Showing 312001 words to 315000 words out of 355604 words
tare da riƙo hannayenta a cikin nasa.
Kwace hannu ɗaya ta yi tare da fara shafa kyakkyawar gashin kansa tana matukar kaunar daddyn nata.
"Babyn daddy ayi wa daddy afuwa ko" ya faɗa ba tare da ya ɗago kan nasa ba.
"Daddy to ka saka mani kaya ka ji ko?" Ɗan ɗago da kan nasa ya yi ya saci kallonta yana faɗin "E yanzu kuwa dan ma muje asibiti".
Zaro idanu ta yi kamar zata yi kuka ta ce "Daddy ni bana son asibiti, ina tsoron su yi mani allura ka ji?" Zura hannayensa ya yi ta kugunta ta baya ya ɗan riƙota yana faɗin "To shikenan bari na sanya Abbi ya kira mana likitarsa ya turo mana nurse mace ta zo ta duba mani ke kin yarda?" Gyaɗa mashi kai ta yi tana faɗin "E daddy amma ita ma ba zata yi mani allura bako?" Sai lokacin ya kalli fuskarta kai tsaye, cikin sauri ta rufe idanunta dan kunyarsa da take ji.
"Baby da allura da kuma abin da na yi maki daren jiya wanne ya fi zafi?" Shiru ta ɗan yi kafin ta ce "Daddy ni ai sau ɗaya ma aka taɓa yi mani allura lokacin bani da lafiya sosai, mamana ta roƙi wata makwabciyar mu ta kai ni asibiti, amma gaskiya akwai zafi allura sosai kuma shima...." Ta kasa fitar da shima abun da ya yi mata akwai zafi sosai fiye da allura, maganar ta kasa fita baiwar Allah, sai ta yi shiru.
"Baby ina matukar kaunar ki, duk abin da ake buƙata a tattare da mace kafin ta cika mace ta gari kin haɗa shi, kina kaunar daddy kamar yadda yake son kuwa?" Cikin sauri ta ɗaga mashi kai tare da fara shafa kyakkyawar gashin dake a matsayin sajensa izuwa wajen kewayayyar gashin dake a bakinsa.
"Daddy Allah ina son wannan gashin, yana yi maka kyau sosai da sosai, nima kuma yana yi mani kyau sosai da sosai". Ta faɗa tana mai cigaba da shafa gashin kewayen bakin nasa.
Hannun nata ya riƙo tare da kaiwa ɗan bakinsa ya yi mata cizon soyayya har sai da ta ce "Wash daddyna akwai fa zafi". Wash ɗin nan da ta ce yasa ya miƙe tare da riƙo hannunta ya sauƙeta kasa.
Kara ta saki tare da kankame shi dan har ga Allah ta ci bakar wuya a hannunsa, bata iya taka kafarta.
Sorry ya ce mata tare da duƙawa akan ta hau bayansa, ba musu ta haye ya goyata tare da juyi da ita a cikin ɗakin yana mai jin matukar farinciki abinsa, abin gwanin ban sha'awa da kuma burgewa.
Ya jima yana juyi da ita tare da gaya mata kalamai masu daɗi kafin ya sauƙeta a saman bed nasu ya ɗauki wayarsa ya kira layin Abbi.
Lokacin kuma shima Abbi yana hannun Hajiya Hadiza, idan baku manta ba mun ɗan koma baya ne dan ku ji abin da ya faru wunin ranar a gidan na Abbi, kafin mu kai daren da jelly ta dawo, kuma idan baku manta ba Hajiya ta zo ta ɗauki Abbi ɗazun a palo.
Sau biyu yana kiran Abbi amma shiru bai ɗauka ba dan shima baya duniyar mutane, ɗan kallon babyn tasa ya yi baya son fita ko nan da palo ya barta ita kaɗai a ɗakin, hakan yasa ya kira layin Irfan, shima Irfan a lokacin yana hannun Akila tana zuba mashi shagwaɓa son ranta, duk ya birkita bawan Allah, suna a cikin mota suna zaune, yau Akila ta hana shi komawa, kuma Allah ya rufa masu asiri Ammie tana ta zuba barcinta bata tashi ba.
