Showing 192001 words to 195000 words out of 355604 words
yau ma, Aafia ta sha ruwan mamaki ganin yan bandits ɗin dayawa yau, da alama sun dawo kenan.
A gaban idanunsu babba daga cikin yan bandits ɗin ya fito da wani abin a cikin gora, ya bawa kowanne daga cikin bandits ɗin suka sha, kowa kurɓa ɗaya yake yi ya miƙawa na kusa da shi. Sai da gaba ɗayan su suka sha, kusan su 40 ne a wajen, sannan ogan nasu ya masu umarnin a kan su tafi, wucewa suka yi, suka kutsa da cikin daji, da alama wani aika-aika za su je yi, wannan abin da suka sha kuma ba komai bane, fa ce abune wanda zai kawar masu da tausayi da Imani, dama idan za su fita aiki sai sun sha shi domin ya ɗebe masu imani su ji daɗin aikata duk abin da za su aikata ba jin tausayi ko ɗigo a ransu.
Bayan wayan can sun tafi ne kuma wasu wajen su 10 suka kariso wajen a kan mashin, ɗaya na goye da ɗaya, wani ma mutun biyu ya goya, Dukansu matasa ne da ba za su wuce daga shekara 23 zuwa kasa ba.
Daga ɗan baya suka kashe mashunan nasu suka sauƙo izuwa kusa da ogan nasu, yana tsaye fuskarsa na rufe da wannan rawanin nasu. Umarni ya ba su akan su fitar da sabbin zuwa da aka kawo, su karɓi number yan uwansu bari ya kira kafin ya wuce, dan akwai aikin da zai je.
Haka kuwa akayi, suka ware su Aafia a gefe suka fara karɓar numbobin yan uwansu. Ko da suka zo kan Aafia sai ta ce masu bata haddace number kowa a gida ba, a nata wautan wai tana tsoron ta bada number yaya Irfan, dan idan ta koma zai mata duka ya ce waye ce ta bi Rufee, me ya kai ta wajen, shiyasa ta ki bada number, ta ce bata da number kowa.
Wani mahaukacin mari bandit ɗin ya sakar mata a kumatu, wadda ya sanyata kurma wani irin razanannen ihu mai razana kwakwalwa.
"Zaki bamu number yan gidan ku ne, ko sai na fasa ki da bindiga?!!!" Ya kai karshen maganar yana sanya kafa ya hanɓareta, faɗuwa kasa ta yi tana kuka kamar ranta zai fita, cikin kuka ta ce "Wlh ni ban riƙe number kowa a kai na ba"
A haukarta tana ganin idan ta ce masu hakan za su saketa ta koma gida, tana bala'in jin tsoron ta bada number ɗaya daga cikin, Abbi ko yaya Irfan, dan dukkansu ba sauki, ubanta za su ci idan suka san yawo take tafiya, bata san cewa a wannan halin da take ciki sai dai ma su yi mata kuka ba.
Bandit ɗin yana ƙoƙarin sake taka mata wuya da wannan takalmar tasu mai kama da waterproof ɗin, sai ɗaya daga cikin su ya ce "Haba buba ka tsaya mana, kai daga ganin wannan kasan akwai kuɗi a gidansu, idan ka kasheta ka yi mana asara, baka ga jikinta bane? Wannan renon madara ce, ba ƙaramin kuɗi za mu samu ba, oga ina son ku bari zan karɓa maku number".
Kallon shi ogan nasu ya yi ya ce "Sani zai kira wayar ni ina sauri zan fita, kada ku kuskura ku taɓa mace ko ɗaya daga cikinsu, sai na dawo" ya kai karshen maganar yana nufar hanyar dake ta tsakiyar wasu dogayen ciyayi a wajen.
"Oga dabar Yellow zaka je ne?" Wannan da ya ce abar Aafia shi ya tambaya, gyaɗa masu kai ya yi ba tare da ya yi magana ba kuma bai juyoba ya ci-gaba da tafiya har ya ɓacewa ganinsu.
