Showing 180001 words to 183000 words out of 355604 words
jima a haka kafin ya zagayo ta gabanta ya zauna gefenta yana janyota saman faffaɗar kirjinsa, kwanciya ta yi ta lafe a kirjin nasa tana mai da numfashi, hannu ya zura cikin rigarta ta daidai kugunta yana ɗan shafa plat tummyn ta, sai wani yauki take yi mashi tana kara shigewa jikinsa, hakan da take yi kuma ba karamin kara birkita shi yake yi ba, dan haka sai ya cigaba da wasa da cibiyarta, a hankali ya sanya ɗayar hannunsa ya ɗago haɓarta suna fuskantar juna, gently ya matso da fuskarsa sai tin tata, tun bai karisa isowa ba, ta kurma ihu tare da farkawa daga barci, wani wahalallen zufa ne ke tsastsafo mata daga gefe da gefen fuskarta, ta yi sharkaf da fitsari sabida tsoro, wannan masifa da me ta yi kama, dafe kanta ta yi ta fara hawaye tana rokar Allah da ya sawwaƙa mata wannan bala'in kada hakan ya zama sanadiyyar taɓuwar ƙwaƙwalwarta ko kuma ma mutuwarta baki ɗaya, innalillahi wa inna ilaihir rajiun shine abin da ta fi yawan furtawa a ransa.
Tana zaune a wajen ta kasa motsawa har karfe 3, sannan ne ta ja jikinta da kyar ta iya sauƙowa kasa daga saman gadon ta nufi toilet, da kyar ta iya yin wanka tare da ɗauro alwalla ta fito, doguwar riga ta zura a jikinta tare da hijabi, ta shinfiɗa dadduma ta fara sallama tana kai wa Ubangiji kukanta, dan tasan ba mai cireta a cikin wannan azabar sai shi, baiwar Allah sai kugin yunwa cikinta yake, saboda bata ci abincin dare ba, da kyar ma take iya kai sallar saboda jiri na yunwa dake ɗibarta, abin ya taɓa ta sosai, har wani ramar lokaci guda ta yi, duk ta fita a hayyacinta, kuma duk wannan masifaffen son da take yi mashi tun tana yarinya ne ya ja mata hakan.
A daddafe ta yi sallah raka'a shida sannan ta rufe da shafa'i da witiri, ta zauna saman dadduma tana karatun Alkur'ani mai girma kasa-kasa, har lokacin yin raƙatainil fajir ya yi, haka ta miƙe ta gabatar da raƙatainil fajir ɗin ta, a raka'ar farko ta karanta Kulyahayyuwalkafirun, na biyu kuma ƙulhuwallahu ahad, domin Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama ya ce falalar yin sallar raƙatainil fajir tafi duniya da abin da yake a cikinta, amma idan ka karanta wayan nan sururo guda biyun wato ƙulhuwallahu ahad da Kulyahayyuwalkafirun, falalar da zaka samu sai ya kai girman duniya sau biyu, dan haka kada muyi wasa da wannan dama, Allah ya bamu dacewa.
Bayan ta idar da Sallar raƙatainil fajir, ta ɗan zauna kaɗan, kafin ta gabatar da sallar asuba, yin hakan da ta yi kuma yana daga cikin sunnunin manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama, tsakanin sallar raƙatainil fajir da kuma asuba, annabi yana zama ya ɗan bada tazara na ɗan lokacin, yin hakan ma ba karamar falala bace.
Bayan ta yi sallar asuba sai ta yi askar nata, amma bata kai ga kammala askar ɗin ba barci ya ɗauketa a wajen, dan ta samu sauki sosai acikin zuciyarta, ta samu peace of mind, Alkur'ani mai girma maganin cuta komai girmanta, sallar nafila mai kawar da damuwa duk min girmanta, ta yi sallar ta roki Allah da ya shiga lamarinta hakan ya sanya ta samu peace, Baiwar Allah yana barci tana sauƙe ajiyar zuciya.
