Showing 3001 words to 6000 words out of 355604 words

Chapter 2 - Triplets Book 2 Hausa Novel Complete

10 Dec 2024

2732

da Umaisha zata fito, dan a nata tunanin dole ne Akil ya kyale Umaisha ai ta koma gida tun da ba matar sa bace ba a ɗaura auren ba tukun nan, bata san shi kam Akil tuni ya ɗaurawa kan sa auren ba har ma ya raya Sunnah abun sa, sai dai jiran sakamako wato baby kenan.

A wanna hali Abba ya dawo ya same su, hankali tashe Abba yace "ina Akil ɗin yake muje" da sauri Hajiya tayi gaba Abba ya bi bayan ta, Aafia ma bata bari an barta a baya ba tabi bayan su da saurin ta.

Kofar bedroom nasa suka tsaya suna bubbuga wa da karfi, lokacin yana kokarin saka kayan sa ya fito daga wanka, wani nishaɗi da farinciki na musamman yake ji yau, Umaisha kuma barcin wahala ne ya ɗauke ta

Jin bugun kofan yasa ya zura jallabiya kawai ya nufi kofar yaje ya buɗe, yana buɗewa su Abba suna cusa kai cikin ɗakin Hajiya tana faɗin "Yar waye kaje ka ɗauko?" Shafa kan sa yayi kafin yace "Matata ce" Mata Abba ya furta da karfi, eh Akil yace, tashin hankali Akil manya naka ba irin nasu bane

Wucewa Abba yayi ciki dan yaga wace ce Akil ya ɗauko, bayan sa Hajiya da Aafia suka bi dan suje suma su gani, shikuwa oga Akil yana tsaye a bakin kofa, wai yaji kunya su Abba zasu je sugan masa mata kwance Allah ma yasa ya lulluɓeta da bargo, kai jama'a Akil manyan kasa oho Allah wai kunya yaji hmmm

Kallo ɗaya Abba yayiwa fuskar Umaisha yace "Kai Akil amma wannan ai kamar yar gidan Zahraddeen ce ko? Dan ga kamanin Deen sosai fuskar ta" ɗan sunkuyar da kai Akil yayi yana ɗan shafa kan nasa irin kunyar nan yace "Eh Abba ita ce matata ce ai, naje na ɗauko tane" salati Abba yasa kafin yace "Matar ka waye ya aura maka ita? Ko dai kana da wani uban bayan nine?" To fa, ita kuwa Aafia saman gadon ta haura tana kuka tana jijjiga Umaisha, ganin Aafia na kokarin yaye bargon daya rufe Umaisha da shi ne yasa ya daka mata tsawa wadda yasa ta ja da baya daga kusa da Umaisha

Hajiya Umaiya ce ta jawo Aafia tana faɗin "Ya isa kiyi shiru" Abba kam ya rasa bakin magana wai yau Akil ne da hankalin sa da ilimin sa ya yayiwa yarinya fyaɗe, fyaɗen ma ya rasa wadda zai yiwa sai yar kanin sa, kuma fyaɗen ma har gida ya kawo ta gaban kowa yadda zasu gani da idon su bawai suji labari ba, lallai Akil ya cika ɗan duniya mai lasisi

Duk dakin sunyi shiru anrasa mai bakin magana, shi dai Akil ko ajikin sa, soma yake su fice masa daga ɗaki ya samu dama ya sawa matar sa kaya, yau ga ɗan duniya.

Da kyar Abba yace "Yanzu Akil da hankalin ka zaka yiwa yar mutane fyaɗe?" "Abba fyaɗe kuma? A'a ni ba fyaɗe na mata ba dan matata ce ai" a kule Abba yace "Matar ka uban waye ya aura maka ita?" Akil zai yi magana Hajiya Umaiya tace "A'a Alhaji ni kada ka sake yi masa tsawa, dan kawai yayiwa wata yar talakawa fyaɗe shine zaka fara wani ɗaga masa murya, ni bana so, idan iyayen ta sunji ba zasu iya yafewa ba, sai su faɗa min nawane kuɗin budurcin yar nasu sai na biya, kai wannan yar ma da gani ba budurwa bace ka duba bed sheet da suka kwanta mana babu wani alama da zai nuna cewa budurwa aka yiwa fyaɗe a nan" to fah gaba da gaban ta, su Aafia suna ganin su hamshaƙan masu kuɗi ne to ga Hajiya Umaiya ta kira su da talakawa

