Showing 150001 words to 153000 words out of 355604 words
ta miƙe dan ta ɗauko mashi wayar, ɗagowa ya yi ya kalli Rimsha cike da kulawa ya ce "First lady gaskiya kin iya girki sosai kuma ina godiya, wlh na ji daɗi fiye da tunanin ki". Kasa ta yi da kanta tana murza yan yatsun hannunta, bata ce da shi komai ba, a haka akila ta dawo ta same su, hannunta ruƙe da wayarsa, miƙa mashi ta zo ta yi sannan ta koma saman sofar da ta tashi ta zauna tana murmushi.
Picking call ɗin ya yi tare da kara wayar a kunnansa yana faɗin "Hello Dr ya akayi ne?" Daga ɗaya ɓangaren Nawid ya ce "Wlh na mance ne ban bawa Rismha wayarta ba ga shi sai kiran layin nata ake yi zan bawa driver ya kawo muku". To Imran ya amsa mashi da shi sannan suka yi sallama ya dawo da kallon sa kanta "First lady dama kina da waya har yanzu ne?" Gyaɗa mashi kai ta yi alamar E sannan ta ɗaura cewa "E wannan da nace maka ya taimaka mana a Ilorin shine ya saya mani wayar" yana ƙoƙarin sake yin wata maganar wayar tasa ta sake fara ruri, mai do da kallonsa kan wayar ya yi AA Salahuddeen shine sunan da ya bayyana akan screen ɗin.
Picking ya yi tare da karawa a kunnansa ya ce "Hello AA" daga ɗayan ɓangaren Ahmad ya ce "Prof ina cikin matsananciyar damuwa da tashin hankali wadda yake yi wa rayuwata barazana". Zaro idanu Imran ya yi yana faɗin "A'A me ya yi zafi haka? Haba bana boss kada mu yi haka, tukun nan ma menene sila faɗi in ji, ba dai yarinyar da ka bani labarin nan bace?".
Tamkar Imran na a gaban shi haka ya yi ya gyaɗa kai yana faɗin "Wlh Prof ita ce, kwana biyu ina kiranta bata ɗaga waya, sai yau da safe, shima muna magana ta katse ko gaisuwar kirki bamu yi ba, na sake kiranta sau ba adadi, amma bata ɗauka ba, ni narasa ina zan saka rayuwata, duniyar gaba ɗaya bata yi mani daɗi".
Jinjija kai Imran ya yi kafin ya ce "A'A na tausaya maka, amma ina son ka sani halin da ni nake ciki ko rabin shi baka shiga ba, matata shekara 15 muna tare ina kula da ita rana ɗaya na nemeta na rasa, ta ɓata, duk duniya idan ka cire iyayena ba wadda nake so biyunta, idan na tuna hakan jin zuciyata nake tamkar zata fashe ta fito waje, gara ma kai kana iya kiran wayar tata, ɗauka ne sai time to time take yi, ni kuma fa? In da take ma ban sani ba, bana jin Muryarta bana gani ba, bansan ai na zan ganta ba ya ilahi ya lillihi". Ya kai karshen maganar kamar zai yi kuka.
Zuba mashi ido Akila da Rimsha suka yi suna kallon shi gwanin ban tausayi.
"Yanzu Prof wani shawara zaka bani?" Shiru ya ɗan yi yana sauƙe ajiyar zuciya kafin ya ce "Shawarata a nan shine ka rabu da soyayya da gaibu, ka kama dahir, yanzu yaushe zaka shigo Kd? Idan ka shigo sai mu tsaida matsaya ko?" Jinjina kai Ahmad ya yi sannan ya ce "Toh shikenan zan shigo next week" to Imran ya amsa da shi, sannan suka yi sallama, ya miƙe zai wuce bedroom nasa dan AA ya fama mashi ciwon dake a cikin zuciyarsa, sallamar da akayi a bakin kofar shigowa ce ta dakatar da shi, amsawa ya yi tare da bada izinin shigowa dan ya san mai wannan sallamar, baba mai gadi ne.
