Showing 201001 words to 204000 words out of 355604 words

Chapter 68 - Triplets Book 2 Hausa Novel Complete

10 Dec 2024

2789

ba, bayan jininma aihuwa lokaci guda, Triplets ai dole a sami irin hakan.

Yan kame-kame Tga ya fara yi, domin shida kansa idan zai gayawa kansa gaskiya ya san dai babu wani waje guda ɗaya da akace yau musulmai sun yi ta'addanci a wannan wajen, amma da yake basu son gaskiya sai ya fara kakalo karya ya ce "Ba ga shi ba musulman Pakistan suna ta kashe Indiyawa, bayan haka suna yi masu zagon kasa, sun hana indiyawa zaman lafiya, sannan ga musulman Palestine sun addabama Israel, sun farmakesu, suna kashe su, kuma ga Musulman....." Ɗaga mashi hannu Michael ya yi yana faɗin

"Uncle T baka son gaskiya, kai da kanka kasan tsakanin indiyawa da yan Pakistan suwa ye suka takurawa juna, India da Pakistan duk abu guda ne daga baya aka raba, amma saboda zalunci yanzu ka gaya mani wanne daga cikin su tafi kyau? Suwaye suka fi jin daɗin rayuwa? Suwaye kasashenmu ke Maganar su? Ba India ba? Kana jin ana Maganar Pakistan ne? Ba'a maganar ta saboda kasar a mace take, Ko iya haka ya isa ka gane masu gaskiya a ciki, idan ma baka gane ba ƙwaƙwalwar ta toshe to bari na gaya maka, indiyawa ne suka takurawa musulman Pakistan, suke kashe su, su ne yan ta'adda, su haɗa ta'addancin su daga baya su ce wai Pakistan ne, kuma su suka yi kayan su da kansu, saboda sun ga Pakistan bata da manyan kasashen dake a bayan ta, batun Palestine da Israel kuma kana sane da masu gaskiya, a nan kafin Lion ya tafi sai da kuka yi magana da shi yake gaya maka musulman Palestine suna shan azaba a hannun Israel, Israel sun takura masu ya yi yawa dole ne yasa suka fito domin kare kansu, domin su nemawa kansu yanci, ko kana tunanin ban ji ku bane? To idan haka kake tunani ma ka makara, domin duk wani abin da Lion ya sani dole zan sanshi, saboda nima ai ina bincike a cikin laptop nasa, kuma wata sain idan kuna hira ai ina jin ku, to ni dai bani da matsala da ko wace addini, dan haka ba zan taɓa zagin kowa ba, kowa yana da dama ya yi addinin sa, kuma babu wanda ya isa ya hana shi, so ka fita harkar uncle Hosain!!".

Rai a matukar ɓace Tga ya yi kansu, ko motsawa Michael bai yi ba yana tsaye duk da ya san cewa e tabbas Tga zai iya yi mashi dukan mutuwa, amma yasan Lion ba zai taɓa barin hakan ta faru ba, dan saboda ya san da cewa Lion ɗin ya sanya camera a wajen yana kallonsu, shi Tga shine bai san da cameran ba, na biyu kuma jiya Lion ya sanar da Michael ɗin cewa shima Musulmi ne, hakan yasa ya gayawa Tga duk maganar da ta zo bakinsa saboda ya san ba wani abin da ya isa ya yi masu, tunda mai gayya mai aiki yana tare da su.

Damƙo wuyar Michael ɗin ya zo ya yi ya shaƙesa yana faɗin "Ni kake gayawa magana har kake ce mani James ne ɗan ta'adda, wato mu Kristen mune yan ta'adda kenan ba?" Da kyar Musharraf ya iya miƙewa yana kokarin cire hannun Tga ɗin daga shakar da ya yi Michael ɗin, dan da a taɓa Michael gwara shi bala'in ta kare a kansa, saboda Michael mutun ne mai kyauta, sadaka, kaunar bayin Allah, taimako, zuciya mai kyau, irinsa acikin al'umma suna da matukar amfani.

