Wannan shi yasa Ayla ta suma, da ta farfaɗo kuma ta kasa faɗa musu me ta gani yasa har ta suma. Haka ta miƙe sai tambayar ta suke amma ta ce ba ta sani ba, ita ba ta san komai ba, haka suka kyale ta, Iya da Kausar suka koma cikin gida tare da Ayla, ita kuma Rimsha tsayuwa ta yi a wajen tana tunanin ina Malika ta tafi lokacin guda haka, ko alamarta babu, sannan me ya sanya Ayla suma? Sosai ta shiga duniyar tunanin sai dai kuma babu wata amsa da ta samu.

A hankali ta sako kafarta ba ta daddara ba ta sake komawa cikin ruwan saman ta ci gaba da wankanta, don ita da ruwan sama ba a raba su. Sai juyi take, wannan bakin gashin nan nata rabi ya kwanto mata a fuskarta rabi kuma ya kwata har gadon bayanta, sai sheki yake gwanin ban sha'awa.

Ruwan saman ya kai awa ɗaya yana zuba kamar da bakin kwarya, haka Rimsha ta tsaya a cikin ruwan tana wanka har sai da ruwan ya ɗauke. Ba yadda Ayla da Iya ba su yi da ita a kan ta fita cikin ruwan ba, amma taki, har sai da ruwa ya ɗauke sannan ta koma cikin falo, sai ɗigar ruwa take.

Tana shiga falo ta wuce ɗakin Kausar wanda yanzu ya zama ɗakinsu. Canza kaya ta yi zuwa riga T-shirt da wani wandon palazo jeans na Kausar, ta yi kyau sosai, don wankan da ta yi a cikin ruwan nan ba karamin fita ta yi ba, har wani sheƙi fatarta take sosai ta yi kyau kamar ita ta yi kanta.

Sai bayan da ta gama shiri ne, ta dawo falo ta ɗauki abincinta, ta ci gaba da ci, tana yi tana murmushi tana shafa kirjinta wajen zanen sunan GAR kamar ba lafiya ba.

Bayan sun kammala cin abincin ne suka zauna shiru kowa da abin da yake tunani.

Can kamar wadda aka tsikara Rimsha ta miƙe tana faɗin, "Kausar bari na tambayo Iya ko tana da waya, in saka lambar mamana ko sister na in ƙira in ji ko tana shiga." To, kawai Kausar ta ce mata, wucewa Rimsha ta yi zuwa bedroom na Iya.

A bakin kofa ta tsaya ta yi sallama, daga cikin ɗakin Iya ta amsa tare da ba ta izinin shigowa. Ciki Rimsha ta shiga tana faɗin "Sannu da hutawa Iya" da fara'a Iya ta amsa mata tana daga kwance saman gadon ta. Daga ɗan gefe ta tsaya cikin girmamawa ta ce "Iya dan Allah idan kina da waya ki taimaka min da ita zan saka number mamana ko sister na ne na gwada kira." Ba tare da Iya ta sake yin wata magana ba, ta ciro babban wayarta kirar Tecno ta miƙa mata, cikin sauri Rimsha ta karɓa wayar, jikinta har wani kerma yake wajen karɓan wayar.

Cike da zumuɗi ta fara gwada number mum. Sai da kirjin ta ya ba da wani dum-dum lokacin da kunnuwan ta suka ji layin mum a kashe.

Sake gwadawa ta yi, nan ma a kashe, kamar za ta yi kuka ta sanya number Jehan, shi ma a rufe, nata number ta sa ta gwada ƙira, shi ma a kashe, turo ɗan bakin nan nata tayi kafin ta gwada number daddynta duk da ta san tasa wayar a kashe take, saboda tun kafin ta bar gida, numbersa ba ta shiga.

Kamar a mafarki ta ji number daddy ta shiga, cikin sauri ta ciro wayar daga kunnanta don ta gani shin da gaske numbersa ta sanya da kyau, ko kuma akwai in da ta yi kuskure.

Tabbas da gaske ne babu wani kuskure number daddy ne. Sai dai wayar ta yi ringing har ta katse ba a ɗaga ba, Iya dai tana daga kwance ta zuba mata ido. Sake kira na biyu tayi, nan ma ba'a ɗaga ba, sai a karo na uku ne, aka ɗaga.

