Showing 183001 words to 186000 words out of 355604 words
kuma babu wani abin azo a gani, tun farko shi ya yi kuskure, shiyasa daga lokacin bai sake yi mata dole ba, ya barta sai ta buƙata da kanta, ya daure ya cigaba da azumi da sallar tsakiyar dare🤣
Kasa-kasa ya ce "Na sani My wife nasan ya maki zafi a rana ta farko amma ki sani ba zai kara yi maki zafi ba, ki natsu kuma ba zan takura maki ba har sai idan ke da kan ki kika bukata" ya kai karshen maganar tare da ɗaukarta cak suka haye gado yana goge mata hawaye yana rarrashin ta.
(Nima na haɗa kayana dan naje na nemo masoyina James ko ya goge mani hawaye da bakin cikin rashin masoyi😭 sai mun haɗu Monday idan mai dukka ya kai mu a part ɗin su Rimsha Queen of beauty 🤨)
💖💖TRIPLETS💖💖
51-52
💖💖RIMSHA💖💖
Sai karfe 12 baiwar Allah nan ta iya tashi da ga barcin wahala da ya ɗauke ta, da kyar ta iya waro sleeping eyes nata da suka rine suka yi ja sosai saboda barci, ɗakin ta fara bi da kallo kamar bakuwa. Ta ɗan jima kwance ka fin nan ta yunkura da kyar ta miƙe zaune, gaba ɗaya jikinta ciwo yake yi ma ta, tamkar an yi mata ɗan iskan duka da itace, sai wani yauki take yi, tana haɗe gerar sama da ta kasa, nan take kuma zazzaɓi mai zafin gaske ya rufeta, wani irin sanyi mai ratsa kashi take ji yana ratsata, jan jikinta ta yi ta lallaɓa zuwa saman bed nata, haka ta kwanta tare da jawo bargo ta shige ciki. A wannan hali Imran ya shigo ɗakin ya sameta, yana shirye cikin wanda dakakkiyar shadda milk color, ɗinkin ta zauna mashi sosai a jikinsa, sai tashin kamshi yake yi, hannunsa na ruƙe da wayarsa da kuma key ɗin motarsa, zai ta fi neman Lion ne, domin tun safe yake kiran layinsa baya ɗauka, kuma wayar tana shiga, hakan ya sa ya shirya zuwa nemansa, dan bakonsa ne, kuma duk cikin abokansa ba wanda yake so biyun Lion, ya fi son shi fiye da kowa, sannan kuma saboda shi Lion ya sauƙa a Nigeria, ba dan shi ba da ba zai zo ba, hakan yasa ya zama mashi dole ya fita nemansa.
Cikin sauri ya kariso cikin ɗakin ganinta a cikin bargo, bakin gadon ya zauna tare da yaye bargon yana faɗin "First lady lafiya kuwa?" Ta kasa magana hakwaranta sai garuwa da juna suke yi, saboda bala'in sanyi da take ji, ganin hakan yasa ya sanya hannunsa a saman kumatunta, jikin nata ya yi zafi jau kamar wuta. "Subhanallah" shine abin da ya iya furtawa tare da miƙewa a zafafe ya yaye mata bargon gaba ɗaya, tana cikin hijabin da ta yi sallah bata iya cirewa ba.
Ɗan gyara hannun rigarsa ya yi ya ɗauketa cak suka nufi waje, ya zo zai fita palo kenan ita kuma Akila tana shigowa,.
"Yaya Imran lafiya? Me yasa Meta? Ta yi maganar cike da nuna kulawa, kuma fuskarta ɗauke da tsantsan tausayi.
"Heartbeat mu je ki buɗe maki kofar mota kin ji?" To ta amsa da shi tare da wucewa da sauri ta nufi parking space ɗin gidan, gidan baya ta buɗe mashi ya kwantar da ita sannan ya shiga gidan gaba da sauri.
