Showing 309001 words to 312000 words out of 355604 words

Chapter 104 - Triplets Book 2 Hausa Novel Complete

10 Dec 2024

2773

gado dan ya huta.

Imran kuwa sai zarya yake yi a wajen har tsawon minti 30 kafin kiran Nawid ya sake shigowa cikin wayarsa alamar ya iso kenan, da sauri ya nufi waje har yana haɗawa da gudu. Lion kuwa idanunsa a lumshe kamar mai barci.

Yau Imran bai jira soja ya buɗe mashi gate ba, da kansa ya buɗe gate ɗin ya fita, sojan kuwa bai hana shi fita ba saboda yasan tsakaninsu da Lion.

Yana fita ya sami Nawid ya fito daga cikin motarsa shima yana ta zarya a wajen, cikin sauri ya karisa wajensa yana faɗin "Ina take Dr?" Buɗe mashi gidan baya Nawid ya yi yana faɗin gata nan tana kwance tamkar babu rai a jikinta.

Kallon farko da Imran ya yi mata tabbas bai ganeta ba saboda gyara da ta sha da kuma yunkurin tsafi da akayi niyar yi da ita, abin ya ɗan taɓa ta, amma da ya zuba mata idanu ya gane ita ɗin ce.

"Prof dan Allah ka ɗauke ta zan wuce gida ne dan akwai babbar bala'in da na baro a gida". Cewar Nawid ɗin ya yi maganar tare da komawa cikin motar dan yana sauri kada Abbo ya karya kofar ya je ya hakewa ɗaya daga cikin yaran bikin da suka zo ko kuma wani mummunar abu ta faru a gidan, hakan yasa yake sauri.

Ɗaukarta a kafaɗa Imran ya yi kwata kwata ya kasa yin magana, yana son yin magana da Nawid amma ya kasa saboda wani irin nauyi da harshensa ya yi mashi, sannan kuma shima Nawid ɗin yana sauri ba damar su yi magana.

Yana fitar da ita daga cikin motar Nawid ya figi motarsa da gudun gaske ya bar wajen, shi kuma Imran da kyar ya iya nufar cikin gida da ita, ita kuma tanajin ɗumin jikin Imran ta farka tsafin da Abbo ya yi mata na barci ya saketa sakamakon idan baku manta ba jinin Umaiya ba komai yake iya taɓa su ba. Tana farkawa kuma da sabon kukan ciwon ciki ta farka Mashi, jin kukanta yasa ya yi sauri ya karisa cikin palon da kyar.......nima da kyar na iya kawowa nan kafin na dasa aya. I need your prayers my people's 😌

GA ASKARS ƊIN DA NACE ZAN RUBUTO MAKU👇

NA FARKO
﴿قُل هُوَ اللهُ أحَدٌ...﴾
﴿قُلْ أعُوذُ بِرَبِّ اْلفَلَقِ...﴾
﴿قُلْ أعُوذُ بِرَبِّ النَّاسِ...﴾
[ثلاث مرات]


NA BIYU


أصْبَحْنَا وَ أصْبَحَ المُلْكُ لِلَّهِ، وَ الحَمْدُ لِلَّهِ، لَا إِلَهَ إِلَّا اللهُ وَحْدَهُ لَا شَرِيْكَ لَهُ، لَهُ المُلْكُ، وَ لَهُ الحَمْدُ، وَ هُوَ عَلَى كُلِّ شَيْءٍ قَدِيرٌ، رَبِّ أسْألُكَ خَيْرَ مَا في هَذَا اليَوْمِ وَ خَيْرَ مَا بَعْدَهُ، وَ أعُوذُ بِكَ مِنْ شَرِّ مَا في هَذَا اليَوْمِ وَ شَرِّ مَا بَعْدَهُ، رَبِّ أعُوذُ بِكَ مِنَ الكَسَلِ، وَ سُوءِ الكِبَرِ، رَبِّ أعُوذُ بِكَ مِنْ عَذَابٍ في النَّارِ وَ عَذَابٍ في القَبْرِ.(١)وَ إذَا أمْسَى قَالَ: أمْسَيْنَا وَ أمْسَى المُلْكُ لِلَّهِ.
وَ إذَا أمْسَى قَالَ: رَبِّ أسْألُكَ خَيْرَ مَا في هَذِهِ اللَّيْلَةِ وَ خَيْرَ مَا بَعْدَهَا، وَ أعُوذُ بِكَ مِنْ شَرِّ مَا في هَذِهِ اللَّيْلَةِ وَ شَرِّ مَا بَعْدَهَا.


