Showing 270001 words to 273000 words out of 355604 words
aikin sosai, kuma ya mai da hankali sosai wajen koyan abubuwa da dama daga wajen daddy, hakan yasa ya iya abubuwa da dama dan gane da kula da lafiyar jikinsu.
Komawa ɗakinsa ya yi ya ɗauko laptop nasa ya dawo, connecting na wannan na'uran ya yi da laptop nasa, nan take ya fara bincike akan lafiyar Areef ɗin da kuma abubuwa dake a jikinsa, a zafafe yake aikin, da kallo ɗaya zaka yi mashi kasan a ƙage yake da ya kammala aikin.
Good 1 hour ya ɗauka yana wannan binciken nasa kafin nan ya tattare komai ya kashe laptop ɗin nasa.
Wayarsa ya ɗauko ya kira Dr Tyrion bugu ɗaya Dr ya ɗauka, ba tare da ɓata lokacin ba ya sanar da Dr yana son da shi da wasu likitoci uku su dira a cikin Nigerian daga nan zuwa gobe da yamma, dan aikin da za'ayi wa Areef ba shi da time da zai iya yin wannan aiki, akwai abubuwa sosai a gabansa, kuma zai fi son ma dama manyan likitoci su yi mashi wannan aikin don shi ya fi bawa aikin sojan shi mahimmanci.
Bayan ya gama waya ne ya dubi Areef dake bin shi da kallo a nutse ya ce "Yanzu dai ka bar CIA har abada, kuma kasani sai na baka hukunci mai tsanani na laifin sayar da rayuwar ka da kayi, kana tunanin rayuwar taka ce kai kaɗai? Baka san cewa muma muna da hakki a kan ka bane? Iyayenka fa? Duk baka yi tunani akan wannan ba, good ka kyauta daka bani bakar wahala, ban taɓa aiki mai wahala ba irin aikinka, good 2 weeks na ɗauka ko barci bana samu bare kuma cin abinci all because of you, babban abin haushin ma sai ina bincinken ina kake sai na sake cin karo da wata ɓarna da kayi, dole na dakata nayi settle komai, kayi abubuwan dana kashe wutar bansan adadi ba, Allah dole na hukuntaka saboda gobe, ko da sunan wasa kada ka sake yi mana irin wannan gangamin, baka tunanin wani hali Aseef zai shiga? Bawan Allah da bai san komai ba sai kaunar mu, baya magana ɗaya biyu ba tare da ya kira mu a ciki ba, duk baka tuna haka ba kenan!".
Ya kai karshen maganar tare da miƙewa ya fice daga cikin ɗakin. Shiru Areef ya yi yana tunani, shi da kansa ya san ya yi babban kuskure, yasan cewa idan wani abin ya same shi to ba makawa daddy mutuwa zai yi, bayan daddy kuma Aseef, Aseef shine mutun na biyu da zuciyarsa zata iya bugawa idan ya ji wani abin ya same ni, gara Lion yana iya jurewa, amma shima sai ya ji ajikinsa ba kaɗan ba, babu wani ɗan adam da ya isa ya ce tun da rayuwarsa ne zai yi abin da ya ga dama da ita, hakan ba zai yi wu ba, saboda akwai haƙoƙin mutane da dama a tattare da wannan rai ɗin naka, na farko Ubangijin mu, Allah ya bamu wannan rayuwa ne domin mu bauta mashi ba dan mu sai data ga wani ko wata ba, bayan nan akwai iyayenka, suna da hakki akan wannan rai ɗin naka, sannan ƴan uwanka, to kada ya zama kana tunanin cewa ai ranka ne kana da damar yin abin da kake so da shi, a'a ba haka bane!!.
Yau sosai Areef ya yi nadama ba kaɗan ba, har hawaye sai da ya zubar, kuma a shirya yake da ya karɓi duk wani hukuncin da Lion zai yi mashi, domin yasan ya aika babbar kuskure mai girma, da ya mutu ta wannan hanya da bashi da amsoshin da zai bawa Aseef da daddy a ranar gobe kirayama dan dai yasan mawuyacin abune su biyun nan su rayu bayan mutuwarsa, sannan ba shi da amsar da zai bawa Ubangijin sa.
