Showing 153001 words to 156000 words out of 355604 words
wata macen sai ta fi shekara ba tare da sun kwanta da mijijta ba, kinga kuwa tunda ba dutse ke da akwai a kirjinta ba, dole ta fita neman mafita, to kin ji na maza kuma shine Hajiyar daɗi take tara su a nan dan saboda business ɗin ta ya kara karfi..." Katse ta Jehan ta yi da cewa "To mutanen ba su iya gudu su bar gidan ne?".
Shiru A'isha ta ɗan yi kafin ta ce "E ni dai ban taɓa jin ance ga wata ta gudu ba, ke gidan nan fa da kin shigo za ki ji baki son fita, wlh da kin yi ido biyu da Hajiya zaki ji ke fa ko mutuwa ba zaki so ta raba ki da gidan nan ba, kuma kin san gidan ne akwai daɗi, idan kin bawa hajiya goyon baya wlh har shopping zata rinƙa sanyawa ana ɗaukan ki kuje a sai miki mayukan gyaran jiki da kaya masu kyau dan saboda ki fito da kyau yadda masu kuɗi za su yi rububinki, babu abin da Hajiya bata saya mana, ni kam ai na sha zuwa shopping tare da ita ma, sau ba adadi, amma idan kika ki bata haɗin kai zaki sha wahala, ni sau ɗaya ma na taba ganin wadda taki yarda ta bawa Hajiya haɗin kai, amma daga baya yarinyar nan tafi kowa zaƙewa a cikin gidar nan, tana nan yanzu ma haka, sai dai yanzu tauraronta ya dishashe bata kawo wuta sosai, ba kowani Alhaji bane idan ya zo zai kwasheta.."
Shiru Jehan ta yi tana tunanin ta yadda zata bar gidan, dan wlh ba zata zauna ba. "Amma A'isha idan Alhaji ya ɗauke ki fita kuke yi ne? Ko dai a cikin gidan nan ake gama yin komai?" Yar dariya A'isha ta yi kafin ta ce "Kai Jehan tunanin me kike yi da kika yi mani wannan tambayar?" Girgiza kai Jehan ta yi alamar ba wani tunanin da take yi.
"Akwai alhajin da zai ce fita za ku yi kuje ku yi kwana biyu, akwai kuma wanda zai ce a nan zai biya bukatarsa ya wuce" ajiyar zuciya Jehan ta sauƙe sannan ta ce "Amma Hajiya bata tsoron idan an fita da yarinya ta gudu?" girgiza kai Aisha ta yi tana faɗin "Ai hakan ma ba zai yi wu ba, kin manta na gaya maki duk wadda ta shigo gidan nan ba zata so fita ba? Saboda daɗin shi, sannan kuma ba haka kawai Hajiya take barin wani ya fita da yarinya ba, a'a sai idan ya ajiye maya makudan kuɗi da zata yanka mashi, idan ya dawo da yarinyar kamar yadda ya ɗauke ta, to sai ya karɓi kuɗinsa, idan kuma yarinyar ta sulala ta gudu, shikenan wayannan kuɗin sun zama na Hajiya a madadin yarinyar" "Amma Aisha su alazawan basu tada bala'i aba su kuɗin su?".
Wani irin dariyar shakiyanci Aisha ta yi kafin ta ce "Lallai Jehan baki san waye Hajiyar daɗi ba, ke dai kiyi fatar Allah yasa zuciyarta ta soki kema kuma ki sota, amma wlh ni banga wanda ya isa ya nunawa hajiya yatsaba, ke kinga yadda take zarewa manyan mutane ido kuwa? Amma fa kawata Afnan na ɗakin gaban mun nan ta ce mani wai abin da yasa Hajiya take zare musu ido su ji tsoron ta wai magani take yi masu, amma fa ni baruwa na ban sani ba" Ta kai karshen maganar tana girgiza kai tare da yarfe hannu alamar ba ruwanta.
Shiru Jehan ta yi tana tunain yadda za'a yi ta bar gidan ita da Adiva.
