Showing 30001 words to 33000 words out of 355604 words
a jikin ta sumul take.
Zuba mata ido Rimsha tayi tana kallon ta, har ta kammala aikin shafawa su Ayla maganain da ta taho da shi, sannan ta miƙe tana faɗin "Nan da minti biyar za su tashi, kuma za su tashi lafiya lou ba tare da wani ciwo ba" ta kai karshen maganar tare da juyawa zata bar wajen, cikin sauri Rimsha tace "mun gode mai taimako"
Wannan cool murmushi nata irin na Rimsha ta saki, har sai da dimple na ta irin na Rimsha ya bayyana a nitse tace "Ba sunana mai taimako ba, sunana Malika" tana kai karshen maganar ta wuce da sauri ta bar wajen, dawo da kallon ta kan su Ayla Rimsha tayi tana faɗin "Allah nagode maka, Malika kema mun gode miki"
Kamar yadda Malika ta faɗa haka su Ayla su ka tashi lafiya Lou, sun yi sumut da su, sai yar waige-waige su ke kamar ma su neman wani abun "Ayla sannun ko, Kausar kema sannu" Cewar Rimsha tayi maganar tana kallon su miƙewa zaune suka yi, suna zare ido kamar ma su neman wani abun, matsowa Rismha tayi ta riƙo hannun Ayla tana faɗin "Ayla akoi in da yake miki ciwo ne?" Girgiza kai Ayla tayi kafin tace "A'a babu" riƙo hannun Kausar ma Rimsha tayi ta tambaye ta, ko akoi in da ya ke yi mata ciwo, ita ma a'a tace, miƙewa Rimsha ta yi tana faɗin "To ku tashi muje ko?" a tare suka miƙe Ayla da Kausar suna jin kamar sun yi mafarkin an mu su duka, abun ya zama musu tamkar a mafarki, ita ma kuma Rimsha bata sanar da su cewa a zahiri ne ba a mafarki ba, sai ta kyale su kawai suka ci-gaba da tafiya.
Sun yi tafiya mai nisa kafin su isko wani karamin titi, lokacin karfe goma na safe zai yi.
Sun jima tsaye a bakin wannan ɗan karamin titi kafin su samu wani mota wanda ya ɗauko katako, irin wayan nan taxi ɗin ne, masu kirar mota 206
Cikin sauri Kausar ta daka tar da motar, dan sun gaji da tsayuwa a bakin titi bayin Allah, da farko kamar mai motar ba zai daka ta ba, amma ganin yanmata tsaye a wajen wannan daji yasa ya tsaya, cikin sauri Kausar ta karisa wajen nasa, su kuma Ayla da Rimsha suna tsaye.
Da harshen yarabanci Kausar ta yiwa mai motar magana, a kan ya taimaka ya kai su eyankorin, hakuri ya bata kasan cewar babu filin da zai ɗauke su su dukan su a motar nasa, cikin sauri Kausar tace masa, "Baba zamu zauna a gaba" dawo da kallon sa yayi wajen da Kausar ke nuna masa zasu zauna yace "Ku uku a gaban mota kuma kan kujera ɗaya" da sauri ta gyaɗa masa kai tana faɗin "Eh baba zamu zauna, dan Allah ka taimaka mana, idan ka wuce ba mu san ya za mu yi ba" jinjina kai yayi kafin yace "To shikenan ku shigo mu tafi" da sauri ta juya ta kwalawa su Rimsha kira, da yar gudun su, suka kariso wajen.
Ayla ce ta fara shiga sai Kausar, suka ɗaura Rimsha a saman cinyar su, saboda ita ce karama kuma bata da nauyi, dan yar siriri ya ce, sai kallon su mai motar yake kamar zai yi masu magana, sai kuma ya fasa ya kunna motar kawai suka bar wajen.
Sai satar kallon Rimsha yake ta cikin mirror taxi ɗin nasa, shi dai tun da yake bai taɓa kallon yarinya mai bala'i kyan Rimsha ba, musamman ma idan ta ɗan motsa ɗan karamin bakin ta, dimple nata ya lotsa, subhanallah idan mutun yayi wasa kyan Rimsha sai ya sa shi ya saki kan motar sa, duk da wuyar da ta sha na Daular Mutuwa ga kuma tafiyar da suka yi a dajin nan, duk da haka, ba wani canji a fuskar ta sai ɗan rama kaɗan da tayi, amma kyan ta na nan.