"Dan Allah Sani kazo ka kira wayar nan yanzu dan wlh bani da kuɗi" cewar buba. Daga cikin wani ɗaki dake ɗan gefe ɗan nesa kaɗan Sanin ya fito, shima duk shigarsu iri ɗaya ne, kuma dukka matasane masu jini a jika, dan shima ba zai wuci 25 years ba, (matasa manyan gobe😭)
Yana zuwa ya fara karɓar numbobin yana kira iyaye da yan uwan mutanen da suka kama, da wata wayarsa Tecno mai botir, duk ta ji jiki. Sun kware wajen yankawa mutane kuɗin da sai sun ji kaban su ya faɗi, wasu ma za su iya suma idan suka ji kuɗin da suka kira.
Da suka zo kan maman Hanan, ta ruɗe ta rasa number waye zata bada, saboda Mahaifiyarta tana asibiti, idan ta bada number yan gidansu za su sake shiga tashin hankali kan tashin hankali ne, idan kuma ta ce ta gefen familyn ta na Katsina ne, wato gefen babanta, babu mai waya ma a cikinsu.
Ta nutsa cikin tunani ne bubu ya daka mata wani irin mahaukacin tsawa wadda ya sata fara karato number kanin mamanta dan shi kaɗai ta iya riƙe numbersa.
Suna saka number bugu ɗaya ya ɗauka, ba ɓata lokaci suka sanar mashi da abin da yasa suka kirashi, salati bawan Allah ya fari yi, a wulakance Sani ya ce "Ka ajiye salatin ka a gefe, gaba zai maka amfani, yanzu dai ku kawo kuɗin fansa ku karɓe ta ko kuma mu kashe ta" daga can ɓangaren yayan nata ya tambayi naira nawa ne, nan suka yanka mashi kuɗin da kwakwarsa suka kasa ɗauka mashi, 40 million, daga suka faɗi kuɗin wayar ta yanke dif, da alama ya suma ne, ko kuma dai ya razana ya saki wayar ta faɗi kasa ta tarwatse, ko wani abu makamancin haka.
Tsaki sani ya ja yana faɗin "An jima zan waiwayeka idan ka dawo daidai" ya kai karshen maganar tare da kallon Aafia yana mai bata umarnin akan ta basu number yan gidan su, ai kuwa ta kafe akan lallai ita bata riƙe number kowa a kanta ba, hakan yasa suka tambayi sunan anguwarsu dan su nemo number da kansu, nan fa tsoro ya kara kamata, jikinta ya hau kerma, sosai take ambato sunan Allah a ranta.
Suna a wannan hali Sani ya zuba mata ido suna jiran amsa, ba su ankaraba, kawai sai gani suka yi ɗaya daga cikin bandits ɗin ya kariso wajen, hannunsa ruƙe da zangegen bulala, yana zuwa ya fara zabga mata a jikinta. Irin mutanen nan ne masu gaggawa a kan abu, basu da hakuri, ga saurin hawa, shiyasa ya fara dukanta, wai ta raina masu wayo ne, sai ihu take yi tana juyi a wajen.
Shi kuma buba ɗaga bindigar hannunsa ya yi sama ya fara sakin wuta, Ihu sauran yan bandits dake a wajen suka fara yi suna shewa.
Nan take duk sabbin zuwa dake a wajen, wayan da ba su saba ba, suka rungumi juna suna kuka. A zafafe A'afia ma ta rungumi Hanan suna kuka kamar ransu zai fita, duk sun birkita masu kwakwale, shi kuma bandits mai zane Aafia haka ya cigaba da sauƙe masu bulala a jiki, daga Aafia har Hanan ɗin da suka rungumi juna, a tare suke shan bulalar.
Cike da jin haushin abin da suka yi Sani ya dakatar su ta hanyar daka masu tsawa. Ba dan sun so ba, suka dakata, rai a ɓace ya fara magana "Yanzu me amfanin hakan? To da kuka birkita su ai Shikenan, kuna tunanin yanzu za su iya bamu amsa ne, me yasa kukam wata zubin baku abu da ƙwaƙwalwar ku ne? Dan Allah ku wuce ku bani waje a nan hai". Ya kai karshen maganar tare da wucewa ya bar wajen ransa a matukar ɓace, suma wucewa suka yi suka bar wajen, sai wani kumbure-kumbure suke yi, suka nufi in da ya kasance nan ne ɗaku nan su yake. Haka su Aafia suka ci-gaba da zama cikin kunci suna hawaye, duk sun birkice bayin Allah. Sani ya ce zuwa anjima zai dawo dan ya karisa karɓar numbobin yan uwan nasu, kafin nan sun ɗan sami natsuwa....
