Showing 222001 words to 225000 words out of 355604 words

Chapter 75 - Triplets Book 2 Hausa Novel Complete

10 Dec 2024

2760

ayyuka domin cetar kasarsu, dan shima Lion kafin ya taka matsayin da ya taka sai da ya yi ayyuka fin haka.

Abin da ya faru aka maka shi a Nigeria kuma da har Lion yake jinjina wa yan Nigeria shine, bayan ya kammala kashe gaba ɗaya dabar su dake a Spain ya biyo sahu dan ya karisa wayen dake a Nigeria, ba gaba ɗaya wayen dake a Nigeria bane yan Nigeria, no akwai turawa yan uwansu a ciki, wayan da suke haɗe da baban fatan mu, su dai sun ɓuya ne a cikin wannan gidan suna bawa bakaken fata umarnin da su kashe ko kada su kashe, to ya biyo ne ya shiga cikincin dan ya kashe su, ya yi amfani da ogansu dake dabar Usa wadda bai kashe shi ba, kuma dama bai kashe shi bane ya bar shi, ya ɗaure shi a asalin office nasu na ROW dake a karkashin kasa a Usa, dayawa daga cikinku zaku iya tuna wannan office ɗin, in da ya hukunta wayan nan sojojin, to ya bar wannan ogan nasu na dabar da ya yi ɓaɗɗa kama a ciki ne saboda ya cigaba da gaya mashi ina sauran yan ta'addan suke, shiyasa ya yi aiki sosai ya shiga jikin ogan nasu ya so shi sosai ta yadda baya ɓoye mashi komai, ya mai da shi babban yaronsa, to da wannan dama yake amfani yana mashi wayo yana kashe yan daban, wata sain haka kawai zai kashe wasu daga cikinsu idan ogan ya tambaye me yasa ya kashe su, sai ya ce ai ya gano su yan leken asiri ne wata kungiyar ta'addancin ne, hakan yasa ya zama ko ya kashe wani a cikin su ba'a tambayarsa dalili, kuma hakan ne yasa ya zama makusancin su saboda a tunaninsu yana da baiwa yana kama masu yan leken asiri, babu san yana yi masu kisan mummuƙe bane.

Yana shigowa Nigeria da kallo ɗaya yan daban Nigeria suka yi mashi suka kama shi, suka ce lallai ba ɗan ta'adda bane wannan, ya gaya masu waye ya turo shi, daga karkashin wace hukuma yake, wannan shine abin da ya sa Lion ya jinjinawa kaifi kwakwalwa ta yan Nigeria, yan kasashe da dama basu iya gane cewa James ba ɗan ta'adda bane, babba ne a cikin hukumar CIA, amma yan Nigeria da kallo ɗaya sun yi ram da shi, abin ya sa Lion ya jinjinawa Nigerians. Shi kuma wanda yan ta'addan nan suka yiwa yanka rago, ba kowa bane fa ce shine DIA babban mataimakin James ɗin ne awajen aiki, lokacin Lion ya gane hakan ya yi farinciki ganin James ba ɗan ta'adda bane, so kuskuren da James ya yi a wajen shine yadda ya shiga cikin yan ta'addan tsundum, kuskure na biyu kuma ɓoye masu da yake yi, kuskure na uku kuma sayar da rayuwarsa da ya yi. Duk guje gujen da yake yi yana yi ne dan kada TRIPLETS nasa su gane ne, saboda yasan ba za su taɓa yarda da hakan ba, kuma yanzu ma ba za su yarda da hakan ba, ya yi aiki sosai wadda ko General ba zai gwada mashi aiki ba, wannan dalili yasa Lion ce wa Tga James ya fi karfin sa, abin da ya yi abune mai kyau amma Lion ba zai taɓa yarda da hukumar CIA ba domin a yanzu haka James ba mallakin su bane, mallakin CIA ne domin ya riga da ya sayar masu da kansa. BABBAR MAGANA, A TAKAICE WANNAN SHINE WANENE JAMES DA KUMA HALIN DA YAKE CIKI A YANZU, KO BAN ZURFAFA BAYANI BA ZAKU IYA FAHIMTAR INA AKA DOSA!! MU KOMA CIKIN LABARINKU.

Story

Shiru ya yi na tsawon mintoci kamar 10 haka kafin ya fara magana gently. "Prof James ba ɗan ta'adda bane, kamar yadda ka ɗauka, amma dole zan hukunta shi, dole ya karɓi hukunci mai tsanani domin ya yi mani laifi" Zaro ido Imran ya yi yana faɗin "Ban gane ba dan Allah ka yi mani baya ni dallah dallah". Shiru ya yi, ya ɗan jima a haka kafin ya bawa Imran labari sama-sama kamar yadda dai na gaya maku waye James ɗin.

