Showing 93001 words to 96000 words out of 355604 words

Chapter 32 - Triplets Book 2 Hausa Novel Complete

10 Dec 2024

2809

ta dake ta fita da wani irin sauti kamar mai minsharin barci, sannan numfashi tata ma, zafi ne da shi kamar me.

A haka har barci ya yi awon gaba da ita.

Can cikin barci ta ji ana ƙoƙarin zame mata wandon dake jikinta, a zabure ta farka tare da buɗe idonta, mai ɗauke da ciwo karara.

Karaf sai cikin idon boda Jami'u,. idanunta suka sauƙa, ga shi idon nasa sun yi jawur kamar jini, dama ga shi ɗan baki.

Ihu ta saki, sai dai ihun nata ba sauti saboda matsananin zazzaɓin da take ji, da kyar ma take iya buɗe bakinta, tattara iya karfin ta tayi zata miƙe, da hannu ɗaya ya mai da ta ya danneta da karfi.

Sai ihu take yi, amma ba wanda zai iya jin ta saboda ihun tata ba sauti.

Zame hannunsa da ya danne ta ya yi yana kokarin cire mata wando, wani irin karfin ta ji ya zo mata, da iya karfin ta na karshe ta ture shi ya faɗi saman gadon kan shi a kasa, saboda tsawon gadon ya kare ta wajen.

A zafafe ta miƙe ta nufi hanyar fita daga ɗakin, sai dai bata kai ga fita ba, ta ji ya danko gashin kanta.

Ita dai Rimsha bata da wajen kamawa a jikinta sai gashin kanta, saboda suna ganin shi har baya, yana da daɗin kamawa, koda gudu take yi, za'ayi saurin riƙota ta gashin nata.

Janyota ta ya yi da gashin nata, wani wahalallen ihu ta saki, domin har ga Allah ji ta yi kamar zai tunɓuke mata gashin tata, saboda da iya karfin sa ya ja gashin.

Jan ta ya yi har zuwa saman gadon, ya kwantar da ita sannan ya sauka ya nufi wajen drawer kayan Kausar, dama gaba ɗaya kofofin gidan basa rufuwa, jam lock nasu ya ɓaci kuma ba su da key. Kofar palo ne kawai ke da sakata, shima an saka mishi sakatane, saboda shine na fita waje, da su Iya suka tafi, Rimsha bata rufe kofar ba, saboda bata ma san yadda ake rufewa ba.

Ganin ya tafi wajen drawer kayan Kausar ne yasa ta sake tattara iya sauran karfinta, ta miƙe ta diro kasa, ta nufi palo, yana ganin ta amma bai wani damuba, sai bincike yake yi cikin kayan Kausar.

Ita kuwa tana fita Palo ta nufi kofar fita, sai kuma me? Ashe azzalumin ya rufe kofar, dama ashe yana laɓe a cikin gidan tun da ya ji su iya za su ta fi biki, ita Rimsha ta ce ba zata je ba, shikenan sai ya laɓe yaki fita wajen aiki, har sai da suka tafi ya fito ya rufe kofar palon.

Cike da tashin hankali ta fara ƙoƙarin cire sakatar, bata iya ba, kuma bata taɓa ganin irin sakatar ba sai da tazo gidan. Sai jan sakatar baya take yi, tana yi tana kukan a kawo mata ɗauki.

Bata ankara ba, ta ji ya riƙo hannun ta, ya fisgota da karfi, ya ja ta zuwa cikin ɗakin, tun tana kokarin ihu ko za'a kawo mata ɗauki, tana tirjewa, har ta hakura dan yanzu muryar ta ma ya dai na fita ya dashe.

Saman gadon Kausar ya kwantar da ita, tana kokarin miƙewa, ta ki yarda ta kwanta, kafarsa ɗaya ya sanya ya take kafafunta dukka biyu, da karfi, sannan ya damki hannunta ɗaya, ya dauko wani gyalen Kausar ya ɗaure hannun nata da jikin kafar gado, shi kuma ɗayan hannun nata ya ɗaure a jikin window.

Bayan ya gama ɗaure hannu sai ya cire kafarsa a saman nata da ya take, kamar jira take yi ya cire, ta fara wuncila kafafun nata sama, alamar bata so, tana haɗa shi da girman Allah ya rabu da ita, ya kyaleta, amma ina babu imani ko kaɗan a ransa.