Karisowa ciki mai gadin ya yi tare da dukawa kasa suka gaisa sannan ya miƙa mashi wayar Rimsha yana faɗin "Ga shi nan wai na baka in ji driver su Dr" karɓa Imran ya yi tare da yi mashi sannu ya juya ya miƙa wa Rimsha wayar sannan ya wuce ya nufi bedroom nasa yana faɗin "Akila zan ɗan kwanta zuwa la'asar domin kaina yana yi mani ciwo sosai" bai jira amsar su ba ya wuce ciki, shi kuma baba mai gadi ya miƙe ya koma bakin gate, su kuma suka miƙe suka wuce cikin ɗakin da ya kasance mallakin Rimsha a yanzu.
Saman gado suka kwanta Akila tana faɗin "Bari naga wayar taki". Lokaci guda suka yi sabo kamar sun jima a tare, saboda Akila akwai shiga rai ita ma sannan ga shi bata da mugunta tana son mutane sosai ga fara'a Masha Allah.
Miƙa mata wayar Rimsha ta yi, ta karɓa tare da kunna wutar screen ɗin, miss call ɗin Ahmad guda 20 ta gani, cikin sauri ta miƙa wa Rimsha wayarta tana faɗin "Ga shi nan yaya Ahmad naga ansa ya kira ki miss call har 20" karɓar wayar ta yi, kamar dama jira yake yi, tana karɓa sai ga kiran shi ya shigo, picking ta yi tare da kara wayar a kunnanta.
"Hello yaya Ahmad" nauyayyar ajiyar zuciya ya sauƙe kafin ya ce "Why my Queen why zaki azabtar da zuciya ta haka? So kike yi na mutu ko?" Cikin sauri ta girgiza kai tana faɗin "A'a yaya Ahmad bana so ka mutu" "To baki so na mutu me yasa kika ki ɗaukar wayata?" Ɗan satar kallon Akila da ta tsare ta da ido ta yi tana faɗin "Kayi hakuri wayar ne bata kusa da ni, ina wuni? Ya karfin jiki?" Shiru ya ɗan yi mata, can kuma sai ya fara magana "Lafiya lou Alhadulillah, amma dan Allah kada ki sake yin nisa da wayar nan, idan ba haka ba zuciyata zata iya fashewa" gyaɗa mashi kai ta yi kamar tana gaban shi, nan fa ya shiga zuba mata surutu tana bin shi da eh da kuma a'a, har ta ga ji shi kuma da alama yanzu ma ya fara.
Ganin haka yasa Akila ta karɓe wayar, ta kara a kunnenta tana faɗin "Yaya Ahmad amarya tana jin barci, ta gaji da magana ka rage mata maganar da zata yi maka anguma mana". Ta yi maganar cikin raha da wasa.
Ita kuwa Rimsha kamar wadda aka raba da ƙaya, Akila na karɓar wayar ta miƙe ta kwanta abinta, sosai Ahmad da Akila suka rinƙa zuba hira ta ce mashi ita sister Rimsha ce uwa ɗaya uba ɗaya, rashin sani ya fi dare duhu ai kuwa ya yarda har da cewa ta bawa mama waya su gaisa, nan fa ta sake shirga mashi wata karyar wai mama bata nan, ai kuwa nan ma yarda ya yi ya ci-gaba da bata labarin yadda suka haɗu da Rimsha da sauran tarihin rayuwarsa.
Rimsha kam bata ma san lokacin da suka gama waya ba, sai dai ɗagowa Akila ta yi bayan ta gama wayar sai ta tarar ta yi barci, ajiye wayar ta yi saman bedside drawer ita ma ta kwanta a jefenta ba jimawa barci ya yi awon gaba da ita, dama a gajiye ta dawo daga school.
A ɓangaren Jehan kuwa.