Ganin kiran bappan nasa wadda ya fi kauna yasa ya ɗauki kiran, badan daddyn Jelly bane ya kira shi da ba zai iya ɗaukar kiran kowa ba bayan Abbi, amma da yake yana bala'in kaunar daddy shiyasa dole tasa ya ɗauki kiran. Sallama ya yi tare da ɗagawa bappan nasa gaisuwa.
Daga ɗayan ɓangaren daddy ya ce ya turo mashi da number Aunty idan yana da ita, to ya amsa da shi tare da katse kiran ya tura mashi number.
Number na shigowa daddy ya fara kiran layin tata, da yake ita tana da number daddyn ta ɗauka a wayar Abbi sai ta gane cewa shine, a lokacin da kiran ya shigi ta gama shan kukanta akan abin da Hajiya Hadizatu ta yi mata, ta sha kukanta son ranta tana kwance saman gado.
Tana ganin kiranshi ta ɗauka, bai jira dogon gaisuwarta da kuma sallamar ta ba, kawai ya ce "Sadiya Maik ne please ki saka Hanan ta kawo wa baby kayanta". Da yake ita ma bata cikin mood mai kyau sai kawai ta amsa mashi da to, ba dan haka ba da sai ta tsokane shi, amma da sai ta ce to ya dawo mata da kanwarta haka ya isa, shima dai yau baya jin jan magana da ita shiyasa kawai ya yi mata maganar a takaice.
Miƙewa ta yi ya shiga toilet, furkarta ta wanke sannan ta fito ta nufi ɗakin su Hanan ɗin. Kwance ta isko Hanan tana duba wasu littattafan A'afia kamar tasan me aka rubuta a ciki.
"Hanan tashi ki ɗauki kayan Ayla masu kyau ki kaiwa mijinta". Shine abin da aunty ta faɗa tana ƙoƙarin juyawa ta bar wajen.
"Aunty ina wuni?" Shine abinda Hanan ɗin ta faɗa, a takaice aunty ta amsa sannan ta wuce ta koma ɗakinta.
Miƙewa Hanan ta yi sauri sauri ta ɗauki kayan ta fito. Shi kuma daddy yana gama magana da Aunty ya rubutawa Abbi massage akan suna buƙatar likita mace dan ta zo ta duba mashi babynsa.
Bayan ya tura saƙon sai ya mayar da wayar saman bedside drawer ya jawota jikinsa yana shafa bayanta a haka Hanan ta yi masu sallama a palo.
Yana ƙoƙarin miƙewa ta riƙe shi tana faɗin "Daddy Hanan ce fa, ni ka bari zan je in karɓo kayana". Wani irin mamakine ya kama shi, wato Ayla ta fara kishin shi kenan? Gaskiya ba ƙaramin daɗi abin ya yi mashi ba, bai san time da ya runhumeta sosai yana matse ta a jikinsa ba, sai yanzu ya kara tabbatar da tana son shi so irin na aure, da yana mata kallon kamar tana son shi so irin na uba da ƴa ce kawai.
"Daddy bari na je na karɓo ko?" Girgiza mata kai ya yi kafin ya ce "No baby ba zaki iya tafiya ba, kuma idan kika fita yanzu Hanan zata tambayi me ya same ki, kin ga kuma wannan sirrin mijinki ne, daga ke sai ni, tun da baki so nayi magana da ita Hanan ɗin ne kice ta ajiye kayan a palo ta ta fi, idan ta tafi sai na je na ɗauko ko?" Gyaɗa mashi kai ta yi tana ɓoye fuskarta a kirjinsa.
"To ki ce ta ajiye kayan ta tafi". Ɗan ɗago kanta ta yi daga kirjin nasa tare da ɗaga murya ta ce "Hanan ki ajiye kayan a saman sofa zan zo in ɗauka". To Hanan ta amsa mata da shi, sannan ta ajiye ta tafi. Duk wanda ya zauna da Aunty sai ya koyi kalmar to ko yana so ko baya so, tafi kwarewa a iya amsa to kawai, bayan shi babu wani action kuma, yanzu ga shi Hanan ma ta koya.
