Showing 165001 words to 168000 words out of 355604 words

Chapter 56 - Triplets Book 2 Hausa Novel Complete

10 Dec 2024

2814

kayana sai mun haɗu gobe idan mai dukka ya kai mu, dan jin yadda zata kaya*)

💖TRIPLET'S💖💖


47-48

Gidan Abba.

Sosai su Rimsha suka shirya haɗaɗen girkinsu mai rai da lafiya, bayan sun kammala suka jere a saman dining table, Sannan Akila ta wuce part nasu dan ta je ta yi wanka, ita kuma Rimsha ya wuce ɗakin ta dan yin wanka.

After some hours da ba su fi biyu ba.

Zaune suke a palo sun baje suna cin abinci suna hira, Imran, Akila, Rimsha, tamkar sun saba sosai haka suka kasance, suna ci cike da nishaɗi da kuma santi, sai hirarsu suke yi.

Bayan sun gama cine, Akila ta ɗauko Alqur'ani mai girma a ɗakin Imran tana faɗin Rimsha ta kara mata karatu, dariya sosai Rimsha ta yi kafin ta ce "Aunty Akila ina da tabbacin kin wuceni a karatu" "A'a Rimsha Allah ban wuce ki ba ni dai ki kara Mani" to Rimsha ta amsa mata da shi sannan ta karɓi Alqur'ani ta fara karatu, kunna recording Imran ya yi a wayarsa yana recording na zazzakar murya nan nata.

Cikin suratul Maryam take karatun a nutse, a wannan hali Akil ya shigo ya same su, saman sofa ya zauna yana gaishe da Imran, da fara'a Imran ya amsa sannan suka yi shiru suna sauraron kira'ar Rimsha dake tashi, ga zazzakar murya nan nata ba'a magana.

Sai da ta kai aya sannan ta ce "Aunty Akila wani sura zan duba Maki?" Akila na ƙoƙarin yin magana Akil ya rigata da cewa "Yaya Imran wannan ita ce wadda ka gaya mani jiya a kan ka kawota gidan nan ko?" Gyaɗa mashi kai Imran ya yi alamar e.

Dawo da kallonsa kanta ya yi tun kafin ya yi magana ta rigashi da cewa "Ina kwana?" lafiya ya amsa mata da shi sannan ya ɗaura da cewa "A ina kika tsaya da hadda?" Akil kenan yana bala'in kaunar ya ga mutun yana karatun Addini, ko da bai san mutunba matukar zai yi karatun addnin tofa zai taimaka mashi ba kaɗan ba.

Bayan ta gaya mashi ne, sai ya ce "To zan koma Madina nan da wata mai shiga, kafin na koma sai ku rinƙa zuwa ina kara maku har ma da na boko, kullun karfe 5 na yamma zuwa shida zamu yi lesson, yanzu ma bari na baku hadda koda shafi ɗaya ne, amma fa duk wacce ta yi wasa zan zane ta, bana son wasa da karatu". Sai murna suke yi suka amsa mashi da to, tare da kawo mashi Alkur'ani kowace ta faɗi daga in da zata tashi, nan ya kara masu shafi bibbiyu dan sun ce ɗaya ya yi masu kaɗan.

Bayan ya kara musu ne ya jaddada masu karfe 5 daidai su same shi a garden na gidan dan su kawo haddan su ya kara masu wani.

Sai daɗi suke ji suka amsa da to tare da miƙewa suka nufi bedroom ɗin Rimsha.

Suna shiga Rimsha ta ajiye Alqur'ani mai girma a saman mirror drawer, sannan suka haye gado suka fara zuba hira. Suna tsaka da hira Ahmad ya kira, cikin sauri Rimsha ta jawo wayar, tana ƙokarin yin picking kenan Akila ta ce "Kai Rimsha ki rinƙa jan aji mana kada ki ɗauka da wuri ki bari sai wayar ta kusa katsewa, idan ba haka ba yaya Ahmad zai ce kina da arha sosai, ko muna son abu ya kamata mu rinƙa jan aji akan shi". Harara Rimsha ta watsa mata kafin ta ce "Ni na ce maki ina son shi?" Yar dariya Akila ta yi tana faɗin "Ai ba ke kika ce ba, alama ce ta nuna, har da wani saurin ɗaukan kira, kai Rimsha, ki tasa Bawan Allah a gaba kina zuba mashi shagwaɓa da malamai har sai ya susuce maki ko? Wlh yaya Ahmad yana ruwa, thank God ni ba ni da saurayi amma fa duk saurayin da ya zama masoyina sunansa Sorry" ta kai karshen maganar tana dariyar iyashege.

