Showing 102001 words to 105000 words out of 355604 words
har barci ya ɗauki ke shi kwance ya tada kai da cinyar Musharraf, ganin ya yi barci yasa ya cigaba da tofa masa addua'o'i yana mai jin kaunar Michael James har Lion da ya dake shi, duk yana jin kaunar su a ransa, domin a cewar sa dukkan su sun yi mashi rana, kuma duk cikin su Lion ma ya fi yi mashi rana, domin idan bai taimaka ya bashi gurbin zama a gidan ba, su James ba su isa su zaunar da shi ba, bai isa ya zauna har ya saba da su ba, kai idan Lion baya son shi ma, ko duba jikinsa James ba zai yi ba, domin kuwa da tun farkon zuwan shi Lion zai ce ayi waje da shi, kuma ya zama dole a fitar da shi, ko da James baya so, ya zamar masa dole ya bi abinda Lion yake so.
Musharraf ya jima a haka yana ta faman karantawa Michael Addu'a har shima barci ya ɗauke shi yana daga zaune, ya jingina jikinsa, da jikin bangon kayin gadon.
Duk wannan hirar da suka yi, basu san da camera a ɗakin ba, domin Lion ya sakawa duk wani dake gidan ido, dan yaga me suke yi, tun bayan abin da ya faru da James, sai dai ba kasafai yake samun time na duba cameras ɗin ba, sai irin tsakiyar dare bayan ya kammala aikin da yake yi, sai ya ɗan bincika ya ga me suka aikata yau, amma fa wani lokaci ya kan yi kwana biyu bai bincika ba, saboda yanzu ba sai an gaya muku ba, kun sa abubuwa sun masa yawa.
(To bari mu koma Nigeria dan jin wani hali suke ciki)
💖💖GIDAN ABBO💖
Zaune Jelly take a tsakiyar palon Ummi, ta baza kayan cimanta a gaba, ciki harda nama, wato soyayyen kaza, ya ji kayan kamshi da kayan haɗi, sai tashin kamshi yake yi, kun san dai jelly akwai amana tsakaninta da kaza tom.
Sai faman yagar cinyar kazar nan take yi, ga su hollandia da Yoghurt a gefenta, Ummi ta kira mai kunshi ta tsara mata kunshi sosai da sosai, ya fito zane mai kyau, ya yi maroon color, sai ɗaukan ido yake yi, idan ba ku mance ba Jelly farace tas, hakan yasa jan kunshin ya yi mata bala'i kyau, sannan kuma an zana mata baki a saman kafarta, ta samar jan kunshin, haka su ma hannayen ta an zana bakin kunshi, zannen manya-manyan flowers masu kyau, abin ba'a cewa komai, Jelly ta yi kyau sosai.
Sanye take da doguwar riga na kanti, daga samar rigar ya kamata, daga daidai kugunta zuwa kasa kuma ya yi wani bala'i buɗe wa sosai kamar umbrella, Ummi ta wanke mata gashin kannan nata, ta busar mata da hand dryer, sannan ta ɗaure mata shi a tsakiyar kanta, bayan ta shafe mata shi da mayuka masu kyau da kanshi da tsada, sai kyalli gashin nata yake yi.
Haka zalika Ummi da kanta ta yi mata simple make up a fuskar ta, yau dai Jelly ta fito a asalin Jellyn daddynta, tayi kyau sosai.
Tun daga bakin kofar palon ya tsaya ya zuba mata ido yana kallonta, ya kasa ɗauke idanuwansa daga kanta, kuma ya kasa karisowa cikin palon, sai famar yagar nama take yi abinta, bata ma san da wani na kallonta ba.
Ya jima tsaye a wajen yana kallon duk abin da take yi, wani lokaci idan namar ya yi mata tauri ta kasa gutsira, sai ta turo ɗan bakin nan tana kunkuni ita kaɗai, abin ba karamin burgeshi yake yi ba.
Ya shagala da kallon ta kamar a mafarki ya ji an ce "Nawid lafiya kake yi wa baby irin wannan kallo haka?" Yar firgita ya yi ya maido da kallonsa kan Ummi dake tsaye hannunta riƙe da robar ice cream, kwata-kwata bai ma ga shigowar ta ba, ya shagala da kallon Jelly.
