Showing 333001 words to 336000 words out of 355604 words

Chapter 112 - Triplets Book 2 Hausa Novel Complete

10 Dec 2024

2842

ya fice daga Palon dan ya ba su waje su sha hirarsu.

Bayan Hajiya Batula ta kai Ayla ta dawo, nan fa suka ba ke hira su uku, Abbi, daddy, da kuma ita Hjy Batular, sai hiran baya suke yi.

Misalin karfe 6:30 Imran ya shigo tare da Rimsha, yadda su Akila suka bar su Hjy Batula haka su Imran suka zo suka same su.

Tambaya Imran ya yi akan ina su AKILA, suna sama Abbi ya bashi amsa, cewa Rimsha ya yi akan ta bi su sama su zauna tare shi kuma bari ya duba Irfan yana zuwa. Da haka suka rabu, sai kallon Rimsha Hjy Batula take yi, ɗazun ribibi sun yi yawa, bata samu damar ganin Rimshan ba sai yanzu da su Nawid suka tafi, komai ya saitu.

"Batula lafiya kike kallon Rimsha haka?" Cewar Abbi, ajiyar zuciya ta sauƙe kafin ta ce "Wlh ta yi mani kama da Baban su HAROON ne, sosai fa shiyasa nake kallonta".

"Babansu Haroon kuma?" Cewar Daddyn Jelly, E ta amsa da shi. "To ko dai suna da dangantaka ne?" Cikin sauri ta girgiza kai tana faɗin "Kai ina baban su Haroon ba shi da wasu bakin ƴan uwa da ban sansu ba, kama dai ce kawai, shima kamar ai hancin ne da ido sai yanayin fuska".

To masu karatu kada ku mance Mummy'n Rimsha ƴan uwan mahaifinta ƴan Maiduguri ne, kuma a halin yanzu can ta tafi neman ƴan uwan nata, zata iya yi wu suna da alaƙa da mijin Hjy Batula, mu dai je zuwa dan jin yadda wannan cakwakiya zata warware mana.

Haka suka ci-gaba da yin hirarsu while su kuma ƴan matan suna sama suna zuba iya shege san ransu, AKILA ta tasa su a gaba tana koya masu shagwaɓa kirsa da kisisina na jan hankalin miji, Aunty dai ta saki baki tana kallon yadda Akila ke zuba masu lecture.