Kasan cewar shi Akil yana son Umaisha da gaske sai bai ji daɗin abun da Hajiya tace ba ran sa ya sosu sosai, rai a ɓace yace "Haba Ammie bai kamata kice wa matata haka ba, nifa da gaske nake son ta ba wasa ba, kuma bayan ita ba wata mace da nake so, babu wadda kuma zan so" zaro ido waje Ammie tayi a kule tace "Wace ce matar taka? Ba dai jinin Abban kaba sai dai wasu ƴaƴan manya shuwagabanni ko sarakuna, amma wannan yarin ba dai ina raye ne zata zama matar kaba" tirkashi, shi dai Abba bawan Allah shiru yayi ya zuba kusu ido kawai yana kallon ikon god

Turo baki Akil yayi yace "Ni ita nake so kuma ita ce zaɓi na, sannan ita ba kamar yadda kike tunani bace tana da hankali ba namijin daya taɓa taɓa ta sai ni" yana kai karshen maganar ya fice daga ɗakin da sauri dan ma kar Ammie ta masa baki a kan Umaisha ko wani abu dan yasan halin Ammie sarai yadda bata son family Abba ko kaɗan ɗin nan ba abun da bazata iya faɗa ba in dai a kan sune

Sakin Aafia Hajiya tayi ta bi bayan Akil dan ita bazata taɓa yarda da ya auri Umaisha ba, Allah sarki Abba yana tsaye shiru ya zubawa sarautar Allah ido, ita kuma Aafia sai kuka take.

Ko da Ammie ta fita bata ga Akil ba dan ɓuya yayi baya son su sake maganar Umaisha da ita, sama yayi kasa yayi wallahu a'alam bata gan shi ba, shima Abba jiki ba kwari ya fito ya wuce bedroom nasa dan ya rasa bakin magana abun yafi karfin sa.

Yana shiga bedroom nasa ya isko Akil kwance saman gadon sa ya ɗaura hannu a saman fuskar sa kamar mai tunani, Ammie kuma tana can tana neman shi a cikin gida

Kusa da shi Abba yazo ya zauna a gefen gadon cikin nitsuwa yace "Haba Akil me yasa zaka yiwa yar ɗan uwana haka?" Miƙewa zaune Akil yayi cikin nitsuwa shima ya fara magana "Kayi hakuri Abba na, amma magana ta gaskiya shine Umaisha mata tace, da igiyar aurena uku a kan ta" juyowa da kyau Abba yayi suna fuskantar juna cike da murna yace "Yaushe hakan ya faru?" Yar murmushi Akil yayi kafin yace "Tun kafin na koma school, naji ba zan iya tafiya ba tare da an mana aure ba, dan ina ganin kamar idan na tafi bappa zai aura mata wani, shine bayan naje munyi sallama da ita, na wuce wajen Bappa na rokesa daya aura min ita kafin na tafi, da farko bappa yaki yarda sai da yaya Imran da yaya Irfan suka sa baki sannan ya yarda na bashi sadaki, a masallaci bayan sallar la'asar aka ɗaura mana aure, daman abun da yasa ban sanar daku ba, na bari sai na dawo ne in ɗauko ta in kawo muku ita, to ina shigo kasar nan kuma na wuce school nasu dan naje na ganta na ɗauko ta na kawo muku ita ku ganta, shine ta ɓata min rai har hakan ta faru tsakanin mu" kallon gefen ido Abba ya masa irin hararar wasan nan ya masa kafin yace "A'a ba dai ta ɓata maka rai ba, dama can da muguntan ka kadawo" ɓuye fuska Akil yayi a jikin Abba yana dariya kasa kasa, cakulkuli Abba ya shiga yi masa yana faɗin "A'a baka isa ba ai sai ka buɗe fuska muga juna ido da ido zai fi, dan rashin kunya ka kwaso zafin ka kazo tsakiyar rana ka sauke a kan ƴata gidan nan duka suna jin ka bakaji kunya ba sai yanzu zaka wani ɓoye fuska to wlh baka isa ba maza ɓuɗe muyi ido biyu" a shagwaɓe Akil yace "Kai Abba ka bari mana ni wlh kunyar ka nake ji" "Eyee kunyata ba, ai dole kaji kunya ta irin wannan ɗanyen aiki daka yiwa ƴata to Allah dai yasa ina da rabon jika" kara ɓoye fuska Akil yayi yana dariya yana jin farinciki

