Showing 162001 words to 165000 words out of 355604 words

Chapter 55 - Triplets Book 2 Hausa Novel Complete

10 Dec 2024

2806

fyaɗe, daya tambaye su shine suka gaya mashi cewa kayan mayen Josephine za su kai wa, ita tayi oder su, sai ya yanke mu su gaba na fyaɗen da suka yi, ya kuma miƙa wa Tga su dan ya yi mu su hukuncin dillancin kayan maye da suke yi, wannan dalili yasa ya sanya mata camera a kofar gidan ta, domin shi baya yanke hukunci da kai kawai, baya yanke hukunci daga jin zance daga bakin wasu, no sai ya yi bincike yake hukunci.

Kunna laptop ɗin ya yi yana wani lumshe dara-daran idanuwansa alamar akwai wani abin da yake tunawa.

Baki ɗauke da excuse Tga ya shigo cikin ɗakin, hannunsa ruƙe da cup mai bala'in kyau sai ɗaukan ido yake yi fari kal da shi, ɗan cup ɗin yana ɗaure ne saman wani kyakkyawan plate karami mai bala'in kyau, hot coffee ne a cikin cup ɗin, sai turiri yake yi.

Kusa da Lion ya zo ya zauna tare da miƙa mashi coffee ɗin, shiru Lion ya yi bai karɓa ba kuma bai juyo ba. Idan da sabo sun saba da halinsa hakan yasa ya ce "Good morning sir" nan ma shiru aikin da yake a gaban sa kawai yake yi.

Almost 10 mins sannan ya ɗan juyo da kallonsa kan Tga ɗin, calmly ya fara magana "Ni na ce maka ina buƙatar coffee ne?" Cikin sauri Tga ya ce "No sir kawai dan naga kasha jiya ne that is why na yi tunanin Maybe zaka buƙata a yanzu ma".

A maimakon ya ba shi amsa sai ya ce "Tafiyar sirri zan yi, ko daddy ba zan gaya ma ba, but idan ya tambaye ka just tell him the truth akan cewa na yi tafiya, and then ka kula da lafiyarsa sosai, ni kaɗai zan je za mu yi waya". Ya kai karshen maganar tare da miƙewa ya shiga toilet, bin shi da kallo Tga ya yi yana mamakin hali irin na sa, tabbas ko a magana ba zaka taɓa gane in da ya dosa kai tsaye ba, yana magana ne a murɗe kamar yadda yake shima a murɗe, yanzu maganar da ya yi a nan wajen Tga ya kasa fahimter ina maganar ta dosa kai tsaye, zaman ka lafiya shine kawai idan ya ce ka yi abu, tofa kawai ka yi shi, idan ba haka ba, ka ce sai ka binciko ka gane asalin in da abin ya dosa, tofa zaka shekara babu abin da zaka fahimta, karɓar umarni ya fiye maka sauƙi in ba haka ba ƙwaƙwalwarka ta tarwatse.

Yana tsaka da tunani sai ya ji laptop ɗin Lion dake a gabansa ta yi yar kara, ɗaura cup ɗin ya yi saman bedside drawer ya jawo laptop ɗin ya fara dubawa, abin mamaki kuma abin al'ajabi da Tga bai taɓa sammani ba shine ya gani a cikin laptop ɗin.

Zaro idanuwansa sosai ya yi yana kallon abubuwan dake a ciki, ɗago kai ya yi ya kalli kofar toilet ɗin, afili ya ce "Jinjina mai girma, a ya za dole ka yi tafiya, kuma ya zama dole jiya ka shiga yana mai daɗi" ya kai karshen maganar tare da fita daga wajen ya shiga bincike akan ina aka tsaya dan gane da wayan da suka kama James.

A wannan hali Romeo ya fito ya same shi ɗaure da towel a kugunsa, ga kuma wani ƙaramin a hannunsa yana goge dark black curly hair sa da shi.