Ba wanda ya tashe su domin su yi sallar asuba, da yake ita ta saba tashi, time na cika ta farka, bayan ta yi alwala ta zo ta fara ƙoƙarin tashin su A'isha, amma ina sun ki tashi, cewa ma suka yi ba za su yi sallar ba, Adiva ce kawai ta tashi suka yi Sallah tare da Jehan ɗin, sai dai fa dukkansu biyu ba wadda ta san ina ne ainahin gabas a cikin ɗakin, kawai sun fuskanci in da suke ganin ya fi yi musu kama da Gabas ne suka gabatar da sallar su.
Bayan sun idar suka zauna suna askar har gari ya yi haske, still har lokacin ba wanda ya shigo ɗakin da nufin zai tashe su ko wani abu makamancin hakan, abin ya bawa Jehan mamaki, kenan su a gidan nan ma ba ruwan su da kayi sallah da karka yi duk ubansu ɗaya kenan, Allah ka tsare mu ka barmu da imanin mu, Jehan ta faɗa a cikin zuciyarta.
Sai Misalin karfe 8 Aisha da Maryam suka farka daga barci, wanka suka yi sannan suka fito suka shirya cikin kayan su mai bala'i kyau, riga da wando, ita ma Jehan wanka ta yi Adiva ta bata kaya, amma taki sakawa domin kayar gaba ɗaya ba na hankali a cikinta, duk kayan yan iska ne, kayanta da ta tuɓe shi ta ɗauka ta maida jikinta, ko wacce ta gyara gadonta.
Zama suka yi Jehan ta ce "Aisha ina jinki dan Allah ki ci-gaba da gaya mani menene tarihin wannan gida? Da kuma abubuwan da suke aikatawa a cikinta" gyara zama Aisha ta yi sannan ta fata magana tana dariya.
"Jehan sarkin sauri, ai da kin natsuma zaki ji komai, amma tun da kin matsa bari mu ci-gaba, akan Maganar yan lesbian, kin ga wannan part ɗin na maki bayani yadda ya kamata sai dai in kina son karin haske a kai" Cikin sauri Jehan ta ce "Ni ina son ki gaya mani ainahin abin da yake saka matan aure zuwa irin gidan nan na Hajiyar daɗi ne?".
Guntun tsaki Aisha ta ja sannan ta fara magana kamar haka "Na gaya maki wasu matan auren wlh basu da raayi a kan ire-iren wayan nan abubuwa Hajiyar daɗi ke shiga jikinsu da sunan kawance, sai ta yi ta sakar masu kuɗi, sai sun saba sannan ta jawo ra'ayin su a hankali, idan ke mai kwaɗayin abin duniya ne to sai ki tsinci kanki a ciki dumu dumu, wani lokaci ma baki sani lokacin da zaki faɗa cikin harkar, saboda daɗin duniya, kafin ki farga sai kigan ki kin rufta ko in ce Hajiya ta ruftaki, wa su kuma su da kansu suke neman Hajiya da ta samo musu maza irin ƴan yara shekara 23 zuwa 25 haka, manyan mata fa, sai ki ga sun maƙalewa yara sa'annin ƴaƴan cikin su, irin Hajiyoyin nan ne da mazan su basa zama a gida, irin matan manyan nan, kin gane ai?" Gyaɗa mata kai Jehan ta yi alamar ta gane.
