Showing 108001 words to 111000 words out of 355604 words

Chapter 37 - Triplets Book 2 Hausa Novel Complete

10 Dec 2024

2785

wannan tambayar, wadda ya ji ta tamkar saukar aradu, domin kuwa idan har ya gaya mata cewa gidan bappansu suke zuwa neman yar uwarsu ta gefen Abba, to ba makawa tsine masa zata yi, ga shi shi kuma bai iya karya ba, shiya lokacin da ya auri Umaisha ya fito karara ya gaya musu gaskiya, bai ma san ta ina zai fara yin karyar ba, to idan ma zai yi karyan me zai faɗa mata.

Ganin ya yi shiru ne yasa ta ce "Akil lafiya kake kuwa?" Yar firgita ya yi ya ɗago yana kallonta "Ammie na ga ji sosai ne, daga Kano fa nake, dan Allah ki bari naje na huta kin ji? Idan ba haka ba zan iya faɗuwa". Jin haka yasa ta ce to ya wuce part na sa da wuri ya je ya huta, kuma a gaskiya ita bata ma san asalin garin da yan uwan Abba suke ba, bata san suna Kano ba, a iya nan Kaduna ta sani, shiyasa bata yi wani tunani ba ta ce ya wuce part na shi, da ta sani ko tana zargin yan uwan Abba na Kano to ba faɗuwa Akil zai yi ba ko mutuwa zai yi sai ya gaya mata gidan uban da ya je, idan kuma ya gaya mata, ta ji cewa wajen yan uwan Abba ya je, to ba makawa tsine mashi zata yi, kamar yadda ya faɗa.

Da sallama ɗauke a bakinsa ya shigo part ɗin, gaba ɗayan su suna palonsa, Akila, Rufee, Aafia, Umaisha, kasan cewar 24 hours akwai wuta a gidan su, hakan yasa gaba ɗaya ko'ina haske ya gauraye cikin palon.

Akila da Umaisha ne suka ta shi a tare suka nufe shi suna faɗin "sannu da dawowa yaya Akila". Wani haɗiyar yawu Rufee ta yi, a ranta ta furta "dama nan ne gidan gayen nan? Sorry Umaisha dole na ari mijinki na yan kwanaki"

(Tofa rashin sani ya fi dare duhu, in dai Akil ne bismillahi)

Cikin rawar kafa ta miƙe tsaye tana faɗin "Sannunka da dawowa mijinmu" galala Aafia ta saki baki tana kallonta. Da yake shima Akil ɗan air ne ko kallon in da take bai yi ba, ya rungumo Akila ta gefe Umaisha ta gefe yana faɗin "Na yi missed na ku my pleasures".

Lafewa suka yi a gefe da gefen kirjinsa suna fuskantar juna, sai murmushi suke yi kamar dukkan su matan sane.

Cike da zolaya ya ce "Heartbeat ke daga nan na sallame ki, ki zauna a nan da su Aafia, ke kuma my baby mu je ki yi mini wanka ki mini tausa dan na gaji sosai". Turo baki Akila ta yi, ta turɓune fuska a shagwaɓe ta ce "Wlh yaya Akil kana cimin fuska, kana saka Aunty Umaisha tana rena ni, kuma na fita shekaru, haka ranar ma har da ce mini ta yi wai mijinta ya kusa dawowa na wuce ɗaki na, wannan cin fuska Allah ya yi mini yawa" ta kai karshen maganar tana raba jikinta da na shi, ita a dole ta yi fushi.

Cikin sauri ya jawota ta dawo jikin nasa, cikin sigar rarrashi ya ce "Haba my heartbeat wasa nake yi miki ai, ke ai kin san tawa ce, ban isa ba, amma yanzu dai ki zauna a nan ina zuwa" ya kai karshen maganar yana jan hancinta,

Turo baki ta kuma yi kamar zata saki kuka, ita dai Aafia bin su kawai take yi da ido, abin gwanin ban sha'awa, sai fatan Alkhari da fatan kasancewa cikin farinciki na har abada take yi musu, saɓanin Rufee da take kallon su take ayyana wa a zuciyar ta, wannan farinciki da ita ya kamata Akil ya rinƙa yi, duk wannan tarairaya da soyayya ita ya kamata ya yi wa ba Umaisha ba.