NA UKU


اللهم بِكَ أصْبَحْنَا، وَ بِكَ أمْسَيْنَا، وَ بِكَ نَحْيَا، وَ بِكَ نَمُوتُ، وَ إلَيْكَ النُّشُورُ.(١)وَإذَا أمْسَى قَالَ: اللهم بِكَ أمْسَيْنَا، وَ بِكَ أصْبَحْنَا، وَ بِكَ نَحْيَا، وَ بِكَ نَمُوتُ، وَ إلَيْكَ المَصِيْرُ.


NA HUƊU


اللهم أنْتَ رَبِّي لَا إلَهَ إلَّا أنْتَ، خَلَقْتَنِي وَ أنَا عَبْدُكَ، وَ أنَا عَلَى عَهْدِكَ وَ وَعْدِكَ مَا اسْتَطَعْتُ، أعُوذُ بِكَ مِنْ شَرِّ مَا صَنَعْتُ، أبُوءُلَكَ بِنِعْمَتِكَ عَلَيَّ، وَ أبُوءُ بِذَنْبِي فَاغْفِرْ لي فَإنَّهُ لَا يَغْفِرُ الذُّنُوبَ إلَّا أنْتَ.



NA BIYAR


اللهم إنِّي أصْبَحْتُ أُشْهِدُكَ، وَ أُشْهِدُ حَمَلَةَ عَرْشِكَ، وَ مَلَائِكَتِكَ، وَ جَمِيْعَ خَلْقِكَ، أنَّكَ أنْتَ اللهُ لَا إلَهَ إلَّا أنْتَ وَحْدَكَ لَا شَرِيْكَ لَكَ، وَ أنَّ مُحَمَّداً عَبْدُكَ وَ رَسُولُكَ. [أرْبَعَ مَرَّاتٍ]


Na shida


أللهم مَا أصْبَحَ بِي مِنْ نِعْمَةٍ، أوْ بِأحَدٍ مِنْ خَلْقِكَ، فَمِنْكَ وَحْدَكَ لَا شَرِيْكَ لَكَ، فَلَكَ الحَمْدُ وَ لَكَ الشُّكْرُ.(١)و إذَا أمْسَى قَالَ: اللهم مَا أمْسَى بِي...


NA BAKWAI


اللَّهُمَّ عَافِنِي فِي بَدَنِي، اللَّهُمَّ عَافِنِي فِي سَمْعِي، اللَّهُمَّ عَافِنِي فِي بَصْرِي، لَا إِلَهَ إِلَّا أَنْتَ، اللَّهُمَّ إِنِّي أَعُوْذُ بِكَ مِنَ الْكُفْرِ، وَالْفَقْرِ، وأَعُوْذُ بِكَ مِنْ عَذَابِ القَبْرِ، لَا إِلَهَ إِلَّا أَنْتَ.[ثَلاثَ مَرَّاتٍ]



NA TAKWAS


حَسْبِيَ اللهُ لَا إلَهَ إلَّا هُوَ عَلَيْهِ تَوَكَّلْتُ وَهُوَ رَبُّ العَرْشِ العَظِيمِ [سَبْعَ مَرَّاتٍ]