A fusace Tga ya damƙo Musharraf ɗin ya haɗa kansu gwarel da na Michael ɗin, sai ga goshin Musharraf ya fashe ya fara jini, rai a ɓace ya yi wurgi ta Musharraf ɗin can gefe guda saman machine ɗin motsa kafa, ihu Musharraf ya kurma sau ɗaya sai kuma ya yi shiru kamar an ɗauke wutar nepa, da alama suma ya yi.

Jin haka yasa Michael ya ji wani karfi ya zo mashi, wani kukan kura ya kurma tare da damƙo wuyar Tga ɗin suka fara kokawa.

Rai a ɓace Tga ya ɗaga shi sama ya buga shi da ƙasa, wani wahalallen ihu ya saki tare sa sakarwa Tga.....✍️.

Duk abin sa suke yi Lion na kallonsu ta cikin laptop nasa, abin sa ya sanya bai shiga faɗan ba, yana son kallon a iya ina hankalin da kuma natsuwar Michael ta tsaya, sannan yana son sanin shin Michael zai iya kwatawa kansa yanci ne ko yaya, a lokacin shi kuma Imran ya shiga toilet dan yin wanka.

Ni kuma na haɗa kayana izuwa 🤔sai dai mun haɗu goben kawai idan mai dukka ya kai mu

💖💖TRIPLETS💖💖

55-56

*Idan kun samu typing error amin afuwa 👏 keyboard ɗin tana bani matsala sosai kwana biyun nan, to na yau ma ya fi tsananta, sai na danna A sai ya koma B😭*




🔥Washington DC🔥


Rai a ɓace Tga ya ɗaga shi sama ya buga shi da ƙasa, wani wahalallen ihu ya saki tare sa sakarwa Tga ɗin wayan nan kwarin nasu na Triplets.

Duk abin sa suke yi Lion na kallonsu ta cikin laptop nasa, abin da ya sanya bai shiga faɗar ba, yana son kallon a iya ina hankalin da kuma natsuwar Michael ta tsaya, sannan yana son sanin shin Michael zai iya kwatawa kansa yanci ne ko yaya, a lokacin shi kuma Imran ya shiga toilet dan yin wanka.

Ihu Tga ya fara yi yana bubbuge kwarin, amma ina kamar kara hura masu wuta akeyi, sai wani kara hawa kansa suke yi, suna bashi a jikinsa, da dai ya ga da gaske zasu lahana shi, sai ya kwasa da gudu ya bar wajen ya yi cikin gida.

Yana barin wajen jibga-jibgan sojoji biyu suka iso wajen, kowannan su ya ɗaki ɗaya, ɗaya ya ɗauki Michael ɗayan kuma ya ɗauki Musharraf dake a sume, kai tsaye cikin gida suka wuce da su.

Umarni Lion ya yi masu akan su kai su word room, haka kuwa suka wuce da su word room ɗin, saman kyawawa lausasan kuma tsadaddun gadajen dake a cikin word room ɗin suka kwantar da su, sannan suka juya suka fita.

Da fitarsu ba'a fi minti goma ba sai ga su sun dawo tare da manya-manyan likitoci sanye da kayan aikinsu, suna zuwa suka fara duba su.

Shi kuma Tga Lion ya dakatar da kwarin saboda suna da aiki gobe, yau za su bi jirgin dare zuwa Nigeria gobe za su yi wa wajen da James yake dirar mikiya, su tarwatsa kowa su fito da James, kuma Lion ya riga ya tsara cewa da Tga ɗin za'a yi tafiyar, idan ba ku mance ba kuma, baya magana ya canza, hakan yasa ya dakatar da kwarin, amma dai ya tanadawa Tga hukuncin da ta dace ya yi mashi bayan sun gama aikin da zasu yi na ɗauko James, ya zama dole ya hukunta shi saboda ya cutar da Musharraf, shi kuma baya goyon bayan a cuci mutun ba tare da ya yi maka komai ba, baya bin bayan zalinci ga koma wace addini.