Umaisha kuwa tana lafe a kirjin mijinta ta fito da ɗan harshenta waje tana yiwa Akila gwalo, a kule Akila ta ɗaga hannu zata make bakin nata, cikin sauri Akil ya tare hannun nata yana faɗin "So kike yi ki fasa mini baki na ko? To baki isa ba, ai gara ki buge nawa ba nata ba, dan idan kika buge nata sai na fita jin zafi da ɓacin rai"

(Akwai wanda ya gane zancen Akil kuwa?🤔)

"Kai yaya Akil yanzu wlh ka dawo mai son kai sosai" "Wai ku ba zaku kyaleni naje nayi wanka na huta ba, sai na faɗin muku a nan ne? Ku dama idan kuka haɗu kuka sani a tsakiya Allah ne kawai ke kwatata".

Raba jikinsu Umaisha ta yi tare da riƙo hannunsa tana faɗin "Muje hai yaya Akil, muje na maka wanka bar heartbeat ɗin nan bata da aikin yi sai dai ta zo ta dame mu" ta kai karshen maganar tana yi wa Akila gwalo, kwafa Akila ta yi tana faɗin "Wlh ba zan bari ki ba, kin ɗauki bashi, kuma sai na rama, nice ma bani da aiki ya ba? Ba komai".

Shi dai murmushi kawai yake yi, yana matukar kaunar Akila dan tana son duk wani abin da yake so, kuma tana goya masa baya sannan ta taya shi kula da wannan abin, idan baya nan sosai take kula da Umaisha, ko motsi Umaisha ta yi sai ta tambaye ta me take so, sai dai idan ta tafi school ne, sannan suna sharing secret tare da Umaisha, suna kuma rufawa juna asiri, yanzu ma duk abin da Ammie ke yi wa Umaisha Akila tana sane, sai dai abin da yasa bata gayawa Akil ba, tana tsoron idan ta faɗa Ammie zata iya saka shi ya saki Umaisha, shiyasa ta yi shiru, amma fa tana nan tana kulla ta yadda za'a yi Akil ya canzawa Umaisha gida, dan kullun sai ta yi mata kukan abin da Ammie ke yi mata, sannan kuma in dai tana nan Ammie tasa Umaisha aiki to tare suke yin wannan aikin, shiyasa yanzu ta iya wanke-wanke da ɗan aikace-aikace gida.

Wucewa cikin ɗaki Akil da Umaisha suka yi, ita kuma Akila ta dubi su Aafia ta ce "Kuzo mu je ɗaki na mu zauna, idan yaya Akil ya fito zai mayar da ku gida..." A hanzarce Rufee ta tari numfashi ta da cewa "A'a ki dai bari mu zauna a nan ɗin tun da mu bakin Umaisha ne" da yake Akila bata kawo komai a ranta ba, sai ta biye musu kawai suka zauna a wajen.

Shi kuma Akil su na shiga ɗaki ya jawo matarsa ya runguma yana faɗin "Nayi kewar ki my baby", ya kai karshen maganar yana sumbatar goshinta. Hannayenta ta kai saman botir na rigarsa ta wuya ta fara ɓalle wa tana faɗin "Ai nima na yi kewar ka yaya Akil". Cire hannayen nata ya yi ya kankame ta a jikinsa sosai, a nitse ya haɗe bakin su ya fara bata hot kiss, ba ɓata lokaci ita ma ta fara mayar masa da martani, nan take suka birkicewa juna, hannun sa ya zura cikin rigarta ya fara bata sako na musamman.

Sun jima a haka har sai da karfin su ya kare, Umaisha na kokarin faɗuwa mashi kasa, sannan ya yi saurin sakin ta, idanuwansa duk sun sauya launi, har wani duhu-duhu yake gani. Da kyar ya iya sai ta nitsuwarsa ya wuce toilet dan yin wanka.