Daukar wani zanin Kausar ya yi ya ɗaure kafar ta ɗaya a jikin wannan window kusa da gadon, in da ya ɗaure hannun nata, sai dai ya ɗaure hannu ta a farkon window shi kuma kafarta a karshen window, sannan bai matse kafar nata da window ba, dan window ya ɗan yi sama, sai ya saki igiyar wato gyalen, ya ɗan yi musu balance, shi kuma ɗayar kafarta, a jikin kafar gadon ya ja igiyar zanin ya ɗaure a wajen, ɗaiɗai ya yi da ita kamar ana gasa kaza.

Ta yi kuka har hawayen ta suka dai na fita, sauka ya yi ya fita zuwa na shi ɗakin.

Yana fita ta fara kokarin tsinke ɗaurin da ya yi mata, amma ina ta kasa, dan gyale dai yana da kaurin da ba za ta iya tsinke shi ba.

A haka ya dawo cikkin ɗakin ya sameta, hannun sa rike da almakashi, zaro sleeping eyes nata ta yi wadda yanzu suka rine saboda kuka, da kyar da kyar ta ke iya maga, muryar ta baya fita, ga zafin zazzaɓi, amma a haka take ta haɗa shi da Allah ba gajiyawa.

Ganin tana takura masa da, Uhm, uhm ɗin dake fita da ga bakin ta ne, ya sanya ya ɗauko wani rigar Kausar ya cusa mata a cikin bakinta, sai girgiza kai ta koma yi, abin gwanin ban tausayi, duk wanda ya ganta sai ya mata ruwan hawaye.

Sanya almakashin nan ya yi, ya fara yanka mata wandon jikinta, daga kafar wandon ya fara har zuwa ƙugunta, ta gefe kenan. Bayan ya yanke wannan gefen ya dawo ta ɗayar gefen ma.

(Kai wannan Jami'u anya akwai Allah a kamarinka kuwa? Anya kai Musulmi ne? Marainiyar Allah ta'ala? Sai haɗaka da Allah take yi, amma kaki bari, Kai jama'a duniya ina zaki damu)

To ni dai ba zan iya wannan abin ba dan haka na haɗa kayana sai mun haɗu gobe idan mai dukka ya kai mu


💞💞TRIPLET'S💞💞


E29-30




Sanya almakashin nan ya yi, ya fara yanka mata wandon jikinta, daga kafar wandon ya fara har zuwa ƙugunta, ta gefe kenan. Bayan ya yanke wannan gefen ya dawo ta ɗayar gefen ma.

Runtse idanuwanta ta yi a cikin zuciyarta take faɗin "Ya Allah, kai kace mu nemi taimako ka a lokacin da muke bukata, matikar munyi yakini da kai kuma mun yarda kai ne zaka iya biya mana bukatar mu, ya Allah ina tawassuli da sunayenka tsarkaka guda 99 ya Allah ka kawo mini ɗauki, kada ka bari wannan mugun ya lalata mini rayuwa, ya Allah alfarma girman zatinka da izzar ka, albarkacin girmanka ya Allah ka sauko mini da ni'imar ka a gareni, na kareni daga wannan azzalumi, kaine arrahmanu ya Allah, mai rahma a kan bayinsa, mun saida, kuma na miƙa wuya agareka, babu wanda ya isa ya yi wa bawa abin da baka tsara masa ba, ba kuma wanda ya isa ya hana bawa abin da ka tsara masa, babu abin da ya isa ya yi motsi a dukka faɗin sammai da kassa ba tare da izinin ka ba, ya Allah ka taimake ni, wasbunallahu waniimal wakil, daga karshe ta rufe addu'ar tata da salatin Annabi salatin ibrahimiyya

Shi kuma boda Jami'u almakashin yasa yana, ya fara yanka ɗayan gefen wandon nata. Yana tsaka da yanka wa kawai ya yanke jiki ya faɗi a gefen ta, ita kuma dama ta runtse ido tana hawaye.

Jin ya faɗi kusa da ita ya sanya ta waro idanuwanta da sauri, dan a tunaninta ya gama yanke mata kayan ne zai fara lalata mata rayuwa.