Ci-gaba da magana A'isha ta yi "Wa su matan kuma talaucine ya yi musu yawa, mazansu basu kula da su, basu basu ci da sha a wadace, ga kuma yara sannan ba su sauƙe musu sauran buƙatu da kuma hakkin da ya rataya masu akansu, haka za su sa kafa su fita su bar gida da yunwa ga yara, kinsan uwa kuma ba zata iya jure ganin ƴaƴanta suna kukan yunwa ba, sai kiga ta fita neman taimako, to kin dai san yadda taimakon kasar ta mu ta kasance yanzu, chuɗa ni in chuɗa ka ne, ban gishiri in baka Manda, dayawan mutane basu taimako saboda Allah, sai dai idan za su mori wani abin daga wajen ka suma, kamar wata mata da Zinariya ta zo tana gayawa Hajiya last week, ina jinsu ta ce wlh matar mace ce kyakkyawar gaske ga diri iya diri sai dai talauci ya yi musu katutu, yarta bata da lafiya ta kaita asibiti amma likitoci sun ki su kula yarinyar nan, yarinya kamar zata mutu, amma ba likitan ko Norse ɗin da ta kulasu, wai dan ba su yanki kati ba, kuma ko Naira biyar basu da shi, hakan yasa ta fita goye da yar ta mai shan nono da kuma ɗayar yarta yar shekara 10 dan su je neman taimako, Mahaifin ƴaran nata yana nan yana tura ruwa a kura, to yanzu kin san ruwa a kura ba kowa ke saya ba, yana iya bakin kokarinsa wajen ganin ya basu abin da za su ci, haka matar ta fita neman taimako, ta sha wahala har ta ga ji bata samu komai ba, saboda rayuwar ta yanzu sai a hankali kowa ta kai ta kai yake yi yana neman abin da zai sanya a cikinsa, haka taje wajen wani mutumi ya ce sai ta bashi kanta, da farko taki yarda daga baya da bata da mafita sai ta dawo wajensa ta yarda ta bashi kanta, ta sauƙe yarta na goye ta bawa karamar akan ta riƙe mata suka shiga cikin ɗakin mutumin, bayan ya gama biyan bukatarsa ya ɗauki Naira 500 ya bata ya ce idan tana son karin wani gobe ma ta dawo ya sake biyan bukatarsa ya bata wani 500 ɗin, idan kuma zata bashi wannan yar tata mai shekara 10 ita ma ya kwanta da ita, to zai ba su 1000, ƙinyarda ta yi ta ce ya bar mata yarta ta karɓi 500 tana kuka suka dawo asibiti......" Jehan ta kasa bari Aisha ta dire zance ta tari numfashi ta da cewa
"Iskancin banza dana wofi, bata zuwa ta nemi aikatau ne, sai ta bada kanta, to ba gara yarinyar ta mutuba akan abin da ta aikata, wlh ba duniya ce ta lalace ba zuƙatan mutanen duniyar ne ta mutu murus, ga aiki kala-kala Allah ya yi yawa da su a cikin al'umma, amma ta kasa zaɓar abu guda ta kama dan rufa wa kanta da ƴaƴanta asiri, wlh ban ga laifin mutumin nan ba, laifinta na gani akan me zata bada kanta? Na san cewa azamanin yanzu dama ba komai da komai namiji zai iya ɗauke wa mace ba, shiyasa dama abin da ya fi tun farko kada ki yi zaman banza ki kama sana'a, da ya kasance lokacin bikinki an zuba maki kaya a ɗaki gara abaki kuɗin ki fara sana'a, idan Allah ya sanya mashi albarka kyasayi abin buƙata, dama rayuwar yanzu waye yake ta kayan ɗaki, ku koyawa yara Sa'a a gida shine babban abin riƙewa, da shi za su riƙe miji har ku juya shi, domin idan kina da sana'a har dangin miji ba wanda zai yi gigin kawo maki raini, shima miji zaki ga har wani tarairayar ki yake yi, amma kunzo kun saki jiki an zuba muku kayan kallo idan kuka kafe Tv da ido bakwa tashi kuyi sallah a kan lokaci, ta ina za ku ga daidai? Ni bance maza basu laifi ba, amma mafi yawan laifin na mata ne, ko in ce na iyaye ba zaku binciki sana'ar mutun ba yana samu sosai ko yaya, zai iya riƙe yarinyar ku da abin da zata haifa ne ko yaya, yana da zuciyar nema ne ko zuciyar amace take, amma ku kuna saurin ku aurar da ita ku huta, to wlh in dai haka ne ba zaku taɓa hutawa ba a rayuwar nan, wahala wani na tafiya wani na zuwa, sai ki ga namiji bai da sana'ar arziki amma matansa biyu ko uku, sai ki rasa me iyayen matan suka gani suka aura mashi matar, wani fa ko mace ɗaya da take gidansa ya kasa riƙewa, amma za ki ga wai ya je neman wani auren, kuma sai iyaye su ɗauki yar su bashi, ko da ba abinci a gidan shi, ya je ya buɗe wa yarinya hanyar zina ya kasa riƙeta, ya sake su a gari suna nema suna ciyar da kansu, duk ba ga shi nan ina gani ba, kuma mummy tana bani labari ita da gwaggo wlh idan...." Bata kai karshen maganar ba Adiva ta rufe mata baki
(*Kada ku mance duk wannan surutu da Jehan ta yi, cikin harshen turanci ta yi shi, sannan abu na gaba kada ku mance, duk abin da za ku gani na rubuta dan gane da gidan Hajiyar daɗi ko abin da za su faɗa a cikinta True life story ne, da gaske ne sai dai akwai abubuwan da na kara a ciki dan ya kawata abun ciki kuma har da shi kanshi gidan Haniyar, amma dai duk wani abin da za ku ji ku gani dangane da gidan gaskiya ce ta faru ne*.)