Wayar har ta katse Rimsha bata ɗauka ba ta biyewa Akila. "Aunty Akila ni fa abin da ya sanya zan ɗauki wayarsa da wuri haka, saboda ina son tambayarsa number wannan yar uwar tawa Ayla da na baki labari jiya, shine fa yasa zan ɗauki wayar".

Hararar gefen ido Akila ta yi mata cike da zolaya ta fara magana "To haka ne? Amma dai kada na ji an kashe murya, ayi mashi magana kamar yadda ake yi mani, idan ba haka ba zan mashi recording naki idan kina magana da ni, na tura mashi na ce ya ji muryar ki yadda kike yi mani magana, duk da cewa ma dai voice ɗin naki ƙarshe ne a daɗi" ta kai karshen maganar tana juyawa ta bata baya.

Rimsha tana ƙoƙarin yin magana kiran Ahmad ya sake shigowa a karo na uku kenan, cikin sauri ta yi picking tare da kai wayar kunnanta, a nutse ta fara magana "Assalamu alaikum Yaya Ahmad ina kwana?" Ajiyar zuciya ya sauƙe kafin ya amsa mata da "lafiya Lou Alhamdulila My beauty ya kika kwana?" Lafiya ta bashi amsa sannan ta ɗaura da cewa "Dan Allah yaya Ahmad number Ayla nake son ka turo Mani" To ya amsa da shi sannan ya katse kiran ya turo mata number tare da sake kiranta.

Ba dan taso ba ta ɗauki wayar suka fara hira, kamar dai kullun E da a'a shine kawai abin da take bin shi da shi, bai wani damu ba, shi dama burinsa kawai ta ɗauki wayar.

Har Akila ta yi barci Ahmad bai ga ji da yiwa Rimsha surutu ba, sai da ya ji ta daina amsa mashi da e da a'a ɗin ma, sai ya ce to za su yi waya anjuma, to ta ce mashi suka yi sallama.

Kamar jira take yi dama, yana katse kiran ta fata kokarin gwada layin Ayla, layin a kashe, ba dan ta ta so ba, ta ajiye wayar ta miƙe ta ɗauko Alkur'ani mai girma ta fara biya karatun da Akil ya kara mata, domin tana son kafin yamma ta haddace, ta yadda zata kai babu gargada, kuma tana son ya kara mata a yau ɗin, tana son rufe haddarta gaba ɗaya, a yanzu haka tana da izu arba'in a kanta, to tana son rufe ashirin ɗin gaba ɗaya.

Sosai ta dage tana karatu ita kuma Akila tana barci, ni kuma na haɗa kaya na zuwa wajen su Aafia.

🥺💔BANDIT'S💔🥺

Suna zaune cikin wannan bakin ɗaki mai cike da bakin ciki da tashin hankali, babu wanda yake iya ce da ɗan uwansa uppan, kowannensu bala'in yunwa yake ji sosai, gaba ɗayan su kusan buri ɗaya ke a zuciyoyinsu. Wannan buri kuma ba wani buri bane fa ce a kashesu su huta, amma sai dai bandits ɗin sun ki su kashe su.