A ɓangaren su Jehan kuwa, barcine ya yi awon gaba da su dukkansu tun lokacin bayan da suka gama rikici da wannan Alhajin.
Barcin awa biyu suka yi Jehan ta farka, nan ta sami Aisha idabunta biyu itama ta farka tana zaune ta buga uban tagumi.
"Aisha me yake faru na ganki kin yi shiru haka?" Ta tambaya tana kare mata kallo.
Nisawa Aisha ta yi kafin ta matso ta ruƙe hannayen Jehan ɗin cike da damuwa tab a ranta ta ce "Jehan zan gaya maki ainahin abubuwan da suke faruwa a cikin gidan nan wadda ba kowa ya san da hakan ba, da farko abin da yasa ban gaya maki ba dan ina tunanin kema kamar mu ce, kema hakura zaki yi ki bada jikinki domin bamu da wata mafuta, wannan gidan da kike gani ba gidan arziki bane, wlh Allah wannan gidan bala'i ne Jehan, na san idan suka san cewa nasan wannan sirrin za su iya kashe ni ko dai su jefar da ni, kai da wuya ma su jefar da ni nasan kashe ni za su yi, Jehan sanadiyar cetar Maryam da kika yi tasa na samu karfin gwiwa na cewa sanadiyyar ki zamu iya barin gidan nan har mu kai kara ga hukuna cewa ga abin da ake yi a cikin gidan nan..."
Dakatar da ita jehan ta yi da cewa "Kin san hanyar fita daga gidan nan ne?" Girgiza kai ta yi tana faɗin "Kamar yadda aka kawo ki da tsakar dare, haka ake kawo kowa da tsakar dare, sannan babu wani alhajin da ya isa ya fita da ke da rana sai da daddare, bugu da kari magana ta gaskiya babu wanda idan ya shigo gidan nan yake sha'awar fitarta, shiyasa hajiya bata damuwa take bari a fita da ƴan matan, dan tasa ta asirce su ba zancen fita, amma na sha mamaki tun da na ga kin ceci Maryam nasan dole akwai nasara a tattare da ke, wlh asiri suke yi wa mutun ya zauna a cikin gidan nan, ina da tabbacin hakan ne, ka zauna kayi ta bada jikinka, lokacin dana fara yin hakan, da aka kawoni ina sabuwa, duk time dana kwanta da wani, zan kwanta ne cike da annashuwa da farinciki, idan mun gama abin da zamu yi kuma nadama tare da dana sani ne zai biyo bayan abin a tattare da ni".
Shiru Jehan ta zuba mata idanu tana jiran ta ji me yake faruwa. "Jehan kamar yadda kika sani ne ana fita da yarinya, Alhazawan nan suna zuwa da ita su kwana da ita a hotel da sauransu, amma fa ki sani ba kowani Alhaji bane yake zuwa ya kwanta da yarinya dan biyar bukatar kansa, a'a akwai masu zuwa su kwanta da yariya dan bokansu matsafansu sun basu wani abin su zaubawa mace a cikin cikinta dan samun kuɗi ko nasara ko dai wani biyan buƙatunsu, kuma duk wannan hajiya ta sani, domin kafin ya fita da yarinya sai ya bawa hajiya makudan kuɗaɗe ya gaya mata ga irin aikin da zai yi da yarinyar, da yake ba ƴaƴan ta bane, sai ki ga ta yarda ta karɓi kuɗin ta bada yariyar, ki sani fa wannan abin da suke zubawa mace a cikin cikinta wlh idan ya yi wuta in suka dawo da yarinya ta kara kwana biyu sai gawa, akwai kawata da muke wannan ɗakin kafin ku zo sunanta Zuwaira, yarinyar nan so silent, bata da hayaniya, to ranar da wani aljaji ya tafi da ita da daddare, bai dawo da ita ba