Ɗan sunkuyar da kansa kasa ya yi yana ɗan murmushi yana sosa kai.
Sosai Ummi ta ji daɗi, dan a nata ganin Nawid ya fara son baby.
Karisowa cikin palon ya yi, sai wani yan kame-kame yake yi, kawar da kallon ta daga kansa Ummi ta yi tana faɗin "Baby ga Ice cream ɗin"
Cikin sauri ya ce "Haba Ummi ashe kace kike goyawa baby baya tana wannan ciye ciyen da take yi". Hararar wasa ta wurga masa sannan ta ce "Ina ruwan ka to? Cikin ka ta ke kaiwa ne?" Girgiza kai ya yi yana faɗin "A'a My Ummu, uwa ta gari, ni ba ruwana ta ci iya cinta, idan ma bai isheta ba, ni sai na karo mata wasu cimar".
Nauyayyar ajiyar zuciya Ummi ta sauƙe tana godiya ga Allah da ya sa Nawid ya fara sauƙowa a kan lamarin baby.
Duk wannan abin da ke faruwa Jelly bata san komai ba, ita dai tana duniyar nama, kwata-kwata bata jin me suke faɗe, in fact bata ma san da su a palon ba.
(Tashin hankali a lallai Jelly kin shahara, wai🤔)
Sai miƙa mata ice cream ɗin Ummi ke yi tana magana, amma ina Jelly bata ma san da tsayuwar ta a wajen ba.
Nawid ne yazo ya karɓi Ice cream ɗin yana faɗin "Ke dai Ummi bani nan, bari na zauna na jirata, wata kila idan ta kammala cin namar ta karɓa Ice cream ɗin". Ba musu Ummi ta miƙa masa robar sannan ta wuce cikin bedroom nata.
Zama ya yi kusa da ita yana kallon asalin kyau babu miss, sai tashin kamshin take yi abinta.
Yana zaune ya zuba mata ido har ta gama cin namar tas, sannan ta ɗago kai tana kallon shi.
"Yaya Nawid kai ma ka zama ɗan iska ne?" Zaro ido ya yi da mamaki yake kallon ta, ɗan iska kuma, ya maimai ta kalmar a zuciyarsa.
Ganin ya mata shiru yasa ta sanya hannunta zata karɓi Ice cream ɗinta dake hannunsa, wani irin shock ya ji lokacin da hannunta ya taɓa shi, lokacin guda ya ji wani irin yana yi mai wuyar misaltuwa a gare shi, zuba mata ido ya yi ya kasa ɗauke wa, yadda take shan Ice ɗin kawai yake kallo, yadda lips nata ke motsawa ba karamin jefashi cikin yanayi take yi ba.
"Yaya Nawid baka amsa mini ba? Kai ma ka zama ɗan iska ne?" Da kyar ya iya saita nitsuwarsa murya kasa kasa, cike da annashuwa ya ce "Baby me nayi kuma na zama ɗan iska?".
"Kana kallon mata mana, ai san duk mai kallon mata ɗan iska bane? Shiyasa ranar ai nacewa wannan Abbon kwarto". Zaro idanuwansa waje ya yi, a ɗan razane ya ce "Me Abbo kuma ya yi da kika ce masa kwarto".
Nan fa ta shiga bashi labarin abin da ya haɗa ta da Abbo ranar, tana yi tana shan Ice cream ɗinta, yana sanyaya mata zuciya, har wani lumshe ido take yi abinta, daga karshen ta rufe masa da cewa "Dana gayawa Ummi Abbo ya yi mini kwartanci sai ta ce wai na dai na ce masa kwarto babana nane, kuma ni na gani a Tv duk mai taɓa mata kwarto ne, mai kallon mata kuma ɗan iska".
Mutuwar zaune Nawid ya yi ya kasa tantance a wani matsayi zai ajiye Abbo, wannan wace irinyar lalacewa ne, ace yarinya kusan jijarka tana ce maka kwarto, kuma duk kai kaja, kawai ka samu yarinya ka fara shafa mata wuya, wa iya zubillah.