Rinannun idanuwanta ne suka mata arba da Ayla tsaye riƙe da katon katako a hannu ta, sai haki take yi, tana mai da numfashi.

Cikin sauri Rimsha ta yi kokarin yunkurawa ta tashi, ta mance a ɗaure take, ba zata iya tashi ba, kuka ta saka da wannan dashashiyar muryar tata, ga kuma rigar Kausar a bakinta, ita ma Ayla kukan ta saka tare da yin wurgi da katakon ta haye saman gadon ta rungumo Rimsha tare da cire mata tsummar rigar Kausar ɗin dake bakin ta, suka ci gaba da hawayen a tare.

Abin da ya faru shine, lokacin da Rimsha ke jan sakatar kofar ta kasa buɗe wa, to da ya zo ya fisgo hannunta, wannan jan ta da ya yi, dama hannun ta ɗayar na kan sakatan, yana jan ta, ta janyo sakatar ya fita, sai dai dukkansu basu lura da cewa sakatar ta fita ba.

Ayla kuma bayan sun je gidan, ta kasa samun nitsuwa, ta kasa zama waje guda, sai tunanin jikin Rimsha take yi, har kuka ta rinƙa yi a ɓuye.

Su iya suna can suna cin uwar sabada, an sake musu kiɗa, sai tikar rawa suke, shine ita ta lallaɓa ta saci hanya ta bar gidan bikin, ta kamo hanyar gida dan tazo ta duba jikin Rimsha ko zata samu nitsuwa, baiwar Allah ta kasa samun sukunin.

Kasan cewar bata san hanya ba, sau uku tana ɓata hanya sai ta sake komawa baya, da kyar ta Iya gane hanyar.

Lokacin da ta shigo gidan Allah yasa bata yi magana ba, kawai ta nufi ɗakin Kausar, tun da ga ɗan bakin-bakin kofar ɗakin take jiyo nishin Rimsha hakan yasa ta karisa da sauri.

Turus ta tsaya a bakin kofa ganin abin da ke faruwa, lokacin ya gama ɗaureta yana kokarin yanka mata wando, ga shi ya toshe mata baki. Ganin haka yasa Ayla ta ja da baya a hankali, zuciyar na tafasa kamar zai fashe ya fito waje, har ta fara hawaye, addu'a take yi Allah yasa bai lalatawa Rimsha rayuwarta ba.

Kitchen ta fara shiga, bata samu madaki ba, sai ta fito waje, da farko katon dutse ta ɗauke, sai ta ji bai yi ba, hakan yasa ta jefar, ta fara yan dube-dube, can ta hango katako, shine ta ɗauko cikin sauri ta koma cikin gida.

Ta shiga ɗakin a hankali-hankali take tafiya, Allah ma yasa Rimsha ta runtse idanunta a lokacin, shi kuma hankalin shi ya yi nisa yana tunanin yadda zai fara shigar Rimsha.

Tana isowa wajen ta ɗaga katakon da iya karfinta na karshen ta buga masa a kai, shine ya yanke jiki ya faɗi sumamme ne ko matatce ne wallahu a'alam, wannan shine abin da ya faru.

Sosai suke kuka. Sai da suka yi mai isar su, sannan Rimsha ta ce "Ayla kwanceni" Ayla bata iya jin me Rimsha ke faɗe saboda maganar nata baya fita sosai, sai da ta matso da kunnenta sai tin ɗan bakin Rimsha ɗin, sannan ta iya jiyo me take faɗa.

Cikin sauri ta sanya hannu tana kokarin kwancewa amma ina abin yaci tura, ba ɗaurin wasa ya yi mata ba.

Ganin ba zai kwancu ta daɗi bane ya sanya ta ɗauko wannan almakashi da ya fara yanka wa Rimsha wando, ta fara yanka kayan Kausar ɗin dukka tana zubarwa.

Bayan ta kammala, Rimsha ta miƙe ta rungumeta da kyau tana zuba mata godiya.

Itama Ayla godiya ta rinƙa yi mata, domin a cewar ta kome zata yi wa Rimsha ba zata iya biyan ta ba, domin Rimsha ita ce silar fitarsu Daular Mutuwa, shekara uku Ayla tana Daular Mutuwa, har ta cire ranta da fita sai ga shi Rimsha ta tazo ta zamo musu silar fita, hakan ya sa take kula da Rimsha sosai.