Suna zaune a haka har bandits nan suka zo bakin kofar wajen suka ce da su su fito, da yake sun saba sai suka yi maza suka ta shi. Aafia ta sha ruwan mamaki ganin yadda suke rige-rigen wajen fita, har suna ture juna, abin ya ɗaure mata kai, kamar waƴanda za'a bawa wani abin a wajen, sai mamaki take yi tana tafiya a hankali ta bar Rufee kwance a wajen. Bata ankara ba sai jin saukar wata shegiyar bulala ta yi a tsakiyar gadon bayanta, ihu ta kurma a guje ta bazama wajen sauran mata da suka yi gaban. Abin da yake faru wadda ita bata sani ba shine, idan bandits ɗin suka ce ku fito, to kayi maza ka yi gaba, idan ba haka ba ka tsaya baka sauri to za su zane maka jiki da shaggun bulalun nan nasu, to ita bata sani ba, ta tsaya tana tunane-tunanenta, shiyasa ta sha bulala.

Can cikin wani ciyawa da suka kewaye da wasu kirare suka je suka zazzauna.

Wata mata dake zaune ɗan gefe da Aafia ne yaron ta na goye ya fara tsallara kukan yunwa, cikin saurin matar da ta zauna da Aafia a ɗaki ɗazun ta sanya hannu ta toshewa yaron baki, buge mata hannu uwar yaron ta yi tana faɗin "Baki da hankali ne ke? Kashe mani yaron zaki yi? Ya zaki toshe mashi baki yana kuka?" Kallon bandits dake kewaye da su matar ta yi kasa-kasa ta ce "Wlh idan kina son yaronki to ki sanya shi ya yi shiru, na lura ke bakuwa ce a nan, amma ni dai na gaya maki idan ba haka ba zaki rasa yaron nan, domin sun tsani kukan yara, last week suka kashe wani jariri a nan wajen, to kema ki yi da taka tsan......." Bata iya kai karshen maganar ba sakamakon wani bandit da ya shigo cikin wajen ya fisgo wannan yaro daga bayar uwarsa ya fice da shi, ihu uwar ta kurma ta miƙe zata bi bayansu, bandits dake tsaye a wajen ruƙe da bindiga ne suka yi mata barazana tare da dakatar da ita ta hanyar harba bindiga a in da take yunkurin saka kafarta, cikin wani irin gigita da kiɗima tare da matsananciyar tashin hankali uwar yaron nan ta ja burki tare da komawa baya.

"Koma gi zauna ko kuma yanzun nan na fasaki da bindigar nan!!" Cewar ɗaya daga cikin bandits dake a wajen, jikinta sai kerma yake yi haka ta koma ta zauna tana hawaye.

Lokacin da suka saki wannan harbin bindigar tsabar tsorata yasa Aafia ta tamki matar da aka yiwa yarta fyaɗen nan wato maman Zahrau, nan take ta fara hawaye, bata taɓa jin karar harbin bindiga a gaske ba, sai dai a film, amma yau ga shi a gaban idanuwanta aka saki harɓi, abin ya gigitata.

Suna cikin wannan hali wani bandit ɗin ya kariso wajen yana jan Rufee a kasa kamar shanuwa, da alama kuma ta suma, yana karisowa wajen ya wullota cikinsu ya juya ya bar wajen.

Sosai A'afia ta tsanan ta kukan da take yi mara sauti, abin ya ɗaga mata hankali fiye da tunanin mai tunani, wannan bala'i ma kawai ya isa ya sanya ƙwaƙwalwar mutun birkicewa, ɗaya daga cikin matar dake a wajen ne ta ce da matar da akayiwa yarta fyaɗen "Maman Zahrau ki sanya yarinyar nan ta yi kuka kasa-kasa ko kuma ta yi shiru, idan ba haka ba, ita ma tana gab da rasa tata rayuwar" Jin haka yasa A'afia ta yi saurin toshe hakinta da hannunta, jikinta sai kermar tsoro yake yi, abin gwanin ban tausayi.

Suna cikin wannan yanayi bandits guda uku suka kariso wajen hannunsu ruƙe da manya manyan tray masu ɗauke da shinkafa da miyar, layi-layi suka fara bi suna raba wa su Aafia abinci, ko da suka zo kan ta ƙin karɓa ta yi, wai ba zata iya ci ba, Mama Zahrau ce ta ɗan taɓa ta alamar ta karɓa, domin idan bata karɓa ba za su ce gidan su akwai kuɗi sosai dan haka idan dama millon ɗaya suka saka kuɗin fansa sai su kara dan kin ki cin abincinsu hakan ya nuna daga gidan daɗi kika fito kenan.

