Showing 72001 words to 75000 words out of 355604 words
ke nufi kenan? Yana nufin a je a jefar da yaron ko me. Yaro kuwa sai tsala kuka yake yana jin yinwa, shi kuma Romeo yana gama magana ya wuce ya koma part nasa, duk cikin su babu wanda ya yi gigin rokarsa ko ya nemawa yaron alfarma dan sun san Lion idan ya yi magana babu wanda ya isa ya sa shi ya canza, shi kaifi ɗaya ne, kamar dutse yake baya tankwaruwa.
Wucewa Tga ya yi, ya karɓi yaron daga hannun daddy ya fice daga palon, daddy kamar zai yi kuka, dan yana son yaron sosai, yana son jika, ga ƴaƴan nasa kuma babu tunanin auren a lamarinsu, duk cikin su ma ba wanda yake da lokacin magana da na miji ma ballantana kuma mace.
(Allah sarki daddy haka zaka ci gaba da hakuri, domin koma me suka yi kai ne mai laifi tun da kai ka renesu a kan hakan, kai ka ki yarda ka yafewa mum ɗin su tazo ta basu kulawa, da ita ta renesu ai da lamarinsu ya zo maka da sauƙi, amma renon namiji, ai a mazan zasu taso, uwa uba kuma ba addini hmmm abin ba'a magana)
Zama daddy ya yi saman kujera yana tunanin ya Jay zai ji a ransa, irin wannan abin ɗa guda. Shi kuma John ɗan ba ruwana ko a jikinsa, dan shi ko kashe yaron ma a kayi ba abin da zai ji, saboda shi sammakal ne, komai daidai ne irin Michael.
Tga kuma yana fita palon ya wuce wajen da ya ɗaure Jay, Allah sarki Jay idan ka gan shi sai ka rantse da Allah baya numfashin ya mutu, saboda yadda numfashin nasa yake fita a hankali-hankali dan wahala, duk wannan hukunci da Lion ya masa, su Tga ba su ga laifin Lion ba, domin a wannan gaɓar a kan gaskiya yake hukunta Jay, dan bai shiga hakkinsu ba, ya ce musu idan suna son mace to su yi aure, kada su kusanci mace ba tare da aure ba, amma Jay ya yi fatali da maganar, dole ya karɓi hukunci.
Kusa da shi Tga yazo ya tsaya, Allah sarki jin kukan yaronsa yasa ya ɗan waro wahalallun idanun sa, da suka ji uban jiki, "Jay ina ne family House na su Jennifer?" Ciki ciki Jay ya ke magana, ba ka jin komai sai iska dake fitowa daga bakinsa, matso da kunnensa Tga ya yi daf da bakin Jay ɗin, da kyar ya iya samun damar jin abin da jay ke faɗa na kwatancen in da gidan su Jennifer ya ke.
Wucewa ya yi zuwa parking space bayan ya gama jin kwatancen Jay, motarsa ya je ya shiga da yaron, kai tsaye ya hau titin zuwa babban gate. Ko da ya isa gate na farko sai da ya tsaya wannan na'ura tayi scanning na motarsa tsab sannan ta buɗe masa kofa ya fita izuwa babban gate da zata sada shi da wajen. Kai tsaye gidan su Jennifer ya wuce, ya je ya kai musu yaron, yana miƙa musu ya fice, sai tambayar sa suke, ina Jennifer, shiru ya musu bai kula su ba ya wuce abinsa dan ba shi da amasar da zai ba su.
Lion kuma yana komawa part nasa ya kwanta saman bed nasa ya mance ma da wata takarda da yake bincika, ransa ya ɓaci, a kan me zasu kai Jennifer asibiti, ya zama dole ya musu hukunci mai tsanani, dan nan gaba su rinƙa tsayawa suna sauraron abin da yake basu umarnin a kai da kyau.
To bari mu koma Nigeria dan muga wani lamari ne ke gudana
💓💓KATSINA STATE 💓💓
Bayan tafiyar Yarima shima Nawid ya wuce ɗakin ɗaya da ya sauka a cikin Hotel ɗin.
