Showing 90001 words to 93000 words out of 355604 words
ya ba shi, kuma Jay bai wani suma sosai ba, bai fi suma biyar ya yi ba fa, kuma da aka kai shi word room iya wuni ɗaya daddy ya ɗauka kafin ya samu ya ceto rayuwar sa".
Dangware masa kai Tga ya yi yana faɗin "Close your mouth hai, ba kai ma ka kara musu zafi kan zafi ba, ai kai punishment da ka yi wa Jay ya fi zama masa tabo a zuciya fiye da wahalar da Lion ya ba shi".
Turo baki Michael ya yi a shagwaɓe ya ce "Me kuma na yi?" Hararar wasa Tga ya watsa masa kafin ya ce "Ka harbe masa beb ɗin sa mana, ga shi kuma Lion ya ce ajefar da babyn boy ɗin sa da suka haifa" kasan cewar yanzu Michael ya san daidai da ba daidai ba, sai zaro ido yana faɗin "Uncle like how a jefar da baby kuma? Me babyn ya yi?".
Tga zai yi magana suka ji dakun tafiya, wadda duk gidan shi kaɗai ke irin wannan tafiya.
A zafafe kowa ya kama matsayar sa, dukkan su suka nitsu, Michael ya fara aikin training ɗin sa, ga ruwan da daddy ya zuba masa kamar zufar gaske.
Gaskiya daga daddy har ƴaƴan sa Michael da James duk sun iya basaja over wai, ko da yake gado ba ka ranbani ba, a wajen sa suka koyi basaja.
Lion na shigowa wajen da kallo ɗaya ya musu ya san basu da gaskiya kwata-kwata, sai wani yan kame-kame suke yi, shi kuma Michael har da wani nishi, irin na wanda ya sha wahala sosai ɗin nan.
A nitse Lion ya tako izuwa cikin ɗakin, jikinsa na sanye da Ripped Jeans blue color, ta sama kuma yana sanye da Turtle high, ya yi wa kayan kyau kamar me, shike yiwa kaya kyau, ba kaya ke masa kyau ba, sai tashin wannan fitinannen kamshi perfume ɗin nasa yake mai bala'i daɗin kamshi, yau dai ya ɗaure ga shin kansa a bayan wuyar sa, while shi kuma guntu na gaban goshin sa yana nan.
Tsare su ya yi da ido yana kallon rashin gaskiya karara a bayyane a fuskar su.
"Who changed this setting?" Ya yi maganar yana nuna saitin na lokacin da aka shiga ɗakin, domin shima kofar ɗakin yana da ma ajiyar bayan yaushe aka shiga, yaushe kuma a ka fita, to shima Tga ya canza, sai dai garin sauri ya je ya saka karfe 6 na dare a maimakon na safe.
Tsuru-tsuru suka yi da ido, sun kasa magana.
Kallon daddy Lion ya yi, cikin sauri daddy ya girgiza masa kai ala'mar shi bai san komai ba a kan hakan, shiru ya ɗan yi kafin ya maido da kallonsa kan Tga, tun bai yi magana ba Tga ya yi sauri cewa "Tun karfe 6 ya fara" Kai daga jin yadda Tga ya yi maganar kasan a tsorace ya yi ta, kuma karya ya labka, kallon machine ɗin Lion ya yi, already Tga ya kara mata gudu wadda yake nuna tun awa biyu da suka wuce a ke amfani da ita, shi kuma Michael munafiki sai wani hakin karya yake yana mai da numfashi da kyar da kyar kamar da gaske. Yan basaja.
"Daddy shiga ciki" shine abin da Lion ya ce, tun da John ya ji haka sai ya yi sauri ya riga daddy miƙewa zai bar wajen, da ido kawai Lion ya gan shi ba tare da ya masa magana ba, a ɗari ya koma ya zauna, nan take jikinsa ya fara kerma, sun taro match,
Na dama Tga ya fara yi na karya da ya yi, sun biyewa Michael suna goya masa baya, bayan kuma sun san in dai Lion ya zo wajen tofa sai ya gane su, sai dai sun sa a ransu zasu jure duk wani hukunci amma ba zasu iya ganin Michael cikin wannan ukubar wahala ba, dan bai saba ba, kwata-kwata ma yaushe ya tashi daga ciwo Romeo zai ɗaura masa wata azabar.
