Showing 219001 words to 222000 words out of 355604 words

Chapter 74 - Triplets Book 2 Hausa Novel Complete

10 Dec 2024

2830

iriyar hula kamar na sanyi ya sanya a kansa ya ɓoye gashin kansa, da kuma Black face mask, hannunsa na ruƙe da pistol gun, a zafafe yake taku cikin zafin nama ya fice daga ɗakin.

Kai tsaye wannan motar tasa ya je ya shiga, da kansa ya ja motar da wani irin mahaukacin gudu, ya fice tare da kunna map a wayarsa, duk wannan abin da ake yi Imran yana barci a ɗakinsa.

Sosai Lion yake sharara gudu akan titi. Tafiyar 30mins ya yi ya isa wajen, saboda gudun da yake sherarawa, yana isa wajen ya tarar da bakin gani, domin kuwa kamar yadda suka faɗa sun yi wa James yankar yaro a gaban kowa, ga shi kwance cikin jini malalan.

Abin da ya faru shine da suka yi ƙoƙarin yanka James ɗin sai Tga ya buɗe masu wuta, wani daga cikin yan bindigar ya shigo ɗakin ta baya ya harbi Tga ɗin da kuma Tyrone ɗin, duk ya harbe su, kuma a kafa ya harbe su dan baya son kashe su, yana son suga mutuwar ɗan uwansu a gaban idonsu, bayan ya harbe su ne kuma suka zube kasa, su kuma yan ta'addan suka kwantar da James ɗin suna ƙoƙarin yanka shi, Tga ya daure ya miƙe a zafafe tare da ɗaukar bindigarsa dake a kusa da shi ya fara yi masu ɓarin wuta, hakan yasa suka sake harbin shi a ɗayar kafar tasa shine, ya faɗi kasa, suka kuma kwantar da James Tga yana ji yana gani suka yi mashi yankar rago. INNALILLAHI WA INNA ILAIHIR RAJIUN, WAYYO TRIPLETS WAYYO JAMES 😭

Lion na shigowa wajen yan ta'addan suka miƙe tare da taitashi da gun ɗin hannunsu, ba tare da ɓata lokaci ba a fusace rai a matukar ɓace ya harbi ogansu dake a zaune saman kujerar, da wannan kattin muryar ta su suka kurma ihu tare da........✍️



BAZAN IYA CIGABA BA, NAYI BAKIN CIKI DA YAU YA KASANCE BA JUMMA'A BA, INA SON HUTAWA SABODA NAYI KUKAN MUTUWAR JAMES KAMAR TAREEF NE AKA CE MANI YA MUTUM!! NA JI RAƊAƊI HAR CIKIN ZUCIYA TA BA KAƊAN BA, YAYA MICHAEL ZAI JI IDAN YA JI CEWA JAMES YA MUTU, YAYA DADDY ZAI YI, KUNA TUNANIN ZA SU IYA RAYUWA KUWA? WANI HUKUNCI LION ZAI YI WAYAN NAN AZZALUMAN? INNALILLAHI WA INNA ILAIHIR RAJIUN SAI DAI MUN HADU GOBEN KAWA!!!😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭

💖💖TRIPLETS💖💖



*Idan kun samu typing error amin afuwa 👏 keyboard ɗin tana bani matsala sosai kwana biyun nan, to na yau ma ya fi tsananta, sai na danna A sai ya koma B😭*


*💔😭DEDICATE TO AUNTY RIFAT 🥰DAMA NACE ZAN MAKI KYAUTAR PAGE ƊIN MASOYIN KI, KIN FI KOWA SON JAMES DOLE NA BAKI WANNAN PAGE ƊIN!!*