Da shigarsa ɗakin bai yi minti 20 ba ya kira Ibraheem a waya a kan ya turo masa Jehan yana da aiki da zai bata, cikin hanzari Ibraheem ya yi maza ya isar mata da saƙon Nawid, da farko ta ce ba zata je ba, amma daga baya da ta tuna cewa Nawid ya mata rana yau, ya ceceta daga hannun yarima, sai ta hakura ta nufi ɗakin nasa.
Jehan mutunce wadda bata manta alkhari komai kankantarsa, in dai ka taɓa mata wlh ba zata taɓa mancewa da kai ba, ko da ka mata sharri daga bayan wannan Alkhari, to zata rinƙa ganin kane da wannan Alkharin, haka zalika bata manta sharrin idan ka mata, komai Alkharin da za ka mata bayan wannan sharri tofa in dai sharrin ka fara yi mata shi zata riƙe.
A bakin kofar ɗakin nasa ta tsaya ta kwankwatsa masa, kamar jiranta yake yi dama, cikin sauri ya buɗe kofar. Fuskar sa ɗauke da kayatatcen murmushi ya ce "Sannu ki" ɗaure fuska sosai ta yi kamar wadda aka aikowa da mutuwa, wani irin faɗuwar gaba Nawid ya ji lokacin da ya ga yadda ta ɗaure fuskar tata.
"An ce kana nema na lafiya?" Shine abin da ta ce masa, wani wahalallen yawu ya haɗiye kafin ya ce "To malama da farko dai sunana Nawid kuma Ni..." Bata bari ya kai karshen maganar ba ta ɗaga masa hannu alamar bata son jin maganar tasa, shiru ya yi ya zuba mata ido.
A yatsene ta ce "An ce kana nema na me kake buƙata, oder me zaka bada?" Ta yi maganar a nitse cikin kwanciyar hankali, da kallo ɗaya zaka mata kasan izza ya samu mazauni a tattare da ita, gata kuma kaifi ɗaya ce, bata magana ta sauya ko me za a yi mata, idan tana magana ɗai ɗai take yin shi, kuma a nitse take, ba ta haɗa ɗaya da ɗaya.
Kakalo murmushin dole ya yi, dan harga Allah bai ji daɗin yadda ta tarbe shi ba, duk da cewa izzarta yasa ya kamu da son ta, amma da ta yi masa shi, bai ji daɗi ba.
"Malama ki bari mana na faɗa miki sunana tukunnan ko?" Kawar da kanta gefe ta yi kafin ta ce "Sunan ka baya cikin jadawalin tsarin aikina, so please ina ganin girmanka, ka kama kanka, just tell me what you want direct kawai dan ina da abin yi" Ta yi maganar tata cikin harshen turanci, dan har yanzu hausa bai zauna a bakin ta ba,
Sosai ya yi mamakin jin yadda take rero turancin nan kamar dan bakin ta a ka yi yaren.
Wow ya furta a ransa, a fili kuma daurewa ya yi ya ce "To shikenan tun da baki bukatar jin sunana bari na gaya miki me yasa na kiraki" kara ɗaure fuska ta yi ba tare da ta yi magana ba, kuma bata kalli in da yake ba.
"A gaskiya malama ba zan ɓoye miki na cuci kai na ba, ke ɗin kyakyawa ce ajin farko, kuma na kamu da matukar kaunar ki da kallo farko" ko aji kin ta, bata yi wani alama da zai nuna cewa ta ji wani abu ko wani mamaki da jin zancen sa ba.
"Malam ba mu sayar da kyau da kuma Kauna a wannan restaurant ɗin nan, daga shinkafa da miyar steew, sai jolof da su tuwon semo, pepper chicken, pizza, burger, shawarma, da dai sauran kananan kayan cima, amma gaba ɗaya cikin jadawalin girke-girken mu babu me ma kace sunan abin cin? Yauwa kyau da kuma Kauna ko? To su dai babu su".
Tofa, Babbar magana me Jehan ke nufi kenan?🤔
Mutuwar tsaye Nawid ya yi tare da kara zaro idonsa yana kallon ta da kyau.