Jin motsin Ammie na zuwa ne yawa dukan su suka yi shiru Abba ya ɗan matsa gefe yayin da shi kuma Akil ya diro kasa daga saman gadon ya nufi hanyar fita

A bakin kofa sukayi karo da Ammie da sauri ya wuce ta ya koma bedroom nasa, kafin ma ta ɓuɗe baki tayi wani magana ya wuce ta, girgiza kai tayi tace "Zamu haɗu ne" ta kai karshen maganar tare da wucewa cikin bedroom ɗin Abba.

Akil kuwa yana shiga ya samu Aafia zaune kusa da Umaisha tana hawaye, kusa da ita yazo ya zauna yana faɗin "Kiyi shiru ki dai na kuka ki tashi kije ɗakin Akila ki kwanta ki huta kafin Akila ta dawo school sai kuyi hira zan kira bappa a waya na faɗa masa kina nan" banza tayi da shi ta ci-gaba da kukan tana mai jin kamar ta shaƙe shi dan haushin ya raba kanwar ta da budurcin ta a banza ba auren ta yayi ba, kuma ga maman sa tana cewa ba zai auri Umaisha ba shikenan ya cuci rayuwar Umaisha a tunanin Aafia kenan.

Ganin taki tashi ta tafine yasa ya miƙe ya riƙo hannun ta ya miƙar da ita, tana kokarin kwace hannun ta a fusace ya ɗaga hannu kamar zai mare ta sai kuma ya dakata, da ɗan karfi yace "Karki fara wuce mu tafi!" ganin ya haɗe rai sosai ne yasa ta hakura tabi bayan sa suka tafi ya kai ta ɗakin Akila ya dawo ya ɗauki jallabiyar sa ya sanyawa Umaisha ya wurzawa kofar ɗakin su key ya dawo ya kwanta kusa da ita yana mai jin matikar farinciki da annashuwa har cikin ransa.

Ita kuma Aafia kwanciya tayi saman gadon Akila tana kallon sama tana hawayen bakin ciki, har barci ɓarawo ya ɗauke ta

Ammie kuwa bala'i ta tsayar wa Abba wai dole yasa Akil ya dai na zancen auren Umaisha dan ba zata taɓa yarda ƴaƴan ta su aurin ƴaƴan talakawa kamar family sa ba, ayya Abba da yake tariga ta shanyesa yana son yan uwan sa amma babu halin nuna musu soyayya, sai kawai ya shiga bawa Ammie hakuri yana ce mata dole Akil ya bar zancen auren Umaisha, ba zai aure taɓa, ya nemi wata, sai daɗi Ammie take ji, bata san Umaisha kam already matar Akil bace.

Wannan kenan mu leƙa Daular mutuwa mu ga meke faruwa sai mu dawo

👹👹DAULAR MUTUWA👹👹

Gudu Rimsha take sosai kamar zata tashi sama Kausar na biye da ita a baya, kasan cewar cikin ramin akoi hanyoyin da dama sai suka kauce hanyar da suka bi da farko suka kama wata hanyar daban saboda tashin hankali da ruɗu, su kuma su barbushi sunyi gudu mai nisa a wajen basu haɗu da su Rimsha ba, suma su Rimsha ɗin sunyi gudu sosai har suka kasa ci-gaba da gudu basu ga daular mutuwa ba ya ɓace musu, zama sukayi kasa a wajen suna numfashi sama sama kamar ba zasu yi rai ba bayin Allah.