A haka Akila ta iskota misalin karfe 8 na safe, yau bata samu damar tashi ta yi shara ba bare kuma wanka da gyaran ɗaki har a kai ga girki. Akila ta sha mamakin ganinta a hakan, gabanta ta karisa tana ƙoƙarin taɓa ta, sai ta ji muryar Imran daga bayan ta yana faɗin "No heartbeat kada ki taɓa ta, ki kyaleta". Cikin sauri Akila ta juyo da kallonta kanshi, yana tsaye a bakin kofa jikinsa sanye da kayan barci riga da wando, da alama yanzu ya tashi daga barci, kuma da alama da tunaninta ya kwana shiyasa yana tashi ya nufi ɗakinta kai tsaye.
"Yaya Imran lafiya? Ko dai bata da Lafiya ne?". Juyawa ya yi ya nufi waje ba tare da ya yi magana ba, dan baya son su tashe ta daga barci, da sauri Akila ta miƙe ta bi bayansa, a palo ya tsaya yana bata amsa "Akila nima dai bansan meke damun Rimsha ba, amma dai tabbas na lura tana da damuwa, jiya ina da tabbacin bata samu barci ba, shiyasa take barci yanzu kada ki tasheta ki kyaleta idan ta tashi ta yi wanka muka samu natsuwa sai in ji menene damuwarta". Lokaci guda yanayin Akila ya canza, mood nata ya juya, sosai ta ji ba daɗi tana son jin meke damun yar uwarta.
Ganin ta shiga bad mood yasa Imran ya ce "Heartbeat kada ki damu ba komai In Sha Allah yanzu dai zoki gyara mana palo ko?".
To ta amsa mashi da shi, amma dai jikinta duk a mace, ta ji wani irin yanayi mara daɗi, ita bata son jin ance wani yana cikin damuwa ko kaɗan, hakan ba karamin ɗaga mata hankali yake yi ba. Ganin ya juya zai koma bedroom nasa ne yasa ta yi saurin cewa "Yaya Imran jiya waye ya zo ɗakin kan nan? Na gan shi da face mask ban iya ganin face nasa ba, amma dai daga ganin ga shin kansa nan ba ɗan Nigeria bane".
Ba tare da ya juyo ya ce "Heartbeat kin iya gulma ashe, to Saif ne, kuma ma ya tafi abinsa, sai na je nemansa yanzu, ki yi mani addu'ar Allah yasa na gan shi". Cikin sauri ta ce "In Sha Allah zaka gan shi" Allah yasa ya faɗa tare da wuce wa cikin bedroom nasa, ita kuma ta fara aikin da Rimsha take yi, dan yanzu ita ma ta iya.
To a ɓangaren su Michael kuwa, Wato Washington DC.
Yau zai koma school, tun safe ya shirya tsab ya haɗa duk abin da zai buƙata, suka yi sallama da Musharraf ya fito, da motarsa ya wuce school, kuma kamar dai a baya da su copper ya tafi, Lion ya ce 100 level zai koma, bai wani damu ba, ya yarda dan yanzu ilimi yake nema ido a rufe.
Michael na tafiya ba jimawa Tga ya shigo cikin ɗakin ya ce da Musharraf ya zo su ta fi, ba musu Musharraf ya biyo bayansa suka fito palon kasa, kai tsaye waje Tga ya nufa, dan yasan akwai camerori a cikin gidan, duk abin da ya yi Lion zai gani, hakan yasa suka nufi waje kawai.
Kai tsaye gym ya wuce, Musharraf na biye da shi, kuma bai kawo komai a ransa ba. Tsabar tsanar da ya yi wa Musharraf, baya son shi ko kaɗan, hakan yasa ya fara bashi horon sojoji, manya-manyan karafuna ya sanya shi ya fara ɗaga wa, Bawan Allah bai iya ba, amma saboda sanin bakin hali na Tga yasa ya fara koya, kullun Michael yana bashi labarin bakin halin da mugunta irin na Tga, yau kuma ga shi nan ya tabbatar.
Wani zabgegen bulalla Tga ɗin ya ɗauko ya ajiye a gefe, sannan ya ɗaurawa Musharraf wasu mayun karafuna a hannunsa ya ce dole sai ya yi tsayuwar minti talatin da su a hannunsa, Innalillahi wa Inna ilaihir rajiun, a wannan hali John ya zo ya same su, cikin halin nuna ko in kula John ya ce "Uncle T what is going on here?".
