Showing 144001 words to 147000 words out of 355604 words

Chapter 49 - Triplets Book 2 Hausa Novel Complete

10 Dec 2024

2839

lumshe idanuwansa gaba ɗaya alamar barci ya zo kenan. To Lion asuba ta gari.

A ɓangaren Michael da Musharraf kuwa a tare suka yi sallar isha, sannan suka kwanta suna hira, a nan ne fa Michael ke sanar da Musharraf ya kamata su je masallaci gobe, tun da ya ce mashi yin sallar Jumma'a a cikin masallaci yana da falala mai girmar duniya da abinda ke cikinta, to ya kamata gobe su je sallar Jumma'a a masallaci, ba karamin daɗi Musharraf ya ji ba, har wani murmushi na musamman yake yi, dama shi ya jima yana son tambayar ina masallaci yake, to da yake bai san waye zai tambaya ba sai ya yi shiru, amma yanzu tun da ga shi Micheal ya ce akwai masallaci sai su koma yin sallah a can, dama sallah a nan gida suna yin shi ne cikin tsoro da fargabar kada wani ya zo ya gansu, sai sun kulle kofar da key suke samun damar yin Sallah, to yanzu tun da akwai masallaci, sai suka tsara cewa za su rinƙa yin sallar asuba a gida, azahar kuma su fita zuwa masallaci, idan sun yi azahar ba za su dawo ba, sai an yi la'asar sai su dawo bayan sun yi, daga nan ba za su sake fita ba sai lokacin sallar mangariba idan suka fita shima sai sun yi isha za su dawo, sosai Michael ya ji daɗi kuma ya ce shi da kansa zai rinƙa jan su a motarsa suna zuwa masallacin.

(Amma kuna ganin yadda Lion ya sa musu tsaro yanzu zai iya barin Michael ya fita ba tare da sojoji ba?🤔)

Wannan shawara suka yanke kafin su yi sallama da juna, Michael ya wuce bedroom nasa, shi kuma Musharraf ya yi addu'ar barci sannan ya kwanta.

Shi kuma Michael da ya shiga ɗakin sa, wanka ya yi ya shirya cikin kayan barcinsa masu kyau da tsada, sannan ya haye saman bed nasa ya yi addu'ar barci dan yanzu ya iya har da addu'ar shiga toilet dana fita gida, da sauransu, bayan ya yi sai ya kwanta ya ja blanket zuwa kirjinsa, ba jimawa barci ya yi awon gaba da shi.

A ɓangaren Tga kuwa, da tunanin yadda zai ɓullo wa Musharraf ya yi barci, ya ci alwashin idan Lion ya tafi sai ya binciki wanene Musharraf, dan ba zai iya hakurin jiran har Lion ya dawo sannan ya yi bincike a kan shi ba, dan haka ya kuduri niyyar azabtar da Musharraf ɗin sosai idan Lion ya tafi.

(To fa ni kuma na haɗa kayana na zuwa Nigeria dan na gano yan hanyar Kaduna, shin sun isa ne ko kaka, na yi nan sai kunzo.)


💖IMRAN💖


Sai misalin karfe 2 na rana su Imran suka shiga Kaduna, kai tsaye gidan su Nawid suka fara zuwa dan su sauƙe shi, saboda da motar Imran suka je. Bayan sun isa gidan sun yi parking Nawid ya ce sai dai ya zo su shiga cikin gida, Imran ya ce "A'a Dr kasan dai ba dan dole ba da ba zan shigo da kai har cikin gida ba ko? Kasan dai bana zuwa gidan nan sai dole, dan haka kawai ka gaishe mini da Ummi".

Guntun tsaki Dr Nawid ya ja kafin yace "Kai ai yanzu Abbo ya raba mana part Ni kai na ina fin wata wlh ban saka maman su Afnan a idanuna ba, dan haka yanzu sai ka dawo zuwa kamar da" girgiza kai Imran ya yi sannan ya ce "A'a ni ba zan shiga ba gaskiya, saboda bana son matsala, kai dai ka gaishemini da Ummi kawai" yana kai karshen maganar ya tashi motar suka bar gidan, ita kuma Rimsha sai barci take yi abinta, ta kwantar da kanta jikin lallausar kujerar motar ga sanyin Ac na ratsata.

