Showing 33001 words to 36000 words out of 355604 words

Chapter 12 - Triplets Book 2 Hausa Novel Complete

10 Dec 2024

2750

sanya takalman Kausar mai ɗan tudu kaɗan a kafarta, hakan yasa take jan kafa a hankali. Jama'a sai tambayar Kausar suke yaushe ta dawo, ina kuma ta samo yar Indiya, wasu ta ba su amsa wasu kuma ta share su

Sun zo za su wace wasu gidaje da ke jere kamar tagwayen gida, komai na ginin iri ɗaya, wata yarinya dake zaune a tsakanin gidajen tana wasan ƙasa ne ta ce "Kausar iya Ganiyu ta fara zane, masu kyau." Ƴar yarinya ba za ta wuce shekara bakwai ba, cikin sauri Kausar ta ce, "Da gaske kike Waliya?" Gyaɗa mata kai yarinyar ta yi tana duƙe tana wasan kasarta.

Cikin sauri Kausar ta juya tana faɗin, "Meesha ku zo mu je Iya Ganiyu ta yi mana zane." Girgiza kai Rimsha ta yi tana faɗin "Ni Kausar ba na son yawon nan mu koma gida." Ƴar dariya Kausar ta yi kafin ta ce, "Kada ki damu idan mun je wajenta, ta mana zane sai mu dawo gida." Shiru Rimsha ta yi ba ta sake yin magana ba, wucewa gaba Kausar ta yi suka bi bayanta, kamar raƙumi da akala, duk in da Kausar ta yi haka suke daurewa ga yunwa suna jan ƙafa su bi bayanta, ita kuwa Kausar har wani taku take ta ci ta ƙoshi abinta.

Kafin su kai gidan iya Ganiyu suka iso ko wani shagon kanti. "Kausar bari na sayi drinks a nan shagon kin ji?" Cewar Rimsha ta yi magana tana fito da wannan ₦2,500 ɗin da sarki da matarsa suka ba su.

Kausar ko a jikinta, wai an yakushi kakkausa ta ce, "Ki saya mana Meesha, duk abin da kike so ki saya." Miƙa wa Ayla dubu ɗaya Rimsha ta yi tana faɗin, "Ayla ke ce babba ki riƙe wannan, ni da Kausar kuma sai mu raba ragowar ₦1,500 ɗin." Cikin sauri Kausar ta ce, "A'a ni ba na so, ni da na dawo gida, na bar muku tunda ni na iso gida." Kallon Ayla Rimsha ta yi, abin gwanin ban tausayi, murya a raunane saboda yunwa ta ce, "To shi ke nan Ayla ga ɗari biyar ɗin nan, ki haɗa ni kuma zan riƙe 1k Kausar mun gode." Girgiza kai Ayla ta yi tana faɗin "Ai yanzu tsakanin mu babu zancen raba kuɗi, ki bar kuɗin duka a wajenki, ki riƙe mana, idan buƙatar su ta taso sai mu yi amfani da su." To, kawai Rimsha ta ce tare da karɓar kuɗin ta haɗa, sannan ta shige cikin shagon bakinta ɗauke da sallama.

Sai kallon ta mai shagon yake, da Yarabanci ya ce da Kausar "Kausar ina kika samu wannan ƴar Indiyar?" Kallon banza Kausar ta masa ta ce, "Sadudin amma kamar na ce kada ka sake yi mini magana kafin mu yi tafiya da Iya ko?" Shi ma kallon sama da kasan ya mata kafin ya wuce ya je ya ɗauko wa Rimsha Coca Colar gora biyu, masu sanyi daga fridge ɗinsa, sannan ya haɗo mata da biscuits guda biyu, kamar yadda ta buƙata.