A ɓangaren daddy da Uncle Herry kuwa, duk wannan badakala da ake yi a cikin gidan basu sani ba, suna can cikin lambu, dan dama mayun zama a lambu ne, hakan yasa aka yi masu katafaren lambu a gidan, dan su rinƙa sakata suna walawa son ransu.

Su kuma John da Jay basa nan, John ya tafi party, shi kuma Jay ya tafi yawonsa.

Wannan kenan abin da yake faruwa a Washington DC kenan, idan kuma muka koma wajen*JEHAN*

Wunin ranar Jehan da yunwa ta wuni, ta ki cin abincin dan ta ce lallai dole abin da ta ci shi Adiva zata ci, hakan yasa ta wuni da yunwa, dan sun ƙi yarda Adiva ta ci abincin.

Ganin haka yasa Jehan ta fara zargin lallai akwai wani abin dan gane da wannan abincin, ace lallai sai ita kaɗai za'a bawa kamar ba lafiya ba, sai tunani take a kan hakan har can yamma, su Aisha dai sun ci sun ƙoshi kayan su, sunci na safe da rana.

Da yamma sun yi wanka su A'isha anci uban kwalliya kamar yadda aka saba, an sha su eyelashes ga jambakin nan ba'a magana, kamar wata aljana haka ta zama domin ta lapta uban attachment a kanta.

Ita ma Jehan ta yi kwalli amma bata sanya irin su eyelashes da kunba kamar Aisha ba, simple make up ta yi kamar yadda Adiva ma ta yi, ita kuma Maryam baiwar Allah, ko kaɗan bata yi kwalliyar bama.

Ita kwata-kwata ma bata saki jikinta da kowa ba, da alama akwai ciwo a cikin rayuwarta sosai, ganin haka yasa Jehan ta Matso kusa da ita tana tambayarta ko lafiya.

Kamar jira take yi a tambayeta sai ta fashe da kuka, da sauri Adiva ta matso kusa da ita suka fara rarrashinta.

Sun ɗan jima suna rarrashinta sannan suka samu da kyar ta yi shiru. Ruwa Adiva ta ɗauko mata daga ɗan madaidaicin fridge dake a cikin ɗakin, dan ɗakin nasu kusan komai a akwai, duk gidan ɗakin su shine na uku a kyau, ɗaku nan hawa hawa ne, kamar yadda suma matan suke hawa hawa, akwai ɗakin yan 14 years, wadda ya fi kowanne kyau saboda su ne kananan yara, za'a jima ana zan zare da su, za su kawo kuɗi sosai, (a cewar Hajiyar daɗi fa tom, ba ni ba) Sai kuma ɗakin yan 15 years wadda suma nasu yana da kyau, sai dai bai kai na yan 14 years ba, dan yan 14 sune farko, daga shi sai na su Jehan, sai yan 17, haka ɗaku nan suke, na yan 14 katon freezer ne a ciki, da kuma manyan gadaje, yara su sakata su wala, kamar gidan ubansu, na yan 15 kuma mabi da shi ne.

Karɓar ruwan ta yi ta sha tana sauƙe ajiyar zuciya. Sai da suka barta ta ɗan huta sannan Jehan ta ce muna jin ki me ya faru.

Idonta cike tab da kwalla ta fara magana kamar haka, "Ni dai yar asalin garin Kano ce, kuma mu biyu iyayen mu suka haifa, ni da yayata wadda ita ma ta bar gida a yanzu haka, dan tare muka baro gida, wani iftilai ya afka mana mu ka rabu". A ƙage Jehan take da jin kan zance dan haka sai ta ce "Maza ki gaya mana da wuri"

(D.P.O ba wasa, akwai san jin kan zance da wuri🤣)