Ita kuma ta kasa binshi ta cire masa kayan, a bakin gado ta zauna tana sauƙe ajiyar zuciya dan dama in da sabo ta zaba Akil ya kware wajen iya soyayya, yanzu zai sata ta mance duk wani damuwa da take ciki komai girmar damuwar, hakan yasa da ya dawo gida duk wata matsalar ta, ta kau kenan, sai zallar farinciki.

Tana zaune a wajen ta kasa motsawa har ya fito wanka ɗaure da towel a kugunsa.

"My baby this time fa kin yi kewata sosai kema na ga alama" ɓoye fuska ta yi tana murmushi, domin kuwa ya faɗi gaskiya ta yi kewar shi sosai da sosai.

Yau dai komai shi ya yi wa kansa, har kayan sawa shiya ciro wa kansa dan ya lura babyn tasa ta karɓi wuta sosai har lokacin bata dawo normal ba.

Jallabiya ya sanya a jikinsa sai tashin kamshi yake yi, ya shinfiɗa dadduma ya gabatar da sallar mangariba, ita kuma Umaisha miƙewa ta yi da kyar ta fito wajen su Aafia, ta ce suje ɗakin Akila su yi sallah a tare, ko kuma su shiga ɗayar ɗakin kusa da nasu, Rufee ce ta ce lallai su shiga ɗakin kusa da nasu, a nan za su yi sallah, A'afia ta lura Rufee bata son barin part ɗin ne tun da ta kalli Akil ya dawo, Allah dai yasa ba wani abin take shiryawa ba.

A ɗayar ɗakin suka yi sallah a tare gaba ɗayan su har Umaishan, sai dai ita Rufee bata yi sallar ba, ta ce musu wai tana period, Aafia tasan karya Rufee keyi domin kuwa kullun haka take ce musu a school wai tana period, har suka gane karya take yi, a zahirin gaskiya kuma wani lokaci bokanta ke hanata yin sallar gaba ɗaya, wani zubin ya ce mata iya sallar mangariba kawai ya halakta mata da tayi, wani lokaci kuma sai ya ce kwata-kwata ma kada tayi.

Bayan sun idar da sallah ne suka fito palo suka zauna suna hira.

Cikin dabara Umaisha ta zame jikinta ta gudu wajen mijinta abinta, dan tana kewar shi sosai, ashe Rufee na ankare da ita, tana ganin tafiyarta, sai wani ciza laɓɓa take yi alamar tana kishi da Umaisha, kuma tana jin haushi.

Umaisha kuwa tana shiga cikin ɗakin ta isko shi yana miƙe a saman bed nasu.

Cikin sauri ta tafi ta faɗa jikinsa tana murmushi, shiru ya yi mata kamar bai san da zuwanta ba. A shagwaɓe ta ce "Yaya Akil meyafaru?" Shiru ya yi kamar ba shi a wajen, ganin haka yasa ta kama lips nasa na kasa ta fara tsotsa kamar sweet.

Kwace lips nasa ya yi yana lumshe idanunsa alamar ya ji daɗin hakan, sai dai kuma fushi yake yi da ita, kasa ta yi da murya cikin girmamawa ta ce "Kayi hakuri" a kule ya ce "Ba zan yi ba, ai baki damu da ni bane, har da zaki tafi ki barni a ɗakin nan tun jiya fa rabon mu da juna..." Bata bari ya karisa maganar ba ta yi maza ta cabke lips nasa tana mashi wasa da hannun ta a saman babban sashe.

Jin wannan salon yasa ya mance da fushi ya kara jawota jikinsa suka lula duniyar sama jannati.

Su Aafia kuwa sai hira suke yi a palo, amma ita Rufee kunnanta da hankalinta duk yana jikin kofar bedroom ɗin su Akil, tana mutuwar son taga meke faruwa a cikin ɗakin, burinta kawai ta ga me suke yi a cikin.

Kiraye kirayen sallar isha ne ya dawo dasu daga duniyar sama jannati da suka lula, da kyar ya iya saita kan shi tare da kamewa, sannan ya miƙe zaune duk idanuwansa sun rine tamkar ba shi ba, ita ma Umaisha duk ta birkice masa, sai wani lumshe idanu take yi.