Gaban mirror ya zo ya tsaya ba tare da ɓata lokaci ba ya shafe jikinsa da Lotions nasa masu kyau da tsada, da ga nan ya gyara gashin kansa tare da shafeshi da mayuka gashinsa masu kyau da tsada, ya fesa perfume nasa mai bala'in kamshin nan, wadda tun kafin ya iso waje perfume ɗin yake riga shi isa saboda bala'in kamshinta, already kamshin ta kama jikinsa, ko bai saka ba kamshi yake yi sosai, amma kullun sai ya sa, ya riga da ya saba.

Bayan ya kammala ya wuce dressing room nasa. Komai nasa a nutse yake yi daki daki, ɗaya na bin ɗaya, a nutse ya shirya cikin Ripped Jeans blue color da high neck t-shirt black color, ya ɗaure gashin nan nasa a baya, ya bar wannan guntu na gaban goshin nasa, sai tashin fitinannen kamshi yake yi, ya yi wani masifaffen kyau, sai kyalli fuskarsa take yi, ga idon nasa wani irin idan ka gansu sai ka rantse da Allah kwalli yake saka masu saboda tsabar kyau.

Ko sannu bai ce da Tga ba da ya fito, wayarsa kawai ya ɗauka ya nufi waje, palon kasan babu kowa a lokacin, kai tsaye waje ya nufa.

Yana fita dubbanin jibga-jibgan sojoji dake harabar gidan suka fara ɗaga hannu suna sara mashi, ji kake dim sun buka kafa a kasa alamar girmamawa, ko mutun ɗaya bai ɗaga ido ya kalla daga cikin su ba, gaban sa kawai yake kallo, kai tsaye ya wuce cikin lambun daddy dake cikin gidan.

Akwai wata rumfa mai bala'i kyau da akaiwa daddy a cikin lambun dan hutawa, da zana irin na zamani aka yi shi, an jera wasu irin kujeru wadda aka yi su da wani irin abu kamar zana, kujerun nan sun haɗu ba kaɗan ba, launin dark brown suke, a tsakiyar su kuma sai aka sanya tables mai bala'in kyau shima, gaba ɗaya rumfar kewaye take da wasu irin fitillu masu bala'in kyau suna bata hasken wuta kala biyu, su bada blue su kuma bada fari, ga shuke-shuke iri daban-daban a cikin lambun, akwai fruits kala-kala har da bishiyar tuffa wato apple abin ba'a magana sai wadda ya gani, amma dai lambun ya haɗu sosai.

A saman ɗaya daga cikin kujerun ya zauna tare da tura massage akan a kawo mashi fruits da maltina. Ai kuwa ba ɓata lokaci sai da jibga-jibgan bodyguard guda uku sun doso wajen, ɗaya hannunsa na ruƙe da kwanton fruits irin wanda ake yin sa kamar sakarnan, kwandon ba shi da zurfi sai faɗi, amma yana da bala'i kyau sosai, sun shaƙe shi da fruits kala kala wayan da ba'a yanka ba, ɗayan bodyguard ɗin kuma yana ɗauke da wani katon plate mai shaƙe da fruits kala-kala wayan da aka yanka su, bayan an yanka su kuma sai aka sanya fork spoon a cikinsu ta yadda mai sha zai rinƙa ɗauka kawai yana kaiwa baki, sannan an rufe plate ɗin da wani plate shima mai kyau, dan kar wani abin ya hau kan fruits ɗin, shi kuma bodyguard na karshe ɗauke yake da plate mai ɗauke da maltina guda uku sa glass cup mai ɗan karen kyau, irin dogayen glass cup ɗin nan ne, wanda kasansu yake a baje, a ɗayar hannunsa kuma yana riƙe da tissue a cikin abin sanya tissue ɗin.

Kai tsaye saman table ɗin gabansa suka zo suka ajiye mashi, sannan suka tsaitsaya a gefensa suna jiran umarni, ko kuma ko zai buƙaci wani abin. Kwantar da kansa ya yi a saman jikin bangon kujerar sannan ya ɗaga kan nasa sama tare da lumshe idanuwansa, bai ce da su ko uppan ba.

Almost 10mins suna a tsaye, daga karshe sai ya yi masu alama da hannunsa akan su tafi ba tare da ya buɗe ido ba, kuma bai yi magana ba, ɗan dukar da kai kasa suka yi kafin su wuce cikin gida, a al'adar su yin hakan shine girmamawa.