A wannan hali Zinariya ta shigo cikin ɗakin ta same su, tana sanye da wata arniyar wandon jeans gundu zuwa cinya da yar karamar riga, kamar dai jiya ta ci uban make up kamar me, "Ke Aisha ku fita kuje kitchen ku karɓi abincin ku, sannan idan kun gama ci Aisha ki same ni a office na" tana kai karshen maganar ta wuce ta fita.
Miƙewa Aisha ta yi tana faɗin "Kuzo mu je mu karɓi abinci" "Abinci kuma?" Jehan ta maimaita, gyaɗa mata kai A'isha ta yi alamar e, "Waye mai sayan abincin?" "Kuɗin da muke samowa wajen alazawa mana, da shi Hajiya take bamu abinci mai rai da lafiya sau uku wata sain ma sau huɗu ga mayukan gyaran jiki, turarukan, da kayan sawa, ga su ice cream da su chocolate, shiyasa nace maki zaki ji daɗin zaman gidan nan komai akwai wlh, sai dai muce Alhadulillah, ban da kema da abinki idan Hajiya bata gyara mu ba, ta yaya zamu fito tsab har agan mu ace ana yi da mu".
Zubawa Aisha ido kawai Jehan da Adiva suka yi, ba shakka bariki ya zauna wa Aisha sosai, ta kware a duniyanci ba'a magana, wannan da ba dan sun tabbatar sheɗan shi kaɗai ne bai da yan uwa kanne da yayyuba, da sai su ce tabbas Aisha kanwar shaɗan ce, yarinya kamar shaiɗan ya mata fitsari a kai, wai badon ana gyara su ba ta ya za'a gansu a buƙace su, innalillahi wa inna ilaihir rajiun. Duk wannan zance Jehan ke yin shi a cikin zuciyarta.
Suna zaune a wajen har Aisha ta dawo hannun ta riƙe da plate na abinci sai tiriri yake yi, lafiyayyiyar jolof rice ce, ta ji kayan kamshi da kayan haɗi, ga kwai a gefe guda sai kayan ganye su cucumber and cabbage da sauransu, saman carpet ɗin dake a cikin ɗakin ta zauna tare da ɗaukan spoon ta fara ci, su dai ido kawai suka zuba mata. Ita ma Maryam da ta ga su Jehan ba su da niyar tashi sai ta tashi abinta ta nufi waje dan zuwa kitchen ɗin karɓar nata abincin.
Suna zaune shiru, ita kuma A'isha tana ta kai loma bakinta. Zinariya ce ta sake turo kofar ta shigo cikin dakin, kai tsaye wajen Jehan ta nufa, ba tare da ta yi musu magana ba ta riƙo hannun Jehan suka fice waje. Kai tsaye wani ɗaki ta kai ta, a nan ta zaunar da ita saman wani luntsumemen sofar mai bala'i taushi, bayan ta zaunar da ita sai ta koma saman table chair dake a cikin ɗakin ta zauna tana faɗin "Ki saki jikinki Hajiya ce ta ce kada a baki abincin da ake bawa yan gida, ta ce a rinƙa baki abinci na musamman har sai ta dawo, dan haka yar gold zata shigo maki da abinci yanzu".
"Me yasa ba za'a haɗa mu a bamu abinci iri ɗaya ba?" Cikin sauri Zinariya ta waro ido tana kallon ta, mamakine ya bayyana karara a kan fuskarta anya yarinyar nan kanta ɗaya kuwa? Har ki samu an yanta ki shine zaki yi wata magana, lallai wannan da zafin ki kika zo, amma zama ki yi sanyi ne, duk wannan zancen zuci Zinariya take yi.
Ganin ta yi shiru yasa Jehan ta ce "Duk abin da zan ci, shi Adiva zata ci, domin yar uwata ce ta jini, idan kuma ba za ku bata abin da za ku bani ba, to nima bana buƙata" ta kai karshen maganar tare da miƙewa zata bar wajen. Tsawa Zinariya ta daka mata wadda ya sanya ta dakatawa ba tare da ta shirya ba. "Koma ki zauna!!" shine abin da Zinariya ta ce.