"Ta shi kiyi wanka kizo ki yi sallar isha sai ki shiya ki saka nikaf zamu fita restaurant" ya yi maganar da murya kamar mai raɗa.

Ɗan zaro idanuwanta ta yi murya a dashe ta ce "Yaya Akil wanka kuma?" Gyaɗa mata kai kawai ya iya yi, dan ya kasa magana.

"To ai yaya Akil naga ba mu yi komai ba, in dai yi alwala idan na yi sallah in zamu kwanta barci sai na yi wankar" girgiza kai ya yi yana kokarin sauƙa daga gadon ya ce "Wanka za ki yi saboda ai kin more" shiru ta yi tana tunanin kalmar ta more, "to me na more yake nufi? Shifa yaya Akil ɗin nan haka yake sai ya rinƙa gayawa mutun magana ta sigar da ba zai gane ba" ta faɗa a cikin ranta.

Tana kwance ta kasa ta shi har sai da ya yi wanka tare da ɗauro alwala ya fito tana kwance.

Bakin gadon ya zo ya tsaya tare da miƙa mata hannunsa a kan ta kama ta miƙe, da kyar ta iya miƙa masa hannun nata, a hankali ya miƙar da ita, ta sauƙo kasa ta nufi toilet.

Kafin ta fito ya gabatar da sallar sa yana zaune saman dadduma. Ita ma shiryawa ta yi ta zo ta yi sallar.

Bayan ta idar ne yake tsokanar ta a kan yau ta hana shi yin Sallah a masallaci, domin kafin ya yi wanka an idar da sallah. Kwanto da kanta a saman kafaɗarsa ta yi tana zuba masa shagwaɓa, a hankali ya kai hannunsa yana shafar kumatunta yana zuba mata addua'o'i tare da sanya mata Albarka.

Sun kwashe good 10mins a haka kafin nan su miƙe ya ɗauki laptop nasa da wayarsa, ya ce ta same shi a cikin mota idan ta gama shiryawa, kwata-kwata ya mance da su Aafia dake palo.

Yana fitowa Rufee ta miƙe tana faɗin "Angon mu ai tun ɗazun nake jiran fitowar ka domin in maka godiya, tsayawa ya yi yana kallon Akila dake ta famar turɓune fuska, ita a dole tana fushi da shi.

"Heartbeat fushi kike yi da yaya Akil naki?" Ya yi maganar cikin sigar rarrashi.

Akila bata kai ga yin magana ba, Rufee ta rigata da cewa "Angon mu a gaskiya muna godiya sosai, domin Umaisha ta gaya mana yadda kake bata kulawa sosai, ta ce mana ka iya soyayya da kula da mace, ka iya tarairaya, sannan ka kware a kan gado"

A sukwane ya ɗago kai yana kallon ta, ba iya shi kaɗai ba har da Akila da Aafia sai da suka girgiza da jin zancen da Rufee ke yi, duniyar tunani Aafia ta faɗa na yaushe Umaisha ta basu wannan labari, ita da iya hirar school kawai suka yi da ita, amma shine Rufee zata yi mata wannan sharrin wajen Akil, lallai Rufee ta iya makirci.

Ita kan ta Akila sai famar karyata zancen zuciyar ta keyi, duk da tana zuwa school bata wuni da su ba, amma dai ta yi wa Umaisha farin sani, ta san cewa ko A'afia ita kaɗai Umaisha ba zata gaya mata sirrin aurenta ba, domin kuwa ko ita da suke tare dare da rana Umaisha bata taɓa gaya mata abin da ke tsakanin ta da Akil, sai ita Rufee ce zata gaya wa, lallai wannan magana ta Rufee abin dubawa ne.

Ita kuwa Rufee ganin Akil ya ɗago yana kallonta, abin nema ya samu dama attention nasa take bukata, dan haka sai ta ci gaba da cewa "Gaskiya Umaisha ta more sosai, dan yadda ta bamu labarin ka, na yi mata murna ba kaɗan ba, amma fa kayi hakuri, na buge mata baki domin abin da ta yi bai dace ba, shiyasa na mata faɗa sosai, na ce kada ta sake faɗin sirrin mijinta ga wata, Allah ma yasa mu ta gayawa ba wasu a waje ba, shiyasa nayi saurin taka mata birki, fatan ba zaka ji babu daɗi ba dan na yi mata faɗa ta rinƙa rufe maka sirrin ka? Kasan irin ku wayan da suka kware wajen iya soyayyar nan basa son a yiwa matansu faɗa".