Shiru suka yi ba wan da yayi wa ɗan uwan sa magana, har suka isa eyankorin junction, a nan mai motar ya sauke su, kwance kuɗin dage ɗaure a igiyar rigar ta Rimsha tayi suka bawa mai mota, kin karɓa yayi yace suje dan Allah ya kawo su, sai murna suke, suka masa godiya tare da tsallaka titi suka nufi hanyar ogele, suna tafiya suna hira kaɗan kaɗan, jikin su duk ciwo yake musu.
Gaban wani ɗan ma ɗai-ɗai cin gida suka tsaya, gida ne na mai kuɗi dai-dai gwargwado, gaba ɗaya gidan rufi ɗaya ne, kun dai san yadda ginin yarabawa yake, basu cika yin fencing na gida ba, haka suke barin sa, basu da sirri komai a wangale ake yin sa, a waje suke girki wanke-wanke, wanki da sauran su.
Kausar ce ta sanya hannun ta ta fara knocking na kofar palon, dan na gaya muku dama ba fencing gidan, rufin ɗaku na ne kawai. Daga cikin ɗakin wata murya tace "Tani? Nbowa (waye ne? Ina zuwa)" shiru Kausar tayi tana tunanin yadda zata ga maman ta.
Sun kai 3mins tsaye a wajen kafin nan wata mata wadda da ka ganta kaga bahaushiya, kuma kaman ta ɗaya da Kausar, ita ce tazo ta buɗe kofar tana faɗin "Kilode (menene)"
Ihu ta kurma lokacin da idon ta ya sauka kan fuskar Kausar, rungume ta Kausar tayi, ita ma matar ta rungume Kausar tana faɗin "oh oluwa" kun san dai yadda shaukin soyayya tsakanin uwa da ƴa yake, musamman a ce sun jima basu haɗu ba, abun ba'a cewa komai, dukan su hawaye suke sun rungume juna, sai ihu iya Kausara take tana kiran oluwa oluwa, kan kace me makota sun tattaro cincirindon dan suzo su ji lafiya iya Kausara ke ihu haka.
Ganin Kausar yasa suma suka fara na su ihun murnan, su Rimsha sun tsorata sosai da jin yadda suke ihu, basu san yarabawa bane, yarabawa idan suna magana cikin kwanciyar hankali ma sai ka ɗauka faɗa ake, saboda Allah ya zuba musu murya mai sauti, har sama idan suna magana, ina ga kuma abun murna ya samu, ai shikenan kuma sai dai wanda bai saba ji ba ya toshe kunne
Gaba ɗaya sun cike anguwar da ihun Kausara ta dawo Kausara ta dawo, wannan ya ja Kausar ta nan wannan ya ja ta ta can, farinciki a wajen su ba'a magana, babu wanda ya kula da Rimsha da Ayla, Allah sarki bayin Allah sai bin su kawai suke da ido, sun ga abun da yafi karfin su.
Almost 20mins ana wannan ihun murna na dawowan Kausara kafin iya Kausara ta jata zuwa cikin gida tana faɗin suje tayi wanka taci abinci sannan tazo ta basu labarin ina ta ɓata, suma makotan kowa ya wuce gidan sa, suka bar su Rimsha tsaye sun rasa madafa, sai zare ido suke gwanin ban tausayi.
Har sun shige cikin gida, Kausar ta fito da gudu tana faɗin "Iya friends ɗina" bin ta da ido iya Kausara tayi tana kallon ta, har ta fito wajen palon.
In da ta bar su Rimsha tsaye wajen ta fito ta same su, sun kasa ko motsawa Allah sarki, tunanin nasu iyayen kawai suke, ita Rimsha tana tunanin ita ma idan ta koma gida kila haka su Jehan za su yi mata, ita kam Ayla ƙoƙarin ɓoye hawayen dake ƙoƙarin zubo mata take, dan ganin Kausar cikin yan uwan ta, ya jefa ta cikin tashin hankali, dan ita ba ma ta da yan uwan bata da kowa sai maman ta kawai.