Shiru ta tsaya tana tunanin ta koma ko kada ta koma. A wannan hali wata yar figaggiyar mata ta shigo wadda kuma da alama ita ce yar gold ɗin, domin kuwa ga shi ta yi kalar gold ɗin, fuska golden color kafa bakinkirin kamar zunubi, ta ci bleachin ta ƙoshi, har wani ɗayewa fatar kumatunta ya yi, tsabar ta shafa mai ɗin ya mata yawa, har wani ɗanye-ɗanye fatar fuskarta ta yi, kana iya ganin jan namar ciki, tana sanye da wani kafurin doguwar riga wadda ya matseta sosai, ga bayan nata a shafe kamar anyi pilastar dakali da siminti, ba ta da shape ko kaɗan, amma ba laifi kyakkyawa ce jinin hausa fulani, sai dai tana nan kamar bulala saboda sirranta, abin ba'a magana.
Hannunta ruƙe da ƙatuwar tray mai ɗauke da abinci mai ji da lafiya, fried rice ne ya ji su green beans carrot da sauransu, sai kamshi yake tashi, daga gefe kuma wani karamin plate ne mai ɗauke da haɗin salat, ga gasashen rabin kaza a gefe, sai hollandia ɗaya da ruwan swam water.
A gaban Jehan ɗin ta zo ta ajiye tana faɗin "Ya na ganta a tsaye?" Fuska a ɗaure Zinariya ta ce "Rabu da yar nema wai dole abincin da muka bata shi za mu bawa yarinyar nan da Hajiya ta turota shekaran jiya, wai yar uwarta ce dole ta re za su ci".
Zaro wayan nan shegun idanun nata yar gold ta yi, ga idanun nata saboda tsabar shaye-shaye sun sauya launi zuwa kalar fuskarta, wato golden color, dama kuma idanun nata ba farare bane, sannan gasu a tsaye a bushe kar. Tsawa ta dakawa Jenan "Ke wuce ki zauna ki ci abinci ko kuma na kira madaka katti su ɗura maki abincin nan tas!!".
Kare mata kallo Jehan ta yi tsab, fuska a yatsune ta ce "Idan kuma bani da niyar ci, na ce na ƙoshi fa? Akwai dole ne?" Wani irin bakin ciki yar gold ta ji, ranta a matukar ɓace ta wankewa Jehan fuskarta da mari. Cikin sauri ta dafe kuncin nata, idanuwanta suka ciko da kwalla yau shine karo na farko da aka taɓa marin wannan kyakkyawar face ɗin nata, ga shi marin ya shigeta sosai, tunani ta fara yi shin ta rama ne ko dai ta hakura sai ta gama sanin yadda gidan yake.
"Uban me kike kallo da kika tsareni da ido? Ko zaki rama marin ne? Idan rashin kunya kike ji da ita to gidan ta kika zo, ki wuce ki zauna ki fara cin abinci nan, idan ba haka ba mu yi maki dukan kawo wuƙa". Ba tare da ta yi magana ba ta nufi hanyar fita daga cikin ɗakin.
Damƙo rigarta yar gold ta yi ta janyota baya har sai da ta faɗi kasa, a fusace ta miƙe ta damki wuyar yar gold, domin ta kure hakurinta, ta ɓata mata rai sosai.
Zinariya na ganin haka ta yi maza ta taso suka haɗu suka fara naɗawa Jehan ɗan iskan duka domin su sauƙe mata wannan ji da kan nata, sosai Jehan ta yi ƙoƙarin kare kanta dan kada su ji mata ciwo, amma da yake su biyu ne, sai suka yi mata ɗan iskan dukar kawo wuƙa.
Tun tana iya kuka mai ɗan sauti har kukan nata ya dai'na fita, sai da suka ga sun raunatata, sannan suka kyaleta suna mai da numfashi, Zinariya ta koma mazauninta ta zauna, ita kuma yar gold cike da izza da bada umarni ta ce
"Ki yi maza ki tashi ki ci abincin nan ko kuma na kara maki wani dukan wadda sai kin kasa motsi, har mu zaki buɗewa ido? To tun kafin kizo duniya mukenan, iyayen ki ne mu a iskanci da rashin kunya, in dai a gaban mu kike to ba a ma haifeki ba a rashin kunya!!".