59-60



Lion na shigowa wajen yan ta'addan suka miƙe tare da sai ta shi da gun ɗin hannunsu, ba tare da ɓata lokaci ba a fusace rai a matukar ɓace ya harbi ogansu dake a zaune saman kujerar, da wannan kattin muryoyin nasu suka kurma ihu tare da buga kafafu a kasa, Lion bai bari sun yi wani yunkuri ba ya yi masu rubdugu, ya nuna masu kwarewa a wajen aiki, ya nuna masu ba a banza ya zama The General of The Army ba, wani irin kisan walakanci ya yi masu, dukkansu ba wanda ya harba a wajen mutunci, daga wanda ya harba a baki bullet ɗin ta fito ta keya, sai wanda ya harba a gabansa, dukkan su takwas dake a cikin wajen ya kashe su, dama su goma ne Tga ya kashe biyu daga ciki, suma sun yi yunkurin harbin Lion ɗin lokacin da yake harbinsu, da yake dai ya kware a bakin aiki sai ya rinƙa kauce masu, kun dai san kafin Mutun ya taka matsayin THE GENERAL OF THE ARMY ba karamin abu bane.

Bayan ya kashe su dukka ne ya wuce ya nufi ogan nasu dake a sama kujera wadda ya harba farkon shigowarsa, mai da pistol gun nasa ya yi a cikin aljihun wandonsa ta baya, sannan ya saɓi mutumin a kafaɗar sa suka fita waje.

Kai tsaye cikin bayan motarsa ya je ya sanya shi, bayan ya kwantar da shi ne sai ya zaro gun ɗin daga aljihunsa tare da saita daidai saitin kirjinsa ta sama, in da dai ya ce Tyrone ya harbi James, nan ya saita ya harbi mutumin, sai bayan ya harbe shine ya furta "Kayi kuskure sosai James!" Ya kai karshen maganar tare da juyawa ya koma wajen su Tga.

Har zai shiga ɗakin kuma sai ya dakata tare da kiran sojoji uku daga cikin wayan dake ɓarin wuta a wajen akan su zo, da gudu suka karaso kabansa suna risinar da kai kasa, wucewa cikin ɗakin ya yi ba tare da ya yi masu magana ba, cikin takunsu na sojijin yaki suka bi bayansa.

Tga da Tyrone ya nuna masu akan su ɗauke su zauwa cikin motar, su saka Tyrone a baya Tga a gaba, domin Tga ya fi shan wahala, kuma dama shi bashi da koshin lafiya, karfin hali kawai ya yi, amma yana fama da zazzaɓi saboda hakwaransa biyu da suka fita, danma a lokacin ya je ya yi allura ne yasa bakinsa bai kumbura ba, bayan allura kuma ya sha magani, to wannan fitar hakwaran ne tasa mashi zazzaɓi mai zafi, kuma duk da haka ya daure ya zo cetar James. JINI BA WASA BA.

Har lokacin akwai sauran yan ta'addan a gidan, saboda gidan akwai lunguna sosai a cikinsa.

Wayan nan sojojin suna kokarin ɗaukar Tga da yake har lokacin bai suma ba, kuma bai fita hanyyacinsa ba, saboda bullet ɗin bata zauna a jikinsa ba, fita ta yi shiyasa abin ya ɗan ragu mashi, ganin za su ɗauke shi ne yasa ya ce "Lion James, please help him, please check maybe he is alive!" Ba tare da ya kalli in da suke ba ya ce

"Uncle this is not James, so ka kwantar da hankalin ka wanda na harba a hannu farkon shigowa shine James, kwana biyu da suka wuce, ba na gaya maka wayan da suka kama shi sun san waye suka kama ba? To sun gane waye suka kama ne ta hanyar wani ɗan ta'addan da ya zo yana dukan shi a fuskarsa, sai wanna fake face ɗin nasa ta goce, shine suna cire face ɗin suka ga ainahin face nasa, to wannan da suka yanka babban yaron James ɗin ne, shine suka sanya mashi fake face ɗin James ɗin dan su tayar mana da hankali, amma su sun san ba za su iya kashe James kai tsaye ba, saboda muna kewaye da su, lokacin da nake bincike ne na samu daman gane cewa sun gane James, amma batun sanyawa baban yaron sa fake face na san, wannan kuma sai da na zo nan na sani".