Shi kuwa haka ya cigaba da zama shiru a wajen idanuwansa a lumshe da alama wani abin yake tunani.

(Ni kuma na haɗa kayana izuwa Nigeria dan naga yadda abin zata kaya, Lion sai na dawo, wata kila kafin lokaci ya ɗan ci wani abin Bawan Allah)

Bari mu fara da maman Sadiq Katsina mu gani.

Sosai suka ji daɗin wannan kuɗi da Imran ya basu, zuwa maman Sadiq ta yi ta ɓoye kuɗin har sai da Sadiq ya dawo daga wajen aiki da daddare, bayan sun ci abinci sun yi sallah ne suka zauna take gaya mashi abubuwan da suka faru, sosai ya taya Rimsha murna, a cikin zuciyarsa kuma yana kukan rashin Jehan dan yana bala'in sonta.

Maman sa ne ta tambaye shi ya za su yi da kuɗin, nan fa ya kawo shawarar akan su kama hayar shagon nan da yake ɗan gaban layin nan nasu kaɗan, tun da ance za'a bada shi haya, kuma bashi da wani tsada 20k ne kuɗin hayar shekara, to su kama sai su sawo kayan provision da sauran 180k ɗin su zaba a ciki shigon, sai Yusuf ya rinƙa zama a ciki yana kula da shi, shi kuma sha'aban ya rinƙa bin shi suna tafiya gareji a tare, sosai maman Sadiq ta ji daɗin shawarar ta kuma karɓa hannu bibbiyu, shima Yusuf ya ji daɗi sosai ko ba komai zai bar zaman banza alayi, kuma zai rinƙa samu ɗan na kashe wa.

Da haka suka yi ta hirarsu cikin farinciki har can dare wuraren karfe 10 sannan suka yi sallama da juna suka wuce ɗakin su, ita kuma maman Sadiq ta miƙe ta rufe kofar ɗakinta ta haye yar katifar ta ta kwanta, cike da farinciki ta yi barci. Asuba ta gari.

A ɓangaren Su Rimsha kuwa.

Tun karfe bakwai na safe Akila ta baro part nasu zuwa nasu Rimsha ɗin, domin yau babu school sai murna take yi za ta wuni tare da Rimsha.

A palo ta isko Imran yana zaune yana kallon News a Tv, kusa da shi ta zauna suka gaisa cike da kaunar juna, sannan ta miƙe ta nufi ɗakin Rimsha tana gaya mashi ba wajen shi ta zo ba, dan haka ta tafi wajen wadda ta zo, sai murmushi kawai yake yi abinsa.

Da sallama ɗauke a bakinta ta shiga bedroom ɗin, Rimsha sarkin son gayu da kwalliya, wani irin fitinannen kamshi ne ke tashi a cikin ɗakin, ta sha wankanta ta yi fes, tana sanye da doguwar riga fari tas mai bakai kyau, an yi mashi kwalliya da wasu duwatsu jajaye masu bala'in kyau, sannan ta gyare ko ina a cikin ɗakin nata, ba abin da ke tashi sai sanyin Ac da kuma kamshin air freshener sannan ga kamshin perfume dake a cikinta, sai suka haɗu suka bada kamshi na musamman, tana kwance saman lallausan bed nata ta ɗaura kafa ɗaya bisa ɗaya, an samu duniya, komai ya daidai ta, tana ruƙe da wayarta tana latse-latse.

Jin sallamar Akila yasa ta ɗago tare da ajiye wayar, ganin Akilar yasa ta sakar mata wani irin cool murmushi wadda sai da fuskarta ya zaman tamkar tauraruwa mai walwalin haske a tsakiyar duhun dare, ga shi ta sanya lips balm a lallausan lips nasa, sai ta kara kyau sosai.