Ita dai Zinariya sai haki take yi kamar wadda ta yi tseren gudu, ba karya sun jibji Jehan iya san ransu, sun gwada mata karfin shekaru da iya bariki.
"Wai ba zaki tashi ba ina magana!!" Yar gold ce ta sake magana, ko gezau Jehan ba ta yi ba, kamar bata a cikin ɗakin, tana kwance rashe-rashe a kasa tana hawaye tare da fitar da kuka mara sauti sosai.
Ganin taki tashi yasa Yar gold ta kariso wajen ta sanya hannu ta ɗagota ta zaunar da ita tare da turo mata tray ɗin abincin a gabanta, kin ci ta yi kamar ma bata ga abincin ba. Abin ba karamin fusata yar gold ya yi ba, cikin fushi ta ɗaga hannu zata mareta, sai lokacin Zinariya ta sanya baki ta hanyar dakatar da ita, domin ta lura Jehan mace ce mai taurin kai ga kafiyar bala'i, idan suka biye mata to za su ji mata babban ciwo wadda idan hakan kuma ta faru to fa ba makawa sai sun biya Hajiya kuɗin da ta sayeta.
Miƙewa ta yi ta kariso wajen a ya yin da take sallamar Yar gold, gaban Jehan ta zo ta tsugunna tana faɗin "Shawarar da zan baki a nan shine idan zaki sauƙe wannan rashin kunya da wani jiji da kai to garama ki sauƙe tun wuri, idan ba haka ba, zaki ci bakar wahalane kawai a banza, domin duk wanda kika gani a gidan nan idanuwansa a buɗe yake, kowa shegen kanshi ne, so is better for you da ki natsu ki bi mu sau da kafa, domin ki zauna lafiya, yanzu ki ɗauki abincin nan ki ci!".
Tamkar babu Jehan a wajen haka ta yi shiru ta kyaleta, domin ta riga ya kafe a kan ba zata ci abincin ba. Ba yadda Zinariya bata yi ba, amma Jehan ta ki ta ci abincin nan, haka ta hakura ta kyaketa ta ce ta koma ɗakin su.
Jikinta har kerma yake yi saboda dukan da suka yi mata, haka ta miƙe zuwa ɗakin nasu, tana shiga Adiva ta taso da sauri ta riƙe ta tana faɗin "Jehan lafiya? Me yafaru naga bakin ki a fashe?". Shiru ta yi masu ba magana, zama suka yi saman katifar gadon nasu, Aisha da Maryam dake cin abinci ma suka taso suka zo wajen. Aisha ce ta ce "Sun dake ki ko?" Gyaɗa masu kai Jehan ta yi alamar e.
Jinjina kai Aisha ta yi kafin ta ci-gaba da cewa "Ai in dai kina son zama lafiya da su, to fa sai dai ki yi hakuri ki zauna a yadda suke son ki kasance". Kuka Adiva ta fara yi tana faɗin "Jehan dan Allah ki gaya mani ina daddyna, na gaji da wannan bakar wahala, wlh tun da ya fita ya ce zai je gidan ku na jira shi, shikenan bai sake dawowa ba".
Ita ma Jehan ɗin wani sabon kuka ta fara yi ba tare da ta yi magana ba.
Wai shin wace ce Adiva, Adiva ya ce ɗaya tilo ga uncle Shitu wato abokin daddyn su Jehan, uncle Shitu yana bala'i son Adiva sosai da sosai ita kaɗai Allah ya bashi, sosai abaya suna samun ciki kafin Adiva, wasu cikin zubewa suke yi, wasu kuma ana haifa yaranne basa zama suna mutuwa, Adiva ce kawai Allah ya bar musu, suna bala'i sonta.