Karɓa Rimsha ta yi tare da miƙa masa 1k da ke ɗayan hannunta, karɓa shi ma ya yi ya ɗauko canjin 400 ya miƙa mata, ta karɓa ta fito, ta zo ta miƙa wa Ayla Coca Colar guda ɗaya da biscuit ɗaya, ita Kausar ta ce ba ta buƙata, karɓa Ayla ta yi, suka wuce suna hira

"Ku sha lemon mana Meesha." Cewar Kausar, kallon ta Rimsha ta yi kafin ta ce "A'a ya za a yi mu ci abu muna tafiya a kan hanya?" Dariya Kausar ta yi tana faɗin, "Meesha nan fa ƙasar Yarabawa kuke, ba cikin Hausawa ba ne, mu a nan babu ruwanmu da kowa, ko a tsakiyar titi kika ji za ki iya cin abin da kike so za ki ci, ba ruwan wani da ke, ke ba ki ga wancan gidan da muka wuce in da Waliya ke zaune tana wasan nan ba ne? Ba ki ga a waje suke girkinsu ba ne? Ku Hausawa ku ne kuka san wani abu wai sai an shiga gida ake wasu abubuwa, mu ba ruwanmu da hakan, a nan kowa yana da ƴancin ya yi abin da yake so." Shiru suka yi dukansu, don daga Rimsha har Ayla babu wanda zai iya cin abinci a kan hanya, don ba su saba ba, ita ma Kausar ɗin da ta ga ba su da ra'ayi cin abu a kan hanya, sai ba ta takura musu ba, don ta san Hausawa ne su, ta sha zuwa garuruwansu ta san yadda suke rayuwar daban da ta Yarabawa, su Hausawa suna siririnta abubuwansu da dama, amma su Yarabawa babu ruwansu, abin da suka yi ra'ayi za su yi kuma ko a ina ne a cikin garinsu.

Da sallama suka shiga wani gida, wanda ba za a iya ce masa gida kai tsaye ba, sai dai a ce ɗaki, domin babu katanga gidan, ɗaki ɗaya ne a wajen kamar shago, sai wani waje daga ɗan nesa da ɗakin wanda aka kewaye da bulo, ba gini aka yi ba, an ɗaura bulon ne ɗaya kan ɗaya, kuma ba har sama ba, iya rabi aka yi shi kawai, kana tsaye daga ɗan nesa ma kana iya hango abin dake cikin wajen, murhun girki ne da gingima-gingiman tukane da sauran kwanuka, da alama shi ne kicin na masu gidan.

Ganin ba kowa a wajen yasa Kausar ta sake kwaɗa sallama, wata mace ce mai ƙiba ta fito daga cikin ɗakin wadda da ka gan ta ka ga asalin Bayerabiya. Cikin harshen Yarabanci ta yi musu sannun da zuwa, sai murmushi take saboda ta san Kausar, da fara'a ita ma Kausar ta amsa mata tare da gaishe ta.

Bayan sun gama gaisawa ne Kausar ta sanar da ita abin da ya kawo su. To matar ta ce tare da wuce wa ta koma cikin ɗaki, su kuma suna tsaye, Rimsha da Ayla sai faman bin garin da kallo suke, ita kuma Kausar sai wani murmushi take kamar ba lafiya ba.

Jim kaɗan matar ta fito hannunta riƙe da wata baƙar gora mai ɗauke da wani baƙin ruwa kamar tawada, ɗayan hannun kuma ɗauke yake da wata ƙatuwar kujera.

Ajiye kujerar ta yi a ta gefe da bakin kofar ɗakin nata, sannan ta zauna tana faɗin me za ta zana musu, Rimsha ta ce ita kam ba ta so, ganin Rimsha ta ce ba ta so, ya sa ita ma Ayla ta ce ba ta so, kuma da ma ita Ayla ba ta sa a ranta za ta yi wani zane ba, da ma dai ta ce idan Rimsha ta yi, ita ma za ta ce a mata, idan kuma Rimsha ba ta yi ba, to ita ma ba za ta yi ba.

Kausar kam cike da zumuɗi ta miƙa hannunta ta bayan hannun ta ce a zana mata sunan boda Jamiyu, kama hannun nata matar ta yi ta fara zana mata da wani abu mai kama da fensir.
Duk wanda ya san asalin Yarabawa ya san mafi yawancinsu da irin wannan zane, na zana sunan miji a jikinsu da wannan abu kamar tattoo ɗin amma ba tattoo bane.