sai washegari da daddare, lokacin da ta dawo nan wlh sai kin matsa mata kwallah, a nan ne take bani labarin abin da yake faruwa, domin ta ji duk yadda Hajiya ta yi da wannan alhajin, ta ji yadda suka yi da hajiyar daɗi, kuma ita ma ta gani da idanunta, lokacin da ya gama amfani da ita, ta ga wani bakin abu a cikin gabanta kamar garin lepton, abin ya so ya yi kama da kasa haka, tun daga lokacin ta fara jin ciwon ciki, shi kuma alhajin ya ɗauki kuɗi makudai ya bata sannan ya ce ta je ta yi wanka, haka ta je ta yi wanka ta wanke gabanta ta zo ta kwanta, da yamma ya sake dawowa ya yi amfani da ita ya sake zuba mata wannan abin, ga shi na safe da ya zuba mata ma sai ciwo cikinta yake yi mata, haka ba imani ya sake mafani da ita ya zuba mata, wlh yarinyar nan in takaice maki bata yi kwana biyu da dawowa ba ta rasu, hajiyar daɗi ta sa aka fita da gawarta ban san ina suka kai ba, cos a yanzu ba kowa yake yin zinar ba ma tsakani da Allah, wasu musamman ma manyan mutanen nan, wlh wani abin suke sanyawa mutun a jiki dan samun wani abu da suke nema, wani kuma su lalata mashi hanji ya ruɓe ya mutu, wani abin kuma idan suka saka maka ka haukace daga nan a rasa gane kanka, to yanzu dai ya kamata masu yin zinarma su kula dan yanzu ba zina kamar na da ake yi ba, kinga a ɗakin bayan mun nan, yarinya ƴar shekara goma sha huɗu wani alhaji ya ɗauke ta, yarinyar nan ya tafi da ita, wlh jehan virgin ce yarinyar nan, bata san komai ba, ga ƙananun shekaru, dan rashin imani ya je ya yi amfani da ita ta gaba da kuma ta baya, kuma ya zuba mata wani abin ta bayanta, wlh karki so kiga yadda yarinyar nan ta kare a cikin gidan nan, Allah sai kin yi mata kuka, kuma ita kam ma marainiya ce, iyayenta sun rasu ta gudun wa wahalar matar uban tane, ranar da yarinyar nan ta rasu na yi mata kuka ba kaɗan ba, so akwai abubuwa sosai da suke faruwa a cikin gidan nan, ciki kuma har da sayar da ƙodar mutane, sannan akwai kwashewa ƴara kayan cikinsu, abubuwa dai wayan da ba za su kirguba JEHAN laifukan da ake yi acikin gidan nan ba za su faɗu ba, a kama yaro aje a sayar da ƙodarsa makudan kuɗaɗe, idan ya fara rashin lafiya ko yarinya ta tashi a aiki sai aje wani garin a jefar da ita, kuma mafi yawancin lokaci idan sun cirewa yaro ƙodarsa ne suke zuwa wani garin su jefar da shi, sai ki ji ana cewa an tsinci yaro ɗan gari kaza a gari kaza, amma an tsinceshi lafiyarsa kalau ana neman iyayensa, ba wata lafiyarsa kalau, ba ta yadda za'ayi su saci yaro kuma su kai shi wani gari su jefar da shi ace ba wani abin da suka yi mashi, dole akwai dai wani abin, kamata ya yi idan yaron ku ya ɓata kuka gane shi, first abin da zaku fara yi akai shi asibiti ku biya ko nawa ne a chaje maku shi fes, ku tabbatar babu wani abin da ya rasa daga wani sassa na jikinsa, sannan kuce lafiyarsa kalau, domin akwai wani abin da idan aka cire a jikin mutun ba lallai ne ya yi ciwo a bayyane ba, kuma ma ya kan iya ɗaukar tsawon lokaci bai yi ciwo ba."