"Yaya Imran dan Allah zan biku " ta yi maganar idanunta cike tab da ruwan hawaye, gyaɗa mata kai kawai ya yi alamar to, da sauri ta shiga ta zauna a front seat. Da sauri ya figi motar, kafin su isa bakin gate mai gadi ya buɗe masu gate ɗin, a guje suka danna waje.
Kai tsaye asibiti ya nufa, sai gudu yake shararawa, cikin ƙanƙanin lokaci suka isa Hospital ɗin, kasan cewar kuɗi na aiki, idan kana da kuɗi ba abin da ba za'a iya yi maka ba, kuma Dr Nawid yana nan, yau yana hospital ɗin, hakan yasa aka karɓi Rimsha hannu bibbiyu, cikin ƙanƙanin lokaci aka mata gwaje gwaje, da testses a kan me matsalar ta.
Akila sarkin tausayi sai ruwan hawaye take yi, tun ma bata ji menene ke damun Rimsha ɗin ba, sai faman rarrashinta Imran yake yi. Sun kwashi almost awa ɗaya da rabi zaune a office ɗin Dr Nawid a yayin da ake bawa Rimsha taimakon gaggawa, a ɗaki na musamman.
Sai da suka kara wajen minti talatin sannan Dr Nawid ya shigo bakin sa ɗauke da sallama, yana ƙoƙarin cire hand gloves dake a hannunsa, a lokacin Akila har ta yi barci kwance saman doguwar kujerar dake a cikin office ɗin, tasha kuka dan ita har ga Allah bata son ganin wani ɗan adam a cikin damuwa, tana da tausayi sosai da sosai, ga saurin kuka, da zarar ta ga abin tausayi zata fara ruwan hawaye, shiyasa ta yi wa Rimsha hawaye, kuma tana bala'in kaunar Rimsha sosai da sosai.
Hannu Dr Nawid ya bawa Imran suka gaisa yana faɗin "Prof sannu da zama, na barku zaune ku kaɗai ko? Ga heartbeat har ta ga ji ta yi barci". Girgiza kai Imran ya yi yana faɗin "babu komai" yau kwata-kwata babu dariya a fuskar Imran ɗin ko kaɗan, abubuwan sun mashi yawa, ga tunanin ina Lion ya shiga, duk da ya san cewa ba wani wajen da ba haka zai je ba yananan, kawai yana son ganin shi ne dan wajensa ya zo, ga kuma rashin lafiyar Rimsha.
"Dr meke damun sister na ne?" Yadda ya yi maganar kasan akwai damuwa a tattare da muryar tasa. Shiru Dr Nawid ya yi na ɗan lokacin kafin ya ce "Gaskiya Prof sister tana da matsala wadda idan ba'a yi kokarin wajen canza mata akala ba zata iya fuskantar barazana da rayuwarta" zaro ido sosai Imran ya yi yana faɗin "Me kake faɗe ne Dr? Please ka mani baya ni sosai da kyau dan in gane".
Riƙo hannunsa Dr Nawid ya yi cike da sigar kwantar da hankalin ya fara magana "Prof ba wani abin bane, ciwon nata bai tsananta ba, amma idan har ba ku yi ƙoƙarin wajen ganin kun bata abin da take so bane, to za'a iya samun matsala, ciwon nata zai kara girma ta yadda zai iya huda mata zuciya".