Ya jima shiru kafin ya ce "Baby kada ki sake ce masa kwarto kin ji ko?" Gyaɗa masa kai ta yi alamar e. "Yauwa My baby, baban ki ne kamar yadda Ummi ta gaya miƙi" shiru ta masa sai shan Ice cream nata take yi, dan ita in dai tana cin abinda ranta ke so, to idan ba ya zama dole ba, bata magana.
Shiru suka zauna har ta kammala shan Ice cream ɗin duka, sannan ya ce "Baby gyara na yi miki hoto kin ji ko? Ƙunshin nan ya miki kyau sosai zan miki hoto na ajiye tarihi" to ta amsa masa da shi, sannan ta gyara zama ya fara ɗaukar ta hoto.
A wannan hali Abbo ya shigo ya same su, cikin fushi ya ce "Kai Nawid me kuma ya haɗa ka da baby haka? Me ya zaunar da kai kusa da ita" miƙewa tsaye Nawid ya yi yana mamakin karfin hali irin na Abbonsa, kuma dama ya san haka zata iya faruwa, tabbas yana jin wani abu a zuciyarsa game da baby, amma bai ɗauka soyayya bace, ya fara kula tane dama dan ya nisanta Abbonsa da ita, tun da ya yi kokarin fargar da Umminsa amma taki ganewa, shiyasa ya biyo ta wannan hanya domin ya nuna yana son baby ko Abbo'nsa zan ji kunya ya daina wani tunani a kanta, idan ma yana yi, amma shi zance na gaskiya Jehan yake so ba baby ba.
Tsawa Abbo ya sake daka masa "Ba da kai nake magana bane Nawid?" Sunkuyar da kai kasa Nawid ya yi yana ɗan sosai kai, kasa kasa cikin girmamawa ya ce "Abbo ka manta Ummi ta ce ita zan aura ne?". A fusace Abbo ya ce "A'a ai na gaya maka ba zaka auri tsintaciyar mage ba, mai asali zaka nemo mana, bamu son mara asali a cikin zuriar mu".
(Toh fa, lallai Abbo)
Ɗago kai Nawid ya yi yana kallon Abbonsa, mamaki karara ya bayyana a kan fuskarsa, tunani ya fara yi anya Abbo nan shine babansa kuwa.
Muryan Jelly ne ya katse masa tunanin sa da cewa "Yaya Nawid ka gama hoton ne in tafi ɗaki?" Kakalo murmushi ya yi tare da sakin fuskarsa sosai, ya miƙa mata hannusa yana faɗi "Riƙe hannuna muyi selfie" yana magana yana satar kallon Abbo.
Cikin sauri Jelly ta riƙe hannunsa, matso da ita jikinsa kaɗan ya yi tare da ɗaga wayarsa sama yana faɗin "Oya yi murmushi....." Bai gama rufe baki ba Abbo ya daga musu tsawa "Ke baby wuce ki tafi ɗaki, kai kuma Nawid daga yau idan ka sake bari na ganka da rana a gidan nan sai ranka ya ɓaci!!!"
Turo baki Jelly ta yi a shagwaɓe ta ce "Ni dai ba zan tafi ko ina ba har sai yaya Nawid ya gama yi miki hoton da ya ce".
Sanin halin Jelly da kafiya ya sa Nawid ya bi umarnin Abbo ya sa kai ya wuce, dan yasan Jelly ce kawai maganinsa.
Ai kuwa bai kai tsakiyar palon ba Jelly ta zube kasa tana mirgina kafafu a kasa tana ihu kamar ba lafiya ba.
Da yar gudu Ummi ta fito daga cikin bedroom nata, shi kuma Nawid cak ya tsaya a cikin zuciyarsa yana faɗin "Ai beby dolle ma na rinƙa kulaki dan kece kawai maganin Abbo"
Ganin Ummi ta fito yasa Abbo yasa kai ya wuce ya nufi nashi bedroom ɗin.