A kule Tga ya ce "John this guy ashe musulmi ne" a sukawane ya juyo da karfi ya furta "What??!!" Yayi maganar yana zaro ido waje.
"Yes John musulmi ne, ɗazun by 5:30 na shiga bedroom na Michael zan tasheshi daga barci ya zo ya fara gym, na shiga bedroom nasa baya nan, har zan fita part ɗin sai kuma na ce bari na leƙa ɗayar ɗakin ko yana can, to a nan na gan shi yana bautansu, shi kuma Michael ban gan shi a cikin ɗakin ba, a lokacin na kira Lion bai ɗauka ba, sai daga baya ya kirani da na gaya mashi sai cewa ya yi wai na bari sai ya dawo, Musulmi fa a gidan nan, amma Lion yana cewa abari sai ya dawo, to ba zai yi wu ba, kafin ya dawo dole na fara bashi horon, sai ya yi dana sanin zuwan shi gidan nan, kai sai na ma ji dalilin da ya sa ya zo gidan nan, dan daga gani kasan turoshi aka yi, kasan musulmai yan ta'adda ne, wata kila wani abin suke shiryawa, to mun fi karfinsu, shima Michael dole ya rabu da mutumin nan, yana dawowa idan na gaya mashi musulmi ne, dole zai rabu da shi, bakin shaiɗani, mugaye yan ta'adda mu dai mun fi karfin ku" ya kai karshen maganar yana wani huci kamar zaki.
Rai a matukar ɓace John ya ce "Tabbas Uncle T wuya zaka ba shi ba ɗan kaɗan ba, sai ya yi danasanin zuwan shi duniya, sai ya gwammaci da bai san familyn William jacop" ya kai karshen maganar tare da ɗaga kafa ya taka Musharraf ɗin a kirjinsa da karfi.
Baya baya Musharraf ya yi Allah sarki ya faɗi kasa ga kuma karafuna a hannunsa, suka danne mashi hannun, wannan zabgegen kafuran bulalar Tga ya ɗauko, ya fara zana mashi a jikinsa wai ya faɗin, bulaka biyar masu lafiya ya yi mashi sannan ya ɗage shi ya tsaida shi, ya sake sanya mashi karfen ya ce wai sabon kirga za'a fara.
Bawan Allah shi zane shi da suka yi ma bai wani dame shi ba, abin da ya dame shi nauyin wayan nan karafuna.
Cike da bada umarni Tga ya fara zuba mashi kashedi da kuma dokoki kamar haka "Daga yau kullun karfe 5 na safe ka tabbatar ka zo nan ka fara ɗaga karafuna kafin na fito, na biyu kuma da yamma dole ka kasance a wajen ruwan kankara, da daddare idan kowa yana barci, dole kai ka zo wajen tsere da doki domin ku yi tsere da dawakan, ba zaka taɓa yin barci ba sai ka yi tsere da dawakan kafa 30, da rana kuma ka kawo kanka da kanka cikin tsakiyar rana ka kwanta kana kallon sama, ka kalli rana sosai, idan kuma ka sake ka gayawa Michael sai na kashe ka, ko da yake ma shima Michael ɗin idan ya san kai Musulmi ne to ba zai barka ba, zaka karɓi nasa horon". Bawan Allah da kyar ya iya amsawa da to, haka Tga ya cigaba da zabtar da shi da horon sojoji har zuwa karfe 11 na rana sannan ya kyale shi ya wuce cikin gida domin ya je ya shirya ya wuce wajen aikin
Zama a wajen Musharraf ya yi ya kasa motsawa saboda gaba ɗaya ko ina na jikinsa ciwo yake yi mashi, hannunsa duk sun kumbura, da kyar yake iya numfashin, daga karshe kwanciya ya yi a wajen saboda bala'in azaba da ya sha.