Tsare Dr da ido kawai Imran ya yi yana jiran cikakken bayanin menene asalin damuwarta. Cigaba da magana Dr ya yi "Imran akwai abin da sister take so, wadda ya tsaya mata a zuciya sosai, wannan shiya haifar mata da matsalar yawan razana rashin kuzari har ma da zazzaɓi, tana da damuwa sosai kuma ni ina ganin rashin yan uwan nan nata ne, yana da kyau ku ja ta ajiki sosai domin ku rage mata raɗaɗi, dan ma yarinyar tana da karfin imani sosai ba dan haka ba, idan wata ce wlh da mutuwa za ta yi, ba uwa, ba uba, ba yar uwa, kuma dukka lokacin guda, bayan kuma a baya a tare suke rayuwa, kai abin ba karamin abu bane, pls Prof ku ja ta ajiki, ku cire mata danuwa da tunanin da take a ciki, kada ku bari wani abu ya rinƙa razana ta ko tsorata, idan ba haka ba zata rinƙa yawan suma wadda hakan kuma zai iya taɓa kwakwalwarta, bayan haka kuma zai iya sawa ta yi paralyzed (palarais,) saboda yawan faɗuwa da zata rinƙa yi, duk wani abin da take so, dan Allah ku yi kokari ku bata shi da sauri, ni ba zan ɓoye maka ba Prof ina sonta, ina sonta fiye da son da nake yi wa Jehan, tun lokacin da na ganta na ji na fi sonta akan Jehan, idan ba damuwa zan so ka bani izinin in ɗan rinƙa kasancewa kusa da ita, domin na kara kwantar mata da hankali, a yanzu kai ne uwa kuma ubanta, so ina neman izini daga wajen ka dan neman soyayyarta" . To fa Babbar magana ga A'A SALAHUDDEEN ga kuma DR NAWID dukka kuma friend ya kuke ganin abin zai kasance? Kada kuma ku mance ita Lion take so.
Allah sarki Imran shima a nashi tunanin rashin su mum ya sanya ta a damuwa haka, bai san da dakon soyayyar da ta yi na shakara 7 ba, basu kawo hakan a zuciyar su ba kwata-kwata, ba su ma taɓa tunanin tasan Lion ba, shi Nawid ya ga zanen da ta yi a kirjinta lokacin da yake dubata, sai dai ba dukkan zanne ya fito ba, ya so jan rigarta kasa kaɗan dan yaga zanen sai dai kasan cewar a lokacin idanunta biyu kuma son aure yake mata ya sa bai yi gigin yin hakan ba, dan saboda kada ta yi mashi mummunar fahimta, shiyasa sai ya bar zancen amma ya so ganin me ta rubuta a wajen, kuma ya yi alkawarin in dai ya samu dama sai ya gani.
"Dr In Sha Allah zan yi kokarin ganin na sanya Rimsha farin ciki sosai, sai magana ta gaba kuma I knew kai mutumin kirki ne, idan har ka iya samun soyayyar Rimsha to wlh ko da iyayenta sun bayyana zan tsaya maka, duk abin da zai sanya ta farin ciki ina maraba da shi a Yanzu, dan haka idan har Rimsha zata yi farin cikin kasancewa da kai, to ina maraba da kai, duk lokacin da ka zo gida zaka samu ganinta, all the best my dear" ya kai karshen maganar tare da miƙawa Dr hannun, miƙo mashi shima Dr ya yi suka bugi juna kamar yadda suka saba lokacin suna primary school.
"Amma Dr ba wani magani ko wani allura da za ku bata ne?" Cikin sauri Dr ya ce "Akwai sosai ma, yanzu ma na ɗaura mata karin ruwa domin akwai maleria a jikinta sosai, ina ga gidan da ta zaunan nan sauro sun taɓata, amma zamu yi treatment yanzu kuwa". Imran zai sake magana wayarsa dake a cikin aljihunsa ta fara kara.
Cikin sauri ya ciro wayar tare da bin screen ɗin da kallo, dan a tunaninsa Lion ne. A'A SALAHUDDEEN shine sunan da ya bayyana akan screen ɗin wayar, murmushi ya yi kafin ya ce "Dr ga mutumin yana kira, shima yana fama da halin da muke cikin, wato soyayya, Allah dai ya fitar da mu lafiya" ya kai karshen maganar tare da yin picking call ɗin.
Tun bai yi magana ba Ahmad ya riga shi da cewa "Yau ba ko sallama dan Allah Prof ka tashi zuwa Katsina ka je ka duba mani Queen of beauty ko tana lafiya ne, tun jiya bata ɗaukar wayata, ina ji a jikina wlh bata da lafiya, zan yi ta ƙoƙarin kiranta da ta ɗauka zan tambayi address kawai na turoma ka je ka gan mim ita ka jimin meke faruwa ne".