NA TARA


أَصْبَحْنَا وَ أَصْبَحَ المُلْكُ لِلَّهِ رَبِّ العَالَمِيْنَ، اللَّهُمَّ إِنِّي أَسْأَلُكَ خَيْرَ هـَذَا اليَوْمِ: فَتْحَهُ، وَنَصْرَهُ وَ نُورَهُ، وَ بَرَكَتَهُ،وَ هُدَاهُ، وَأَعُوذُ بِكَ مِنْ شَرِّ مَا فِيْهِ وَ شَرِّ مَا بَعْدَهُ.
و إذا أمسى قال: أَمْسَيْنَا وَأَمْسَى المُلْكُ لِلّهَِ رَبِّ العَالَمِيْنَ، اللَّهُمَّ إِنِّي أسْأَلُكَ خَيْرَ هـَذِهِ اللَّيْلَةِ، فَتْحَهَا، وَنَصْرَهـَا، وَنورَهـَا وَبَرَكَتَهَا، وَ هُدَاهـَا، وَ أَعُوذُ بِكَ مِنْ شَرِّ مَا فِيْهَا وَشَرِّ مَا بَعْدَهـَا.


💖💖TRIPLETS💖💖




E81-82💖




Yana fitar da ita daga cikin motar Nawid ya figi motarsa da gudun gaske ya bar wajen, shi kuma Imran da kyar ya iya nufar cikin gida da ita, ita kuma tanajin ɗumin jikin Imran ɗin ta farka, tsafin da Abbo ya yi mata na barci ya saketa sakamakon idan baku manta ba jinin Umaiya ba komai yake iya taɓa su ba. Tana farkawa kuma da sabon kukan ciwon ciki ta farka Mashi, jin kukanta yasa ya yi sauri ya karisa cikin palon da kyar.

Duka ta fara kai mashi a baya tana sambatu tana faɗin "Yaya Nawid ni ka saukeni, ɗan iska kawai, bana ce kada ka kuskura ka taɓa ni ba, wlh sai na gaya wa Ummi, na ce bana sonka ana dole ne? Mugu kawai ka sauke ni bana so".

Raunin zuciya ya sa Imran ya kasa karisawa da ita ɗakinsa, ya kasa haurawa saman benen, a palon kasa ya sauketa, idanunta a rufe amma tana surfa masifa, ganin abin Imran yake yi tamkar a mafarki, tabbas yau Jelly'nsa ce a gabansa, ya kasa motsawa daga in da yake ma bare kuma a kai ga ya yi mata magana.

Bayan ta gama surfa masifar tata ne ta juya tare da buɗe idanunta akan zata tafi ɗakin Ummi dan ita duk a tunaninta a a gidan Abbo suke.

Tana juyawa kuma sai ta tsaya turus dan taga yanayin tsarin palon ba irin nasu Ummi bane, cikin sauri kuma ta juyo dan ta tambayi Nawid ɗin ina ne nan kuma.

Kai tsaye sai cikin idanun Imran idanunta suka sauƙa, zuba mashi idanu ta yi tana kallonsa, nan take kuma ta dafe kanta tare da sakin kuka mai sauti, kafin Imran ya yi wani yunkuri ta sukale kasa sumammiya.

Da sauri ya yi kanta yana ambatar sunanta, ina ta sume. Jikinsa har kerma yake yi wajen ɗaukarta tare da tattara duk karfin da ya saura mashi ya haura sama da ita.

Kai tsaye ɗakinsa ya wuce da ita, a saman bed nasa ya kwantar da ita tare da sauƙowa ya ɗauko ruwa mai sanyi daga cikin fridge nasa dake a cikin ɗakin, da yake gabaɗaya ɗakunan gidan akwai fridge a ciki.

Saman gadon ya dawo tare da buɗe bakin robar ruwan ya tarbo ya shafa mata a fuska, shiru bata motsa ba sake ɗebo ruwan ya yi ya shafa mata, nan ma shiru, sai a karo na uku ne ta ja dogon numfashi tare da fara sambatu idanu a rufe. "Ni gidansu yaya Imran za ka kaini, idan kuma ba zaka kaini can ba to na tafi, kai ka yanka ni kuma sai kace wata rago? Ba zan shiga ɗakin ba, tun da naga ka matsa na shiga na san ba alkhari bane a cikin ɗakin" sambatun maganarta ta karshe da mutumin daya ɗauketa da nufin zai taimaka mata ta karɓo school bag ɗin sai ya kaita gidan shi yana ƙoƙarin lalata mata rayuwa, shine magana ta karshe da ta yi fitar ta gidan kenan su Ummin Nawid suka bugeta da mota.