Riƙo kunnan jelly da kyau Akila ta yi tana faɗin "Wlh ki natsu ki sanya mani yayana cikin farinciki, kin san dai yanzu ba zan bi bayanki ba sai an buga football, idan yaya Imran ya cinye kwallon sai na dawo bayanki, amma dai yanzu gaskiya ina bayan ɗan uwana, ki saurareni da kyau, fagen shagwaɓa ba sai na koya maki ba wannan kece shugaba, kin kware ta wannan hanya, sai dai mu koma salon iya magana, iya magana yana sanya miji ya yi abu ko bai yi niya ba, idan kina magana da shi kuma ki rinƙa ɗan yin wasu abubuwa kamar karamar yarinya, hakan zai ja hankalinsa ba kaɗa ba, amma fa ki tabbar kin iya yin hakan sosai ta yadda zaki sanya shi jin daɗi ne ba wai ki ɓata mashi rai ba, dan wata idan ance ta yi abu kamar yarinya sai ta je tana yi mashi shirme da hauka tasa ya ji kamar ya ɗauketa da marin da sai ta suma a wajen dan haushi, to na dai gaya maki ba haka ake yi ba, yanzu idan kina son ce mashi ku fita zuwa anguwa, ba kawai zuwa zaki yi ki ce mashi yaya Imran zamu fita zuwa anguwa ko? Ba haka zaki yi ba, zuwa zaki yi ki kwanta a jikisa, dama gaki da shegen san jiki kamar mage, to idan kika kwanta, ki yi ta yi mashi kukan shagwaɓa ki na ɗan jan hancinsa, idan ya ce maki lafiya, ba haka kawai zaki ba shi amsa ba a'a, cikin salo mai ɗaukar hankali ki juya idanun nan na ki, ki yi mashi fari kafin kice kyau ka yi mani mijina aljannata, shiyasa na ji ina son in zo in yi ta kallon fuskar ka ina ɗan jan wannan kyakkywa kuma dogon hancin naka, wlh ko bai nuna maki ba sai ya ji daɗi a cikin ransa, ki cigaba da zuba mashi shagwaɓa da wasanni na taɓa wasu ɓangarori daga jikinsa, sai kun yi nisa kun lula duniyar da ba zai iya yi maki musu ba a can, sannan ki gaya mashi abin da kike so ta sigar da dole ya amince ko da baya so ɗin, sannan kuma kada ya kasance lullun ta hanya ɗaya zaki rinƙa bi wajen isar mashi da saƙon abin da kike so, idan ya zamana ta hanya ɗaya ne to zai gane ki ya zama watara ma da kin zo kin fara yi mashi ma zai ce kawai ki faɗi abin da ya kawo ki dan yasan ba haka nan ba, so akwai hanyoyi da dama da zaki rinƙa isar mashi da saƙo ba tare da ya gane hakan ba, ciki kuma har da girki tare da kula da shi a lokacin da yake cin abincin, idan da dama ki rinƙa bashi a baki, kuma kada ki yarda ya zamana sai kina son abu a wajensa ne zaki nuna mashi soyayya, a'a kullun ya zama cikin zuba mashi sabon salon soyayya mai rikitarwa kike yi, mace bata tsufa kuma bata girma a gaban mijinta, dan haka ki saki jiki ki kula da shi, wlh miji ko tsohone yana son kulawa, sai kuma batun sanya kaya, kada ki yarda ki ce zaki sanyawa yaya Imran ɗina manyan kaya, idan na ji kin yi hakan zamu haɗu dake ne, idan kuna ɗaki ku biyu, ki samo wasu shegun kayan barci masu birkita tunani da kuma lissafin ƙwaƙwalwar ɗan Adam, su zaki ɗauko ki sanya ki taho gare shi, wani lokaci kuma kada ki zo kai tsaye, ki rinƙa ɗan yawo ta gabansa kamar mai yin wani abin, zaki ga da kansa zai jawoki jikinsa dan ya ƙosa ki zo ke kuma kin ki, kinga gidan yaya Imran ke kaɗai ce, to dan haka duk wasu manyan kaya ki ajiye su a gefe guda, ki kwaso shegun kaya dan a buga harka, sannan kada ki rinƙa sanya breziya da daddare, ina ki barsu su kai mashi saƙon suna da buƙatar shi, idan ya gansu a tsaitsayen nan ba karamin haukace miki ya birkice maki zai yi ba, kada ki kuskura ki bar mani kwakwalwar yaya Imran ta zauna shiru har ta yi tunanin wani abin, idan yaya Imran zai yi wani tunani to ya zamana tunaninki ne ke kaɗai da kuma kayan abubuwanki, ga ki dirarriya, dan haka ki diranwa tunaninsa a ko da yaushe ki......" Bata karisa ba Aunty ta rufe mata baki da hannunta tana salati domin yau ta ji abin da ya fi karfinta.

Gaba ɗaya cikin ɗakin babu wanda bai nisa ba, wasu kam irin su Rimsha har da jan dogon numfashi.

"Akila shekarunki nawa?" Cewar Aunty, ta yi maganar tamkar ba lafiya ba, muryarta cike da mamaki tab, bata taɓa jin karatu irin na Akila ba, ba wanda ta taɓa jin yana bada irin wannan shawari sai a bakin Akilar.

Cire hannun Auntyn Akila ta yi daga bakin nata tana faɗin "Aunty me ya faru? Shekaruna ai ɗaya ne da Umaisha 18 to 19 muke". Mamaki ya hana Aunty sake yin magana.

Akila na ƙoƙarin sake tambayar auntyn ko dai lafiya. Sai ta ji wayarta ya yi kara alamar shigowar sako. Wani irin sihirtaccen kayatatcen murmushi ne ya bayyana akana face nata domin tasan sakon abin son ta abin begenta ne wato ɓoyayyen masoyi.