Suna tsaye sunyi jugum jugum babu wanda ya kula su, Kausar tazo ta jawo hannayen su tana faɗin "Kuzo muje?" Bin ta su kayi zalalau-zalalau zuwa cikin gida, duk jikin su a mace, ji suke kamar su yi ta kuka kada su dakata
"Kausar su waye wayan nan?" Iya Kausar ta tambaya cikin harshen Hausa "Iya friends ɗina ne tare muka zo ai" kallon tsab iya Kausar ta musu kafin tace "Ban gane tare kuka zo ba? Ina za su je?"
Saman sofa dake cikin palon Kausar ta zauna tana faɗin "Iya nan mana suka zo, basu da kowa ne shiyasa" tsawa iya Kausar ta daka mata "Dan basu da kowa, sai ki kwaso su ki kawo ma na su? Tukun nan ma daga ina kuke?" Cikin sauri Kausar tace "Daga Daular Mutuwa muka fito"
Har wani bonsin iya Kausar tayi jin an ambaci sunan Mutuwa, dafe kirji tayi tana zare ido tace "oloni Kausara Mutuwa kuma?" Gyaɗa mata kai Kausar tayi tana faɗin "Eh iya Daular Mutuwa" "kaiii Kausara ki dai na kiran Mutuwar nan, wannan suna mai sanya tashin hankali haka, tukun nan ma ai na kuka samu wannan suna?" Tana magana tana zare ido ta dafe kirji "iya gaskiya na faɗa miki daga Daular Mutuwa muka fito, Daular da ba'a shiga a fito a raye, mu Allah ne ya tsare muna da sauran kwana" hannu biyu duka iya Kausar ta ɗaura a kan ta, ta kara zaro idon nan waje, nan take ta birkice musu kamar wadda notir ɗin kan ta ya kwance, cikin sauri ta dawo kusa da Kausar ta zauna, kun san dai yadda yarabawa suke idan suka tsorata "Yanzu Kausar Mutuwa ma har da Daula yake da shi? Na shiga uku ni jummai, Kausara anya kinji me kika faɗa kuwa?" Gyaɗa mata kai Kausar tayi, sannan ta fara bata labari cikin Daular Mutuwa da yadda suke yanka mutane, a zabure iya Kausar ta miƙe da karfi tace "Kai kakai kakai Kausara bari bani wannan labari, bar shi kada ni ki kashe ni, ke basu kashe ki a Daular Mutuwa ba ni kuma zaki kashe ni a nan da labari, ni wlh bana son ji, ya isa haka, bayin Allah sannun ku eyeee wannan bala'i haka, gaskiya na tausaya mu ku" tana magana tana zare ido kamar idon ta zai faɗi kasa, dariya Kausar tayi tace "Iya wannan fa baki ji ko kwata daga cikin labarin abun da muka gani a Daular Mutuwa ba, har da masu canza ido fa" ihu iya Kausara ta kurma tana faɗin "oloni Kausara zan wurgaki waje idan baki dai na kiran wannan bala'i ba, ki dai na kira mun Mutuwa tsirarar ta a nan" abun ma dariya yaso bawa Rimsha da Ayla, ganin yadda iya Kausar ta birkice musu lokaci guda, daga jin sunan Daular Mutuwa, wanna da ita aka kai Daular Mutuwa tsoro da fargaba ne za su kashe ta, mata sai bala'i tsoro, ji yadda take zare ido, tana bahaushiya amma zaman ta da yarabawa yasa ta dawo sak su, ta koyi ɗabi'un su da komai nasu, idan ba kaga fuskar ta na hausawa ba, bazata taɓa cewa bahaushiya bace, duk wani attitude nata na yoroba ne yanzu.
Iya Kausar kam daga jin zancen Daular Mutuwa sai ta nitsu tayi hankali har da yiwa su Rimsha sannu. "Iya ina boder Jami'u?" Cewar Kausar "Baki tambayi dadyn ki ba, kina tambayar boder Jami'u ko?" Dariya Kausar tayi kafin tace "Ai zan manbaye shi ina suke?" Tayi maganar tana miƙe wa ta nufi wani ɗaki mai kama da kitchen "Daddy'n yana Lagos, Jami'u kuma yana cikin Ilorin" iya Kausar ta bata amsa, already Kausar ta shige cikin Kitchen abun ta.