Cike da zumuɗi ta ce, "Hello daddy." Wani murya ta ji wanda da alama Hausa bai ishi mai wannan murya ba, "Hello waye ne?" Mai wannan murya ya tambaya, sake ciro wayar daga kunnenta ta yi don ta sake tabbatarwa da kanta number daddy ne.

Tabbas numbersa ne, sake mai da wayar kunnenta ta yi ta ce "Ina wuni?" Bai amsa gaisuwar ba sai cewa ya yi "Waye ne wai?" A ƙule ta ce "Kai ba musulmi ba ne?" Shi ma da alama ya ji haushin maganar nata, da ɗan karfi ya ce "Ban sani ba, ki kira ni kuma kina neman gaya min magana!" Ɗaure fuska ta yi ƙamar tana gaban shi ta ce "Ka bawa mai wayar wayarsa, ina son yin magana da shi" "Ke wai waye ke ne tukun nan ma?" Kamar za ta masa da faɗa, sai kuma ta tuna cewa daddynta take nema, dan haka sai ta ce "Dan Allah ka bawa mai wayar wayarsa, ni yarsa ce, magana na ke son na yi da shi ka taimaka" "Ke ni bani da wata ƴa, wannan waya kuma wayanane, dan haka kada ki sake kira" ranta ya ɓaci sosai, cike da jin haushi ta ce "Kai malam idan baka bawa mai waya wayar sa ba, wlh sai na saka an ɗaure ka dan kaga ina bin ka a hankali ko?" tofa ba karya jinin dake gudu a jikin Jehan shike gudu a jikin Rimsha, kada ku manta da hakan.

Jin ta ce za ta saka a ɗaure sa sai ya yi kasa da murya ya ce "Ni ban san mai wayar nan ba, wata ɗaya da ya wuce ne, na tsinci wayar kusa da wani gawa, na dawo daga gona zan koma gida lokacin, dan Allah ki rufamin asiri wlh ban san komai ba, wasu ne suka kashe shi".

Saboda tsabar shiga tashin hankali ya ta kasa tsayuwa a kan kafafun ta, zubewa ƙasa ta yi, ta zauna zaman dirshan, nan take hawaye masu bala'i zafi suka fara zarya a kan kuma tunta, cikin sauri Iya ta sauƙo kasa daga saman gadon, ganin Rimsha na hawaye ta tada mata da hankali.

"Bawan Allah a wani gari ka ke?" Rimsha ta faɗa cikin kuka, "A nan agadas nake" sakin wayar Rimsha ta yi, wayar ya faɗi kasa, kuka ta sa mai tsuma zuciyar mai sauraro, yanzu da man da gaske ne daddyna ya rasu, ta tambayi kanta, tambayar da ba ta da amsar shi.

Sosai Iya ta rinƙa bata baki tana bata hakuri tare sa tuna mata da yarda da kaddara. Rimsha tasha kuka har ta koshi, da kyar iya ta iya samo kan ta, har tayi shiru.

Bayan tayi shiru ne ta miƙe jiki ba kwari ta koma ɗakin Kausar dan kanta dake mata barazanar fashewa saboda tsananin ciwo tana son ta kwanta ta huta. Kausar da Ayla suna falo ba su san meke faruwa ba. Tana shiga ɗakin Kausar ta haye gado ta kwanta tana mai da numfashi tare da jan hanci. Tunanin irin rayuwar da suka yi da daddyn su ta fara yi, tana yi wasu siraran hawaye na biyo ta gefen idon ta zuwa kunnen ta. Allah sarki rayuwa kenan, yau gare ka gobe ga ɗan uwanka.

To masu karatu mu leƙo Washington DC wata kila kafin mu dawo Rimsha ta yi shiru.



💞💞Washington DC💞💞

Romeo

Zaune yake saman katafaren lallausan bed nasa, jikinsa na sanye da farin short da farar singlet, hakan ya bayyanar da kyakkyawar kakkarfar surar jikinsa, irin na jarumai sadaukan yaki. Ya ɗaure dark black curly hairsa a bayansa ya bar wannan guntu na gaban goshinsa mai kara fito da kyansa.