Da kyar Rimsha ta iya dirowa kasa daga saman gadon sannan ta miƙe tsaye, sai layi take yi kamar zata faɗi, wajen drawer kayan Kausar ta nufa, dogon riga ta ɗauka ta sanya, sannan ta ɗauki wani dogon wandon jeans ta cire na jikinta daya yanka ta jefar ta sanya wannan, sai binta da ido Ayla take yi.

bayan ta gama saka kayan nata, ta shirya tsab, ta fito da wannan paper da ta yi zanen Romeo a jiki, sannan ta ɗauki takardun girkin da ta saya jiya a kasuwa, ita dai Ayla sai binta da ido kawai take yi.

Sai da ta gama haɗa komai nata, bata bar ko abu guda ɗaya ba, sannan ta riko hannun Ayla tana faɗin muje Ayla.

"Rimsha ina kuma zamu je? Waye muka sani a nan?" Rimsha kamar zata yi kuka, sai layi take yi, ga zafin zazzaɓi, kanta kamar zai fashe mata saboda ciwon da yake yi mata.

Da kyar ta iya fara magana "Ayla kina son ne mu cigaba da zama a nan gidan? Kina son ne mu zauna su lalata mana rayuwa, ko ma su kashe mu baki ɗaya?".

Girgiza kai Ayla ta fara yi tana faɗin "A'a Rimsha bana so su lalata mana rayuwa, to amma abin da zaki duba a nan shine, waye muka sani a nan? Idan mun bar gidan nan ina muka nufa? Dawa muka san zamu haɗu? Gara wayan nan da already mun san halin su, mun san abin da suke nufi da mu, idan muka barnan bamu san da suwaye zamu sake haɗuwa ba, wata kila ma wayan da zamu haɗu da su sunfi wayan nan munin hali, dan haka Rimsha ina son ki tsaya ki yi tunani kin ji?".

Hawaye sosai Rimsha ta ke yi, "Ayla ya zama dole mu bar gidan nan, koma da su waye zamu sake haɗu, dole mu tafi, kada ki manta Ayla, muna Sallah sau biyar a rana, har ma mu kara da nafila, irin su walaha, shafa'i da witiri da sallar dare, sannan kada ki manta muna azumin litinin da Alhamis, muna askar da rokar Allah ya kare mu a ko yaushe, a kuma duk in da muke, In Sha Allah, Ubangijin ba zai taɓa barin rayuwar mu ta wulakanta ba, kada ki manta Allah da kansa ya yi alkawarin tallafawa duk wanda ya riƙe Sallah biyar a rana, yana yin su yadda ya dace kuma a kan lokacin su, ki sa a ranki Ayla Allah na tare da mu, kuma bayin Allah masu taimako basa karewa a duniyar nan, ki yarda dani mu bar gidan nan, kuma idan zamu fita, mu fita da yakinin Allah ya taimake mu ba wani ba, da izinin Allah zai kawo mana ɗauki"

Ta kai karshen maganar tare da fara tafiya tana tangal-tangal.

"Rimsha a hakan zamu tafi? Kina tafiya kamar zaki faɗi kasa" "Ayla kiyi wa Allah kizo mu tafi, idan kuma zaki zauna a nan ne to Bismillah, kada ki duba dan bana iya tafiya da kyau, niyar mu na tseratar da mutuncin mu shi zaki duba"

Tana magana tana tafiya, ganin hakan yasa Ayla ta yi saurin karisawa wajen ta, ta ɗan riƙota dan ta taimaka mata, shi kuma boda Jami'u ya ji bugun katako, ko motsi baya yi, haka zalika baya numfashi, da alama cikin kansa ne ya sha bugun da babu jini ko kaɗan, sai kumburi da kan nasa ya yi kamar anhura balo-balo.

Wajen gidan gaba ɗaya suka fito, sai da suka tsaya na yan mintocin da ba su fi biyar ba, sannan suka fara tafiya ta Eyankorin junction.

Sunyi Sa'a babu kowa, har kofar gidan su waliya ba mutane.

Da kyar Rimsha ta iya kai bakin junction ɗin, daga nan suka miki gabas suka ci-gaba da tafiya.