Zuba mata ido gaba ɗaya ɗakin suka yi har da jelly mai ɗaukar lecture ma binta da ido ta yi, yau Jelly ta natsu tsit tamkar ba ita ba, duk cikinsu harta aunty ba wanda bai karu da karatun nan da Akila ta yi masu yanzu ba, sai saka zancen a ransu suke yi, kowa yana saƙa yadda zai yi wa masoyinsa, ita kuwa Rimsha har ta hangota tana yi wa Lion hakan, ita kam Hanan ta dai ɗauki karantun ta ajiye a cikin zuciyarta dan bata da masoyin ma bare kuma ta ce zata yi tunanin yi mashi, ta dai ajiye ne sai Allah ya kawo mata sai ta yi mashi, Umaisha kam jirama take yi suyi sallar mangariba ta je ta zubawa mijinta kala kala sala sala abin data koya na yau, ita ma dai Aunty ta ɗauki wasu daga ciki, ta kuma yi niyar kwatanta yi wa Abbi ta gani.

Ɗaukar wayarta Akila ta yi ta buɗe saƙon nasa, sai murmushi take yi, a cikin zuciyarta ta fara karanta saƙon nasa.

"My heartbeat gaskiya ke karshece wajen iya soyayya, wannan irin lecture haka? Anya idan muka yi aure zaki barni na fita kuwa? Gaskiya na ji daɗi kuma na mori mata sosai da sosai, Allah ya mallaka mani ke my heartbeat ɗita ɗaya tamkar da billon, nasan kina kewar voice na, amma ki yi mani afuwa zuwa karfe 10 dare zan kira ki ko? Yanzu abubuwa sun ɗan sha kai na ne, amma ayi mani afuwa gimbiyata".

Duk sun zuba mata ido suna kallon yadda take murmushi tana kallon screen ɗin wayarta, a tunanin Umaisha da Irfan take yi, shi take yi wa wannan murmushi, saƙonsa take karantawa, dan a iya saninsu shi kaɗai ne saurayinta.

Suna a haka har aka kira sallar mangariba, a tare suka miƙe dan su je su yi alwala, jelly dai kwanciya ta yi dan bata Sallah, ita kuwa Akila bayan ta yi alwala kafin ta yi sallah sai da masoyin ɓoye ya tura mata massage akan ta yi masu addu'a sosai idan ta yi sallah, dama already ya saba faɗa mata hakan, duk idan zata yi sallah sai ya yi mata massage akan idan ta yi, ta yi masu addu'ar zama mata da miji su mallaki juna, kuma haka take yi, duk in ta yi sallah sai ta yi masu addu'a akan zama mata da miji, daren jiya ma har istihara ta yi akan su shi da Irfan, tana addu'ar Allah ya zaɓa mata wadda ya fi zama mata alkhari a cikinsu, amma abin mamaki shine duk da bata san waye masoyin ɓoye ɗin ba tana ji a jikinta shine zaɓin da Allah ya yi mata, saboda ta fi samun kwanciyar hankali idan ta kasance suna hira da shi, sannan tana yawan mafarkin wata kyakkyawar face ɗin a matsayin tasa, ba barcin da zata yi ba tare da ta kalli wannan fuska ba, sai dai kuma wannan fuska data Abbanta take yi mata kamanni, shine babban abin da yake damunta, wadda take mafarki a matsayin fuskar masoyin ɓoye kamar Abbanta dan dai shi yaro ne kawai, kuma mafarki ai zata iya mai da mutun yaro ta kuma mai da shi babba.

Bayan sun yi sallar isha ne Jelly ta tsara wankarta sosai, ta shirya cikin irin kayan da Imran ya ce yake buƙata, Aunty ta bata wani pant ɗin tare da Always dan ta sanya, karɓa ta yi ta sanya a jikinta sannan ta nufi palo tana gayawa Akila ta tafi wajen yaya Imran dan tun ɗazun yake kiran layin daddy da wayar ke a hannunta.

To AKILA ta ce tare da kara ja mata kunne akan ta natsu ta yi abin da ya dace, kada ta yi mashi shirme, dawowa ta yi ta ringume Akilar kafin su yi sallama, ta rungumi Ayla sannan ta rungumi Rimsha tare da Umaisha suka yi sallama.