Yar dariya Imran ya yi kafin ya ce "Kai AA wlh baka da damuwa, ta ya za'a yi ka bari son macen da baka da tabbacin zaka sameta, ka bari ya shiga zuciyarka da kallon ɗaya haka? Bafa kasan wacece ita ba, wata kila ma matar aure ce, duk baka yi tunanin hakan ba, kai dai kawai daga ganin kyakkyawa, baka san halinta ya yake ba, to ni wai a ina ma ka haɗu da ita ne? A Abuja ko ina? Ni dai ba zan fasa gaya maka ba, ka rabu da ita, ka kama dahir, dama nace idan ka rabu da ita sai na baka number kanwata first lady ku kulla soyayya, to ita ma na mata miji yanzu nan, sai dai na baka heartbeat, ita ma idan ka yi wasa Irfar zai maka kafa dan naga kwana biyun nan sai wani tambaya ta yake yi ya take kamar bai san Hanyar in da take ba, jiya ma har da cewa na bashi number ta, to gara ka yi sauri ka kama dahir". Ya kai karshen maganar yana murmushin shakiyanci shida Nawid sai ɗaga gera suke suna guntse dariya, domin duk abinda Ahmad yake faɗe, Nawid na jin shi, Imran ya kure Volume na wayar.
"Kai Prof wlh bana son iskanci, kuna tare da Dr ko? To wlh ku fita ido na, nabi first lady da kuma heartbeat da gudu, ku baku san zafin so bane wlh, da kun sani da ba zaku ce na rabu da wadda zuciyata ke muradi ba, kun sani ni ban taɓa soyayya ba sai akanta, ko irin soyayyar secondary da ake yi ma ni ban yi ba, a kanta na fara sanin menene so, to dan Allah ku taimaka mani kada na mutu kun ji good friends my bloods". Dariyar da suke guntsewa ne suka tuntsure da shi, cike da shakiyanci Imran ya ce "Kawai ka hakura ka cigaba da shan lemon tsami" Nawid ne ya kai mashi duka a baya suka sake kwashewa da dariyar iskanci.
Ji Ahmad yake yi tamkar ya shaƙosu dan haushi, yana gaya masu damuwarsa suna mai da shi ɗan iska, suna mashi dariya.
"Wai me haka ne Prof? Ni na ce maku auren rage zafi zan yi ne? Son ta fa da gaske nake yi, haba mana bai kamata ku mani haka ba" ya yi maganar kamar zai saka ihu dan haushi.
Tsagaita dariyar Imran ya yi yana faɗin "Wai ka mance lokacin da nake gaya maka matar da zan aura kuma jinina ta ɓata ne? Ka manta me ka rinƙa yi Mani? Ina a nan ka ce mani wai sai na hakura na koma shan lemon tsami shine nima nake mai da maka da abin da ka rinƙa yi Mani".
Shi dai Nawid ɗan gulma sai murmushi yake yi yana jinsu, dan in dai irin wannan iskancin ne sun saba, da A'A da Imran, a baya idan Imran yana bashi labarin Jelly'n sa sai AA ya rinƙa cewa shi wlh bai ga macen da zai so ba a duniyar nan, shi yafi karfin ya ce wa mace yana sonta, sai dai ita ta ce tana son shi, ba kalar tsiyar da ba su yi wa Imran ba a lokacin, har ce mashi suke zai daina shan lemon tsami kenan, idan ya ce masu dama shi baya sha, sai A'A ya ce to idan baya sha meyasa zai yi aure, ba ya ga ji ne da danne abin ba, su yi ta dariya suna mashi tsiya, idan ya gaji ne sai ya tashi ya fita ya basu waje, to suma yau Allah ya kama su, kuma dukkansu akan mace ɗaya, ya kuke ganin wannan abota ta su za ta kasance? Kada ku mance abokaine tun na yaranta, tare suka yi primary school zuwa secondary daga nan suka rabu, Imran ya bar kasar, bayan wani ɗan lokacin suka sake haɗuwa shi da AA Salahuddeen a Harvard University, shi kuma Nawid a India ya karisa karatunsa, sai bayan sun dawo Nigeria suka sake haɗewa, dan dama already sun san gidajen juna, ba jimawa kuma Imran ya sake komawa dan yin degree ɗin sa ta biyu, dukka a Harvard University, shi kuma A'A England ya wuce, suka sake rabuwa, amma kullun suna waya da juna, suna matuƙar kaunar juna.