Ya zubawa system da ke gaban sa wayan nan dara daran blue eyes ɗin nasa, ya yi shiru ya dukufa aiki yake yi sosai a nutse, sai faman cizan lallausan red lips nasa yake, har wani ja sosai lips ɗin nasa ke karawa saboda ciza wa da yake yi.

"What CIA?!" Ya furta da ɗan karfi, kara zaro dara daran idon nasa ya yi, har sai da suka kara haske saboda zaro su da ya yi, kara cizan lips ɗin nasa ya yi da karfi, alamar abun da yake gani a cikin system ɗin ya ɗan ɗaga ma shi hankali, kuma ya bashi mamaki.

Wayarsa dake gefen sa ne ya fara ruri yana neman ɗauki. Sai da wayar ya kusa katsewa, sannan slowly ya mai da idon sa izuwa kan wayar, Dr Tyrion, shi ne sunan da ya bayyana a kan screen ɗin wayar, shiru ya ɗan yi bai ɗauka kiran ba, har wayar ta katse. Kira na biyu ne ya sake shigowa, alamar Dr fa a matse yake, shiru lion ya yi kamar mai tunani.

Kiran na gab da yanke wa ne, ya sa hannun sa a nitse ya ɗauki wayar tare da yin picking call ɗin, tun bai yi magana ba ya jiyo sautin kukan Michael ta cikin wayar, katse kiran ya yi ba tare da ya yi magana ba, ya miƙe cikin sauri ba tare da ya kashe system nasa ba, ya nufi toilet.

A nutse ya yi wanka, sannan ya fito ya tsaya a gaban mirror, kamar yadda ya saba haka ya tsaya ya rinƙa shafe dark black curly hair nan nasa da mayukansa masu kyau da tsada.

Bayan ya gama da kai ne, ya shafe soft skin nasa da wadannan mayukan nasa masu bala'in kamshi da tsada tare da feshe jikinsa da wannan haɗaɗiyar perfume ɗin nan nasa mai bala'i fitinannen kamshi, sannan ya wuce dressing room nasa, sai tashin daddaɗar fitinannen kamshin yake.

Bayan wasu yan mintoci ya fito sanye da wandon jeans fari tas, da Turtle High T-shirt, kasancewar rigar ta kama shi sosai ta bi jikinsa, hakan ya bayyanar da kakkarfar surar jikinsa, damtsen hannun nan nasa kamar za su fashe saboda karfe da yake ɗagawa, ga breast nasa ɓul-ɓul, sai tashin kamshin yake, ya ɗauki wayarsa ya fito ya bar system nasa.

Kodayaushe motoncinsa a shirye suke, duk lokacin da ya fito don su tafi wani waje, to tafiya kawai za su yi, yanzu ma yana fitowa kawai buɗe masa kofar motarsa wani jibgegen Baturen soja ya yi, fari ƙal da shi. Duka sojojin Romeo farare ne kal, masu kirar cikakkun mazaje, kallo ɗaya zaka musu, kasan sun shirya shiga fillin daga a ko wani lokaci, fuskokin suma kawai abun tsoro ne, ganin fuskarsu takan sa hantar manyan maza ya kaɗa, amma a haka, suna mutuwar tsoron fusataccen fuskar Romeo wato lion, duk da cewa kullun a kame suke suna nutse, idan suka gan shi ya fito, har wani damke kakin jikin su suke yi saboda kamewa da suke kara yi idan suka gan shi.

A jere motoncin nasu suka tashi suka miki titin zuwa bakin babban gate, jibga jibgan jaruman security da ke bakin gate ɗin ne, suka wangale musu katafaren gate ɗin gidan, amma kafin su isa babban gate sai da gate na biyu ya yi checking na motocin da wannan na'uran, sannan ya kira numbobin motocin gaba ɗaya ya shigar cikin babban na'uran Romeo dake ɗakin bincike dan already na'urorin a haɗe suke da juna tura sako kawai suke.

Da gudun gaske suka danna hancin motocin waje tare da sakin jiniya tamkar wayan da za su tafi filin yaƙi, kai tsaye hospital suka nufa. Duk wasu abin hawa dake kan hanya, tun jerin motoncin su Romeo bai iso wajen su ba, suke basu hanya dan jin jiniyar sun san jerin motoncin The General of the Army ne.