Shi kuma daddy tuni ya tashi ya wuce cikin gida abin sa, har da saurinsa bayan kuma shi ya hassa komai, shi yake goya wa Michael baya suna zuba tsiyar su, ga shi kuma yau sun zo sun yi wa Lion karyar da sun san dole zai gane su.
(Oh su Tga har da chanza saitin machine ɗin, a tunaninsu sun tsira🤣)
Duba time a jikin diamond watch ɗin hannunsa Lion ya yi, sannan ya ɗago ya kalli Micheal.
Wucewa ya yi ba tare da ya ce musu komai ba, ya je ya kunna na'ura dake saman wajen kusa da camera, sannan ya koma bakin kofar wajen ta waje ya tsaya kamar mai jiran wani abin.
Minti biyu da kunna na'uran gaba ɗaya saman katifar da suke ya fara juyi kamar fanka, sai sama suke suna kasa, Michael daga shi har machine ɗin nasa juyi suke, dan har da mashunan Lion yasa su rinƙa juyawa, dan su Tga su sha wuya, Tga da John sai gwara kansu suke waje guda, ba halin su tsaya, ba zama su iya kama jikin su ba, sai yadda wajen ya yi da su kawai, shima Michael zubewa kasa ya yi daga saman machine ɗin, ya yi joined na su, idan kafitar tayi sama da su sai ta dawo da su, su gwara kai da juna, wani lokaci kuma ɗaya ya faɗo kan ɗaya, rufe musu kofar Romeo ya yi ya tafi ya kwalesu.
Lallai kuna tsaka mai wuya.
Duk bakin Tga ya fashe ya fara jini, saboda buguwa da katon kai ɗin John da ya rinƙa yi, ga shi ba za su iya ta shi bama, bare su kashe na'uran, kuma idan suka yi hakan ma, Romeo zai gansu ta camerar dake wajen, idan ya gansu kuma sun shiga uku, dan sai sun karɓi hukunci mai tsanani sosai, wannan ma iya hukuncin karya da suka masa ne, ba'a zo kan hukuncin karawa Machine ɗin Michael gudu da suka yi ba.
(Tofa kuma kuna ruwa, ni dai bari na je Nigeria na dawo🛫)
💖💖GIDAN ABBA💖💖
Yau wuni su Rufee suka yi wa Umaisha, sai murna take yau ɗaya ta samu farincikin da tun da ta yi aure, idan ba Akil yana nan ba, bata zamun hakan, a gaskiya Akil yana nuna mata kulawa sosai da sosai, dan yana son ta, soyayya mai tsanani, tun bata kai komai ba, yake son ta, hakan zai tabbatar maka ba wani abu na jikinta yake bukata ba, ita ɗin dai yake so, dan tun ba nono a kirjinta ya fara sonta, shiyasa yake nuna mata soyayya fiye da nunanin mai tunani, sai dai ɓatar Jelly ya jefa su cikin wahala, hakan yasa yanzu bata samun lokacin sa, kuma bata ganin laifin sa ko kaɗan, dan idan ya dawo yana biyan duk wayan nan lokutan da ya ɗauka ba tare da ita ba, yana faranta mata ya sa ta mance da a baya ya hanata wasu lokuta nashi, shiyasa bata damuwa, ga shi yanzu ya koya mata wani azababben son shi, wadda ba zata iya rabuwa da shi ba, Akil ya kware a iya soyayya fiye da tunanin mai tunanin.
Sai karfe 7 na dare driver ya zo ya ɗauki su Rufee zuwa gida, amma kafin ta tafi, sai da ta sace wa Akil danƙara-danƙaran watchs nasa masu bala'i tsada guda uku, duk su Aafia ba su sani ba, bayan nan ta ga wasu kuɗaɗe cikin drawer mirror, wadda Akil ɗin yake ajiye wa, idan Umaisha ko Akila za su bukaci wani abin idan baya nan, sai suyi amfani da su.