Wucewa cikin gida Nawid ya yi, zaune ya isko Jelly saman sofa a Palon Ummi tana kallon wani Korean Film. Tsayuwa ya yi daga bakin kofa ya ɗan zuba mata idanu yana kallonta, bata lura da shi ba, hankalinta ya yi nisa a kallon da take yi, har wani abu take yi, idan ta kallin suna faɗa suna firewa sai ta yi kamar zata fire ita ma, idan sun yi wurgi da mutun zai faɗo kasa, har wani sa hannu take yi kamar zata tare shi ya faɗo hannunta.

Ba karamin birge Dr ta yi ba, ta tafi da imaninsa, ga shi dressing nata yau ba'a magana ta yi kyau sosai cikin Pakistan riga da wando, sai dai a maimakon ta sanya gyalen a kanta sai ta ɗaura shi a saman hannun sofa ta bar kai ba ɗan kwali.


Ya ɗan jima yana tsaye yana kallonta kafin nan ya shigo daga ciki bakinsa ɗauke da sallama, kamar bata a palon bata amsa sallamar ba sakamakon ta yi nisa ta lula duniyar kallo.

Gefenta ya zo ya zauna daidai lokacin da Ummi ta fito daga cikin ɗakinta, tana faɗin "Baby kizo ki shirya mu tafi, ko kuma in tafi in barki". Ganin Nawid a wajen yasa ta ce "Yaushe ka dawo Nawid?" Ajiyar zuciya ya sauƙe kafin ya ce "Yanzun nan na dawo, dan Allah Ummi ina Abbo? Ina son yin magana da shi" "Abbonka yana nan, yana part ɗin su Afnan sai ka bari sai ya fito ko kuma ka kirashi a waya, bana son ka je can, dan dai kasan sauran, idan kaje ba zaku wanye lafiya da su ba".

Guntun tsaki ya ja irin yana cike da haushin su Afnan ɗin, a yatse ne ya ce "No zan jira shi sai ya dawo part ɗin nan, amma ina zaku je na ji kina cewa baby ta zo ku tafi". Murmushin ne ya bayyana a kan fuskarta ta ce "Wajen Aunty Hajizatu zan je mana" ɗan kishingiɗa ya yi yana faɗin "Yaushe Aunty Khadija kuma ta dawo?" "Kwana uku da suka wuce ta shigo kasar, tun da ta shigo take kirana wai nazo muje gidan mijinta, to ban samu zuwa ba sai yanzu nake son in je in ji me kuma zata je yi a gidan tsohon mijin nata". Jinjina kai ya yi yana faɗin "Hmm adawo lafiya, amma dai Ummi dan Allah kada ki biyewa Aunty Khadija duk da take yarki ki" Harara ta wurga mashi kafin ta sa kai ta wuce wajen Jelly take ta zuba kallonta kamar bata a cikin palon.

Hannunta ta kama ta mikar da ita tana faɗin "Wuce mu je ko na tafi na barki". Ba dan ta so ba ta miƙe suka wuce cikin ɗaki. Shima Nawid ya miƙe ya wuce bedroom nasa.

A ɓangaren Imran kuwa, kai tsaye gidan su ya nufa. Ya na yin parking ya fito ya buɗe kofar gefen da Rimsha take a ciki, cikin natsuwa ya sanya hannu ya ɗauke ta cak, domin shi har yanzu kallon yarinya karama yake yi mata, jin an ɗauketa yasa ta farka a razane, ganin ta buɗe idanunta ya sa ya ce "Kin tashi lafiya?" Ya yi maganar ba tare da ya sauƙeta ba, kuma bai daina tafiya ba, kokarin zamewa daga jikin nasa ta yi ba tare da ta yi mashi magana ba, ganin haka yasa ya sauƙeta yana faɗin "Sorry bana son tashin kine shiyasa" shiru bata yi masa magana ba, domin kanta wani mugun ciwo yake yi mata, har wani jiri take gani saboda barci bai ishe ta ba.