Abin da ya faru lokacin da Lion ya ga video ta hanyar camerar da ya sanya wa Tyrone a gaban botirin rigarsa, da yake yana ƙage da aikin alokacin, bai tantance cewa e ba James bane, sai da ya shiga mota yana zuwa ƙwaƙwalwarsa ta fara tariyo masa yanayin jikin wannan da kuma na James ɗin, a nan ne sai ya gane ba ɗaya bane, abin ka kuma da baban soja cikin kankanin lokaci ƙwaƙwalwarsa ta tariyo mashi mutanen dake a wajen, a nan ne ya fahimci wanda yake zaune a ɗayar kujerar da ogansu ke zama tabbas shine James, daga yana yin jikinsa ya gane, alluran barci suka mashi sanna suka rufe mashi fuska da mask, da Lion ya shigo wajen kuma, kallo ɗaya ya yi mashi ya gane tabbas shi ɗin ne, shiyasa ma ya harbe shi a hannu dan kada su harbe shi su, wannan shine abin da ya faru!!

Ba karamin daɗi Tga ya ji ba, har wani nauyayyar ajiyar zuciya ya sauƙe, haka sojijin suka ɗauke su zuwa cikin motar.

Kamar yadda Lion ya tuƙo motar ya zo haka ya tuƙata ya bar wajen tare da su Tga da James dake kwance rai a hannun Allah, ya sha harbin bindiga sau biyu, hannu da kuma kirji, haka suka tafi suka bar sojojinsu suna karisa sauran aikin.

Kai tsaye gida ya nufa da su, yana parking motar a parking space na gidan ya fito a zafafe tare da buɗe gidan baya na motar ya saɓi James a kafaɗarsa zuwa cikin gida, har lokacin akwai wannan mask ɗin a fuskar James ɗin. Jini sai tsiyaya yake yi, duk in da suka wuce sai jini ya zuba haka ya wuce da shi ɗaya daga cikin ɗakunan kasa.

Saman bed mai shinfiɗe da farin bed sheet tas ya kwantar da shi tare da sanya hannunsa ya tsage rigar James ɗin daga farko har ya direta.

Kamar yasan hakan zata faru ya taho da wasu kayan aikinsa, da yake dama su basu wani cika rabuwa da A box da sauran kananan tafi da gidan ka na kula da lafiya ba.

Cikin zafin nama yake takowa ya fito daga ɗakin izuwa nasa ɗakin. A box da sauran kayan aiki ya ɗauko ya nufo waje, daidai Palon saman suka yi karo da Imran lokacin kuma karfe 11 rana ta yi.

Daga ganin yadda Lion yake Imran ya san ba lafiya ba, dan haka sai ya yi saurin bin bayansa. Lokacin da Lion ya dawo ɗakin da James ke kwance, ya tarar da Tga da kuma Tyrone, sojan dake a bakin gate ne ya taimaka masu zuwa cikin gida, shi Tga ma kwata-kwata baya iya tafiya, gara Tyrone da yake kafa ɗaya aka harba yana iya jan kafar tasa.

Kokarin cire bullet ɗin jikin James Lion ya fara yi, su kuma suna kwance a gefen James ɗin, shi kuma Imran da ya shigo da ya ga meke faruwa ai sai ya fara ruwan hawaye, da sauri ya kariso wajen gadon, da farko bai gane cewa James bane, sai da ya matso kusa sosai, saboda duk sun saɓa mashi kamanni, fuskar tasa ta suntuma sosai, idan ba ka yi mashi farin sani ba, ba zaka taɓa gane cewa shi ɗin bane, yan ta'addan nan sun zalunce shi sosai.

Sosai Lion yake aiki babu kama hannun yaro dan cewa rayuwar ɗan uwansa, yana yi yana haɗa zufa, da sauri Imran ya kara gudun Ac dake a ɗakin, amma duk a banza, domin kuwa bai dai na zufar ba, kamar ma kara mashi ake yi, ganin haka yasa Imran ya wuce bedroom nasa ya ɗauro alwala ba ɓata lokaci ya fara gabatar da sallar nafila yana rokar Allah da ya bawa James lafiya, ya tashi kafaɗunsa.

Sai wuraren karfe 1 Lion ya samu ya iya kammalawa da James, ya yi nasarar cire bullet ɗin, sannan ya mashi dressing na wajen, sai barci James yake yi domin alluran da suka mashi tana da karfi sosai da sosai wata kila zai iya kai wa dare kafin ya farka.