Sai da Jehan ta yi kukar rashin mahaifi sosai yau, sannan ta goge hawayen da yake akan fuskar, sai hakuri su Aisha suke bata amma bata kula su ba, sai da ta yi mai isarta tukun nan ta yi shiru dan kan ta, kallon Adiva ta yi cike da kwarin gwiwa da kulawa ta ce "Adiva da daddyna da daddyn ki dukka Allah ya yi musu rasuwa, dan haka yanzu mu za mu yi faɗa domin rayuwarmu, dole ne mu san abinyi, su daddy ba za su iya zuwa in da muke ba bare su taimake mu, mu zamu tai maki kan mu da kan mu, yanzu ina son ki gaya mani ina mummy ki?". Sosai Adiva take kukan jin daddynta ya rasu, sun shaku sosai da shi, uncle Shitu ya bata kulawa fiye da tunanin mai tunani, rayuwar farinciki tun ranar da tasan wace ce ita, tun ranar da ta iya tantance mutun da dabba, yau rana tsaka ta yi wani irin rabuwa mai muni tsakaninta da iyayen ta, wannan wace iriyar rayuwace.
Rungume ta Jehan ta yi ta fara bata hakuri, tana bata hakurin ita ma tana hawaye, domin yau ta yi kukan rashin daddunta sosai, da ace daddynta yana nan da wayan nan shaiɗanun ba su isa sun dake ta ba. Sai basu hakuri su Aisha suke yi, amma ina sun ki yin shiru, su kaɗai suka san raɗaɗin dake a cikin zuƙatansu, su kaɗai suka san azabar da suke ji, bayin Allah duk wanda ya gansu a haka sai ya matse musu kwallah.
Sun kwashi mintuna 20 suna shan kukansu, sai da suka ji zuciyoyinsu sun musu sanyi sannan suka raba jiki dana juna, Jehan ta miƙe ta nufi toilet dan zuba ruwa, idan ba haka ba, zata iya sumewa a wajen.
Bayan ta fito Adiva ma ta shiga ta zuba ruwa. After some hours da basu wuci biyu ba. Zaune suke a saman gadon Adiva, dan Jehan ta ce ba zata rabu da yar Uwarta ba, haka ita ma Adiva ɗin.
"Adiva ina mummynki?" Jehan ta tambaya tana tsareta da ido, kamar za ta yi kuka ta ce "Mummy ban ganta ba" "Kamar ya ya baki ganta ba? Ina ta je?!" "E naje school na dawo naga gida ba bu kowa sai masu aiki, dana tambayi baba mai gadi ya ce mum ta fita, na jirata har dare bata dawo ba, washe gari masu aiki suka yi girki na yi wanka na shirya zuwa school, na je na dawo ban ga mum ba, bata dawo ba, na tambayi mai gadi ya ce E bata dawo ba, haka har sati ɗaya ban sake ganin mummy ba, na kira layinta bata shiga, shine tun daga lokacin ban sake saka ta a ido na ba, ina cikin wannan hali wa su mutane suka zo wai banki na bin daddy kuɗi kuma lokacin biya ya yi dan haka mu fita a gidan za su yi gwanjon gidan, ni bansan in da zan ga kowa na yan uwan daddy ko mummy ba, kinga daddy shi ɗan Niger ne, mummy kuma ni ban sani ba, to alokacin ban wani damu ba domin ina tunanin kuna gida, haka na haɗa kayana abubuwan da nake buƙata tare da wayata na ce driver ya kai ni gidanku, haka ya ɗauke ni a mota muka nufi gidan ku, tun a bakin babban gate na ku ya sauƙe ni na juya kan motar domin har da motar a cikin gwanjon da za'a yi, na sha kuka lokacin da na je naga gidan ku a rufe, ba bu kowa, nan ne hankalina ya yi mugun tashi, zama na yi a kofar gate ɗin ku ina ta kuka, ban kawo komai a zuciyata na ɓatar daddyna ba, na yi tunanin ko sun yi tafiya da daddynku ne, tun da kunga suna yin hakan wani lokacin, da na zo naga gidan