Jelly na fita massage ɗin Masoyin ɓoye ya shigo wayar Akila, cikin zumuɗi Akila ta duba, saƙo ne kamar haka. "Heartbeat ɗina wannan yarinya da ta fita yanzu ta yi mani kama da brother na fa, sai dai ba sosai ba ido ne ya yi kama". Shiru ta yi tana haɗa maganganun a cikin ƙwaƙwalwarta, tunani take yi koma waye masoyin ɓoye nan tana ji a jikinta na kusa da ita ne, kuma da wuya idan ma ba ɗan uwanta bane domin a mafarki tana kallon shi mai kama da Abbanta, yanzu kuma ya ce idanun Jelly kamar na ɗan uwansa, to kenan akwai alaƙa a tsakaninsu ne ko yaya. Tana tsaka da tunani massage nasa ya sake shigowa.

"Heartbeat ki ɗauki duk abin da zuciyarki zata gaya maki a kaina, amma dai am sorry to say kamar ni ba mutun bane, but kada ki ji tsoro kin ji ko? Ni bana cutar da kowa sai dai ya so kowa da alkhari, sisterki da ta fita yanzu abin da yasa na yi magana akanta saboda tana da manyan idanu sosai kamar wannan ɗayar sister ta ki wato Rimsha, girman idanun nasu yasa nake ganin kamar brother na, amma ba wani abu bane, ni dai fatana kada ki gujeni".

Wurgar da wayar tata ta yi jin ya ce shi ba mutun bane, nan take jikinta ya fara kerma, da sauri ta diro kasa daga saman gadon ta yi waje wanjensu Abbi dan ma kada ya kamata. (TO FA YAU DAI GA AKILA NA GUDUN MASOYIN ƁOYE🤣🙃)

Su Umaisha kuwa ganin ta fita yasa suma suka miƙe suka fice suka bar wayar tata a tsakiyar gado, ita ma Ayla tana jan kafa a hankali haka ta bi bayansu.

Suna fita wayar ta kawo wutar screen da kanta daga nan kuma ta shiga massage da kanta ta goge massages ɗin ɓoyayyen masoyi na karshe daya turo na cewa shi ba mutun bane, wayar da kanta ta goge saƙon sannan wani saƙo ya shigo na ɓoyayyen masoyi akan wasa yake yi mata shi mutun ne, daga nan wayar ta yi switch off na kanta da kanta. To fa Babbar al'amari kenan

A ɓangaren Jelly kuwa, bata sanya hijabin kamar yadda Imran ya ce mata ba, ta dai sanya wasu shegun riga da wando da Aunty ta bata daga cikin kayan lefenta, su ta sanya a jikinta sai tashin kamshi take yi, duk ilahirin shape da wasu halittu na jikinta sun bayyana, kayan sun matseta sosai ne saboda ta fi Aunty cikar halittu.

A palo ta isko su daddy, Abbi, daddy, Auntyn, Irfan, Hjy Batula, da kuma Akil, sai hira suke yi, shi kuma Imran yana zaune a garden na gidan yana jiranta, tun da suka dawo sallar isha ya wuce can. Kada ku manta duk abin da ake yi Ommu tana sane tana jinsu kawai dai fitowa ne bazata yi ba dan bata jituwa da dangin na Abbi.

Zuwa ta yi ta rungumi daddy tare da yi mashi kiss a goshi, shima kiss ɗin ya yi mata, wucewa ta yi ta nufi waje ba tare da ta yi wa kowa magana ba domin bata sansu ba.

"Jelly baki gaishe da su yaya Deen ba". Cewar daddynta, juyowa ta yi fuska ɗauke da murmushi tana faɗin "Daddy i don't know them ai, among of them who is Yaya Deen ɗin?".

Da hannu ya nuna mata waye yaya Deen a cikin su, juyawa ta yi zuwa jiki Abbin ta haye tana faɗin "Yaya Deen good evening?" Akil ne ya ce mata "Bappa zaki ce not yaya Deen, he is your uncle not your brother". Ɗan kallon Akil ɗin ta yi kafin ta ce "Okey tom uncle good evening". Jelly ba dai son jiki ba, ta ce bata san su ba, amma ta hayewa Abbi jiki ta kwanta.