Sai bayan tafiyar Hanan da kamar minti 5 haka sannan Ayla ta kyale daddy ya je ya ɗauko kayan ya zo kuma ya sanya mata ya shirya kayarsa tsab, abin gwanin ban sha'awa, har lokacin kuma bai daina jin wannan faɗuwar gaba da yake ji ba, sai dai addu'a da yake yawaita yi a cikin zuciyarsa yasa ya sami kwarin gwiwa akan ba wani abu na sharri da zai faru da su. Haka suka cigaba da zuba soyayyarsu son ransu.
After some hours, bayan Abbi ya gane kansa ne ya kalli massage ɗin daddy sai ya kira Dr akan ya turo masu likita mace yanzu.
Ba'a ɓata lokaci ba sai gata ta zo, aunty ce ta yi mata jagora zuwa part ɗin Daddyn, da yake yasan da batun zuwar likitar sai ya ce su shigo, a lokacin kuma Ayla na kwance a saman kirjinsa yayin da shi kuma yake jingine da jikin headboard na gadonsun.
Kunya ne ya kama Aunty ganinsu a haka, daddy ko kunya bai ji ba bare kuma ya yi wani ƙoƙarin raba jikinsa dana Aylar, sai ma wani kara riƙota da ya yi, sai da Dr ta ce zata yi aikinta sannan ne ya kwantar da ita ya miƙe jikinsa na sanye da farar jallabiya.
Hararar wasa ya wurgawa Aunty yana faɗin "Ko dai kina da abin faɗe ne?" Murmushi ta yi kafin ta ce "A'a yaya Maik ni na isa? A'a sai ma anjuma" ta faɗa tare da juyawa ta fice abinta, dan bata cikin yanayi mai daɗi idan ta biye mashi hawan jini zai saka mata.
"Yallaɓoi ka ɗan bamu waje ko?" Cewar Dr. Girgiza kai ya yi kafin ya ce "Aa duk abin da zaayiwa baby ayi shi a gabana ina gani".
Shiru Dr ta yi bata sake yin magana ba dan tasan irinsu daddyn Jelly baa jayayya da su akan matansu, idan suka ce ba za su yi abuba to ba za su yi ɗin bane.
Dubata Dr ta fara yi shi kuma ya koma kusa da ita ya zauna tare da kwantar mata da kanta a saman kirjinsa yana shafa face nata.
A haka har Dr ta gama dubata sannan ta ɗago ta kalle shi ta ce "Sir akwai alluran zazzaɓi da kuma magunguna da zan bata, amma dan Allah sir a yi ƙoƙarin a bata kulawa sosai sannan ta rinƙa shiga ruwan zafi sosai, bacin haka kuma a ɗan barta ta huta, ina nufin kada a kusanceta kamar na sati guda haka, idan ba haka ba za'a iya samin babbar matsala". Jinjina mata kai ya yi alamar okey.
Kuka ta sa mashi tana faɗin "Daddy kai fa ka ce ba za'ayi mani allura ba, amma to naji ta ce zata yi Mani, please daddy wlh bana so". Rungumeta sosai ya yi yana faɗin "Ba zaayi maki ba, Dr bamu magani kawai ban da allura baby bata so". To Dr ta ce sannan ta rubuta mashi magani tare da nuna mashi yadda za'a sha maganin, karɓa ya yi tare da tambayarta kuɗin aikinta, bayan ta gaya mashi ya karɓi account number ta ya zuba mata kuɗinta har da kari, ta yi mashi godiya suka yi sallama ta tafi.
Tana tafiya ya kwantar da babyn tasa ya ɗauki waya ya kira Aunty akan a kawo mashi abinci ya karya, dan sai yanzu ya ji kamar zai iya cin abinci, buƙatarsa ta biya ya ji ba wata babbar matsala ne ya same babyn tasa ba.