"A iya sani na ko yan kauye sun san menene so da kuma Kauna, sun san menene kyau, in fact sun san menene aure, amma yarinya santaleliya kamar Jehan gata kalar wayayyu yan gayu, ga iya zuba turanci, amma ta ce ba ta san soyayya ba, anya ba raina min wayo ta yi ba kuwa?" Sai zancen zuci yake.
Zazzakar muryar ta ne ta katse masa zancen zuci nasa da cewa "In kawo maka shinkafa irin ta ɗazun ne? Ko dai na yi tafiya ta?" Kara mamaki ya yi sosai
"Wai shin da gaske Jehan ta ke yi ba ta san menene soyayya ba ne?" Ya sake tambayar kansa da kansa, tambayar kuma da ba shi da amsarta, domin Jehan ita kaɗai keda amsar, kuma bai ga ala'mar fuskar da zai samu damar tambayarta ba.
Ya yi nisa cikin tunani, sai ganinta ya yi ta sa kai zata wuce ta bar wajen, cikin sauri ya fito daga ɗakin, ya sha gaban ta yana faɗin
"Haba Malama, ya isa haka zolayar mana please" karo na farko da ta ɗaura idon ta cikin na shi, taɓe baki ta yi, alamar mamaki ma ya bata,
"let me pass" shine abin da ta ce masa,
Kin matsa mata ya yi, sai ma kara matsowa kusa da ita da ya yi, ya kara kashe murya kasa kasa, irin salon jan hankalin nan ya ce
"Haba Malama, ni nasan ba halinki bane saboda ba ki yi kalar wulakanta mutane ba, sannan kuma daga ganinki kin san me nake nufi, kuma kin fahimci ina na dosa, wlh ba son wasa na ke miki ba, har ga Allah nake son ki, kuma aurenki zan yi, ba da wasa nazo ba"
tamkar da dutse yake magana haka Jehan ta masa shiru kamar bata a wajen, sai surutu yake zubawa ko uppan bata sake ce mi shi ba, kuma idan baku mance ba Jehan bata da yawan magana bata shiga harkar kowa.
Sun jima tsaye a wajen, bata sake magana ba. Da ta ga ji da jin surutan shi sai ta ce
"Malam ina son wucewa"
mamaki ne ya kama shi kenan yanzu duk wayan nan kalaman soyayya da ya zuba mata bata san su bane ko menene.
A zahirin gaskiya Jehan bata gane kalamansa ba, ta dai san soyayya da kaunar bayan haka duk kalaman da ya mata ba abin da ta fahimta, domin da hausa ya yi su, ita kuma kunsan ba jin hausa sosai take ba,.
Bawan Allah ya zage sai zuba kalamai yake yi ashe duk a banza ya yi su. Kuma sanin soyayya da Jehan ta yi bawai ta san yadda ake yi bane, a'a kawai dai sunan ta sani, dan ita bata kallon finafinai ma bare a ce zata kalli soyayya a wajen, bugu da kari bata da kawaye ko makamancin su, ba wani abin da ta sani game da soyayya bayan sunan shi soyayya.
Ganin Nawid ya yi mutuwar tsaye yana tunani ne yasa ta raɓa gefensa zata wuce, cikin sauri ya riƙo hannunta yana faɗin
"Haba malama kada ki min haka, wlh soyayyarki zata iya yi mini illar ki tausaya min, sosai kika mamaye zuciyata, ta ko ina, har ina ji a jikina ba zan iya rayuwa ba sai da ke, kada ki ce ba zaki karɓeni ba..."
Ji kake tass ta wake masa fuska da wani gigitacen mari ba tare da ya gama kalameta da yake yi ba, a fusace ta kwace hannun ta daga riƙon da ya mata, rai a matukar ɓace ta bar wajen ta bare da ta yi magana ba.
Shiru ya dafe kumatunsa, ya kasa yi mata magana, kuma ya kasa dakatar da ita har ta tafi, ko kaɗan bai ji zafin marin da ta masa ba, sai ma son ta da ya karu masa sosai a zuciyar.