Da hannu ya yi mata nuni da kofar palon, kusan a tare suka shiga, zaune suka isko Ammie saman sofa, bakinsu ɗauke da sallama suka shigo ciki. Juyo da kallonta Ammie ta yi izuwa kansu, a zabure ta miƙe tsaye tana kallon Rimsha, gaba ɗaya tsikar jikinta sai ta shi yake yi, kamar wadda taga wani mugun abin tsoro, jikinta har kerma yake yi, tana haɗe words cikin tsawa ta ce "Wace ce ke?!"

Zaro ido Imran ya yi yana mamakin yadda Ammie ta ɗaga murya haka. "Koma wace ce ke ki fita daga cikin palon nan yanzun nan, bana son ganinki" sosai Rimsha ta tsorata, shi kanshi Imran ya tsorata juyowa ya yi yana kallon Rimsha ko zai ga wani abin a tattare da ita wadda ya sanya Ammie ta ce bata son ganin ta, amma ina bai ga komai ba sai ma kyakkyawar, ga kyawawan dara-daran sleeping eyes nata masu ɗauke da barci.

Tsawa Ammie ta kuma daka musu "Imran idan baka fitar da yarinyarnan daga palon nan ba, wlh zan tsine maka albarka, nace maka bana son ganin fuskarta ko?!!" Tashin hankali juyawa ya yi ya riƙo hannun ta suka fice daga palon. Suna fita Ammie ta zube saman sofa tama mai da numfashi sama sama, alamar fuskar Rimsha ya tsorata kuma ya ɗaga mata hankali sosai.

Shi kuma Imran yana fita palon kai tsaye part nasa ya wuce hannunsa riƙe da nata, wasu siraran hawayene suka fara bin kuncinta, ba tare da Imran ya lura da hakan ba.

Suna shiga part nasa ya ce "Kada ki damu a nan zaki zauna, kada ki je cikin gida, kada ki fita ko kofar palon nan, kiyi zaman ki a nan, heartbeat ɗin mu Akila zata rinƙa zuwa kuna hira, wancan ɗakin shine naki, ni kuma ga nawa ɗayar, kada ki sa komai a ranki, duk abin da kike so ki tambaye ni kai tsaye kin ji ko?" Ya kai karshen maganar yana dawo da kallonsa kan fuskarta.

"Subhanallah Rimsha kukan me kuma kike yi haka?" Ya yi maganar yana goge mata hawayen nata, kasa magana ta yi sai ajiyar zuciya kawai da take sauƙewa, sai rarrashinta yake yi har ta yi shiru, sannan ya kai ta har ɗakin nata ya fito domin ya ɗauko mata trolley ta.

Ɗaki ne mai bala'in kyau kamar dai ɗakin ta time da daddynta yake raye, ɗakin ya yi kyau sosai, ga katafaren bed 6 by 7 an shinfiɗa masa bed sheet na alfarma mai kyau launin pink da white color, abin ba'a magana, sai kamshi ke ta shi a ɗakin. Kai tsaye toilet ta nufa dan yin wanka ta ɗauro alwaya ta gabatar da sallar azahar.

Lokacin da Imra y kawo mata trolleynta tana cikin toilet ajiye mata kawai ya yi, sannan ya wuce nashi ɗakin dan ya je ya yi wanka shima ya yi sallah.

Bayan yan wasu awanni.

Shirye take tsab cikin doguwar riga ɗaya daga cikin wanda Ahmad ya saya mata, ta yafa mayafin rigar a kanta, tayi kyau sosai kamar ka sace ta ka je ka ajiye ta kayi ta kallonta dan kyau, sai dai kallo ɗaya zaka yi mata kasan bata cikin walwala da farinciki. Palon ta fito ta ɗan kara gyara shi fes, sannan ta nufi wani wajen da take zaton shine Kitchen na part ɗin.

Ai kuwa Kitchen ne, ko ina a gyare tsab, sai dai da alama ba'a amfani da Kitchen ɗin sosai, ana kwana biyu ba'ayi amfani da shi ba, ciki ta shiga ta fara yan dube-duben ta, akwai komai da mace zata buƙata a cikin Kitchen ɗin, irin su pot, spoon, plate, cup, da kuma ingredient na miya, da sauransu, sai dai babu kayan abinciki a cikin kitchen ɗin, hakan yasa ta nufi wani ɗan karamin kofa dake cikin Kitchen ɗin wadda take zaton store ne.