Sai dai basu taɓa taɓa ko naira a cikin kuɗin ba, domin ba su bukatar komai, akwai duk wani abin da za su bukata a gidan, sannan ita Akila idan zata je school Ammie da Abba suna bata kuɗi, kuɗi kashewa har yawa yake yi mata, sai dai ta yi ta bawa kawayen ta a school.
Tas Rufee ta kwashe kuɗin ba tare da sanin su Aafia ba, sannan kuma har da wani cewa Aafia gobe zata dawo su wuni, sai Akil ya dawo ya mai da su gida, to kawai Aafia ta ce mata, Anisa kam ta ce ba zata dawo gobe ba, dan ba za'a barta a gida ba, ta fita yau ta fita gobe ba mum ɗin ta ba zata yarda ba.
Wannan sai Rufee uwar sallamammu, kamar an sallamata wa duniya, sai taje waje ta kwana ma ba mai wani damuwa, in dai zata kai musu kuɗin dafa abincin da za su ci ai Shikenan, bata da wata matsala kuma.
Da suka zo tafiya manya-manyan kwalaben turaruka wadda Akila ta sayo mata a shopping, guda huɗu Umaisha ta bawa su Rufee, ita biyu Anisa biyu, bayan haka ta ce bari ta ɗebo musu kuɗi ko za su sayi wani abin a hanya, cikin sauri Rufee ta dakatar da ita, dan ta san idan ta kyale ta, ta je wajen drawer, zata ga ba kuɗin ta kwashe su, asirin ta zai iya tonuwa, shiyasa tayi saurin hana ta.
Haka suka wuce ita da Anisa driver ya mai da su gida.
Misalin karfe 8 na dare bayan sun yi sallar issha Aafia ta ce da Umaisha su je palo su ɗan huta su yi kallo, ta ga ji da zama a cikin ɗakin, nan fa Umaisha ta sanar mata ai Ammie ta hana ta zama a palo, tsaki Aafia ta ja sannan ta riƙo hannunta suka fice daga ɗakin zuwa Palo.
A nan suka isko Ammie da Abba sai Akila, suna zaune suna hira, zama Aafia ta yi tun ba'a bata izinin zama ba, cike da kulawa ta ce "Bappa ina wuni?" Da fara'ar sa ya amsa mata da lafiya sannan ya tambayi ya Abbi da Irfan, suna lafiya ta ba shi amsa, haka suka zauna shiru har zuwa lokacin da mai kawo musu abinci daga restaurant ya kawo musu.
(Ku dai aiki ya ganku kullun sayan abinci tab🤔)
Cikin kwanciyar hankali suka ci abincin su, Umaisha ta samu sake yau, har da hira da dariya tare da Akila, sai karfe 9 da rabi, sannan kowa ya wuce ɗakin sa.
Misalin karfe 12 na dare, Aafia da Umaisha suna cikin barci, kamar a mafarki Aafia ta ji ana ta kwala mata kira a palo, abin mamakin kuma muryan Irfan take ji, ita kuma Umaisha bata jin komai, sai zuba barcin ta take yi cikin kwanciyar hankali.
Miƙewa Aafia ta yi, idon ta duk barci, a hankali ta zuro kafafun ta kasa daga saman gadon, ta laluɓa a cikin duhu ta fito wajen dan ta je palo taga wake kiranta.
Tana isa palo taga duhu ba haske, lallaɓa ta yi zata koma sama, sai ta ji muryan Irfan yana faɗin "Ki kunna mana haske" nauyayyar ajiyar zuciya ta sauƙe, dan da farko ta tsorata sosai, ta ɗauka wani abin ne.
"To yaya Irfan" ta ba shi amsa.
Da kyar ta iya karisawa wajen switch na palon, tana kunna wutar idon ta ya mata arba da abin da kwakwalwar ta ba zai iya ɗauka ba, ihu ta saki tare da watsawa a guje zata haura sama, sai dai kuma ina, kamar wadda a ka sakawa mayen karfe, haka suka jawota.