WATA SHARI'AR SAI A LAHIRA, ALLAH ALHADULILLAH DA YA KASANCE AKWAI LAHIRA, RANAR DA ZA'A KWATAWA MARA KARFI HAKKINSA A WAJEN MAI KARFI, RANAR DA DUK WANI AZZALUMI ZAI ƊANƊANI KUƊARSA, ALLAH KA MANA SAKAYYA DAIDAI DA ABIN DA AKE YI MANA, WANI ABIN IDAN KANA JINSHI WLH SAI KA RANTSE DA ALLAH BA A DUNIYA KAKE BA, DUK WANDA YA GA YANA ZAUNE LAFIYA ACIKIN GIDANSA, YANA CI KO MA YAYA NE YANA SHA KO BA YAWA, TO YA GODEWA ALLAH KUMA YA ZAUNA A IN DA YAKE, WANNAN BALA'IN TA DUNIYARMU TA YAU SAI DAI ALLAH YA KAWO MANA SAUKI. TO IYAYE NA JUYO TA KANKU KALUBALE GARE KU WAƳAN DA ƳAƳAN SU SUKE ƁATA DA KUN GANE SU SHIKENAN AN WUCE WAJEN, AZO YARO KWANA ƊAYA KWANA BIYU YA ZAMA BABU SHI YA MUTU, TO DAN HAKA SAI KU KULA, A KULA DA YARA MASU ZUWA MAKARANTA, DAGA MATA HAR MAZA, YANZU SAYAR DA ƘODAR MUTANE HAR A ASIBITOCI ANA YI SOSAI, SAI A YI MAKI KARYAR ZA'AYI MAKI AIKI WATA MATSALA NA DAMUNKI, DAGA NAN SU SACE MAKI ƘODA, TO DAN HAKA SAI KU KULA, DA ZARAR AN YI MAKI AIKI A WANI ASIBITIN KIKA SAMI LAFIYA, TO KI GARZAYA MAZA IZUWA WATA ASIBITIN DAN A YI MAKI SCANNING NA KAYAN CIKIN KI, KI TABBATAR KOMAI YANA NAN KAFIN KI SAMU KWANCIYAR HANKALI, ALLAH YA MANA MAI KYUA!!!.
STORY💖
Yau dai Jehan ta ji abin da ya kwance mata lissafin ƙwaƙwalwar ta, tunani ta fara yi tabbas akwai wata kawarta Zuhra da ta taɓa gaya mata cewa an sacewa yayan mamanta ƙodarsa a asibiti yanzu haka sun kai kara kotu da suka gane kenan, ashe abin da gaske ne sosai har haka, wato Hajiyar daɗi har da dillancin ƙodar ƴaƴan mutane suke yi kenan? Wannan wace iriyar bala'i ce, wato su kuma Alhazawan nan sai su zubawa ƴar mutane kayan tsafi a cikin cikinta saboda son abin duniya, siyasa ko dai kuɗi ko wani buƙata, innalillahi wa inna ilaihir rajiun wato dai kowa kuɗi kowa kuɗi, ko ta halin ƙaƙa sai anyi kuɗi, wannan bala'i da yawa take, yanzu bayan laifin zinar ma har da na shirka suke haɗawa waje guda, ga laifin cutar da yayan mutane a zuba masu wani kayan tsafin a ciki, ya ilahi ya lillihi wannan duniya ina zaki je damu, TO MATA MASU ZINA SAI DAI MUCE A KULA, IDAN BA HAKA BA ZAKI MUTU BA TARE DA KIN SAN DALILI BA, KU TUBA KU DAINA DOMIN SAMUN RAHMA WAJEN UBANGIJIN KU, KUMA KU TSIRA DAGA SHARRIN IRE-IREN WAYAN NAN ABUBUWA, WANNAN MA KAƊAN KUKA JI, AKWAI ABUBUWA DA DAMA DA AKE YI TA HANYAR ZINA WADDA ZAI ZAMA SANADIYAR RAYUWARKI CIKIN ƘANƘANIN LOKACI, TO DAN HAKA AKULA A TUBA KO DAN A TSIRA DA RAI.
Ko motsin kirki Jehan ta kasa, tunaninta kawai ta ya ya za'ayi ta ruguza gidan Hajiyar daɗi, tabbas ko mutuwa za ta yi sai dai ta mutu amma ba zata bar wannan gida ba sai ta rusa shi, ya zama mata dole ta azabtar da rayuwar Hajiyar daɗi, ta jata akan titi, ta yi rayuwar walaƙanci, bai kamata wannan tsinanniyar mata ta yi mutuwar farad ɗaya ba, dole ta azabtu matuka, to ta wani hanya ya kamata mu fara? JEHAN ta tambayi kanta a cikin zuciyarta, yayin da ita kuma Aisha ta zuba mata idanu tana jiran ta ji me zata ce.
Sun jima a haka kafin su Adiva su farka daga barcin da suke yi, ganin su jugum-jugum yasa Adiva ta tambayi menene yake faruwa? Jehan bata ɓoye mata ba ta gaya mata dan ta samu haɗin kansu su san yadda zasu rushe wannan gida na azzalumai.