"Babana yana sai da rariya da itace a bakin kasuwar kauyenmu, yana da kuɗi sosai, saboda yana noma sosai da sosai, yana da dabbobi irinsu raguna, kuma kullum kara aihuwa ragunan nasa suke yi, sun yi yawa sosai ga awaki, amma duk da wannan tarin niimomi da Allah ya mashi, mun taso cikin bakar wahala, wai kawai dan saboda maman mu ta haifa mashi ƴaƴa mata, shi wai maza yake so wayan da zasu taya shi zuwa gona, hakan yasa ya rinƙa azabtar da mu da yunwa, ga duka da zagi, kyara idan muka zo kusa da shi, baya son ganin mu, maman mu tana shan wahala wajen neman abin da zata ba mu muci, yaya Asma'u ta sha wahala kamar ba zata yi rai ba, akwai lokacin da na kamu da rashin lafiya, kamar zan mutu, amma haka baba ya sa kafa ya yi fatali da ni, a wannan rana ma sai da ya yi mani dukan tsiya, bakin cikin yau da gobe yasa maman mu ta fara rashin lafiya, yan kauyen mu sun san baya bamu abin ci, amma basu san menene dalili ba, kuma sun yi mashi magana akan abincin, amma yaki canza hali, sai cewa ma ya yi babu ruwan kowa da gidansa, kowa ya yi harkar gabansa, maman mu kuma bata da mama sai babanta da matarsa, hakan yasa ta zaɓi zama a gidan mu da zaman gidansu, domin tasan ma ko taje sai babanta ya koreta saboda shi irin mutanennan ne ma su zafi sosai, baya ɗaukar maganarta gaskiya, kai in ta kai ce maki ma ko gidan ta je sai ya tambayi menene ya kawota, wani zubin ma daga kofar gida zai korata, ya ce ta koma gidanta, baya ma bari ta shiga cikin gida, haka muka yi ta fama da bakar wahala, kullun muna yawon neman abin da zamu ci, a haka har yaya Asma'u ta fara sata, lokacin da muka fara sanin daɗin abinci da sauransu kenan, yaya Asma'u tana shiga gidan mutane idan ta ga abu zata ɗauka ta gudu, ko abinci aka ajiye ta gani zata sace ta gudu, ta kawo mana mu ci, hakan ba karamin tayarwa da mama hankali ya yi ba, ya kara mata ciwo kan ciwo, akwai wata rana da aka biyo yaya Asma'u har gida, akan ta shiga gonar mutane ta saci masara kusan rabin buhu.

Har cikin gida suka biyota masu gonar, suka jata zuwa waje suka fara dukanta, sai kuka mama take yi tana basu hakuri, amma basu kyaleta ba sai da suka naɗa mata duka kamar za su kasheta, sannan suka kyaleta suka tafi, sosai mama tasha kuka, daga karshe ta ɗaura ruwan zafi a saman kiraren da muka samo, ta tafasa ruwan ta gasawa yaya kijinta.

A haka har nima na fara ɗaukar abin mutane, domin yunwa na neman kashe mu, dole idan munga abu mu ɗauka dan mu sami abin ci kada mu mutu, haka muke sata, duk abin da muka gani, ko da kuwa ba naci bane ɗauka muke yi saboda sabo da satar.

Akwai wata rana da na kasa mance wa a idona, wannan ta zama rana mafi muni a rayuwata, lokacin mun girma, ina da shakara 15 a lokacin, mun je kauyen kusa da mu biki, ana biki lokacin, muka ga kuɗin wata mata a jakarta ta ajiye, muka ɗauka muka gudo zuwa gida, ashe akwai wadda ta gammu, da akazo ana cikiya ana ta kalawa wasu daga cikin jama'ar wajen sharrin sata, abin har ya kusa haifar da faɗa koma nace maki sun yi faɗa da baki ba da hannu ba, daga baya wannan da ta ganmun sai ta gaya masu cewa mune muka ɗauka. Lokacin kuma har mun sai bread da kuɗin naira ɗari biyu ce, muna tsaka da cin bread ɗin muka ji hayaniya, daidai lokacin kuma baba ya shigo, dama ita mama tana ɗaki tana barci bata san me yake fatuwa ba.