Tsuke fuskar Ahmad ya yi ya ce "Haba Prof ka ajiye duk abin da ya wuce, yanzu dai ka fuskanci matsalata dan Allah" jinjina kai Imran ya yi yana faɗin "Tom Shikenan yanzu dai ka bari sai ka zo ɗin, ni yanzu ina sauri ne kasan GAR ya zo Naija, to kuma ba sai na gaya maka ba, ka dai san halinsa, wlh tun jiya ya fita gida wai gidan bata yi mashi ba, ni bansan ina ya tafi ba, so zan je duba shi ne".
"What!!!" Nawid da Ahmad suka furta a tare, tare da miƙewa tsaye kamar suna a waje guda, kamar kuma abin haɗin baki.
Shi dai Nawid a Tv ya san GAR sai kuma ya taɓa ganinsa sau ɗaya da ya kaiwa Imran ziyara, lokacin yana degree ɗin sa ta biyu, shi kuma A'A SALAHUDDEEN makaranta ɗaya suka yi karatu.
"Kwairai kuwa GAR a Nigeria ni kai na lokacin da ya kirani ya ce mani zai shigo Nigeria karfe 3, wlh ba karamin shock na yi ba, ba don na mashi farin sanin cewa baya faɗan abin da ba haka ba, kuma bamu wasa a lamarin sa ba, wlh da na ce ba haka bane ko kuma wasa yake yi Mani, amma da yake shi dai kunsan magana ɗaya yake yi, kuma ba wasa a lamuransa ko kaɗan shiyasa ma na yarda, karfe 3 kuwa sai ga jirginsu ya sauƙa lokacin kuma already ina airport ɗin, har yau mamakin abin bai sake ni ba, duk da na ganshi da idona ni na ɗauke shi zuwa gida, kuma na san me ya zo yi, amma wlh har yanzu ina mamaki ina ganin abin kamar a mafarki ne".
Ahmad murya har wani watsakewa ta yi nan take ya koma normal da sauri ya ce "Kai gaskiya Prof ka ciri tuta, har muka gama school guy nan bai taɓa daga ido ya kalle ni ba, ban san ya akayi kai yake son ka ba, kuma duk lokacin muna tare, zai zauna da kai tare, amma da zarar munzo mun same ku kuna zaune zai tashi ya bamu waje, ban san me yasa ba, kuma wlh ina masifar kaunar guy ɗin, ko sau ɗaya bai taɓa yi mani magana ba, duk da cewa kai ma ba magana ya cika yi da kai ba, amma dai yana zama da kai waje guda, dan Allah Imran a wannan lokaci ka saka baki mu zauna da shi, ko sau ɗaya ne mu yi magana". Dogon numfashi Imran ya ja tare da sauƙewa a hankali.
Cike da damuwa ya ce "A'A a baya ma Saif bai tsaya ya yi magana da ku ba bare kuma yanzu da yake babban soja? Kada ka mance a baya fa lokacin bai kai haka ba amma yana da bala'in izza ina ga kuma yanzu? To wlh a yanzu izza da miskilancin Lion ta ci uban na da, ni ma ina da tabbacin Allah ne kawai ya jarabce shi da kaunata, da ya rabu da ni, kuma abin da ya sanya ni na musultat da shi, so yanzu ya san yana kan hanya ma daidaiciya kaga kuwa ba zai taɓa mantawa da ni ba, domin ni na nuna mashi daidaitacciyar hanya, ina ga wannan dalili yasa ma Allah ya jarabce shi da kaunata, kuma yasa har yanzu bai dai na kula ni ba, sannan kuma