Su Rimsha sun zuba ido suna ganin yadda matar take zana wa Kausar sunan boda Jamiyu a hannunta, lokaci guda Rimsha ta ji sha'awar abin har cikin ranta, cikin sauri ta ce "Kausar ki ce ni ma ina so a zana mini."

Murmushi irin na mai jin matsanancin yunwa Ayla ta yi kafin ta ce, "Me za a zana miki to? Kin ga dai ita Kausar boda Jamiyu ta ce kuma daga gani wannan boda Jamiyu shi ne mijin da za ta aura, don tun da muka zo nan ba ta da wata magana sai boda Jamiyu, ko dai ke ma boda Jamiyun za a zana miki ne? Ko kuma sunan ki Rimsha? Don na san dai ba ki da saurayi." Cool murmushi Rimsha ta saki, wanda sai da ya sanya kyawawan haƙwaranta bayyana, sannan wannan kyakkyawan dimple ɗin nata ya lotsa gwanin ban sha'awa, a nutse ta ce, "Yanzu Ayla sai ki rasa waye za ki ce a zana mini sai boda Jamiyu? So kike Kausar ta sumar da ni ne yadda take ji da wannan boda Jamiyu, ni har na ƙosa ya dawo na gan shi, in ga waye wannan Kausar ta dame mu da zancensa." Ƴar dariyar yunwa Ayla ta yi kafin ta ce, "To ai na ga ke ba ki da saurayi ne, to ko dai sunanki za a zana miƙi ne?" Shiru Rimsha ta yi tana ta murmushi ita kaɗai, kamar ba lafiya ba, ba ta sake ce da Ayla ko uffan ba, shiru ita ma Ayla ta yi, suka zuba wa Kausar da matar ido kawai suna kallon zane. Duk hirar da suke yi Kausar na jin su sai dai bata tanka su ba.

Bayan an gama yi mata zanen, Rimsha ta miƙe ta je gaban matar ta tsugunna tana faɗin "Kausar kin faɗa mata ne?" gyaɗa kai Kausar ta yi alamar e.

"A ina za a zana miƙi? Kuma me za a zana miƙi?" Cewar matar, ta yi maganar cikin harshen Yarabanci, juyowa Rimsha ta yi tana kallon Kausar tana jiran Kausar ta fassara mata, fassara mata abin da matar ta ce Kausar ta yi, wani haɗaɗɗen murmushin Rimsha ta sake saki a karo na biyu, sai kallon ta su Kausar suke Ayla kam mamaki irin murmushi da Rimsha take ya hana ta yin magana

Miƙa wa Ayla Coca Colar da biscuit dake hannun ta Rimsha ta yi, bayan Ayla ta karɓa, sai ta sanya hannunta, ta cire mayafin kanta, ta ɗan zuge zip ɗin rigarta, ƙasa kaɗan, ta zamo da hannayen rigar nata zuwa kafaɗar ta, su Ayla dai sun zuba ido suna ganin ikon Allah, suna jira suga me Rimsha za ta yi ne wai.

Bayan ta gama zamo da hannun rigar ta zuwa kafaɗar ta sai ta matsowa da matar kirjinta, ta ce a rubuta mata "The General Of The Army Romeo'', Tashin hankali babbar magana, kallon-kallon su Ayla suka fara yi wa junansu ita da Kausar, tunani suke anya Rimsha ba ta samu matsala a ƙwaƙwalwarta ba kuwa? Ta rasa sunan da za ta ce a zana mata sai sunan wannan kafurin Bature da bai san da zamanta a duniya ba, kuma ma ta rasa a ina za a zana mata wannan suna sai a kirji, kai lallai ya tabbata Rimsha ba ta da hankali.

Suna can suna zancen zuci su ba su sani ba Iya Ganiyu ta gama zana wa Rimsha rubutun nan a kirjinta, da kananan rubutu, saboda tsawon sunan.