Ba ƙaramin daɗi Imran ya ji ba, sai dai kuma idan ya tuna cewa Lion ya ce sai ya yi mashi hukunci mai tsanani na sai da kansa wa CIA da ya yi, sai gaba ɗaya ya ji kuma jikinsa ya mutu, baban damuwar ma ba su san iya kar abubuwan da CIA suka sanyawa James ɗin ajikinsa ba, sai dai Lion yana bincike akan me da me suka yi mashi, dan ya san ta yaya za su iya samu su fitar da shi daga hukumar.

(Ni kuma na haɗa kayana zuwa wajen RIMSHA wata kila kafin na dawo su Lion sun ɗan gama jira)

🔥RIMSHA🔥

Sai zumuɗi take yi yau ta je school, fuskarta har wani kyalli yake yi saboda tsantsan farincikin dake a tattare da ita. Karfe 2 na rana daidai ta dawo, Akil ne ya je ya ɗauko ta, duk da busyn nan da yake a ciki, hakan bai hana shi kula da amanar da Imran ya bashi ba, ko da ya ɗauko ta bai tafi ba, ya tsaya yana kallonta har ta shiga part ɗin Imran, sannan ya juya kan motarsa dan suje su san yadda za'a kai kuɗin karɓar Aafia da Rufee, da farko yan ta'addan sun ce da daddare za'a kai kuɗin, daga baya kuma suka sake fasawa wai da rana za'a kawo, hakan yasa ya ce to shi zai kai ya karɓo A'afia ɗin. Kada ku mance Jinin Umaiya basa taɓuwa ta daɗi

Ko menene a jinin Umaiya oho? Waye ma ita ɗin? Mu je dai zuwa akwai labari agaba.

Rimsha tana shiga cikin palon yaya Imran ta tarar da Akila, a lokacin ta gama yi musu girki ta yi wanka.

Tana ganin Rimsha da sauri ta zo ta rumgumeta tana faɗin "Welcome my dear" ita ma Rimsha rungumarta ta yi tana mata oyoyo tare da tambayarta ya gida, nan ta ce mata ai ita ma karfe 12 ta dawo daga school, shine ta ce bari ta yi masu girkin abin da ta iya dafawa wato shinkafa da miyar steew, ita ma Umaisha yanzu da Akil ya fahimci me yake faruwa tsakaninta da Ammie sai idan zai fita, sai su fita tare ya kawo Part ɗin Imran ya ce ta zauna kada ta koma Part nasu sai ya dawo, abin da ya sa kuma bai kai ta gidan saba, saboda babu kowa kuma yanzu yana busy ba zama yake yi ba, ita kaɗai a gidan zata ji tsoro sosai, ya ce sai ya gama abin da yake yi, ma'ana kenan sai sun gama da case ɗin Aafia, zai mai data gidan nasa kafin su koma Madina, hakan yasa yake barinta suna zama a tare gaba ɗaya a part ɗin Imran ɗin tun da shi baya nan.

Wanka Rimsha ta fara shiga kafin komai, ko da ta je yin wanka sai faman shafa sunan Lion take yi, ita kaɗai kamar zautatciya sai murmushin take yi a toilet, har wani lumshe ido take yi kamar shine yake shafa mata wajen, abin da ya bata mamaki kuma ya ɗaure mata kai shine yadda akayi sunan yake matsawa zuwa saman tula-tulan da kyau a nata ganin, bata san cewa asali ma akan su ta yi zanen ba, lokacin dai basu girma bane suna kanana, sai take ganin kamar baa kansu bane, abin da bata sani ba shine, kullun breast ɗin nata kara cikowa suke yi, wajen da ta yi rubutun yanzu duk ya ciko sosai, shiyasa take ganin kamar rubutun na matsawa ne.

Bayan ta yi wanka ta ɗauro alwala ta fito ɗaure da towel a kirjinta, sai santin dark black curly hair ta Akila da Umaisha suke yi, ga shi jiya sun sha gyara gashin har wani kyalli yake yi, kunshintan nan ba'a magana.

Shiryawa ta yi tsab cikin Pakistan wando fari rigar blue gyalen ma blue, ba karamin kyau ta yi ba, sai ta saje da indiyawa abinta, simple make up ta ɗan yi tare da feshe jikinta da perfume ta zo ta yi sallah.