Tana shiga ciki ta yi arba da kayan abinci kala-kala, wani daɗi ta ji, cikin sauri ta fito ta ɗauki pot mai kyau daga cikin sets da suke jere cikin drawer kitchen ɗin, a wanke yake tsab, amma sai da ta sake wankewa, sannan ta ɗaura ruwa a saman gas, farar shinkafa ta dafa, sai kuma ta rasa da me zata yi miya, domin bata ga kayan miya irin su Tomatoes a cikin Kitchen ɗin ba, yan dube-dube ta fata yi ko zata ga kayan miyar, can ta hango wani katon freezer daga gefe, cikin sauri ta karisa wajen ta buɗe, ai kuwa shake yake da kayan miya nama kifi da sauran su, shiru ta yi tana tunanin kenan yaya Imran yana yin girki da kanshi ne? Ko kuma dai yana da mata ta yi tafiya ne?.

Ganin babu wani abin da tunani zai tsinana mata, sai ta ɗebi iya adadin kayan miyar da take buƙata, tazo ta wanke su tas ta ajiye a gefe, sai ta koma ta ɗebo nama kamar an sata, haka tazo ta wanke namar ta gyara shi fes tare da yi mashi haɗi da kayan kanshi da sauransu ta ɗaura saman wuta, bayan ta ɗaura sai ta ɗauki kayan miya ta zuba a blender ta fata markaɗe.

Bayan ta gama nama ya dahu ta soya shi ta kwashe, sai ta zuba kayan miya ta fara soyashi shima. Haka ta haɗa miyar nan ya ji kayan kamshi da nama, sai tashin kamshi yake yi, ta gama komai ta wanke duk wani abin da ta ɓata sannan ta zuba abincin a cikin kuloli masu kyau, ta jera a saman tray ta ɗauka da niyar fitarwa palo, juyawar da zata yi suka yi ido huɗu da shi, yana tsaye ya goya hannu a kirji, yana sanye da jallabi ash color, ya zuba mata ido kallonta kawai yake yi.

Wani irin tsorata ta yi saura kaɗan ta saki tray ɗin abincin ya faɗi kasa. "Asarar abincin zaki yi mini ko? Baki son yau naci girkin first lady kenan?" Ya kai karshen maganar tare da karisowa cikin Kitchen ɗin ya karɓa mata abincin yana faɗin "Waye ya koya miki girki haka? Nafi 30mins ina tsaye ina kallonki, karar blender da kika kunna ta fito da ni". Ya yi maganar yana fita Palo.

Bayansa ta bi tana faɗin "A gidan su Kausar na koyi girki, sannan kuma ina da takardar girkin ina koya".

Saman table ya ɗaura tray sannan ya ce "Gaskiya ne ga shi kamshin abincin duk ya addabawa cikina yasa sai yunwa nake ji, amma fa wannan shine first and kuma last kada ki sake yin girki, domin ba yar aiki na ɗauko ki ba, ki bari zamu rinƙa fita mu sawo, wannan kayan da kika gani a kitchen ɗin ma ina ajiyewa ne saboda abokaina, akwai wasu daga cikinsu basu cin abincin restaurant sai dai su girka da kansu, to saboda su nake ajiyewa". Turo ɗan bakin nan nata ta yi tana faɗin "To nima ai ina daga cikin mutanen da basu cin abincin restaurant, ni ba zan iya ba gaskiya, dan Allah ka bari zan rinƙa yin girkin da kai na". Baya son ɓata mata rai dan haka sai ya amsa mata da to Shikenan, daman kun san ta da son iya girki, sai murna take yi, shi kuma ya ce zai ɗauketa su je shopping anjuma da daddare ya saya mata kayan sawa da su man shafawa da duk wani abin bukata sannan ya saya mata littatafan koyan girki masu kyau.