Su Ayla ba su ankara ba sai jin muryan Rimsha suka yi tana faɗin "A kasan The General Of The Army kuma a rubuta mini, GAR." Tana magana tana kara sauƙe wuyan rigar nata zuwa saman breast nata, tashin hankali da ba a saka maka rana, Rimsha fa da gasken-gaske take, babu wasa a lamarin nata ko kaɗan, haka kuwa matar nan ta rubuta mata sunan Romeo kamar yadda ta buƙata, ga shi ruwa baya wanke abin, idan aka zana maka, tofa ya zauna ke nan, idan kana son gogewa sai an maka aiki a wajen, yau ga ikon Allah.

"Ayla me za a zana miƙi?" Cewar Rimsha, girgiza kai Ayla baiwar Allah ta yi tana faɗin, "Ni jikar mutumin da ban san shi ba, ku rufa mini asiri, ni ba na so, to waye ma nake da shi da har zan zana sunansa a jikina? Sai dai idan sunanki ke da Kausar za a zana mini." Zaro dara-daran idanu Rimsha ta yi ta ce, "Ba mu gane ba? Kamar yaya sunana ni da Kausar? Ki yi mana bayani."

Murya a raunane Ayla ta ce "Da kuke gani na ɗin nan, mamata kawai na sani a duniya, ita ma ban san asalin sunanta ba, don tun da na girma take cikin ciwo har na bar wajenta, babana ko alamar mai kama da shi ban taɓa sani ba, sunansa kawai nake ji, a takaice ma ƴan unguwarmu ce mini suke ba ni da baba wai shegiya ce ni." Ta kai karshen maganar tare ta miƙewa tana kokarin goge hawayen da ke zubo mata, Allah Sarki!

Cikin sauri Rimsha sarkin tausayi ta miƙe ta nufe ta tana faɗin, "Ki yi hakuri Ayla, ki yi wa baba addu'a Allah ya jikan sa kawai." Rungume Rimsha ta yi ta saki kukan da ta jima tana ɓoyewa, "Don Allah Ayla ki daina kuka kin ji ko, addu'a kawai za ki yi wa baba Allah ya jikan shi da rahma."

Cikin kuka mai tsuma zuciyar mai sauraro Ayla ta ce, "Meesha waye ya ce miki babana ya rasu ne?" Hawaye ita ma Rimsha ta fara yi tana faɗin, "To idan bai rasu ba yana ina? Me yasa ba ki san shi ba?" Matsowa ita ma Kausar ta yi ta rungumo Ayla tana ɗan bubbuga bayanta alamar rarrashi, ita dai iya Ganiyu kallon su kawai take, da yake ba ta jin me suke faɗa sai ta bi su da ido kawai, don wannan al'adar Yarabawa ce, in dai ba kai ka kira su cikin magana ba, tofa ko kana yi ba za su saka maka baki ba, musamman ma idan ba da yarensu kake yi ba sai su yi banza da kai.

"Rimsha babana yana nan da ransa, bai mutu ba, amma jama'ar unguwarmu suna ce mini ni shegiya ce, na tambayi mamana ina babana ta ce mini yana nan kuma ba ƙaramin mutun ba ne, babba ne a kasar nan, babba mai faɗa a ji ma kuwa. Sai dai kuma ban taɓa ganin shi ba, ban taɓa sanin inda yake ba, jama'a shegiya suke kira na, mun rayu cikin takaici da ukubar rayuwa, na yi fama da mamana ta faɗa mini me yasa ta rabu da babana, amma ta ki faɗa mini, ta ce babana yana da kuɗi sosai amma kuma ni da ita mun rayu cikin talauci babu cin yau bare na gobe, babu makaranta, wahala kan wahala, wani lokaci ma sai na ji gwara mutuwa da wannan rayuwata" Ta kai karshen maganar tare da sakin kuka mai sauti.

Ganin sosai Ayla take kuka ne yasa iya Ganiyu ta miƙe ta fara rarrashin ta, duk da cewa ba ta san a kan me suke magana ba, ta lura yaran da suna cikin damuwa.