Dafe kai Imran ya yi idanunsa sun yi jawur, da kunnansa ya ji irin gwagwarmayar da ta sha, dukka kuma akan shi domin kuwa sunan sa ne abu na farko data fara ambata, ashe ma Kd ta zo kuma saboda shi Baiwar Allah, abin da kenan yake faɗi a cikin zuciyarsa.

Jin ta ki daina sambatun ne yasa ya ambaci sunanta kasa kasa a kuma nutse, shiru bata amsa ba kuma bata daina sambatun da take yi ba.

Ganin haka yasa ya sanya hannunsa ya tallaɓota a kirjinsa yana mai sake ambatar sunanta, har lokacin bata ji shi ba, sai da ya ɗan ambata da karfi sannan ta tsaya cak da surutan da take yi tare da waro idanunta waje, tabbas ta gane voice nasa domin kuwa ba zata taɓa mance muryarsa ba, tun tana karama take jin muryar nan tasa, kamar hadda haka ta haddace voice ɗin nasa.

Ido cikin ido take kallon shi yayin da shima yake kallonta cikin ido babu ko kyaftawa, dukkansu ba bu wanda ya iya kyafta ido daga cikinsu saboda tsabar farinciki.

Sun jima a haka sai da ya ga hawaye na bin gefe da gefen fuskarta ne yasa ya ɗan kyafta idanunsa tare da sake ambatar sunanta a hankali.

"Yaya Imran" ta ambata a hankali tare da ɗago da hannunta izuwa saman face nasa domin ta tabbatar da shi ɗin ne, gyara mata kwanciyarta a jikin nasa ya yi tare da riƙo hannun nata ya kai saman kukatunsa yana faɗin "Taba ki ji nine Jelly'na nine ba wani ba".

Kuka mai tsuma zuciyar mai sauraro ta saka mashi, shi kuma rungumeta sosai ya yi a jikinsa, a hankali hawayen da suka cika mashi idanu suka fata gangaro mashi a saman kuncinsa. Dukkansu suna ruwan hawaye waye zai rarrashi wani a cikin su to?.

Cikin kuka ta ce "Yaya Imran ina ka tafi ka barni? Ina kaje baka zo Kano ba? Daddy wai zai aura mani wani mutum shine na gudu na zo Kaduna dan na gaya maka, ina tafiya wasu suka kwace mani school bag na, shine wani kuma ya ce in zo ya bani school bag ɗin a gidansa, da muka je ya ce sai na shiga ɗakinsa ni kuma naki yarda dan daddy ya hana ni, shine ya ce zai yanka ni, tun ɗazun yake ta yi mani masifa wai lallai sai na shiga, dana ga zai dake ni shine na gudu na fito waje daga nan kuma ban sake ganin kowa ba, ina ka tafi yaya Imran?"

Tana magana tana kara tsananta kukan da take yi. Imran bawan Allah kuka ya ci karfinsa ya kasa magana, banda kara matseta da ya yi a jikinsa ba wani abin da ya iya taɓukawa.

"Yaya Imran kayi magana mana ko dai ba kai bane? A'a kai ne ma tabbas kai ne, dole kaine!".

Muryarsa ta dashe bata fita sosai, da kyarma ya iya cewa "Nine matata nine, ki kyaleni nayi kuka sosai yau". Ɗan ture shi ta yi tare da ɗago kanta tana hawaye tana faɗin "A'a yaya Imran, ba zaka yi kuka ba, ban yarda ba, ka daina bana so dan Allah ka bari ka ji? Idan baka bari ba zan gayawa daddy kana kuka".

"Ki bari na yi kuka kin ji? Na tara kukan sosai a cikin zuciyata, yau ɗaya ki bari nayi sosai har sai ya ishe ni kinji ko?". Duka ta fara kai mashi a kirjinsa tana faɗin "Bana so bana son kukan, ni ka daina, dan Allah ka bari bana so". "Na bari matata na bari, tun da baki so na bari kin ji ko?" Gyaɗa mashi kai ta yi alamar ta ji.