Wani karin haske game da dodannin nan, in dai kana cikin gidan Abba idan suka zo matikar baka da riƙo da addini sai sun haɗa da kai sun zane ka, Akila baiwar Allah akwai riƙo da addini shiyasa basu taɓa zaneta ba, haka ita ma Umaisha ta fi Aafia riƙo da addini ga askar, shiyasa kome zai faru a gidan su basa ji, Imran da Akil kam dama ba'a magana, wayan nan ai malamaine, kuma dodannin basu iya shiga ɗakin da akwai Alkur'ani mai girma, wannan dalili yasa suka jawo Aafia da dabara, domin part ɗin Akil dai Akwai Alkur'ani mai girma, haka ita ma Akila tana da Alkur'ani mai girma, amma Ammie da Abba ba su da Alkur'ani a ɗakunan su.
Dodannin uku ne suka rike Aafia, wani mummunar katon dodo, ya fito da wani zabgegen kafurin bulala ya hau zabga mata a baya, ga shi sun bankare masa ita gwanin daɗin duka. Sai ihun azaba take yi amma babu mai jin ta bare kuma ya kawo mata ɗauki.
Edited
Suna rike da ita, ta ga Abba da Ammie ma sun fito kamar wayan da a ka kira, kuma dama haka ne, mafiya yawan lokuta dodannin nan suke kiran su Ammie palo, ko su saka su jin yinwan dare dan su fito palo, saboda sun fi jin daɗin azabtar da mutane a palon, dan akwai balance, akwai fili, suyi ta wujijjiga mutun yadda suke so, suna wurgi da shi sama da kasa.
(Yau Aafia jarabar gidan Abba dake ya afka, sai dai mu ce sorryyyyy, kinzo a kan gaɓa🤣)
A guje Abba da Ammie suka juya za su koma sama, Aafia na gani dodanin nan suka riƙo su, suma a ka ɗaura su a kan hanyar karɓan, wannan zabgegen kafurin bulalan.
Aafia tana ihu tana ganin yadda Ammie ke ihu amma ba mai jinsu, sai fashe musu baya mugun azzalumin mummunar dodan nan yake yi,
Abba kam ba'a magana ya azabtu matuka, kuma shi suka fi duka, Bawan Allah, har wani gwalalo idanuwansa waje yake yi.
Good 10mins wannan baki mummunan azzalumin dodan ya ɗauka yana zane musu jiki, kafin nan ya yi wa dodannin da suka riƙe su magana da ido a kan su sauke su, ba musu suka sauke su.
Dukkan su uku har Aafia ba wanda ya iya zama da mazauninsa, domin a daidai wajen ya fi yawan zabga musu bulalan.
Sai numfashin suke sama sama, dukkan su, a kasa suka kwanta suna hawaye, kwanciyar ma ruf da ciki suka yi.
Yau sun ma yi Sa'a iya bulala kawai dodannin suka musu suka bace, sai dai kuma ko da suka ɓace raɗaɗin azaban zafin da suke ji na bulalan, ya jima bai sake su ba, sai wajajen asuba, sannan raɗaɗin ya sake su, yana sakin su kuma suka mance komai suka hau barcin azaba.
Sai karfe 7 na safe Akila ta fito zata je part ɗin Akil dan ta duba Umaisha, Akila Akwai amana, in dai Akil baya gari, to da sassafe zata je ta gaishe da Umaisha, ta tambaye ta ko tana bukatar wani abin, idan ta ce mata bata bukatar komai sai ta wuce ta je ta yi shirin zuwa school.
Ganin su Ammie kwance rashe-rashe a palo, hakan yasa Akila mamaki sosai, daidai lokacin ita ma Umaisha ta fito dan duba Aafia.
Cirko-cirko suka tsaya ita da Akila domin abin ya basu mamaki, ba kaɗan ba, sun rasa ta ina za su fara.
Akila ce ta yi ta maza ta fara kiran sunan Ammie, ta ɗan jima tana kiran sunan kafin Ammie ta farka a firgice tana faɗin "Dan Allah ku bari bana so" .
"Ammie suwa ye za su bari?" Cewar Akila.