Jin maman Zahrau ta taɓa ta ne yasa ta karɓi abinci, wucewa suka yi suka ci-gaba da raba wa sauran abincin. Sai bayan sun gama rabawa sun ta fi ne Aafia ta ce ita kam ba zata ci ba, to kawai maman Zahrau ta bita da shi, sannan ta ɗaura mata da cewa "Kinga idan baki ci wannan abincin ba, wlh in baki yi Sa'a ba sai gobe yi war haka zaki sake ganin abinci, sau ɗaya suke bada abinci, sai wata Sa'a idan sun sami kuɗi sosai kamar idan an fanshi wasu nan ne za ki ga sun bamu abinci sau biyu a rana, kuma kada ki yi zaton iya mu da muke nan ne kawai suka kama, a'a akwai maza suna ta baya, akwai wasu matan ma ta baya, irin wajen nan uku suke da shi, kin ga suna da mutane da dama da suka kama, ba za su iya ciyar da mu sau uku a rana ba, wani lokaci ma ba mu samun ko sau ɗayar sai dai su bamu ruwa, shima ruwan kada ki yi zaton akwai shi available ne, A'a sau biyu suke bada shi arana shima, so dan haka is better for you da ki ci abincin nan".

Kallon abincin A'afia ta yi gaba ɗaya abincin dake cikin robar bai wuce ayi loma ɗaya da shi ba ya kare, amma a hakan idan suka ci kuma sai gobe, wannan wace iriyar bala'i ce, ya Allah ka kawo mana sauƙin wannan musifa da muke acikin.

Ita kuwa uwar yaron da aka kwace ɗan, ta kasa ko da motsin kirki, burinta kawai taga ina yaronta yake, tana ɗaya daga cikin bakin da aka kawo yau da safe, so bata san asalin halinsu ba, sai yar dube dube take yi ko zata hango yaron nata, amma ina shiru ba shi ba alamar shi, ko kukansa da ma yake yi ta daina jiyowa.

Su kuma sauran matan dake a wajen, tuni sun fara cin abinci, hannu baka hannu kwarya, ba za su Barka ka wanke hannu bama, kawai ci ake yi. Aafia tana son tashi ta isa ga Rufee dan ta dubata taga kamar bata motsi ne, amma ina tana tsoro, dan idan ka yi wata wargi tsab za su iya kashe ka.

Suna tsaka da cin abincin bandit ɗin da ya ɗauki yaron matar nan ya dawo wajen hannunsa na ruƙe da zanin matar jini na zuba da ga jikin zanin, ga abu kuma a ciki sun kunso shi.

Kai tsaye matar ya nufa, yana zuwa ya gefa mata yaron ya juya ya bar wajen, jikinta har kerma yake yi, da kyar ta iya buɗe zanin, wa iya zubillah yaron ne suka dafa shi, da alama cikin tafasasshen ruwa zafi suka sanya shi, gaba ɗaya fatar jikinsa ta ɗaye, sai tiririn hayaki ke fitowa daga jikin wannan yaron, gaba ɗaya jikinsa ya kwaile fatar ta cire ya yi wani jawur da shi, daga bakinsa da hancinsa jinine ke zuba daga wajen, da alama a cikin tafasasshen ruwan zafi suka sanya shi, dan ga shi, duk wadda ya ga yaro nan idan bai suma ba, wlh sai ya matse mashi kwalla, sai dai idan zuciyar da babu wani imani ko ɗigo a cikinta, innalillahi wa inna ilaihir rajiun uwar yaron nan a wajen ta yanke jiki ta faɗin, ba ita ka ɗai ba cikin wayan da suka suma harda A'afia da kuma bakin da aka kawo yau da safe a cikinsu akwai Hanan kanwar Sadiq Katsina.