Tukunyar abinci ɗungurungum na shi ta ɗauko , ta dawo palon ta yi zaman yan bori a kasan carpet, ba wanke hannu ba komai ta fara dumbulan abincin tana kai loma bakinta,
"Kausar ba zaki kira friends na ki su zo ku ci bane?" Cewar iya, kallon su Kausar tayi, duk sun yi tsuru-tsuru da su, kamar wasu marayu, kamar biri yana jin matsanancin yinwa, haka suka yi da fuskokin su "Ayla kuzo kuci abinci mana" ta faɗa tana tura abinci a baki, jolof rice ne ya ji kayan haɗi sai kamshi yake, dan ba karya yarabawa sun kware wajen iya girki
Haushi yasa Rimsha tace bazata ci ba, dan a ganin ta Kausar ta wulakanta su ne, ga shi tana jin matsananciyar yunwa saboda jiya ma bata iya cin abincin da matar sarki ta ba su ba, amma ba zata ci abincin nan dake gaban Kausar ba, dan Kausar ta raina su, kuma har ga Allah ita Rimsha bata ɗaukan wannan wulakanci, karku manta duk da Rimsha take shiru-shiru mai sauƙin kai, jinin Nawazudden ne ke gudu a jikin ta, kanwar DPO Jehan ce, family Nawazudden basa ɗauran raini da wulakanci ko kaɗan
Ita ma Ayla ganin Kausar taƙi cin abincin yasa ita ma tace ta ƙoshi, Kausar ko a jikin ta dan sun ce sun ƙoshi, ta ci-gaba da ɗura abincin ta kawai, dan ita bata da burin da ya wuce taci ta ƙoshi, bata wasa da abinci, sannan ko wani irin wulakanci zaka mata, ka mata in dai zaka ba ta abinci to zata ɗauka
Ita ma iya Kausar ba ta wani damu ba, dan su Rimsha sun ƙi cin abinci, haka suna ji suna gani, suna jin matsanancin yunwa haka Kausar taci abincin nan iya cin ta ta mai da sauran kitchen bayan ta ƙoshi, sai wani ƙugi cikin su yake, musamman idan suka shaƙi kamshin abincin sai ka ji cikin su na kulululu saboda bala'i yunwa, Allah sarki bayin Allah.
Bayan Kausar ta mai da sauran abincin Kitchen ne ta dawo tace su tashi su je ɗakin ta su ɗan huta, ba musu suka ta shi, tayi gaba suka bi bayan ta
Ɗaki ne mai ɗan girma, dan ginin yarabawa suna yin sa da girma ɗakunan su, ƙaramin gado ne guda ɗaya a ciki, sai yar drawer saka kaya shikenan. Saman gadon Kausar ta haye tana faɗin "Yau zan yi barci mai daɗi Alhadulillah" gefen gadon Ayla da Rimsha suka zauna suna bin ɗakin da kallo.
To masu karatu sai Allah ya sa da mu bayan na dawo hutu, ku ci-gaba da yiwa Rimshan daddy addu'a, dan har yanzu da sauran ta, bata fita ukubar rayuwa ba, baiwar Allah
💞💞TRIPLET'S💞💞
🌹🌹Episode 11-12🌹🌹
Ɗaki ne mai ɗan girma, don ginin Yarabawa suna yin sa da girma ɗakunansu, ƙaramin gado ne guda ɗaya a ciki, sai 'yar drawer saka kaya shi ke nan. Saman gadon Kausar ta haye tana faɗin, "Yau zan yi barci mai daɗi Alhadulillah!" Gefen gadon Ayla da Rimsha suka zauna suna bin ɗakin da kallo.
"Kausar ina ne toilet naku? Ina son in je in yi wanka." Cewar Rimsha. Miƙewa zaune a tsakiyar gadon Kausar ta yi tana turɓune fuska ta ce, "Idan kin fita falo ta wannan hanya da na bi na je na ɗauko abinci, to ta nan za ki bi toilet na wajen."