Baba yana shigowa kawai ya ɗauki wani katon itace a cikin itacen da muke yo wa mama idan Allah ya bamu abin da za mu girka. Dukan mu ya fara yi da wannan itace yana tsine mana yana faɗin, tsinannu yan asara, ku tashi ku fice mani daga gida, ɗiyar banza ɗiyar bala'i, ku dai kun zame wa mutane annoba da bala'in , to dan ubanku sai ku tashi ku fita waje, bala'in da kuka jajumo suna can suna jiranku. A wannan hali mama ta fito ta same mu, kukan da muke yi ne ya tashe ta daga barcin ta, kuka ta fara yi tana kokarin kwace sandar hannun nasa, da karfi ya hankaɗeta ta yi baya baya ta faɗi kasa, mu kuma sai da ya yi mana duka sannan ya ja mu zuwa waje ya miƙa wa mutanen dake a wajen tare da gaya masu su yi mana dukan tsiya, domin mu bamu da aiki sai sata kullum, to shima ya ga ji da halin mu, haka jama'a suka hau dukan mu, bakin cikin hakan yasa mama ta faɗi ta mutu a wajen, wannan rana na kasa manta shi a rayuwata, haka suka yi mana dukan ɗari biyun su, bayan sun tafi muka dawo cikin gida da kyar, muna shigowa ni ban wani damu ba na nufi bread na da yake yashe a kasa, na ɗauka na cigaba da cusa shi a cikin baki na ina ci domin bala'in yunwa muke ji, ita kuma yaya Asma'u wajen mama ta nufa, da yake ta fini shekaru ita zata kai 18 years sai ta gane cewa mama ta rasu, mun gwammaci mutuwar mu a wannan lokaci da muka samu labari, ba karamin tashin hankali muka shiga ba, haka muka daure har sadakar uku na mama, a jama'ar unguwa, babu wanda ya kula mu, ko zaman makoki ba wanda ya yi wa mama, tun da aka je aka binneta shikenan, kuma duk saboda muguntar babana ne yasa ba masu kula mu.

Babban abin tashin hankali da ya jefamu cikin matsala shine, baba ya zo ya fara kwanciya da yaya Asma'u a maimakon mama, shi ya ɓata mata budurcinta, kullun yana kwana da ita ɗaki ɗaya, tun tana kuka har ta hakura, domin idan bata yarda sun kwanta ba, baya ba mu abinci, kuma ko sun kwanta sau ɗaya yake bamu abincin a rana, duk da haka mun jure bamu damu ba, wata rana da daddare muna barci ya zo ya tasheni akan wai mu tafi ɗakinsa yau da ni zai kwana, shine yaya Asma'u ta ce ba zai yi wu ya lalata ta kuma nima ya yi mani hakan ba, zaginta ya fara yi yana faɗin ina ruwanta, idan bata yi mashi shiru ba sai ya kasheta a cikin daren nan, shine ta ce ya kasheta ɗin idan zai kashe ta, amma ni dai ba zai lalata mani rayuwa tana ji tana gani ba, haka yasa ya ɗauki itace ya buga mata ta faɗi kasa kamar baya numfashi nikuma ya jani zuwa cikin ɗakinsa, ina tsoron yi mashi wata magana dan kada nima ya buga mani itace ya kashe ni, sai na yi shiru ina kuka ina tuna abin da mama take yawan gaya mana, na muriƙe mutuncin mu duk wuya duk daɗi, idan har muka yarda muka zubar da mutuncin mu a titi bata yafe mana ba, sai kuka nake ita tuna mama, shi kuma baba ya cire mani riga zai cire mani zani kanan yaya Asma'u ta buga mashi wata itace ta baya, ya faɗi kasa kanshi ta fashe yana jini, hannu na ta riƙo tare da miƙar da ni muka fita da gudu, cikin wannan dare muka keta daji muna gudu.

A hanya muna tsaka da gudu aka daki yaya Asma'u ta baya, ta faɗi kasa tana faɗin na gudu, ni bansan waye ya dake ta ba saboda duhun dare, na dai ga ta tashi suna faɗa da mutumin, a haka na gudo na barta a wajen, na fito bakin hanya, a nan nakwana,


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login