"Aunty Akila sannu da zuwa" ta faɗa a sanyaye, murmushi ita ma Akila ta sakar mata kafin ta ce "Wow First lady gaskiya kin yi kyau sosai, wai irin wannan ɗaukar wanka haka, dole yaya Ahmad ya ce mani ranar da ya fara ganin ki bai runtsa ba, wai irin wannan kyau ko nima ba zan runtsa ba bare shi, ya ce mani ranar kwana ya yi yana tunaninki Queen of beauty, gaskiya ya zaɓi sunan daidai dake" ta kai karshen maganar tare da hayewa saman bed ɗin ta cigaba da faɗin "Amma me yasa baki saka riga da wando da muka ɗauka iri ɗaya jiyarnan ba? Wlh ba karamin kyau zai yi maki ba, kin ga dai kin fi mu hips kayan za su zauna maki sosai wlh".

Miƙewa zaune ta yi fuska ɗauke da kayatatcen murmushi ta ce "Aunty Akila shi wannan dogon rigar bata yi bane?" Cikin sauri Akila ta girgiza kai tana faɗin "Sosai ma ya yi maki kyau, amma anjuma ki sanya riga da wandon sai mu yi anko, dan nima shi zan sanya idan na yi wankar rana" Gyaɗa mata kai Rimsha ta yi alamar to, sannan ta zuro kyawawan kafafunta kasa ta miƙe ta nufi Palo.

"Ina zaki je Rimsha?" Ba tare da ta dakata da tafiyar da take yi ba ta ce "Palo zan je dan naji kamar yaya Imran ya fito ne, ina son mu gaisa ne sai na tambayi me zan girka mana".

Da sauri ita ma Akilar ta miƙe ta bi bayan ta tana faɗin "Me za ki girma mana ne ko kuma me zamu girka? Ai abin da yasa ki ka ganni a nan yanzu kenan, dan na koyi girki". Ta kai karshen maganar lokacin da suke fitowa Palon.

Yadda Akila ta barshi ɗazun haka suka fito suka same shi, zama suka yi saman sofa mai zaman mutun 3, suna fuskantar juna da shi, cikin girmamawa Rimsha ta ɗaga mashi gaisuwa.

Cike da kulawa ya amsa mata gaisuwar tata, tare da tambayarta ya ta kwana, lafiya ta amsa mashi da shi sannan ta ɗaura da tambayar me za su girka.

Sai lokacin ya ɗago ya kalleta, wani irin kyau ta yi mashi, fuska ɗauke da murmushi ya ce "Ki girka duk abin da kike son ci, ni bana zaɓen abinci, sannan idan ba damuwa anjuma da daddare Dr ya ce zai zo tare da kanwarsa dan ta dame shi su je yawo, to zai kawo ta nan, fatan zaku karɓeta hannu bibbiyu sannan ina son ku yi masu girki mai daɗi" cike da murna har suna haɗa baki wajen cewa "E zamu karɓeta kuma zamu shirya masu haɗaden girki".

Albarka ya sanya masu sannan ya ɗaura da cewa "Rimsha baki gaya mani wani kasa kike son zuwa school ba?" Kafin Rimsha ta yi magana Akila ta rigata da cewa "Yaya Imran tare zaka kai mu, kuma Usa muke so" ɗan murmushin ya yi kafin ya ce "To heartbeat an gama, amma dai banso Usa nan ba, amma ba komai zan san yadda zan yi". Ihu Akila ta kurma tare da tashi ta rungume shi tana dariya, yana bala'in son ganin farincikin Akila, dan haka sai ya kara da cewa "Za'ayi maku komai da wuri nan da next week ko two weeks zaku tafi".

Sosai Akila ta kankame shi, ita kuma Rimsha banda murmushi ba wani abin da take yi. Haka suka miƙe cike da farinciki suka wuce kitchen dan shiryawa kansu abincin safe mai rai da lafiya.

A ɓangaren Jelly da Ummi kuwa, tsab suka shirya suka nufi gidan Hajiya Khadijat wato maman su Irfan.

Suna zuwa ba ɓata lokaci suka wuce gidan su Irfan a tare dan suje suga gidan, da kuma tsarinsa.

Daga waje suka yi parking na motarsu sannan suka fito izuwa cikin gidan. A palo suka isko Aunty tana zaune tana kallo, ta ci wankanta ta sha kwalliya, dan yanzu jikinta Alhadulillah sauki na samuwa sosai sai dai muce Masha Allah.