Miƙewa Rimsha ta yi tana faɗin "Ayla bari na je na yi wanka." Ayla kam ta kasa magana baiwar Allah saboda tsananin yunwa da take ji, haka ta zuba wa Rimsha waɗannan idanun nata da suƙa ƙanƙance saboda wahala tana kallon ta har ta fice daga ɗakin, shiru suka yi daga ita har Kausar ɗin, kowa da abin da yake tunani.
💞💞After some minutes💞💞
Ɗaure da towel nasu da ta ɗauko a toilet ɗin Rimsha ta shigo cikin ɗakin Kausar, yadda ta fita ta bar su haka ta dawo ta same su, tana shigowa Ayla ta miƙe tana faɗin, "Ni ma bari na je na yi wankan ina zuwa." To, kawai Rimsha ta amsa mata da shi, sannan ta zauna a gefan gadon tana kokarin mayar da kayan dattin ta da ta cire kafin ta yi wanka, duk bala'i datti ya canza wa kayan launi, ba za ka taɓa gane cewa wannan pink blouse gown ɗin nata mai bala'i kyau da ta fita da shi gida ba ne, saboda tsananin dattin da ya yi, ya zama launin kasa, har wani maiƙo-maiƙon datti jikin rigan yake.
"Meesha kada ki saka kayan dattin nan kin ji? Ki tashi ki duba kayan da kike so a cikin drawer kayana ki saka." Cewar Kausar, da kamar Rimsha za ta ƙi, sai kuma ta tuna kayan nata warin datti yake sosai, don haka sai ta hakura ta miƙe ta nufi drawer kayan Kausar.
Mafi yawancin kayan dake cikin drawer wandunan Jeans ne da T-shirt, sai gown na kanti da na materials, atamfofi ƴan kwaranni ne a ciki, duk wanda ya san Yarabawa ya san su da sanya ƙananan kaya, daga yaransu har manya, kai har tsofaffi, ba su damu da atamfa ko leshi ba, idan ka gan su da atamfa ko leshi to biki za su je, ko Walima ko dai wani shagali, amma ban da haka za ka ga jibgegiyar mata ga tsawo ga ƙiba, sai ka gan ta da wandon Jeans ya matse ta kamar cinyoyin ta za su fasa wandon su fito waje, kana ganin komai na daga halittarta, a haka suke yawo a cikin gari, a haka suke rayuwarsu ba ruwansu, ba ruwan kowa da kowa, sai wanda ka shigo da shi cikin rayuwarka.
Da kyar Rimsha ta laluɓa ta fito da wata doguwar riga mai faɗi kaɗan, ita ta sanya a jikinta, duk da Kausar ta fi su jiki, rigar ta zauna wa Rimsha sosai a jikin ta, saboda Allah ya mata wata irin halitta wanda Hausawa ke cewa karuwan jiki, komai ta sa zama yake a jikinta ɗas kamar don ita aka yi shi.
After some hours💞💞
Sun gama shirin su tsab, har ita ma Kausar ta yi wanka, ta sha wandon jeans da T-shirt, kayan sun matse ta sosai, sai wani washe baki take, ta ci ta ƙoshi ta bar su Rimsha da jin bala'in yunwa.
Suna zaune a falo, yayin da ita kuma Iya tana cikin kicin tana ƙoƙarin girka abincin rana. Kamar wadda aka tsikara Kausar ta miƙe tana faɗin, "Ku zo mu je ku ga garin Yarabawa yau kam, tunda Allah ya kawo ku." Da farko Rimsha ta ce, a'a ita ba za ta je ba, sai da Ayla ta sa baki sannan ta hakura ta miƙe suka fito a tare, sai wani murmushi Kausar take kamar ba lafiya ba.
Miƙar hanya suka yi zuwa Eyankorin Junction, sai surutu Kausar ke zuba musu, ban da um da uhm ba abin da suke bin ta da shi, saboda yunwa suke ji, ba bakin yin magana sosai, gara ita ta ci ta ƙoshi.
Duk wanda suka wuce in ma mace ko namiji sai ya kara waigawa ya kalli Rimsha, ga shi yanayin yadda take ta fi kama da mai jin barci saboda kasalar da yunwa ta sauke mata, sannan kuma ta