(Umm giyar soyayya ba🤣)
A gaskiya zuciyarsa ma kara yaba mata yake yi ta yi namijin kokarin, hakan kuma ya kara burgeshi, yanzu ya dace ya kara ɗaura ɗamarar neman aurenta, a cewar sa, domin ita ce matar aure, mace mai kare mutumcin kanta wadda ko hannunta bata yarda wani namijin ya taɓa ba.
Sosai Nawid ya sa a ransa dole ya nemi auren Jehan kuma ya zama masa dole ya nemi soyayyarta, ita ta dace da rayuwarsa.
(Tirkashi aikuwa ka haɗa hanya da wahala)
Jiki ba kwari, tunani cike fal a ransa, ya wuce ya koma cikin ɗakinsa. Yana shiga ya tsaya a gaban mirror ɗakin tare da shafo in da ta maresa da hannunsa ya mannawa hannun nasa kiss, har da wani lumshe ido, shi a dole izzar Jehan da kuma kamewarta sun tafi da imaninsa. Shi ga shi ɗan soyayya.
( Soyayya manya.)
Ya ɗan jima tsaye a wajen, kafin ya fara haɗa kayansa dan ya koma Kaduna ya sanar da Ummi abin da ke ransa.
Ita kuma Jehan tana koma, kai tsaye cikin office ɗin Ibraheem ta nufa, yana ganin ta tun daga nesa ya zuba mata ido yana jiran ya ji wani bala'i zata sauƙe masa kuma.
(Ibraheem na cikin gararin da bala'i Jehan🤣 bawan Allah)
"Ibraheem!! Ibraheem!! Ibraheem!! Sau nawa na kira sunan ka?" Shine abin da Jehan ta faɗa lokacin da ta iso wajen, shiru ya zuba mata ido yana kallon ta.
Rai a matukar ɓace ta ce "Na ce ka kiramin ogan ka a waya ya zo nan ina son yin magana da shi"
"Ki yi hakuri zai zo ranar Jumma'a sai ku yi magana" Ibraheem na gama kai karshen maganar ta wuce ta koma bakin aiki ta, tana tunanin idan ogan su ya zo, ya zama mata dole ta faɗa masa, ba ɗakin kato da zata sake zuwa, domin ita ba yar iska ba ce.
Shi dai Ibraheem ido kawai ya bita da shi, dan yanzu shi burinsa ya lallaɓata ta samu ta yi aiki ta biya shi kuɗin sa, shiyasa baya wani biye mata, dan in ta ce ba za ta yi aikin ba, waye zai biya shi kuɗin sa, dan dai yasan gidan su Jehan ba ta in da za'a fitar da dubu ɗari biyar, kuma ko ƙararta ya kai ba ta in da za su iya biyan kuɗin, sai dai ma shi ya sake kashe wa su kuɗaɗen wajen biyan yan sanda da sauransu..
Tofa Jehan yau ake yin ta, ni na haɗa kayana nayi gaba sai mun haɗu da ku a gidan su Aafia gobe idan mai dukka ya kai mu
💞💞TRIPLET'S💞💞
🌹🌹Episode 23-24🌹
GIDAN ABBI💖
A yau a ka dawo da Aunty gida, ba laifi jikin nata ya ɗan yi kyau, amma bata iya tafiya saboda aiki da a ka mata, ba ta iya miƙewa tsaye sosai kamar yadda kowa zai miƙa, dan ma ita ta matsa zata dawo gida shiyasa Irfan ya karɓa mata sallama, baiwar Allah ta damu ne sosai a kan me ya sanya Abbi baya zuwa asibiti sosai, kuma a zahirin gaskiya ba'a faɗa mata me ya faru da ita ba, ba wanda ya gaya mata, ko mamanta da tazo ta yi jinyar ta, ita ma bata san meke damun yar tata ba. Sosai abin ke damun Aunty a ranta, me ta yi wa Abbi ya ke shareta haka.