"To shikenan kema ki daina kukan kin ji ko?" Ya faɗa yana mai ɗago hannunsa izuwa saman face nata dan ya goge mata hawayen fuskarta. Ita ma kai nata hannun ta yi sama face nasa ta fara goge mashi hawayen tana faɗin "Yaya Imran ai bani nake kawo kukan ba, shine yake zuwa da kansa, wlh bani na kira shi ba".

Harshe yasa ya lashe hawayen nata tas kafin ya ce "To na shanye hawayen dukka kada ki bari wani ya fito kin ji ko?" gyaɗa mashi kai ta yi alamar e ta ji.

Zuba mata idanu ya yi yana kallon yadda ta kara wani sihirtaccen kyau na fitar hankali, ita ma kallon shi kawai take yi tana mai matuƙar jin kaunar yayan nata har cikin zuciyarta.

To fah kenan yanzu jelly ta mance da su Nawid? Kenan yanzu bata san waye su ba? Ta dawo daidai ba ta san rayuwar da ta yi a baya ba, kun dai ga daga wajen da wannan mutumin ya ɗauketa daga nan ta faro rayuwarta na yanzu, su Nawid duk ta mance su kun dai ji tace ɗazun ne mutumin yake yi mata magana, kenan duk waƴan nan watanni da ta ɗauka a gidan Ummi sun goge bata san da su ba, babbar magana mu dai je zuwa.

"Jelly" ya ambaci sunanta can kasan maƙoshinsa, na'am ta amsa mashi da shi.

"Kin san wahalar da na shi bayan ɓatar ki kuwa?" Ɗago da waƴan nan dara daran idanun nata kamar ball ɗin ta yi izuwa cikin nasa idanun, a raunace ta fara magana "Yaya Imran ina kewar daddyna sosai, ina son ganin shi, amma dan Allah kada ka gaya mashi ina nan ka ji ko? Idan ka gaya mashi wlh aure zai yi mani da wani, ni kuma bana son kowa, kai kaɗai kawai nake so, dan Allah idan kana da hoton daddyn ka bani na kalla ka ji ko? Ina jin zuciyata tana yi mani zafi sosai".

Hannu yasa ya kwantar da kanta a saman kirjinansa yana kara jin kaunarta tana ratsa shi sosai.

Kwanciya ya fara yi da ita a jikinsa kafin nan ya ce "Daddy ya ajiye batun aurenki da wani ki daina damuwa, yanzu haka da nake maki magana ko yanzu na kira shi nace mashi gaki mun gane ki, to ina mai tabbatar maki a daren nan zai cire sadakin ki da kansa ya miƙawa Abbi a ɗaura mana aure, ki zama mallakina ni kaɗai, dan haka kada ki damu da safe zamu je wajen su".

Kara shegewa jikinsa ta yi cikin shagwaɓa ta ce "Kenan yaya Imran yanzu daddy zai yi mana aure?" Jinjina mata kai ya yi alamar tabbatar mata da maganar tata.

"Jelly daddy ya sha bakar wahala sosai ɓatar ki, idan munje gida gobe ki bashi hakuri, ki nemi yafiyarsa, wlh ya wahala fiye da tunanin ki, ya yi fama da rashin lafiya sosai".

Zubur ta miƙe daga jinin nasa hankalinta a tashe ta ce "Dan Allah Yaya Imran ka kaini wajen shi yanzu ka ji? Ina dai ba zai yi mani aure da wani ba?" Gyaɗa mata kai ya yi alamar e "To dan Allah ka kaini wajen shi ka ji? Ina son ganin daddyna ina kewar shi wlh, Wayyo Allah". Ta kai karshen maganar tare da fara sabon kuka

Jawota jikinsa ya yi ya shiga rarrashinta tare da nuna mata dare ya yi ta kwanta su yi barci zuwa gobe sai suje, da kyar ta yarda ta kwanta a jikinsa, bargo ya ja masu tare da yi masu addu'ar barci ya shafa mata sannan ya kankameta sosai a jikinsa kamar wani ya ce zai kwace mashi ita, ko juyawa zai yi tare suke juyawa tana manne a kirjinsa, ita ma dai kankame shi ta yi kamar an ce mata zata rasa shi ne.