"Nawid lafiya me kayi wa baby?" Cikin sauri ya ce "A'a Ummi ni ba ruwana ita da Abbo ne fa, shi ya hana na ɗauke ta hoto shine take ihu". Girgiza kai Ummi ta yi tana faɗin "A kan me to zai hana a ɗauke ta hoto kuma?" Buɗe hannaye Nawid ya yi yana faɗin "Ni ma dai ban sani ba, amma ki tambaye shi" wucewa ta yi ta bi bayan Abbo ba tare da ta sake yin magana ba.
Tana tafiya Nawid ya dawo kusa da Jelly da sauri, a zuciyarsa yana tunanin ta yadda zai ja ta a jikinsa sosai har su saba, su zama kamar masoyan gaske, dan Abbo ya goge duk wani kudiri dake ransa a kanta.
"Ki yi shiru kinji babyn yaya Nawid? Yanzu ta shi mu yi hoton, kuma anjima da daddare zaki rakani shopping, daga nan sai muje gidan kallo mu kalli film" wani ihun murna ta saki, dan Jelly ba baya ba wajen kallon film, akwai ta da son kallon bala'i, tun ma tana da lafiyar ta haka take. Nan take ta fara murmushi kamar ba ita ce mai kuka yanzun nan ba.
Sai dariya take yi Nawid ya ɗauke su hoto kala-kala sannan ya wuce ɗakin sa yana sake waigowa ya kalleta, ita ma sai kallon shi take yi, yau yaya Nawid ya yi abin kai a cewar ta.
Har ya shige part nasa kallon shi take yi, shima kuma har ya shige juyowa yake yi yana sake kallon ta, yadda kasan masoya na bankwana da junansu.
Sai da ya kurewa ganin ta sannan ta wuce ɗakin ta ita ma, ba tare da ta tattare kayan cimar da ta ci ba, a nan ta barsu watse.
Tana shiga bedroom nata ta haye gado ta kwanta ta yi shiru kamar mai tunani.
A ɓangaren Ummi kuwa, tana shiga bedroom na Abbo ta same shi yana kokarin rage kayan jikinsa zai shiga wanka.
"Abbon Nawid a kan me zaka hana Nawid ya yi wa baby hoto?" Shiru ya ɗan yi yana tunanin ta yadda zai kubce mata. Tsawon minti ɗaya sannan ya ce "Saboda idan ya ɗauke ta hoto zai iya ɗaurawa a media har yan uwanta su gani su zo su rabamu da ita". Yar murmushi Ummi ta yi, da da farko ta shigo ranta a matukar ɓace har zuciyar ta fara raya mata anya zancen Nawid da ya gaya mata a kan Abbo na da wata manufa a kan Babby anya ba gaskiya bace kuwa, amma yanzu jin abin da ya ce yasa ta yi watsi da wannan tunani da ta fara yi ta saki fuska tare da karisawa kusa da shi tana faɗin "Gaskiya ne kuma, to shikenan yanzu bari na koma bedroom na, dan ina shiryawa baby pants ɗin ta, da sauran kananan kayan ta ne a cikin drawer kayana"
"Me ya mai da kayan baby kuma bedroom naki?" Ya yi maganar yana nufa hanyar toilet. Nufa hanyar fita ta yi ita ma tana faɗin "A'a ba na sawan ta bane, sabbin dana saya mata jiya ne, wayan da take amfani da su already suna ɗakinta" ta kai karshen maganar tare da ficewa daga ɗakin, shi kuma ya shiga cikin toilet ransa fes ya yi Ummi wayo.
(Nima raina fes na kwashe kayana zuwa wajen su Rimsha)
💖RIMSHA💖
Sai misalin karfe uku na yamma suka farka daga barcin nishaɗi da ya kwashe su, Rimsha ce ta fara farkawa, sannan ta tashi Ayla. A gurguje suka yi alwala suka fito, kowace ta ɗauki hijabi guda daga cikin hijaban da Ahmad ya kawo musu, can saman kyakkyawar trolley ɗin sa suka hango daddumar.