Babu ko sallama suka faɗo cikin Palon, babu kowa sai Auntyn ita kaɗai, daddyn Jelly da Ayla sun fita shopping, shi kuma Irfan yana part nasa yana barci.

Awannan karon Aunty bata wani damu ba, domin ta san ko su waye, fara zagaye palon Ummi ta yi tana faɗin "Kai Masha Allah Aunty Hadiza ki ce mini abin arziki kam har ya kai haka" ta yi maganar tana taɓe baki, kuma duk cikinsu ba wanda ya kuka Aunty har jelly dake a tare da su.

Wani shu'umin murmushi Ommu ta yi tana taunar chewing gum kas-kas-kas, cike da shakiyanci ta ce "Wlh kuwa kedai Turai bari da ana zaton na mutune za'a mamaye komai, sai Allah ya yi ina raye, kuma gida dai nawa ne, yanzu dai mu haura sama dan muga ɗakunan yadda suke". Kai daga jin yadda Ommu ta yi wannan magana kasan da biyu ta yi shi, sannan kuma mawuyacin abune ayi zaman lafiya da ita, domin babu shi a tattare da ita.

Aunty baiwar Allah ita bama ta su take yi ba, Jelly kawai take kallo, dan taga ta yi mata kama da yaya maik wato daddynta, sai dai kash rashin sani yafi dare duhu, yau ga jelly har cikin gidansu amma Aunty bata santa ba bare ta gane ta, sai dai tabbas taga kamannin dake a kan fuskokinsu.

"Ke me kike wani kallona ido kamar na tsohuwa mayya" cewar Jelly ta yi maganar tana karewa Aunty kallo, ai kuwa maganar da ta yin nan ba karamin jefa Aunty cikin tunani ta yi ba, domin sak muryar daddynta ta ji, amma kuma bata kawo cewa Jellyn da suke nema bane, saboda ganinta da su Hajiya Khadijat da ta yi, ta yi tunanin cewa ƴarsu ce, amma dai har cikin ranta ta jinjinawa wannan kamanni na daddy da jelly ga kuma murya shima iri ɗaya, ita ma Hajiya Khadijat ta sha ruwan mamakin lokacin da ta ga Jelly, dan ita ma taga Kamannin, amma sai Hajiya Turai ta ce da ita ai yar uwan baban su Nawid ne, shiyasa ta bar zancen.

"Kai baby kin cika rigima wlh, ke kuma tsohuwar mayya me kike wani ganinta? To idan ma baby ce wlh a hir ɗin ki ta fi karfinki, sai dai gani sai hange daga nesa" Cewar Ummi ta yi maganar cikin faɗa.

Ommu ne ta ce "Ke ma dai Turai me abin ɓata baki a nan? Ai wannan bata kai ku yi mata magana ba, ni fa bana ɗauka ma a gidan nan akwai mutun, dan haka mu wuce dan Allah, da ku tsaya ɓata bakin ku wajen yin magana da ita ba gara ku yi da bango ba, koba komai ya fita daraja". Shekewa da dariya suka yi tare da haurawa sama, Jelly na biye da su abaya tana wani turo baki kamar biro, da ido kawai Aunty ta bi su, tana ganin ikon Allah yau iya ganin idonta.

*Wannan Hajiya Hadizar ita ya kamata acewa kanwar sheɗan ba A'isha na gidan Hajiyar daɗi ba*

Aunty tana zaune a wajen har suka gama dube-duben su a sama, suka sauƙo suka fice suka bar gidan, ko uppan bata ce masu ba, sai ma addu'ar neman Ubangiji ya tsare ta daga sharrinsu da take yi a cikin zuciyarta. Baiwar Allah tana ganin rayuwa.

A ɓangaren Aafia kuwa babu wanda ya lura da ɓacewar tata, domin Abbi ya san tana gidansu Akil, shi kuma Akila a tunaninsa ta koma gida hakan yasa basu nemeta ba.

(*Tofa Aafia kinga ta kanki, wannan shine ɗaya daga cikin illar gida biyu, mutun ya kasance gida biyu yake, yau nan gobe nan, sai ya ɓata ba wanda zai farga da wuri har sai ma duk abin da zai faru ya faru kafin a farga, ni dai ina jajanta maki kuma na haɗa


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login