Allah sarki, idan muka waiwaya gida Nigeria kuma, Akil yana fita daga part ɗin Imran kai tsaye bedroom nasa ya nufa, Umaisha bata ciki, fitowa ya yi ya duba Kitchen bata nan, abin ya bashi mamaki, haurawa sama ya yi izuwa ɗakin Ammie, ton daga bakin kofa ya fara jiyo kukanta kasa-kasa, cikin sauri ya tura kofar ɗakin ya shiga, tana tsugunne a tsakiyar ɗakin, ta haɗe kai da gwiwa sai kuka take yi, hannunta na ruƙe da tovel na goge goge, ita kuma Ammie tana hakimce a saman gadon ta ɗaura kafa ɗaya bisa ɗaya tana latsar waya.
Da karfi ya furta sunan ta "My wife!" Cikin sauri ta ɗago, fuskarta duk ya yi jaga-jaha da hawaye da majina, da alama dai wani abin mugunta Ammie ta yi mata.
Kasa magana ta yi ta mai da kanta kasa ta cigaba da kukan da take yi, da sauri ya kariso cikin ɗakin ransa idan ya yi dubu to ya ɓaci, dan bai son abin da zai taɓa mashi ita,. Yana zuwa ya sa hannu ya ɗagota ya rungume kayansa, ba tare da ya yi magana ba ya wuce da ita suka fice daga cikin ɗakin, ko sannu Ammie bata ce mashi ba, shima kuma bai ce mata ba, sai bayan ya kai Umaisha bedroom nasu ne ya dawo ɗakin Ammie ɗin, a bedside drawer ya zauna, cike da girmamawa ya fara magana.
"Ammie me ya faru yau kuma tsakaninki da yar taki?". Shiru ta yi mashi bata kula shi ba, ganin haka yasa ya riƙo hannayenta yana bata hakuri.
Ta ɗan ɗauki lokaci kafin ta ce "Ka sakar mani hannu, tun da matarka ta fini muhimmanci, wato ni ban isa in hukuntata idan ta yi mani laifi bako? Shine zaka zo ka gwada mani isa akanta ko? To ka je, ina dai mace ce zaka gani iya ganin idanunka". Kara yin kasa da murya ya yi cikin sigar bada hakuri da rarrashi ya fara magana "Ammie na san ban kyauta ba, amma kiyi hakuri sharrin sheɗan ne, kuma ki dai na cewa baki isa ki hukunta Umaisha ba, kin isa har ma kin yi yawa, nima kika hukunta ni bare mamata, kuma koda ban auri Umaisha ba zaki iya mata hukunci idan ta yi maki laifi ai yarki ce, dan Allah ki yi hakuri". To kawai ta ce mashi, shiru ya ɗan yi yana tunani.
"Lafiya tunanin me kake yi?" Ɗan ɗagowa ya yi ya kalleta tare da sakar mata murmushi yana faɗin "Ina kara godewa Allah da ya bani ke a matsayin uwa, gaskiya na ji daɗi, tunanin da nake yi shine anya akwai wanda ya mori uwa kamar ni kuwa?" Yar dariya ta yi cike da kirsa da makirci ta ce "Tom Allah ya yi maka Albarka ta shi ka je".
Miƙewa ya yi ya nufi waje yana jujjuya abuwan da suke faruwa, ga Umaisha sai uban rama take yi, idan ya tambaye sai ta ce mashi babu komai, sannan ya fara mamaki da irin bala'in kaunar da Ammie ke nunawa Umaishan a gabansa, abin har ya fara yawa, lokaci guda kuma ya fara jujjuya kalaman Akila a cikin ƙwaƙwalwarsa, in da take yawan gaya mashi dan Allah ya mai da Aunty Umaisha gidan sa da ya gina ɗin nan dan ta samu gidan zuwa yawo.
(Kai ka ji wata basira wajen Akila, wato da Ammie ta ce zata kashe Umaisha idan ta tona mata asiri shine Akila ta biyo ta wannan hanyar dan a rabawa Umaisha da Ammie gida, tab lallai jinjina Akila)
Akil akwai kaifin kwakwalwa nan take ya gano lallai akwai matsala a gidan, kuma ya zama dole ya san abin yi, domin duk wani abin da ya samu Umaisha yana da kason nasa zunubin saboda shi ya kawota a karkashinsa take a zaune.