Sun yi tafiya mai nisa har suka sauƙa daga bakin titin suka fara ratsa lunguna.

Daidai wani kangon gida, Ayla ta zube kasa, saboda azababben ciwon mara da ya ziyarce ta lokaci guda.

Hankali tashe Rimsha ta yi kanta tana kiran sunan ta, sai murkusoso take ta riƙe cikinta, nan take ta fara hawaye, wani na bin wani.

"Ayla dan Allah ki yi mini magana, ki faɗa mini meke damun ki, na shiga uku na, Innalillahi wa inna ilaihir rajiun, Ayla dan Allah ki ta shi".

Ina Ayla ko magana ta kasa yi, sai kuka kawai yake yi, Rismha na ƙoƙarin sake yin magana, idanunta suka mata arba da jini a jikin rigar Ayla, da yake doguwar rigar da ta sanya mai haske ne, sky blue ne. Ihu Rimsha ta saki, lokacin guda ta ji karfi yazo mata, dan a tunanin ta wani abinne ya sami Ayla, tabbas ta karanta mace na yin haila, sai dai bata san ya hailar take zuwa ma mace ba.

Da sauri ta miƙe ta bazama neman wanda zaizo ya duba mata meke damun Ayla, ko kaɗan Rimsha ba ta yi dana sanin barin gidan su Kausar ba, sai dai ita Ayla ta yi dana sanin yin hakan ɗin, domin a cewar ta, da tana gidan su Kausar ko ba komai za'a kawo mata ɗauki.

Ta hanyar da suka bi zuwa wajen, nan Rimsha ta bi, sai kuka take yi tana addu'a Allah ya dafa musu.

Tana kokarin fita lungun dan ta nemo mai duba mata Ayla, gaba ɗaya ta birkice, jiri take gani, saboda yinwa da kuma ciwo, bata gani sosai, saboda karfin hali da tausayi irin tata, hakan yasa ta rinƙa ɗaga kafa da iya karfinta kawai tana takawa, bata san inda take sauke kafar tata ba, domin bata iya ganin gaban ta.

Bata ankaraba ta ji ta yi karo da mutun, baya ta yi zata faɗi, cikin sauri ya riƙe hannun ta yana kallon kyakkyawar fuskar ta wanda ya birkice a yanzu.

"Lafiya baiwar Allah? Ina zaki je kike sauri hakan nan? Me ya same ki kike kuka?" Cikin harshen Hausa ya yi mata magana.

Jin an mata magana da Hausa yasa ta yi saurin waro idanuwanta waje.

Wani matashine, irin matasan fulanin nan, masu zuwa karatu ko dai wani abin, daga ganin sa, ɗan arewa ne, ba bayarabe bane, yana da tsabta jikinsa fes fes, ɗan gayu, ya ci gayunsa, daga gani kasan akwai naira a tattare da shi, hannusa ɗaya na riƙe da wani leda da a ka rubuta Item 7 a jiki, ledar tana da girma, sai tashin kamshin yake yi, kai daga gani kasan ba ɗan datti bane, a shekaru ba zai wuce 27 years ba, yana da kyau daidai gwargwado, kunsan jinin Hausa fulani da kyau ba'a magana.

Ganin shi yasa Rimsha ta kara fashewa da kuka, sakin hannunta ya yi yana faɗin "Lafiya ko dai baki jin Hausa ne? To bari na miki yarabanci ko fulatanci sai ki zaɓi yaren da kike ji ki bani amsa" haka ya maimaita tambayar da ya yi mata da farko, da yaren yarabanci da kuma fulatanci, ko zai samu ta amsa masa yare ɗaya.

Ciki ciki ta amsa masa da taimako take nema, sai dai bai iya jin taba saboda muryarta baya fita kuma ga shi tana kuka.

Ganin ta ki yi masa magane ya sa, ya sanya kansa zai wuce ta, cikin sauri ta riƙo rigarsa, tare da sanya hannu ta shake wuyarta tana kokarin kakalo magana da karfi.

Ganin haka yasa ya fahinci tana yi masa magana, amma baya ji ne, wata kila kurma ce ko bebiya, hakan yasa ya fara yi mata yar kurma-kurma, ita ma yar kurma-kurma kawai


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login