Sai lokacin da ta ji muryar Akila sannan ta dawo hayyacinta, miƙewa tsaye ta yi tana faɗin "Akila kin dawo school ne?" Kallon mamaki Akila ke yi mata, wani school Ammie ke nufi kenan, ta tambayi kanta.
Bata kai ga yin magana ba Ammie ta sanya hannu tana ɗan bubbuga Abba tana kiran sunansa, a zafafe shima ya miƙe bayin Allah sun mance komai.
Haka suka wuce part na su, Akila sai mamaki ta ke yi, abin gwanin ban tausayi, gwanin kuma a dasa masa ayar tambaya, dan dai ba lafiya ba.
Umaisha ce ta tashi Aafia, a mai makon ta tashi kamar yarda kowa ke ta shi daga barci, sai ta tashi da banko ashar, wa iya zubillah, Aafia ta iya zagi sosai.
"Aunty Afi lafiya ki ka zo nan ki ka kwanta?" Umaisha ce ta tambaya tana tsare ta da ido.
Ina ai Aafia ta mance komai, dan haka sai ta miƙe ta wuce part na su kawai.
Kallon kallon Akila da Umaisha suka yi wa junan su, lokacin guda, alamar tambaya ya ɗarsun musu a ransu dukkan su, sai dai babu mai basu amsa.
Sun ɗan jima tsaye a wajen ba wanda ya ce da ɗan uwansa uppan, sai daga bisani suka gaisa sannan suka wuce part ɗin Umaisha a tare, sai al'ajabin abin suke yi.
Nima sai al'ajabin abin na ke yi, amma haka na kwashe kayana zuwa kasar yarabawa
💖RIMSHA💖
Yau tun safe ta tashi da matsananin zazzaɓi da ciwon kai mai bala'i zafi, hakan kuma ya samo asaline sakamakon kukan da ta sha tsakar daren jiya, lokacin da duniya gaba ɗaya suke barci, alokacin ita kuma baiwar Allah ta cusa kan ta cikin cinyoyinta tana ta rera kuka. Ayla da Kausar ba wanda ya ji kukan nata, domin yau ba a kan gadon Kausar ta kwana ba, ta ki yarda ta kwanta a gadon, ta zuciya, a kasa ta bakin kofa ta kwanta.
Haka da asuba ma ta sake shan kukanta son ranta, shi kuma kukan asuban da ta yi, ta samo asaline, saboda ta fita yin alwala, boda Jami'u ya fito shima, shine ya zo zai taɓa ta, zata gudu ya damko gashin kanta, dama ita Rimsha bata da wani wajen kamawa a jikinta, sai gashin kanta, kowa ya ta shi kamata, gashin kanta yake riƙowa, saboda tsawon gashin.
Data kware baki zata masa ihune ya yi maza ya sake ta, shine ta dawo ɗaki taci kukanta, tana mai kara jin zafin rashin daddynta a raye.
Misalin karfe takwas na safe, Kausar da Ayla sun ci abinci, amma ita Rimsha tana ɗaki saboda zazzaɓi, ko miƙewa bata iya yi, Iya da kanta ta kawo mata abincin ɗaki sannan ta lallaɓata a kan ta ci.
Kaɗan ta tsakuri abincin ta barshi, ba yadda iya ta iya, haka ta kyaleta.
Ita kuwa Kausar sai murna take yi, yau za su je biki a kasar anguwar su can, sai shiri take yi, ba ta bi ta kan Rimsha ba.
Iya ta yi ta yi a kan Rimsha ta yi hakuri ta tashi ta yi wanka su tafi, amma ina Rimsha ta ki, ta ce ba zata iya zuwa ba, domin sosai take jin zazzaɓin, ga jikin nata kamar wuta saboda zafi, Iya ta ce zata taho mata da magani.
Ayla ma ta ce tun da Rimsha ba zata je bikin ba, ita ma ba zata je ba, Iya ce ta tasa ta gaba ta ce a'a ita tun da tana da lafita ta shirya su je.
Ba yadda Ayla ta iya haka ta shirya suka tafi bikin nan, suka bar Rimsha ita kaɗai, baiwar Allah sai nishi take yi, ga numfashi