A haka Zinariya ta shigo ta same su, umarni ta bawa Adiva akan ta shirya da daddaren nan zata yi baƙo, rai a matuƙar ɓace Jehan ta ce "Babu in da Adiva zata je".
Kallon sama da ƙasa Zinariya ta yi mata kafin ta ce "To sai ki hana mu gani" ta kai karshen maganar tare da juyawa zata fice daga ɗakin.
Dakatar da ita Jehan ta yi da cewa "Ke tsohuwar kilaki, ina mai tabbatar maki da hakan, kuma zaki gani, ba ma Adiva ba, duk cikin mu huɗu dake a cikin ɗakin nan babu wanda zai sake zuwa wajen wani tsinanne kafurin banza, idan kuma kuka matsa sai kun alaƙanta mu da hakan, to wlh ina mai maki rantsuwa da sunan Allah sai na zama sanadiyar rayuwar duk wata marakunya da ta shigo gaya mana akwai baƙo, bayan haka kuma mu haɗa da baƙo duk sai munci ubanku, ƴan iska tsinannu, wlh ina da tabbacin babu abunda kuka isa ku yi mana, domin babu in da karya ta taɓa ɗauruwa akan gaskiya, tun daga farko Al Qur'ani mai girma har karshe ta, maganar Allah ne a cikinta, kuma babu a in da Allah ya yi alkawarin taimakawa azzalumai, sai dai ma ya ruguje daular zalunci, wlh idan baki tuba kin koma ga Allah ba sai kin yi mutuwar walaƙanci, mutuwar kare ma sai ta fi taki daraja, shegu kafuran banza tsinannu, duk abun da kuka ga dama ku zo ku yi Mani, kuma ina son ki buɗe kunnanki da kyau ki saurare ni dukana da kuka yi wlh baku yi shi abanza ba, ki jira kiga karshen iskanci, ku karyar iskanci kuke yi, da JEHAN kike magana, ƴar fari a wajen jaru kuma jajirtatcen jan wuyar namiji, ubana ɗayane tamkar da dubu, baya da tsoro gaskiya kawai ya sa a gaba ya kuma riƙeta, to akan haka ya renemu, ki rubuta ki ajiye wlh nice zan zama sanadiyar rugujewar wannan gidan".
Duk wannan magana da take yi cikin harshen turanci ta yi shi, hakan yasa Zinariya bata wani fahimci kan zancen ba, dan bata yi wani karatu ba, amma dai ta gane zaginta Jehan take yi, dan haka sai ta dawo cikin ɗakin rai a makutar ɓace ta ɗaga hannu zata mare ta.
Yau iya ɓacin rai ran Jehan ya ɓaci, jikinta har ɓari yake yi saboda baƙinci, zuciyarta sai tafasa yake mata, idanunta sun rufe bata ji bata gani, yau zuciyarta ta bushe babu alamar tsoro ko kaɗan a cikinta, dan duk zuciya mai imani idan ta ji abin da ake aikatawa a gidan Hajiyar daɗi sai ta girgiza, a fusace ta ruƙe hannun Zinariya tare da zabga mata wani mahaukacin mari mai doɗe kunne na wucin gadi, wani irin dum Zinariya ta ji, kunnuwanta sun daina jiyo mata sautin komai saboda marin da ta sha wajen D.P.O.
Wani irin daɗi su Adiva suka ji, dama ita Adiva tasan halin jenan sarai akwaita da ɗaukar zafi kuma bata ɗaukar raini ko kaɗa, idan ka kawo mata wargi yanzun nan zata sa kayi nadama, akwaita da jan ajinta bata shiga abinda bai shafeta ba, ko wanda ya shafetan ma idan ba mai girma sosai ba bata kula shi, mace ce ita mai class sosai.
Good 3mins Zinariya ta ɗauka tsaye a wajen dafe da kuncinta tana hawaye, kwata-kwata bata iya jin sautin komai kunnenta ya doɗe, Jehan kuwa tana tsaye tana huci kamar wata zakanya, yau sun kureta, bata san laifin da suke aikatawa ya kai har haka ba.
Bayan minti biyar ne Zinariya ta dawo