Ni kuma na tattara kayana zuwa gidan Abbi gobe idan mai dukka ya kai mu, sai mun haɗe gidan Abbi, masoyan yaya Imran, yaya Irfan, yaya Akil, Abba, Abbi, daddyn Jelly, Umaisha, Akila, sai ku saka A'afia a addu'a, domin kuwa wannan bala'in da take ciki, tamkar gaba ɗaya wayan da na kiran nan ne a ciki, yar uwasu ce, kanwarsu, yar cikin su, dole za su shiga matsanancin tashin hankali idan suka sami labari, Allah ka iya mana da iyawarka, Allah ka kawo mana zaman lafiya a kasar mu, Allah ka shiga lamarin mu😭😭, Ma'assalam......✍️
💖💖TRIPLETS💖💖
53-54
🔥GIDAN ABBI🔥
*BARI MU FARA DA DADDYN JELLY*
Suna fita da Ayla kai tsaye *ABC SUPERMARKET* suka wuce, yana tuki yana kallonta ta cikin mirror motar, ita kuma ya kwantar da kanta a jikin kujerar tana shakan kamshin perfume nasa, ga kuma kamshi turaren motar abin ba'a magana.
"Babayn daddy tunanin me kike yi?" Ya faɗa yana dawo da kallonsa a kanta, fuska ɗauke da murmushi ta ce "Kawata kuma yar uwata Rimsha nake tunani, ko tana wani hali yanzu? Ina kewarta sosai".
Jinjina kai ya yi cike da kulawa ya ce "Very soon zan kai ki wajenta, ba dai kin ce a Katsina take ba?" Gyaɗa mashi kai ta yi tana mai kai kallonta kan shi, shima ita yake kallo kuma yana tuki.
Murmushi ya sakar mata yana faɗin "Yau kin yi kyau sosai kamar my jelly" "Allah sarki daddy Allah ina son kallon Jellyn nan sosai" mai da lallonsa kan hanya ya yi yana faɗin "Very soon da izinin Allah zata dawo gare mu" ya kai karshen maganar yana dawo da kallonsa kanta.
"Allah yasa, kullun ina mata addu'a" ɗan zaro ido ya yi kafin ya ce "A ina kike yi mata addu'ar?" Ya tambaya yana sake kallon hanya. "A Sallah mana daddy, idan na yi sallah ina yi mata addu'a sosai" "Yaushe kika fara sallah ban sani ba?" Zaro ido ta yi yana kallon shi, dawo da kallon shi ya yi kanta yana faɗin "Amsa me, yaushe kika fara yin Sallah?" Sunnar da kai kasa ta yi tana wasa da yan yatsun hannunta, tana tunanin yaushe daddynta kuma yasan bata Sallah, kwata-kwata yau satin ta ɗaya tare da su, kuma yau take sa ran Jinin zai tafi, dan Aunty ta ce mata sati ɗaya yake yi, wata macen kuma kwana huɗu, to yau ta cika sati da fara yi.
Tana tsaka da tunani kamar ance mata ta ɗago kallonta izuwa kan hanyar, daidai lokacin da shima ya kawar da kallonsa daga kanta izuwa kan hanyar, wani irin mahaukacin burki ya ja lokacin da suka kusa taka wani yaro da ya shigo titin da gudu zai tsallaka.
Tsabar tsorata bata lokaci da ta faɗa jikinsa ba, tana sakin kuka, shi kuma ajiyar zuciya ya sauƙe tare da yi wa Allah godiya da ya sanya ba su buge yaron nan ba, dan ma Allah ya tsare ba wani gudu suke yi a kan hanyar ba, kaɗan-kaɗan suke tafiya saboda yasan suna tafiya suna hira hankalinsa ya rabu gida biyu shiyasa yake tafiya a hankali, da gudun haɗari.