Da kyar suka samu Ayla ta yi shiru, tare da taimakawar Iya Ganiyu, bayan Ayla ta yi shiru ne Kausar ta tambayi Iya Ganiyu nawa ne kuɗinta na zane, don su biya ta su koma gida. Kin faɗa musu kuɗin ta yi, ta ce su je ta yafe musu, godiya sosai suka mata sannan suka wuce, Kausar ce ta ɗauka musu Coca Colarsu, don Ayla ta yasar da shi lokaci da take kuka.

Ko da suka koma gida a falo suka samu Iya Kausar tana zaune tana kallon Yoruba Film. Zama suka yi kusa da ita, da kyar su Rimsha suka iya shan Coca Colan da biscuit ɗin, sai shasshekar kuka tare da ajiyar zuciya Ayla take.

Matsowa kusa da su Iya ta yi ta ɗan shafa kan Ayla ta ce "Me ya same ki kayi kuka?" Kausar ce ta yi maza ta cafe zancen ta fara ba wa Iya labarin abin da ya faru, sosai Iya ta tausaya mata, sannan ta tambaye su yadda aka yi suka bar gidan iyayensu, Rimsha ce ta fara gaya mata cewar ta fito sayan ashana ne ƴan Daular Mutuwa suka ɗauke ta, sosai Iya ta tausaya mata tare da ba ta hakuri.

"Ke kuma Ayla ba ki faɗa mana ya aka yi kika bar wajen mamanki ba?" Cewar Iya, ɗaukar last biscuit da ya rage a cikin ledar Ayla ta yi, ta kai bakinta sannan ta ce "Tun da na taso na girma na yi wayo, mamana take cikin rashin lafiya, ba ta iya fita ko tsakar gida, ni nake zuwa na yi bara na samu mana abinci na kawo na bata ta ci a baki, idan za ta je banɗaki ni nake taimaka mata ta je, ba ta iya miƙewa da kanta, sai an taimaka mata, gidan da muke haya kuma, mu kaɗai ne a cikin gidan, babu kowa, ba zan taɓa manta wata ranar Laraba ba shekara uku cikin na huɗu da suka wuce, ranar jikin mamana ya tsananta, na dawo daga wajen bara na same ta tana wani irin numfashi kamar za ta mutu, sai kuka take, na ji tsoron kada ta mutu ta bar ni, sai na fito da gudu don na je na nemo wanda zai taimaka ya duba mini ita, a baya kafin na fara bara, duk inda na je neman taimako sai suce sai na basu kaina kafin su taimaka mini, mamana kuma ta tsawatar mini a kan hakan, ta ce ko mutuwa za ta yi kada na yarda na sayar da mutuncina, shi yasa na daina neman taimakon kowa a layinmu, sai dai na je wajen masu barar bakin kasuwa na zauna na yi bara. To wannan ranar Laraba na fito a gigice kamar mahaukaciya ina neman wanda zai taimaka wa mamana ya duba mini me ke damun ta, na je wajen mutane da dama amma ba su kula ni ba, don suna tunanin kuɗi nake so, na yi tafiya mai ɗan nisa ina neman taimako, har na bar layinmu. A gaba da layinmu na ci karo da wani mai ƙatuwar mota yana tsaye, ban yi wata-wata ba na karasa wajensa, har kasa na duƙa a gabansa ina haɗa shi da Allah da ya taimake ni ya zo ya duba mini me ke damun mamana, bai musa mini ba, ya ce na shiga mota mu je ya gan ta, na ruɗe na kiɗime ba na ganin komai sai mamana, hakan yasa na shiga motar, don mu je ya taimaka wa mamana, ashe ɗan Daular Mutuwa ne, shi ke nan tun da na shiga motar ban kara sanin inda nake ba, sai buɗe ido na yi na gan ni cikin Daular Mutuwa, na sha wahala fiye da tunanin mai tunani, shekarata kusan huɗu a can, babu kalar azabar da ban gani ba, ba irin tashin hankalin da ban gani ba, a gaban ido na ake kwakwalewa yara ido, a yanke wa mata nono da gaban su, baba da kuke ganin nan,


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login