Rimsha ce ta ɗauko musu, suka shimfiɗa suka gabatar da sallar azahar, sannan suka zauna saman daddumar. Sai bayan sun zauna ne, Rimsha take cewa, "Ayla na manta mai haila fa bata Sallah, kuma bata azumi sai bayan ta gaba" zaro ido Ayla ta yi, cike da mamaki ta ce "Dama Akwai lokacin da musulmi ba zai yi sallah bane?" E Rimsha ta bata amsa sannan ta shiga yi mata bayani yadda mai haila ya kamata ta kasan ce, sosai Ayla ta gamsu, ta kuma cire hijabin, ta mai da cikin leda tare da komawa saman bedside drawer ta zauna.
Ita kuwa Rimsha tana zaune a wajen tana askar har a ka kira sallar la'asar, mikewa ta yi ta gabatar da sallah sannan ta koma ta zauna tana karatun Alkur'ani mai girma a fili, kasan cewar tana da hadda a kai sai bata nemi Alkur'ani mai girma ba ta fara karatu da kai kawai.
Sai misalin karfe 4:30 Ahmad ya dawo, bawan Allah hannunsa ɗauke da niki nikin leda mai ɗauke da kayan fruits a ciki. Sannu da dawowa suka yi masa, sannan suka ɗaga masa gaisuwa, da fara'a ya amsa Ayla ta miƙe ta shiga bayi. Su Ayla manya ba'a saba ba, duk lokacin da jinin ya ɓata always ɗin ko kaɗan ne sai ta canza, sai jibga always ɗin take yi cikin shadda tana korawa da ruwa, mani ma kaɗan ya ɓaci amma haka zata cire, daga tashin su barci zuwa yanzu always huɗu ya canza.
(Tab babbar magana)
Yanzu ma canza always ta yi ta dawo ɗakin, zaune ta isko Ahmad da Rimsha, ita Rimsha ta tashi daga kan dadduma ta koma saman drawer, shi kuma yana zaune bakin gado.
Kusa da Rimsha Ayla tazo zata zauna, cikin sauri ya ce "A'a sister zo ki zauna a nan kin ji? Drawer ya yi muku kaɗan ai, ku dai na takure kanku, ku saki jiki, ni yayan kune" ya kai karshen maganar yana nuna mata gefen gadon a kan tazo ta zauna.
Girgiza kai ta yi tana faɗin "A'a yaya wajen bai yi kaɗan ba, ai bamu da ƙiba, zai ishe mu" cikin sauri ya kara waro idon sa yana kallon ta, a fili ya furta "Allah mai halitta, ya sunan ki?" "Sunana Ayla" ta bashi amsa tana kokarin zama.
Miƙewa tsaye ya yi dan ya lura in dai har zai zauna a bakin gadon tofa su ba zasu taɓa yarda su zauna ba, yara kanana da kamun kai sosai haka, ya faɗa a ransa yana nufar wajen da Rimsha ta mayar da daddumar sa ta ajiye.
Ɗaukowa ya yi ya shinfiɗa ɗan nesa da su ya zauna yana faɗin "To ku koma bakin gadon ku zauna dan ku daina takura kan ku". Saboda ganin girmansa basa son yi masa musu yasa Ayla ta zauna a bakin gadon, ita kam Rismha ta makale drawer nan gam taki sakinsa.
"Ayla kin san me?" Ahmad ya tambaya yana ciro wayarsa daga aljihun wandon sa.
Girgiza masa kai ta yi tana faɗin "a'a ban sani ba" "Wlh Ayla muryar ki sak na daddyn mu, bayan haka kina kama da shi sosai, abin ya bani mamaki" yar murmushi ta yi tama rasa me zata ce masa, dan ita ba wani iya magana da namiji ta yi ba, tun da ma ta taso bata taɓa zama da wani namiji kamar yadda suka zauna yanzu suna hira ba, sai baba na Daular Mutuwa da kuma duna, suma ba keɓewa haka suke yi ba, kuma hirar su bata wuce na cikin Daular Mutuwar ɗin.
Ganin ta yi shiru ne yasa ya ce "Ina son ku bani labarin me ya kawo ku garin nan, dan in san ta ina zan taimaka muku".
Ayla ce ta fara bashi labarinta tun ranar da aka sace ta zuwa yau, sosai idon Ahmad ya cika da kwalla, duk dakiya irin na ɗa namiji sai da zuciyar Ahmad ta zubar wa da