Bayan yan wasu mintuna, a hankali ya dawo da manya-manyan idanuwansa irin na Jellynsan nan a kanta, ta kankameshi sosai ta tura kanta cikin kirjinsa.
"Babayn daddy are you okey?" Ya faɗa a sanyaye, cike da tsoro, da kyar kuma a hankali ta ɗago da idonta tana ayyana yadda zata ga sun taka yaron nan a kan titin, bata ma san yaro kam ya wuce abinsa da Allah ya tsare ba'a taka shi ba.
Kai kallonta ta yi saman titin, sai taga wayam babu yaron, sai motoncin dake kaucewa nasu suna wucewa, dan ma Allah yasa motar tasu bata a kan hanya sosai, suna ɗan gefe.
Dawo da kallonta kan fuskarsa ta yi, ya tsare ta da ido yana kallonta, yunkura wa ta yi zata tashi amma sai ta kasa sakamakon lokacin da ta faɗo jikinsa ta sanya hannunta ɗaya a jikin kujerar da yake zaune, da ya dawo da bayansa wajen sai ya ɗan danne mata hannun nata.
Ko motsi bai yi ba yana ta kallon fuskarta, ita kuma tana son tashi ga shi ba hali, dawo da kallonta kan fuskarsa ta yi, still har lokacin kallonta yake yi.
"Daddy hannuna zan tashi" ta yi maganar a shagwaɓe kamar yadda ya saba yi mata magana kullun, sannan ta yi maganar tana sunnar da kai kasa.
Ya kasa motsa Allah kaɗai yasan me yake tunani a cikin ransa, ya kasa yin wani kataɓus. Ganin haka yasa ta koma ta kwantar da kanta a saman kirjinsa, dan ta gaji tana saman iska, ita bata zauna ba kuma bata karisa tashi ba.
Wani irin yanayi mai wuyar misiltawa ya ji a jikinsa, bai san lokacin da ya kai hannunsa yana shafa kanta zuwa bayanta ba, shiru ita ma ta lafe a jikinsa, domin ya saba rarrashinta idan ta tuna da mamanta tana kuka, shi Aunty take kira ya rarrasheta dan tafi jin maganarsa sama da ko a gidan, shiyasa ta saba da rarrashin nasa, wani sain ma har rungumarta yake yi, idan ta yi shiru sai ya ce ta yi murmushi, idan ta yi ne sai ya rungumeta suna murmushi, shiyasa kwanciya a jikinsa ba bakon abu bane a wajenta ba.
"Daddy hannuna yana yi mani zafi, ka danne sosai" ta faɗa murya can kasa-kasa, hannu yasa ya ɗago da haɓarta fuskokinsu su fuskantar juna. "Babyn daddy kin cika tsoro da yawa fa" murmushi ta sakar mashi tare da yunkurawa zata tashi.
"Ina za ki tashi ki je?" "Wajen zama na mana daddy" ɗan ɗago da bayansa ya yi ta zare hannunta, tana kokarin komawa ta zauna, sai kuma ya jawota jikinsa mai gaba ɗaya, bata wani damu sosai ba, domin tana bala'in kaunar shi kuma ta saba.
"Babyn daddy yau haka kawai nake jin bana son ki raba jikin ki da nawa, ina kewar Jelly da mummy ta sosai, komai ya dawo mani sabo yau" ya kai karshen maganar kamar zai yi kuka. Ɗago da kanta daga saman kirjin nasa ta yi suna kallon juna "Kayi hakuri daddy In Sha Allah za su dawo ka ji" ta faɗa a sanyaye.
Jingina kansa da jikin kujerar motar ya yi yana faɗin "Mummy'n Jelly ta tafi in da ba'a dawowa baby, ba zata dawo ba, sai dai mu mu bita, yau kewarta ya dawo mani sabo, lokacin da ta rasu, nafi shekara uku ina jin tamkar tana a gefena, ba zan ina manta ta ba, a wannan shekara uku kullun na dawo gida ina jin motsinta, ina jin duk wani abin da take yi mani idan na dawo, daga karɓa jata har sauransu, idan na dawo gida sai in ga kamar ta zo karɓar jakata, idan na zauna cin abinci, sai in ji kamar ita take bani a baki, yau komai ya dawo mani sabo". Nan take hawayen da suka cika mashi ido, suka fara gangaro mashi a saman kumatunsa, dama kun san shi da saurin kuka idan baku mance ba.