A ɓangaren su Irfan kuwa, yau sun sha soyayya iya soyayya da AKILA har sai karfe 1 na rana sannan suka yi sallama ya dawo da ita gida daga yawon da suka tafi, sun je wurare daban daban, wuraren wasanni wajen yawo na masoya, abin ba'a magana dan sun mace wa junansu sosai yau, ta kara narka zuciyar Irfan a tsantsan kaunar ta.
Lokacin da ta dawo gida a palo ta sami Ammie tana tsaye, da sallama ɗauke a bakinta ta shigo cikin Palon, da yake lokacin da Ammie ta tashi bata same ta ba ta kira layin ta akan ina ta tafi, shine ta yi mata karya akan tana gidansu Anisa kawarta kanwar A'A kenan, tun lokacin a waya Ammie ta yi mata faɗa sosai akan kada ta kara yin hakan, ta fita babu tambaya, da yake dai dama abaya bata taɓa yin hakan ba, ta fita babu tambaya, shiyasa Ammie taba ɗauki wani mataki ba, ta ce tun da bata taɓa yi ba bari ta ɗaga mata kafa na yau kawai, ita kuma Akila ta ɓoyewa Ammie ainahin in da suka je ne dan saboda tasan Ammie ta tsani family'n Abba sosai, idan ta ji da Irfan suke a tare to ba makawa raba su zata yi.
Rungume Ammie ta je ta yi da gudu tana bata hakuri, ita ma Ammie rungumeta ta yi tana mai karɓar hakurin tata tare da ce mata kada ta kara. To ta amsa da shi daga nan ta saki Ammie ta koma ɗaki.
Sai kuma me? Tana shiga ɗaki ta fara duba wayarta ko zata ga saƙon ɓoyayyen masoyi, amma ina shiru bai tura mata komai ba, abin ya dameta sosai da sosai, haka ta wuni sukuku, bai tura mata saƙo ba bai kuma kira ta ba har dare, bayan ta ci abincin dare ta kwanta yaya Irfan ya kirata, ta kasa ɗaukar kiran nasa saboda begen ɓoyayyen masoyi take yi, ba zata iya magana da kowa sai shi, duk ta rasa natsuwarta wadda har da hawaye ta fara yi, ta shiga damuwa ainun, tana jin Irfan yana ta kiran ta amma ta ki ɗauka, a yadda take ji ma ba zata iya yin magana ba sabo ɗacin da zuciyata yake yi mata.
Haka Irfan ya ga ji ya hakura ya kyaleta dan yana tunanin wata kila barcine ya ɗauke ta.
Ita kuwa ta kasa barci har dare ya tsaya, daga karshe ma miƙewa ta yi zaune a tsakiyar gadon tana tunanin mafita, babbar damuwar ba tama da number sa bare ta kira shi ko ta yi mashi massage.
Wasa wasa har ta kai karfe 2 dare tana zaune tana ruwan hawaye ta kasa runtsawa. Soyayya tabarmar kaya kenan, abin da Akila bata sani ba shine, asalin wadda zuciyarta yake so ba yaya Irfan bane ɓoyayyen masoyi ne, shi kuma yaya Irfan soyayyar yaya da kanwa take yi mashi, a nata tunaninta da yarinta irin tata a aboki ta ɗauki ɓoyayyen masoyi, bata san abin ya wuce haka ba.
Sai misalin karfe 2:20 ya kira layinta, lokacin da kiran ya shiga a razane ta kai hannunta ta ɗauki wayar a saman bedside drawer, jikinta har kerma yake yi saboda tsananin kewarsa da kuma kaunarsa ya haɗu kuma da zumuɗin ya kirata yanzu.
Da kyar ta iya picking na call ɗin sakamakon kerma da hannunta yake yi. Ko da ta ɗauki kiran shiru ya yi mata bai yi magana ba, muryarta har ya dashe saboda kukan da ta sha, can kasa kasa ta ce "Hello".
Ya ɗauki tsawon minti 10 shiru bai amsata ba, ita ma shiru ta yi tana jin yadda yake motsi alamar akwai abin da yake yi, domin har karar Tv dake magana a kusa da shi tana ji, shine dai ya ki yin magana.
Cigaba da kukanta ta yi tana goge hawaye da majina da tissue dake saman bedside drawer kusa da ita.