Zaune a bakin gado ya iskota, har lokacin tana kuka kasa-kasa, kusa da ita ya je ya zauna tare da jawota jikinsa yana lallashinta, "Sorry my wife tashi ki shirya muje gidan Abbi mu ɗauko Aafia daga nan sai ki gaisa da Abbi, Aunty, yaya Irfan, bappa Maik, Kinji ko my pleasure?" Cikin dashashiyar muryar ta ce "Ni ba zan je ba kuma ka sake ni dan ina fushi da kai".
Cikin sauri ya ɗago da haɓarta yana kallon face nata "My wife me nayi kika kike fushi da ni? Ni fa zan kai ki wajen su Abbi ne dan ki huce bakin cikin da kike a ciki". Kokarin tashi daga jikinsa ta yi tana faɗin "Akan me ɗazun zaka ɗauki Rimsha?".
Ɗaure fuska sosai ya yi ya fara magana cike da izza "Kin taɓa ganin na taɓa taɓa jikin wata mace ce bayan ke da heartbeat?" Girgiza mashi kai ta yi alamar a'a "To ba wai zan gaya maki ko ki yarda da ni ko akasin hakan bane, idan ma baki yarda ba ya rage naki, ni babu son wata a zuciyata sai ke, ni ban taɓa soyayya ba sai a kan ki, bayan ke kuma bana fatan na sake yin wani, ni ban ɗauki Rimsha da wata manufa ba fa ce bata a cikin hayyacinta, sannan kuma ina son ki zauna ki koyi yadda ake zama da miji, ni yau da za'a zo a gaya mani kin yi abu kaza, tofa ba zan tsaya bincike ko wani abin ba, idan kin yi nasani, idan ma baki yi ba na sani, wannan shine so na gaskiya, ka san iya adadin abin da masoyinka zai iya aikatawa da kuma wanda ba zai iya ba, ta yadda sharrin masharranta ba zai taɓa raba ku ba, baki cancanci zama masoyiya ta asaliba tun da baki san abun da zan iya yi da wanda ba zan iya yi ba" ya kai karshen maganar tare da miƙewa rai a ɓace ya nufi hanyar fita daga ɗakin.
Da gudu ta miƙe ta faɗa zaman bayansa ta rungumo shi tana kara sakin wani kuka mai ban tausayi. Allah sarki zuciyoyin masoya, sai ya kasa cireta daga jikinsa, hasalima jiyowa ya yi, ya rungumeta sosai yana sauƙe ajiyar zuciya, ita ma ajiyar zuciya take sauƙewa tana kuka kasa-kasa.
"Ya isa haka, ki yi shiru" ya yi maganar murya can kasa-kasa cike da so da kauna. Kara kankame shi tayi tana faɗin "Ina son ka yaya Akil, ka daina cewa ban cancanci zama masoyiya ta asali ba, zan iya mutuwa idan kana gaya mani hakan, kai baka sani ba saboda son da nake yi maka ne yasa nake kishinka, ina sonka mijina Allah ina sonka".
"Baki sona My wife, da gaske baki so na" Duka ta kai mashi a kirjinsa tana kara sautin kukanta tana faɗin "Ina sonka wlh ina sonka" "Idan kina so na me yasa kike hanani hakkina? Me yasa? Tun rana ta farko ba ki sake yarda da ni ba, sai dai mu yi wasa kawai meyasa? Baki son haifa mani yara ne? Me na maki kike wahalar da ni ta wannan sigar?" Goga kanta ta fara yi a kirjinsa tana faɗin "Akwai zafi ne yaya Akil, Akwai zafi, ba wai bana son yara bane, ina so amma ba zan iya jurewa ba, akwai wahala".
Bawan Allah bai damu ba sai ya rungumeta sosai a jikinsa dan yasan koma me shi ya ja, saboda dama duk yanayin da ka zo wa mace a rana ta farko, to a haka zata tafi, idan da karfi ka yi mata ya mata zafi, to a haka zata ɗauki abin har abada zata rinƙa jin da zafi