Suna zaune a wajen tun suna ganin haske kaɗan kaɗan har suka fara ganin duhu alamar dare kenan, kasan cewar wajen a karkashin kasa yake ba zaka iya wani banban tashi da yamma ba, danma akoi wasu wurare dake da huji kamar Windows a wajen hakan yasa ake ɗan samun haske kaɗan a wajen, ga yinwa ga kishin ruwa ga gajiya duk abun ya haɗe musu, banda sunan Allah ba abun da suke ambata a zuciyoyin su.

A takaice dai kwana sukayi zaune a wajen, basu samu ganin Ayla ba, suma kuma su Barbushi basu samu damar ganin su Rimsha ɗin ba saboda addua'o'i da suke samu ta ɓangarori daban-daban, dan ko Jehan ta dukufa sosai kwana biyun nan tana yiwa Rimsha addu'a dan kwana biyun tana yawan mafarkin Rimsha ɗin shiyasa ta dukufa da yi mata addu'a sosai, a ɓangaren gwaggo ma haka ne ta dukufa sosai wajen yi ma Rimsha addu'a dan dukkan su kwana biyun nan suna mummuna mafarki a kan Rimsha ɗin, ta gefen guda kuma ga malaman da mum ta bawa kuɗi suyiwa Rimsha saukan Al Qur'ani mai girma suma yau suka gama saukan Al Qur'ani shine ma dalilin da yasa Allah ya bawa su Rimsha damar kuɓuta daga daular mutuwa, sannan ga baba da Mustapha suma ba'a barsu a baya ba sosai suke wa su Rimsha addu'a a zuciyar su, hakan yasa su Barbushi basu samu daman ganin su ba.

Washegari ganin Kausar na kokarin mutuwa ne saboda yinwa da kishin ruwa yasa Rimsha tayi ta maza ta miƙe, Allah sarki itama yinwan take ji amma da ɗan sauran karfin ta tafi Kausar kwari, haka ta tattara karfin ta dukka ta goya Kausar a bayan ta tana jan kafarta a hankali hankali, dan duk kafar nata ya faffashe tun jinin ta na zuba har ya bushe wajen ya dai na zuba, tafiya take kamar zata faɗi kasa dan Kausar ta mata nauyi amma haka ta daure ta cije tana hawaye ta nufi hanyar da sukabi suka zo, ma'ana suka koma in da suka fara tafiya da farko.

Rimsha tayi tafiya mai ɗan nisa da Kausar a goye a bayan ta kafin su iso wata kofar dafaffiyar karfe, da kyar ta iya sauke kausar ta zaunar da ita a kasa, ta sa hannun ta ta kwance ruwan tsafin da duna ya bata wadda ta kulle sa a jikin igiyar rigan ta dan karya faɗi kasa, kamar yadda ya faɗa mata haka ta zuba ruwan kaɗan a jikin kofar sai ga kofar ta buɗe nan take wani haske ya kaure musu ido, lokacin rana ya ɗago tsakiyar duniya, da sauri suka rintse idon su dan sun jima basu ga haske irin haka ba

Sun ɗan jima a haka kafin Rimsha ta buɗe dara daran sleeping eyes nata da sukayi ja sosai, duk sun faɗa kamar ba wayan nan kyawawan idon nata masu kama da audiga dan haske ba, banda zara zaran eyelashes nata dake ɗan taimaka musu wajen fito da su da bazaka taɓa gane su ba saboda wahala da azaba da ta sha

A hankali ta fara bin wajen da kallo, bata ganin komai sai bishiyoyi masu cikar ganye, juyowa tayi tasa hannu zata ɗago Kausar ta goyata, Kausar tayi sauri dakatar da ita ta hanyar yunkurawa da kan ta ta miƙe, rungume juna sukayi dan su tallafawa juna suka fara jan kafafun su da kyar da kyar zawa wajen wurin

Sai kuma me, kungurmin daji ne sosai a wajen wadda baka gane gabas baka gane yamma, ga dogayen bishiyoyi masu abun tsoro, lokaci guda tsoro ya dira musu a ransu, tunani suka fara yi gara musu cikin daular mutuwa da wan nan wajen, domin koba komai cikin daular mutuwa akoi mutane nan kuma fa, sai karan tsuntsaye kuma da alama ba za'a rasa yamun dawa a wajen ba, macizai kam ma guarantee ne sai an same su ba adadi a wajen.