Saboda tsabar murna ji tayi tamkar ta ringume shi, sai zuba mashi godiya take yi. Yau dai Imran zai ci abincin da ba na restaurant ba, ɗaukar plate ta yi ta fara serving nasa.

Zuba nata ido ya yi yana kallon ta, sai da ta shake masa plate ɗin tap da abinci, yana ta ce mata ya isa amma taki bari sai da ta cika plate ɗin, sannan ta tura mashi gabansa tare da miƙo mashi spoon, karɓa ya yi yana zuba mata Albarka, ba ɓata lokaci ya fara cin abinci dan dama yunwa yake ji, wani irin daɗi ya ji lokacin da ya kai abin cin bakin sa, ɗanɗano na musamman ya ji, nan take ya fara santi, ɗaukar wani plate ta yi ta zuba nata abincin ɗan kaɗan tana ƙoƙarin zuba miya, nan fa ya ce bata isa ba, karɓar serving spoon ɗin ya yi ya cika mata plate ɗin shima kamar yadda ta mashi, sannan ya bata dama ta zuba miya ta ɗauka ta wuce bedroom nata.

Subhanallah wani shegen daɗi ya ji lokacin da ya kai tsokar namar cikin miyar bakinsa, wow ya furta afili Rimsha ta iya girki, ga hannunta da zaƙi, haka ya buɗe cikinsa ya fara ci, yau ba abincin restaurant bane, bai san lokacin da ya cinye abincin nan tas ba, cikinsa kamar zai fashe saboda koshi, bai taɓa yin lodin abinci irin na yau ba.

A wannan hali Akila ta shigo ta same shi, dawowarta daga school kenan, tasha ruwan mamaki ganin yadda yake ta santin abincin, ta kasa hakuri har sai da ta tambaye shi.

Daɗi ya hana shi yin magana, da hannu kawai ya nuna mata kular abincin, buɗe kular ta yi, wani daddaɗar kamshin steew ɗin ne ya daki hancinta, cikin sauri ta ɗago ta ce "Yaya Imran wannan abincin wani restaurant ne?" Girgiza mata mai ya yi sannan ya shiga bata labari.

Ai kuwa da murnarta ta miƙe tana faɗin "Kai yaya kace na samu kanwa kuma mai koya mini girki, bari naje wajen ta" bata jira amsar shi ba ta wuce zuwa ɗakin da Rimsha take a ciki, . Akila baiwar Allah bata da matsalar komai, tana bala'i son mutane sosai. Da fara'a sosai ɗauke a kan fuskarta ta shiga cikin ɗakin.

Rimsha na cin abinci, domin lokacin da ta shigo ɗakin ajiye abincin ta yi sai da ta yi wanka ta shirya cikin wata doguwar rigar sannan ta ɗauki abincin ta fara ci, shiyasa Akila ta iskota bata kammala cin abincin ba.

Murmushi ɗauke a kan fuskarta ta ce "Sannunki da zuwa" ɗago kai Rimsha ta yi tana kallonta, lokacin guda ta sakar mata cool murmushi har sai da hakwaranta suka bayyana, a ruɗe Akila ta ce "Wow dimple, open teeth, dogon hanci, karamin baki, kyakkyawar gashin gerar, sleeping eyes da nake mutuwar so, kyau iya kyau duk sun haɗu waje guda, ya ilahi ya lillihi ka bani yarinya mai kama da wannan baiwar taka, kyau iya kyau". Dariya abinma ya bawa Rismha, zuba mata ido Akila ta yi tana kallon yadda take dariyar abin ba'a magana gwanin birgewa.

"Gaskiya kina da kyau sosai" Akila ta sake faɗa tana karisowa wajen da take zaune, saman mirror chair, miƙewa Rimsha ta yi dan ta bata wajen zama tana faɗin "Kece Akila ko?" Da sauri Akila ta gyaɗa mata kai ala'mar sannan ta ce "Yaya Imran ya baki Labarina ko?" "E ya bani labarinki ai ya ce mini ke ce bugun Zuciyar su gaba ɗaya gidan" kara faɗaɗa murmushinta Akila ta yi sannan ta karɓi plate ɗin abincin ta ce "Mu koma tsakiyar ɗakin saman carpet muci abincin a


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login