Kusan komai Irfan ya ɗauki nauyin Aunty, ko wani abin take so shi ake kira, ko shi ko kuma Akil ko Imran, Abbi kam ko sun kira shi baya ɗaukar wayar, idan ya kirasu sau ɗaya da safe to sai kuma gobe da safe, Aunty ta yi kuka sosai sannan ta faɗa wa mamanta cewa tana ganin kamar Abbi na fushi da ita, sosai mamanta ta mata faɗa tare da shawari masu kyau a kan ta rinƙa yi wa mijinta uzuri wata kila wani aikin ne ya sha masa kai, hakan yasa Aunty ta matsa kawai su dawo gida, Allah sarki bata san me zata zo ta tarar a gidan ba.
A motar Irfan suka dawo, kuma shi ya ɗauko su, ita da mamanta, ita kam Aafia tun da taga Aunty ta farfaɗo ba ta mutu ba shikenan sai ta kama shabgar gabanta abin ta, ta koma ruwa, ta je suna kulla wani abin ita da Rufee.
Ko da su Aunty suka shiga cikin gida Abbi baya nan, haka shima daddy'n Jelly baya nan yana part nasu, a palo suka ba je.
Ganin sai zufa Aunty ke haɗawa ne ya sanya Irfan kunna musu Ac sanna ya wuce part na shi, shi da Imran, dan suna tare ko ina za su shiga.
Allah sarki Imran bawan Allah ya rame sosai sai manya-manyan idanun nan nasa irin na Jelly nan suka kara firfitowa saboda rama, gaba ɗaya fuskar sa ta sauya kamar ba shi ba.
Karfe biyu na rana daidai, motar Aafia ya danno hanci cikin gidan, har lokacin Aunty suna falo sai dai su Irfan sun fita basu a gidan, sun sake komawa neman Jelly, bayin Allah, kullun suna zarya tsakanin Kano da Kaduna.
Kusan a tare Aafia ita da Rufee su ka fito daga cikin motar, sai wani yauƙi da rangwaɗa Rufee ke yi, ta ci uwar kwalliya kamar wata aljana, ta labka wani uban eyeliner a ido, ga wani purple color jambaki da ta damɓara a bakinta, ko kyan gani babu, kamar mutun ya yi amai. Sanye take da wasu shegun riga da wando sun matseta sosai, wandon jeans ne da kuma riga top ta ɗaura wani jacket mai ɗan girma a saman kayan, wadda yazo mata iya cinyarta, ta zuba attachment a kanta, kamar wata yar kafurai.
Sai wani taunan chewing gum take yi tana baza baki.
"Aafia anya Auntyn kun nan ta dawo kuwa? Kada na yi zuwan banza ne" ta faɗa tana hura chewing gum da ta ke ci, Aafia tana kokarin rufe kofar motar ta ce
"Eh ta dawo mana, kafin ma su baro asibitin yaya Irfan ya ƙirani, ba kin ji ma lokacin da yake cemin na baro gidanku na wuce na same su a gida za su dawo da Aunty ba"
Wani nauyayyar ajiyar zuciya Rufee ta sauke, irin ta ji daɗin nan, kai da ganin Rufee kasan ba zuwar Allah da annabi ta yi ba, akwai wata manufa da ya kawo ta, ba duba jikin Aunty tazo ba, ko daga yanayin shigarta zai tabbatar maka da cewa ba dubiya ta zo ba, akwai dai wani abin.
Jerawa suka yi zuwa cikin falo. Aafia ce ta kwaɗa sallama, Aunty na kwance saman sofa idon ta cike tab da kwalla abin tausayi, ita kuma maman Aunty ta shiga kitchen dan yi musu girki.
Wani mummunar faɗuwar gaba Aunty ta ji lokacin da idon ta ya sauƙa kan Rufee, kasan cewar mace ita mai addini hakan yasa ta yi saurin karato addu'ar neman tsari daga wani mugun abu ko iska ko ɗan adam ko dai abokin gaba.
اللَّهُمَّ مُنْزِلَ الْكِتَابِ، سَرِيْعَ الْحِسَابِ، اهْزِمِ الأحْزَابَ، اللَّهُمَّ اهْزِمْهُمْ وَ زَلْزِلْهُمْ
Tana karanta addu'ar ta ji zuciyarta ta samu kwanciyar hankali.
Saman sofa Aafia ta zauna tana faɗin "Rufee kizo ki