"Jehan ke dai ba zaki bari mu gama jin labarin gidan nan ba ko?" Cewar Adiva guntun tsaki Jehan ta ja kafin ta ce "Allah Adiva abin ne ya ɓata mani rai talauci hauka ce".
Dariya A'isha ta yi sannan ta ci-gaba da cewa "Ni dai bari na baki iya labarin da ya sawwaƙa, ina ganin dai yanzu mu rufe babin matan auren nan ko..." Tun bata kai ƙarshe ba Adiva ta ce "A'a kada ki rufe ki cigaba da gaya mana".
Jinjina kai Aisha ta yi sannan ta cigaba da cewa "To matan auren dai abubuwa wajen kala huɗu ke kawo su nan, kun ji uku na farko Hajiyar daɗi ke janyo ra'ayin su da kuɗi, na biyu kuma mazansu basu kula da su, na uku kuma talauci, to abu na huɗun kuma wadda shine na karshe ni a iya nawa sanin da yake kawo matan aure cikin wannan harkar, shine masu auren namijin da baya son su, ko kuma mai biye-biyen mata, hakan yakan sa baya kula su baya biya musu buƙatar aure, idan sun ga ji sai su faɗo wajen Hajiyar daɗi neman mafita, wa su kuma kwaɗayin abin duniya, wayan nan sune ke kawo matan aure cikin wannan harkar, amma ni anawa ganin babbar matsalar shine mace ta zauna ba sana'a wato talauci, dan mafiyawancin wayan da Hajiya ke kawo wa nan zaki tarar talauci ya yi masu katutu, idan ka basu kyautar naira ɗari sai su ji tamkar ɗubu ɗari ka basu, saboda ba su samu, wata ma sai ta fi wata guda bata riƙe naira hansin nata na kanta ba, hakan shiyafi yawan kawo su cikin wannan harkar, da za'a samu su kama sana'a abubuwa za su yi sauƙi sosai, yanzu dai mu rufe babin matan aure mu shiga babin maza. Akwai maza a nan masu naman maza, wato yan luɗu, su kuma suna farowa ne daga wasu manya dake lalata su, misali kin ga akwai irin matsafa ko masu zuwa wajen boka, da boka zai ce masu sai sun yi luwaɗi da karamin yaro sannan za su sami biyan buƙatar da suka je nema, wani lokaci ma wani maganin boka ke basu akan su zuba wa karamin yaro a duburansa, to daga haka wasu mazan ke faro luɗu, idan wayan nan sun koya musu sun kuma tafi sun kyalesu basu samun biyan buƙata suna kashe kishin da suka saba da shi, to fa shine suma sai su shiga neman yara suna lallata su, da haka abin yake yawai ta, akwai maza je ma da suke da mata amma ba su son matan sai dai maza yan uwansu shine sai su bar mace tana gantale basu biya mata buƙata, saboda su sun samu sun biya nasu,