Duk bakin da aka kawo yau da safe sai da suka suma ganin wannan tashin hankali, wayan da suka daɗe a wajen kuma masu kuka sun sha kuka, wayan da kuma zuciyarsu ta bushe ko alamar hawaye babu a idanunsu, sai dai ja da idanun nasu ya yi kamar wuta, alamar abin ya taɓa su suma, cikin wayan da ba su yi kuka ba har da maman Zahrau ita ma baiwar Allah zuciyarta ta bushe bata jin komai.

Wannan wace irinyar bala'i?, Wannan masifa dame ta yi kama? Innalillahi wa inna ilaihir rajiun ya Allah ka kawo mana mafita, dayawa daga cikinmu sun saki Allah sun riki duniya gam, ya Allah ka jiƙan bayin ka ya Allah, innalillahi wa inna ilaihir rajiun astafirullah waatubu ilai.

Daya wa daga cikin mutanen dake a wajen, mu samman wayan da aka kawo yau, ba wanda ya iya cin abincin dukkansu kowa ya kasa ci da suka farfaɗo kenan, sai dai wayan da suka daɗe a wajen, suma ɗaiɗaiku ne suka iya cin abincin irin su maman Zahrau. Ya Allah ka kawo mana ɗauki, yanzu a naku tunanin ire-iren maman Zahrau da suka sanya zuciyarta ta bushe babu imani babu tausayi me kuke tunani zata iya aikatawa idan aka bata makami? Allah ma ya tsare da yake ba azzaluman bawa bane sai dai bawa zalunci kansa, sai zuciyar tata ta saura da son Allah da Manzonsa, bayan su ba wani abin dake a cikin zuciyar maman Zahra, ya ilahi ya lillillahi😭

Kasan cewar ogan su mai kiran waya baya nan hakan yasa suka wuni a wajen ba wadda aka kira iyayensa, domin duk cikin bandits ɗin mutun biyar kawai ke da damar kiran waya, saura kuma aikinsu kamo jama'a ne kawai, da kuma kula da su, bayan haka ba wani abin.

Jugum-jugum suka zauna ba sallar azahar bare la'asar har karfe shida na yamma sannan suka sanya su a gaba zuwa cikin ɗakunansu, dayawa daga cikin bandits ɗin basa nan, da alama wani abin suka tafi aikatawa acikin gari, domin kusan rabi da kwatansu basu nan a wajen, yan kalilan suka rage, wadda ba su fi yawan mutanen dake a wajen ba.

Haka aka mai da su cikin ɗaki suka cigaba da zama jugum-jugum ita kuma Rufee da alama fa kamar babu rai ajikinta, domin ƙo motsi bata yi, kuma haka suke janta a kasa kamar shanuwa, a wannan dawo da su da suka yi, sun haɗa Aafia da kuma Hanan kanwar Sadiq waje guda, domin dama haka suke yi, idan sun tashi mai da ku, mafiyawancin lukuta suna canza maku ɗaki domin kada kudaɗe a waje guda har ku shirya masu wani abin, shayasa basu barin jama'a su sarara, tsabar rashin yarda da kai.

(To mun ji ɓangaren Aafia bari mu leƙa ɓangaren su Jelly dan jin yadda zata kaya mana.)

Sai murna take yi za su fita yawo da yaya Nawid, abin ba'a magana har wani kin magana take yi ma mutane, sai kauɗi take yi da rawan kai, ita adole za su fita yawo.

Bayan sun yi sallar isha ne suka zauna cin abinci, da sallama Nawid ya shigo palon, zaune ya isko su saman table Ummi na kokarin zuba masu abinci su ci, yau Abbo ba a part nasu yake ba, yana part ɗin maman Afnan hakan yasa Ummi gaba ɗaya bata son fitar da Nawid zai yi da baby, dan kada ya barta cikin kaɗaici.

"Baby ki tashi mu tafi mana, ba sai kinci abinci ba, za mu ci a can, Prof ya sa an shirya mana abinci". Ba tare da ta kalli in da yake ba, ta ce "Yaya Nawid kaza fa Ummi ta soya mani, ni gaskiya babu in da zanje sai na ci wannan kazar". Bin Ummi da ido ya yi, sai yanzu ya gane me matsalar da gangan Ummi ta kawo mata kaza dan bata son su fita saboda Abbo yana part ɗin su


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login