LION

Bayan ya kammala ne ya nufi su Tga da nufi ya yi Tga dressing ɗin wajen tun da shi babu bullet ɗin a jikinsa, shi kuma Tyrone ya cire mashi bullet ɗin, amma duk azaban da Tga ya ke a ciki, bai hana shi ya ce lallai shi baya son a duba shi ayi treatment ɗin shi a Nigeria ba, saboda wai Nigeria me suke da shi da har za'a duba mashi lafiyarsa a nan, shi baya son kasar ma gaba ɗaya, shi tunda ba wani ciwo sosai ya ji ba zai iya tafiya a jirgi kawai a mai da shi Usa daddy ya je ya duba shi, Lion bai wani damu ba, dan dama baya son matsi sosai, dama ganin gidan yake yi ta yi mashi karama, da kaɗan tafi palon kasarsu na Usa, shi ji yake yi ma da kyar yake numfashin a gidan, duk girmanta amma wai ta yi karami, so da suka zo ɗan jiya kawai ji ya yi kamar sun toshe mashi iskan da yake shaƙa, dama ga zafi, hakan yasa ya ce to su wuce amai sa su, ba musu kuma suka ce to, cikin kankanin lokaci aka yi masu komai, amma kafin su tafi an cire wa Tyrone Bullet ɗin kafarsa, sannan Lion ya ɗan gyara masu wajen suka tafi, shi Lion ba zai yi wu su tafi da wuri haka ba saboda James jikinsa ya yi tsakani sosai, sai ya ɗan sami lafiya.

Yau sai misalin karfe 3 Lion ya samu ya yi sallar azahar, saboda busy da ya yi yawa. Bayan ya yi wanka ya yi sallah ne ya zauna saman bed nasa yana tunanin yadda zai yi da James.

A wanna hali Imran ya shigo ya same shi, sannu ya yi mashi tare da tambayar ya jikin James, jinjina mashi kai kawai ya yi ba tare da ya yi magana ba.

Gefensa Imran ɗin ya zauna yana faɗin "Lion dan Allah ba dan ni ba, kada ka yi wa James hukunci mai tsanani, ni nasan ba haka kawai ya shiga wannan ta'addancin ba, akwai dai dalili, kai ma fa kasan James yana da zuciya mai kyau, ka tausaya mana".

Shiru ya yi na tsawon mintoci kamar 10 haka kafin ya fara magana gently. "Prof James ba ɗan ta'adda bane, kamar yadda ka ɗauka, amma dole zan hukunta shi, dole ya karɓi hukunci mai tsanani domin ya yi mani laifi, ya sayar mana da rayuwarsa".

Zaro ido Imran ya yi yana faɗin "Ban gane ba, dan Allah ka yi mani baya ni dallah dallah".

Na san kowa a ƙage ya ke dan jin cikakken bayani akan James da wannan sarkakiya, to ni *PRINCESS TEEMA* bari na warware maku cikin kwanciyar hankali, maza ku biyo ni.