Da haka barci ya ɗauke ta, shi kuwa ya kasa barcin kwata kwata, kallonta kawai yake yi domin bai kashe wutar ɗakin ba, hakan ya bashi damar kallon kyakkywar fuskarta da kyau, kwata kwata ya kasa runtsawa.

A ɓangaren daddy'n jelly kuwa, bari mu ɗan koma baya kaɗan wunin yau kenan.

Sai misalin karfe 11 na rana ya farka daga barcin da ya ɗauke sa, da mamaki sai baiga Ayla a saman gadon ba, cikin sauri ya miƙe zauna yana ƴar wawwaigawa ko zai ganta.

Can ya hangota saman kujerar mirror ta rarrafa ta tafi wajen, bata iya takawa da kafafunta sai dai rarrafe, bayan ta tashi daga barci ne ta rarrafa ta shiga toilet ta yi wanka sannan ta fito da kyar ta iya hawa saman mirror chair ma ta zauna tana shafa mayunkar Daddyn nata.

Wani irin muguwar faɗuwar gaba ya ji kamar wani abin na shirin faruwa da shi, Allah sarki Uba da ƴa a jikinsa yana jin duk abin da zai faru ko yake faruwa da Jellynsa, innalillahi wa inna ilaihir rajiun ya karanta tare da sauƙowa kasa daga saman gadon da sauri ya karisa wajenta.

Yana zuwa ya sanya hannu ya karɓi mai da take riƙe da shi ya shiga shafa mata, yana yi yana ƙaƙalo mata murmushin dole dan ta yi farinciki, amma shi kuma ba farincikin bane a cikin zuciyarsa, ban da muguwar faɗuwar gaba ba wani abin da yake ji, amma haka ya daure ya kakalo murmushi dan ta yi farinciki.

Kwance towel ɗin jikinta ya yi ya fara shafeta da mai har saman breast nata, yana shafa masu mai yana kuma matsasu, amma kuma yaki yarda su haɗa ido da ita saboda wani irin kunyarta da yake ji, ita ma dai daga jiya zuwa yau bata son su haɗa idanu saboda wani irin kunyarsa da take ji.

Bayan ya gama ne ya zube gwiwowinsa a kasa a gabanta dan ya rage tsawonsa ya zama daidai da tata, kuma baya jin shakkar yi mata duk abin da yake so dan gane da soyayya cikin kuma har da duƙa mata saboda yasan Ayla yarinya ce so silent, and then yanzu take ɗaukar karatu, so a yadda suke ɗin nan duk abin da ya koya mata akan shi zata tashi, yasan babu wani zancen raini a tsakaninsu, ba zata raina shi ba dan yana duƙa mata, dan kuwa daga yanayin mutun kake iya gane waye shi me kuma zai iya aikatawa, da dama daga cikin mu muna ganin idan namiji ya duƙa mana shikenan mun raina shi girmansa ya zube, shiyasa wasu maza basu taɓa yarda su nuna cewa suna son abuma bare kuma har a kai ga zancen duƙawa, ba dan komai ba sai dan kada a raina su, so dan miji ya duƙa maki ba raini bace soyayyace, amma wata daga nan sai ta raina shi tana ganin ai har duƙawa yake yi a gabanta, kuskure ne yin hakan, soyayya take ja ayi komai da bai kaucewa Shari'a ba, dan haka ki duƙawa miji ba raini bane shima ya duƙa maki ba raini bane.

MAZA KU YI MAZA KU KOMA IRIN LARABAWAN NAN DA TURAWA, ANA DUƘAWA ANA MIƘO FURE, MU KUMA KU DUƘA KU MIƘA MASHI KUNU🤣🤣 WASA NAKE YI, KI DUƘA KI MIƘA MASHI KAYAN DAƊI IRIN SU BLACK TEA AND COFFEE 😌🙃.

Bayan ya zube gwiwowinsa ya rage tsawonsa ta yadda zai yi daidai da tata saboda ita tana zaune saman chair ne. Kwanto da kansa a saman cinyarta ya yi


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login