Shin nan ɗin ma wace kasa ce? Wani gari ne? Tashin hankali

Masu karatu sai mun haɗu gobe idan mai dukka ya kai mu


TRIPLET'S💞






# BOOK 2📚📙✍️


💔💔Episode 3💔💔


💔RIMSHA💔


A hankali suka fara kutsawa cikin dajin nan suna tafiya suna tangal tangal kamar zasu faɗi kasa, saboda wahalar da suka sha, duk sunyi wani iri dasu, sun koɗe futu futu, kamar ba su ba, kamar wayan da aka tono su daga rami, ko aka kwato su daga bakin kura, har wani duhun wahala sukayi, gashi sun manne junan su sosai saboda tsoro.

A wannan lokaci da suka fito sun samu damar kiran sunan Allah a baki, gaba ɗaya dark black curly hair Rimsha ya cukurkuɗe kamar bashi ne wannan kyakkyawan bakin gashi mai shekin ba, mai tashin kamshi, yanzu ya dawo duk dattin, kuran daular mutuwa ya buɗe shi, sai warin datti suke saboda wanka ma da ruwa kawai suke ba sabulu, bare kuma mayukan gyaran jiki, ita kam Kausar daman ba gashin gare taba, abunku da kan yarbawa basu da gashi sosai aguiguye kan nata yake, sai dai itama fa ba laifi tana da kyan ta daidai gwargwado.

Sunyi tafiya mai ɗan nisa kafin su iso wani katon rafi mai cike da ruwa, Allah sarki bayin Allah daman kishin ruwa suke ji kamar zasu mutu, suna ganin ruwan sukayi saurin isa wajen, suka kafa bakin su kamar shanu suka fara shan ruwan, basu damu ruwan da datti ko babu ba, su dai burin su kawai su sha ruwa.

Sosai suka sha ruwan sai da sukaji cikin su na musu barazanar fashe wa sannan suka dakata. Sai kuma me cikin sune ya fara murɗa musu, saboda yinwa da ya musu yawa, gashi sun zo sun ɗirka ruwa ciki empty ba abinci.

Kwanciya sukayi a bakin yafin cikin ciyayi dake wajen, suna murkusoso suna juyin azaban ciwon ciki, dukan su babu mai tallafa ma wani, saboda dukan su suna neman tallafi a wannan yana yi, kowannen su ta kan sa yake.

Almost 30mins suna haka kafin su sami ciwon ya ɗan lafa musu. A hankali Rimsha ta miƙe zaune tana kallon Kausar, sai kuma hawaye suka fara bin kuncin ta, lokacin da ta kalli Kausar Ayla ce ta faɗo mata a ran ta shiyasa take kuka. Kausar bata lura da kukan da Rimsha ɗin keyi ba saboda ita bata gama dawowa cikin hayyacin taba.

Sun ɗauki lokacin mai ɗan tsawo a wajen kafin su lallaɓa su tashi su ci-gaba da tafiya, basu san in da suka dosa ba tafiya kawai suke suna fatan Allah ya fitar da su daga wannan bala'i bakin dajin lafiya kar wani naman dawa ko wani abun ya kama su.

Ita dai Kausar bata tsorata da dajin sosai ba, kasan cewar ita bayarbiya ce, kuma asalin kasar yarbawa mafiyawancin gida jen su a cikin ɗan daji daji suke, sai dai ba mai girman wannan ba, ita kuwa Rimsha rainon madara da Ice cream su chocolate bata san wannan wahala ba, gata daman da tsoron bala'i Jehan ta fita jarunta sosai.

A takaice dai sunyi tafiya har rana ta kusa faɗuwa amma basu ga alamar karshen wannan daji ba, daga karshe da suka gaji, kasan wata itaciyar mangoro mai girman gaske suka samu suka zauna a wajen suna sauke numfashi.

Duk sunyi tsuru tsuru dasu gwanin ban tausayi, ji suke gara musu daular mutuwa da wannan azaba da suke ciki a yanzu, ba abinci, ba


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login