Jin ruwa ya zuba mata a saman kumatun tane yasa ta ɗago da kallonta izuwa kan fuskarsa, ganin yana hawaye ne yasa ta ɗan tashi daga kwanciyar da ta yi a kirjin nasa, ta ɗan matso ta zauna a saman cinyarsa, ta sanya hannunta tana goge mashi hawaye tana faɗin "Kayi hakuri daddy Allah ya jiƙanta da Rahma, Allah yasa ta huta, ita kuma jelly zata dawo In Sha Allah".
Ji yake yi wani irin yanayi, yau ya tuna da mummy'n Jelly, ga shi sanyin idaninsa ɗaya ɗayar ma bata a yanzu, dama ita yake kallo yana rage kawar mum ɗin ta, abin ya jefa shi cikin damuwa sosai, sosai kuma yake yin wani irin baƙon yanayi lokacin da hannunta ke a saman kumatunsa tana goge mashi hawaye, a hankali ya sauƙo da wayan nan rinannun idanun nasa a kan fuskarta, ɗago kai ya yi suna fuskantar juna sosai, har suna iya jiyo numfashin juna, zubawa fuskarta ido ya yi yana jin kamar ya san mai irin fuakar nan tata, yau da ya kalleta kusa da kusa, sai ji ya yi tamkar ya santa, ko kuma mai kama da ita.
Ganin yadda yake kallonta sosai ne yasa ta yi kakorin barin jikinsa, tun da ta gama goge mashi hawayen nasa, bata kai ga barin jikin nasa ba ya yi maza ya riƙota. "ina zaki ke?" Ya tambaya yana matso da fuskarsa daidai saitin tata, haka kawai ta tsinci kanta da jin tsoron shi lokaci guda ya kamata, muryar ta har sarkewa yake yi wajen furta "Daddy zan koma wajen zama nane sai mu tafi".
Dogon numfashi ya ja tare da sauƙewa a hankali "Baby shekarunki nawa?" Ya tambaya ya kara matso da ita saman kirjinsa. "Nima ban sani ba daddy, amma dai zan kai 15 haka ko 16 years, dan lokacin da muke tare da mamana ta ce shekaruna 12 yanzu kuma kaga rabona da ita shekara na huɗu kenan" ta kai karshen maganar tana zubar da hawaye, ta tuna mamanta.
"Subhanallahi ni fa babay ba wai na tambaye ki bane dan ki yi mani kuka, kin dai kin san bana son kukan ki ko?" Gyaɗa mashi kai ta yi alamar e. "To ki yi shiru ko?" Ya kai karshen maganar tare da sanya hannu yana goge mata hawaye. "Ni na tambayi shekarun ki ne domin ina son tantance shi kin kai ki zama haramun zama a jiki na ne ko dai". Shiru ta yi tana ɗan shasshekar kuka.
Jawota ya yi zuwa kirjinsa sosai yana ɗan bubbuga mata bayanta alamar rarrashi. Minti biyar suka ɗauka a haka kafin ta ɗago kai da nufin ta yi mashi magana, tana ɗago kai hancinsu ya gogi na juna, domin ya rankwafo da kansa yana kare mata kallo.
Wani irin shock ya ji lokacin da hakan ta faru, ita dai duk da kananan shekarun ta ta ji wani abu da batasan menene bane a jikinta, ɗan baya ta ɗan ja kaɗan tana faɗin "Daddy mu tafi ko?" Jinjina mata kai ya yi tare da fara ƙoƙarin kunna motar, zata tashi ya riƙeta dan kada ta tashi, yau gaba ɗaya ya rasa me yake damun shi, baya son raba jikinsa da tata.
"Daddy zan koma saman kujera ta ce" girgiza mata kai ya yi a ya yin da yake tayar da motar ya ce "No ki yi zamanki a jikin daddynki" "Daddy to taya ya zaka yi tukin motar?".
Ɗan shafa kumatunta ya yi yana faɗin "Sarkin tambaya ba, to zaki gani ai, kedai yi kwanciyar ki a jikin daddynki" to ta amsa mashi da