Suna shiga asibitin suna wuce parking space, kasancewar asibitin yana da girma sosai ya ɗauke gabaɗaya motoncinsu.

Suna parking a guje jibga-jibgan sojojin nan suka diro kasa daga saman bayan motoncinsu, ɗaya daga cikin sune ya buɗe kofar motar lion suka tsaya a bakin kofar motar suna jiran fitowar sa.

Yana sako kafar sa ɗaya waje, a sukawane suka ɗaga hannayen su dake sanye cikin black hand gloves su ka sara masa, ba su sauƙe hannayen su ba, har sai da ya fito ya nufi cikin hospital ɗin.

Sai ya wuce su sannan suke sauke hannayen nasu. Sojoji shida madaka karti ne suka take masa baya zuwa ciki.

Kai tsaye ɗakin da Michael ke kwance wato ɗaki na musamman ya nufa. Tun daga nesa yake ji yo kukan Michael, da ma kuma ya san za a yi hakan, dan ya san halin Michael da ragon ta.

Kwance Michael yake saman bed nasa, na majinyata sai kuka yake, hawaye sharaɓa sharaɓa a fuskarsa kamar ƙaramin yaro, ga shi idon nasa a runtse.

Gaban gadon lion ya je ya tsaya tare da riƙo hannun Michael ɗin, Michael jin an kama hannun sane yasa ya yi saurin waro brown eyes nasa.

Ganin Romeo ne yasa ya kara sautin kukan nasa, yana ƙara kankame hannun Romeo,

kallon jinin da aka kara masa Romeo ya yi kafin ya dawo da kallon sa kan fuskar Michael ɗin.

Gently in a cool voice ya ce "Michael whapped? Why are you crying?" Yun kurin tashi Michael ya yi, cikin sauri Romeo ya mai da shi yana girgiza masa kai alamar kada ya yi yunkurin tashi, kara sautin kukan sa ya yi.

Shafa lallausan dark brown hair sa Romeo ya fara yi alamar rarrashi, cikin kuka da shagwaɓaɓɓiyar murya ya ce "My lion zafi nake ji, jiki na ciwo yake min, ji nake kamar zan mutu, wayyo ka taimake ni".

Ikon Allah shi da ya je zai kashe kansa, an ceto rayuwarsa da kyar amma yake kukan zai mutu zafi yake ji, a taimake sa, lallai Michael tabbas ba laifin ka bane, laifin kwakwalwar kane da take nuna maka komai daidai ne.

Gently cike da kaunar Triplets nasa lion ya ce "Is okey My Tiger zai dai na yi maka zafi ka ji, ka yi shiru, just for a while minutes zafin zai tafi." Kuka sosai Michael yake yi kamar ba namiji ba, har da wani shassheka tare da jan hanci.

Romeo baya son ganin kukan nasa dan haka sai ya juyo ya ce da Dr Tyrion ya yi masa alluran barci. Jin lion ya ce a masa allura yasa ya kara sautin kukan nasa, dama kuma already kun san halin sa da rashin son allura.

Da kyar ya yarda aka ma shi allura, nan ma sai da lion ya karɓi alluran da kansa ya masa.

Bayan an kammala komai, Michael ya yi barci ne, Dr T wato Dr Tyrion ya dubi lion fuska ɗauke da murmushi ya fara magana, "Congratulations Sir." Zuba masa dara-daran kyawawan idanunnan nasa ya yi ba tare da ya yi magana ba. Ci gaba da magana Dr ya yi "Abin da muƙa ɗauki tsawon shekaru muna fafutuka a kan shi, yau mun yi nasaran samun bakin zaren matsalar." Still Romeo bai yi magana ba, ya dai tsare Dr da ido yana jiran ya ji karshen maganar kawai.

"Yau mun yi nasaran samun bakin zaren matsalar Michael, kuma muna sa ran nan da yan kwana ki zuwa watanni zai iya samun sauƙi kwakwalwan sa za ta koma daidai, zai daina yin abubuwa kamar yaro, zai zama cikakken mutun, kuma duka hakan ta farune sakamon buguwa da kansa ya yi a sanadiyar accident da ya sa mu, amma


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login