Da fara'a Abbi ya amsa sannan ya tambayeta wannan kwalliya da ta ci kuma sai ina, ba ko kunya ta gaya mashi yaya Imran ne yake kiranta kuma shine ya ce ta yi mashi kwalliya haka, yau duk rashin kunya irin na Akil sai da jelly ta sanya shi jin kunya, domin a irin yadda yake kallon Imran ustadz bai kai shi har zuwa wannan layin na sanya mace yin wasu dressing ɗin ba.

Shi kuwa Abbi danasanin tambayar tata ya yi domin ta fara bashi labarin har irin kayan da Imran ya ce ta sanya mashi, da dai daddy ya ga zata tonawa yaron shi asiri sai ya ce ta tashi ta tafi surutun ya isa haka. Ba musu ta miƙe tare da miƙawa daddyn wayarsa ta fice abinta, da ido daddy ya bita yana mamakin tare da tausayawa Imran, dan yana da aiki babba a gabansa.

Tana fita ta nufi garden ɗin sai wani kwas kwas take da takalmarta mai tsawo. Gaba ɗaya wutar garden ɗin a kashe, wajen a akwai duhu, ɗan tsorata ta yi da ganin wajen haka, amma sanin cewa Imran yana wajen yasa ta karisa wajen da confidence nata.

A tsakiyar wajen ta tsaya tana ƴan waige waige ko zata ga alamunsa, amma ina shiru. Tana ƙoƙarin juyawa sai ta ji an rungumeta ta baya, nauyayyar ajiyar zuciya ta sauke kafin ta ce "Yaya Imran ka bani tsoro fa".

Murya can kasa kasa ya ce "Sorry my wife, ai so nake na tsorataki dama, amma kuma sai na ji na kasa".

Ɗan murmushi ta yi kafin ta ce "Da ka tsorata ni kuwa da mun ɓata". Juyo da ita ya yi suna fuskantar juna a duhu, a hankali ya jawota jikinsa tare da riƙota ta bayanta yana haɗe goshinsu waje guda.

"Meyasa baki sanya hijabin da nace ba?" Ya yi maganar cikin wata irinyar murya mai kwantar da hankalin mai sauraro. Sarkin son jini, kwantar da kanta a kirjinsa ta yi a shagwaɓe ta ce "Yaya Imran ai ni bana son hijabin ne". Wani irin yanayi ta jefashi yadda ta yi maganar nan tata.

Riƙota da kyau ya yi suka zauna a saman ɗaya daga cikin kujerun wajen tana a saman cinyarsa. A daidai saitin kunnenta ya kawo bakinsa, cikin raɗa kamar wani zai ji su ya ce "Zaki bi mijinki mu tafi tare?" Tana daga lafe a kirjinsa ta ce "E zan bika mana".

Wani irin daɗi ya ji wadda ya sanya shi natseta a jikinsa sosai da sosai. "Yaya Imran zaka ɓallani fa". Ta faɗa a shagwaɓe.

"My wife zaki bawa mijinki damar yin kissing naki? Na yi ko sau ɗaya ne?" Girgiza mashi kai tayi alamar bata so, shiru ya ɗan yi kafin ya ce "To shikenan tun da baki so, ni ma bana so dan bana son abin da bakya so". Ya kai karshen maganar tare da fara shafa bayanta yana mai jan wani irin numfashi yana sauƙewa a hankali hankali.

Jin abin da ya ce yasa ta ɗago kanta daga kirjin nasa tare da gyara zamanta ta haɗe fuskokinsu waje guda. "Yaya Imran ni fa matarka ce, me yasa zaka tambaye ni dan zaka yi mani abin da ya kasance halak ɗin ka?" Nauyayyar ajiyar zuciya ya sauƙe ba tare da ya yi magana ba ya haɗe bakinsu waje guda ya fara bata hot kiss, shiru ta natsu tana karɓar saƙon da yake aika mata da shi, while a can cikin gida


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login