JAMES dai ba ɗan ta'adda bane kamar yadda kuka ji Lion ya faɗa, abin da ya faru shi ne ku saurara ku ji, ya shiga ƙungiyar ta'addancin kala-kala, haka zalika ya kashe mutane kala-kala, sai dai duk mutanen banza yake kashe wa ba na kirki ba, alokacin da Lion yake bincike akan wani mutumi da James ɗin ya kashe ne wadda Lion yake yiwa kallo mutumin kirki, to alokacin ya fara fahimtar cewa duk mutanen da James yake kashe wa na banza ne ba na kirki ba, hakan yasa ya dakata da bincin ina James ɗin ma yake tukunnan, sai ya fara binciken waye James ɗin mai gaba ɗaya? Waye yake saka shi wannan aiki, a nan ne ya gane cewa James shi ne (DOA) DETECTORATE OPERATIONS ARIF na CIA gaba ɗaya, CIA kuma wata katafaren hukumar Row ce ta kasa da kasa, James ya shiga ne tun yana makaranta, da farko ya shiga ne dan kuɗi, daga baya ya koma kishin kasa, sannan ya zo ya shiga cikin manya-manyan yan ta'adda na duniya, domin ya rinƙa kashe su, to lokacin da ya fara sanin daɗin rayuwa ya fara jin tsananin kaunar yan uwansa, yana jin ba zai iya rabuwa da su ba, alokacin ne ya fara ƙoƙarin neman ta ina zai fita CIA, babbar matsalar shine idan aka shiga ba'a fita, domin kafin ka shiga sai ka sa hannu akan ka sayar masu da rayuwarka, idan ka amince da hakan to za su yi maka tiyata su dasa maka wani abin mai kama chemical kakar kuma bom haka yake, da na ura yake aiki, idan kayi wargi kaɗan mai sarrafa nauran zai iya fasa ka, abin da kuma yasa suke yin hakan domin idan yan ta'addan sun kama nasu idan ya ji wuya ya yi ƙokarin tonawa hukumar tasu asiri hakan zai sa su danna wanann abin su tarwatsa mutun ya mutu har lahira, dan kada ya fitar da sirrin hukumar har a iya far musu a gane ina suke, shine amfanin wannan makami mai kama da bom ɗin, ana danna na'uran zata fashe kamar bom ta kashe mutun, ko wani ɗan cikin CIA yana da ita a kirjinsa, shiyasa Lion ya ce kada su Tga su bari a sanyawa James Camera, domin ana sanya mashi CIA da su gani, su kashe shi dan kada ya tonawa hukumar asiri, kamar aljanu haka suke, sai ka zauna a tare da su baka san su bane, idan suka ga James acikin wannan hali to suna iya danna wannan naura abin da suka sanya mashi a kirjinsa ya tarwatsa shi kamar bom ya mutu, haka yasa Lion ya ce Tyrone ya harbi wajen da wanan abin yake, suna harbi wajen abin zai ɗauke daga jikin na'uran CIA kamar network, yana ɗauke wa kuma James ya tsallake layi ɗaya, shine Tyrone ya kasa yin harbin, yanzu babban tashin hankali shine tayaya za'ayi James ya fita daga cikin CIA (ROW)?, domin TRIPLETS ba za su yarda da sayarda ransa da ya yi ba, hakan ma yasa yake ɓoyewa Lion kada ya sani, shiyasa yake yi masu basaja dan kada su gane, ya ci bakar wuya kafin ya zama DOA ya sayar da ransa ya rinƙa shiga cikin kungiyoyin yan ta'addan, kuma abin da yasa da sun bashi contract na kashe wani zai yi sauri ya aiwatar da aiki, dan dama dukka yan ta'addan ne kashe su yake son yi, ya yi aiki tukuru dan tsabtace kasarsa kamar wani baban soja, ya wahala iya wahala, yanzu baraza ɗaya ta rage shine fita daga CIA, babbar matsalar ma Allah ne kaɗai ya san ina da ina suke sakawa mutun wasu abubuwa a jikinsa na tarwatsa sa, lokacin da Lion ya gane hakan ya ji haushi sosai kuma ya kiduri niyar hukunta James ɗin hukunci mai tsanani ta yadda gobe ko hauka yake yi ba zai sayar da rayuwarsa ba, idan aikin cetan kasa yake son yi ya shiga hukumar soja mana, ko siyasa. Batu akan wayan nan sojoji guda biyu da ya kama ya yi masu hukinci a ranar da Lion ya turo a tarwatsa kungiyar su kuma, suma duk gurɓatattune dan ya san su a wata dabar da ya taɓa shiga ya kashe mataimakin mai wannan dabar, shiyasa duk kunguyar dabar da ya shiga suke bala'in ji da shi, dan ya samu kwararren training kamar soja, har mamaki suke yi yadda idan ya kalli abu sau ɗaya zai iya rufe ido ya sa bindiga ya saita abin ya harba, a takaice dai JAMES ya fi Tga ma a samun cikakken horo, shiyasa yake iya dukan Tga ɗin, James jarumin gwarzon namijine sosai, har ya kusa kamo Lion a manya-manyan


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login