"Kin dai san bana son kukan nan naki ko?" Shine abin da ya faɗa, kuma ya yi maganar kasa kasa kamar wadda baya son furta maganar.
Cikin sauri ta goge hawayen nata tare da dakatar da kukan nata tana faɗin "Kayi hakuri". "Me yasa kika yi mani alkawarin da kika san ba zaki cika ba?".
Zaro idanunta waje ta yi a ɗan tsorace ta ce "Me na yi maka kuma?" Shiru ya ɗan yi kafin ya ce "Daga yau na yi niyar fita daga harkarki amma kuma sai na kasa yin hakan, shiyasa kika ga tun da muka yi waya da safe ban sake kira ki ba, kuma ban turo maki sako ba saboda na saka a raina zan rabu da ke ne dan baki ɗauke ni da mahimmanci ba".
Kuka ta sa mashi tana faɗin "Me nayi maka da zaka ce mani hakan?"
A wannan karon da ɗan ɗaga murya ya fara magana kuma da alama ransa a matukar ɓace "Me yasa kika ce ba zaki yi wa Irfan dariya ba kuma kika yi mashi har ma da kwanciya a jikinsa? Me yasa zaki yi mani hakan? Kin dai san ina da kishi kuma na gaya maki tun da wuri, ni ban shiga hakkin ki ba na barki kina hira da shi dan naga kina son hira da shi ɗin, amma me yasa ke kuma zaki baƙanta mani rai har haka? Me yasa da kuka je wajen cin abinci kika bashi abinci a baki? Me yasa zaki bari ya taɓa jikin ki lokacin da ya goge maki ice cream a bakin ki? Kin san ya naji kuwa? Kinsan adadin tafasar da zuciyata ta yi kuwa? Kin san irin cikin azabar da na wuni yau kuwa? Do you know how much i love you kuwa? Meyasa kike kokarin tarwatsa mani zuciyata? Me nayi maki? Laifi nayi ne dan nace ina son ki? Amma dai ba komai dole na koyawa zuciyata kin ki ko zan huta!!".
Sosai Akila take kuka kamar ranta zai fita, ta kasa magana saboda bata da abin da zata gaya mashi.
Sun ɗauki tsawon minti goma a haka kafin ya ce "Heartbeat ki daina kukan nan haka ya isa bana son ji, kina kara mani ciwo akan ciwo kin ji ko?" A wannan karon ya yi maganar tasa cikin sanyin murya da kuma sigar rarrashi.
"Heartbeat ba zan iya yin shiru ba, ba zan iya ba". Kara yin kasa da muryarsa ya yi cike da shagwaɓa da sigar rarrashi ya fara magana "Bana son kukan ki ko kuma in ganki a cikin damuwa, hakan kuma yasa ma na kiraki yanzu saboda naga kin kasa barci kina cikin damuwa har da kuka wadda nima zuciyata ta kasa juran hakan, ki daina ki yi shiru ko kuma nima na fara yi maki nawa kukan, kuma ni gaskiya ina da wuyar rarrashi gara ma ki sani".
Kwanciya ta yi tare da rungume pillow a kirjinta ta ja bargo ta shige ciki tana faɗin "Heartbeat kasan wahalar da ni da ka yi yau kuwa? Tun karfe ɗaya na rana da na dawo cikin gidan nan nake cikin bakin ciki da ɓacin rai na ganin baka kirani ba, me yasa zaka yi mani hakan? Meyasa ka zaɓi ka wahalar da Heartbeat taka? Ko dan kasan na damu da kai ne? Muna hira da yaya Irfan amma kai nake tunani, komai nake yi fa kai nake tunani, why zaka yi mani hakan?".
Nisawa ya yi kafin ya fara magana a nutse tare da yin kasa da murya cikin salo da zai nuna maka ya san me yake yi "Heartbeat duk wahalar da kika sha baki kai ni ba, yau zuciyata kamar zata fashe nake ji, na wuni cikin tashin hankali da rashin natsuwa, na sha wahala, idan na rufe idanuna kawai ke nake gani kina kwance