Tana magana tana nufarsa "Kawo laptop ɗin na kai maka in da zaka zauna" ta faɗa dai dai lokacin da ta fariso wajen da yake tsaye yana kare mata kallo, hannu tasa zata karɓi laptop ɗin, daidai lokacin Umaisha ta fito cikin shiga Abaya baka da hijabi har kasa brown color sai plat shoe shima brown colo, tana riƙe da jakarta baka da bakin nikaf a hannunta

Ganin Rufee na ƙoƙarin karɓar laptop dake hannun Akil yasa Umaisha ta kariso da sauri, tana kokarin yin magana.

Bata kai ga buɗe baki ba ta ga saukar wani mahaukacin mari Akil ya sauƙe wa Rufee, ji kake yi dif kamar an ɗauke wuta haka Rufee ta ji, gaba ɗaya duniya ya tsaya mata cak, har wani taurari ta gani sun gilma mata ta cikin idanunta.

Sai da ta ɗauki 1mins sannan ta samu damar fara hawaye, wani uwar tsawa ya daga mata "Who are you?!!" Ƙasa ta zube a kan gwiwowin ta tana hawaye. Rai a matukar ɓace ya dawo da kallonsa kan A'afia, cikin tsawa ya ce "Wace kazama ce wannan? Kuma me ya kawota cikin gidannan?" murya na rawa Aafia ta ce "Kayi hakuri yaya Akil kawar mu ce ta school..." Ai bata kai karshen maganar ba ya tako zuwa in da take tare da ajiye laptop da wayar dake hannunsa ya hau dukan ta, haɗa hannayen ta dukka biyu ya yi ya riƙe da hannun sa ɗaya, ya ɗaga ɗayan hannun nasa ya fara bata maruka.

Hakan ma bai masa ba, sai da ya dakawa Umaisha tsawa a kan ta ɗauko masa belt nasa a ɗaki, da sauri ta wuce ɗaki dan ta ɗauko mashi, mamaki Akila take yi na me Aafia kuma ta mashi da yake dukanta haka. Umaisha na kawo belt ya karɓa ya hau dukan ta.

Da farko ta daure ba zata yi kuka ba, amma da ta ji duka mai kyau sai ga shi ta fara ihu, Rufee na ƙoƙarin guduwa ta bar palon ya yi saurin kwashe kafafunta da nashi kafar, haka ta zube ƙasa kamar kayan wanki. Ya haɗe su su biyun dukka ya musu dukan kawo wuka, sai kuka Akila da Umaisha suke yi sun rungumi juna, ga shi sun san idan ransa ya ɓaci ba mai iya tinkararsa sai Abba, ko Ammie tsoron shi take yi wani zubin, dan idan mutun ya je ma, zai iya haɗa wa da shi.

Sai da Akila taga da gaske idanuwansa sun rufe zai iya illata su Aafia akan laifin da basu san menene ba, hakan yasa Akila ta fita da gudu zuwa ɗakin Abba, dan tasan shi kaɗai ne zai iya dakatar da Akil.

Cikin mintuna da basu fi biyu ba, sai ga Akila da Abba sun dawo ɗakin, su Aafia kuwa sun daku iya dakuwa, a kan laifin da bai gaya musu ko laifin menene ba.

Da kyar Abba ya iya dakatar da shi, sai huci yake yana haɗa zufa.

"Akil me yafaru? Me suka yi maka haka?" Shiru ya yi yana haki ya kasa magana. "Akila kawo masa ruwa mai sanyi a fridge" da sauri Akila ta wuce tana tafiya tana waigowa domin bata taɓa ganin ɗan uwan nata cikin fushi haka ba.

Saman sofa ya zauna yana runtse idanuwansa kamar zai saka ihu yake ji, zuciyar sa


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login