Bayan ta idar ne Akila ta ce suje su ci abinci, to ta amsa da shi dan dama tana jin yunwa sosai, 1k ɗin da Akil ya bata dan sayan abu a school, bata sayi komai ba, ta dawo da shi a jakarta, dan bata saba ba, abin da ta saba shine tafiya da abinci daga gida, kuma yau saboda zumuɗi bata ɗauki abincin ba, duk kuɗin da daddynta yake da shi bai koya masu saye sayen abin da ake sayarwa a shop na cikin school nasu ba, hakan yasa yanzu ko ba'a basu kuɗi ba sun saba, duk wani kayan cima su biscuit, chocolate, har ice cream, yogurt duk daga gidan mun ɗin su ke shirya ma su a lunch box ɗin su, KUMA HAKAN YA FI SHINE DAIDAI, KADA A SABA BAWA YARO KUƊI, KODA BISCUIT ƊIN NE ARINƘA SAYA MASHI SAI ANA SANYA MASHI A BOX ƊIN NASA, DOMIN BAKA DA TABBACIN ZAKA RAYU DA YARONKA HAR YA KAI MUNZALIN YIN HANKALI, TO YA DAI KAMATA DUK ABIN DA YAKE SO ASAYA A BASHI, KADA A RINƘA BASHI KUƊIN KAI TSAYE!!!

Suna ƙokarin fita daga cikin ɗakin ne wayar Rimsha ya fara kara, haka kawai ta ji gabanta na faɗuwa, kamar ba zata ɗauki wayar ba, sai kuma ta koma ta je ta ɗauka, new number ta gani, zubawa number ido ta yi tana mamakin ita dai tasan cewa Yaya Ahmad da Aunty Akila ce kawai ke da number wayarta, ko Imran bata da number wayarsa, tana ta tunane tunane har wayar ta katse, yana katsewa sai ga saƙo ya shigo, Ki kunna data, shine kawai abin da aka rubuta a saƙon.

Cike da tsoro ta kunna data, tana kunnawa video call yana shigowa tare da wani sakon a WhatsApp, sakon ta fara karantawa da wannan number kuma. Yaya Imran ne ki ɗauki kiran, a wajen heartbeat na karɓin number ki, shi abin da ta gani a WhatsApp ɗin. Bata san time da murmushi ya suɓuce mata ba, da har ta tsorata sosai.

Picking na video call ɗin ta yi tana murmushi, wani irin muguwar kaɗuwar gaba ta ji lokacin da dara-dara sleeping eyes nata suka sauƙa akan Lion ba yaya Imran ba, yana zaune a gefen gadonsa yana ɗan latsa wayarsa, kansa na a kasa, da alama abu mai muhimmanci yake yi, da alama kuma bai san Imran ya sa mashi camera ba, har wani shocked ta ji jikinta ya yi, ta kasa motsawa, yau ga shi nan a gabanta ba face mask, kamar a mafarki, sai faman lumshe dara-dara blue eyes nasa yake yi, kamar mai jin barci, wayan nan zara zaran eyelashes ɗin nasa, da ya lumshe ido sai ki gansu kamar ya sanya na kari sabo tsawon su.

Hannu tasa ta toshe bakinta tana bin jikinshi da kallo shi kuma Imran yana bin fuskar ta da kallo, yana jin matsanancin farinciki yau ya sakata farinciki, zuba mata ido kawai ya yi yana kallon yadda take bin Lion da kallo, da wayan nan dara daran sleeping eyes ɗin nata, kwata-kwata bata kawo a ranta cewa Imran ɗin yana kallonta ba, dan kunga ya juya mata cameran.

Ganin ta yi shiru tana kallon waya ba wani motsi ne yasa Akila ta zo ta leƙa wayar tana faɗin "Me kike kallo kika natsu haka kodai....." Bata karisa maganar ba ta ɗauke wuta sakamakon sauƙa da idon ta ya yi akan Lion, ita kuma Umaisha tuni ta yi waje tun lokacin da Akila ta ce su tafi cin abin, sai tayi gaba.

Suna tsaka da kallonsa basu ankaraba sai gani suka yi ya ɗago wannan fusataccen fuskar nasa, kai tsaye kuma sai kan Imran ya sauƙe idanunsa, yadda kasan su yake kallo saboda saitin cameran yake kallo, razana tasa Rimsha ta saki wayar tata ta faɗi kasa, ba ita kaɗai ba har ta AKILA kwarjininsa ya razanata sosai da sosai, da kyar ta iya jan numfashi tare da haɗiyar wata wahalallen yawu ta ce "Rimsha aiki na gaban ki, wlh dole ki suma ashe haka yake da bala'in kyau, kai kai kai tab sai ki shirya wannan fusataccen fuskar kamar zaki, gaskiya sai kin dage, innalillahi kina ganinsa, wlh ni da nake kallonsa cikin face mask ban zata haka bala'in kyau nasa ta kai ba, ga gwarjinin bala'in, ni nayi nan Allah yasa kada na kara ido huɗu da shi, ya tsaya a iya nan kawai". Ta kai karshen maganar tare da nufar wajen.

Har ta kai kofar fita kuma sai ta ga Rimsha fa ba ta motsa ba, da sauri ta dawo ta taɓa ta tana faɗin "Ke lafiya?" Ashe suman tsaye ta yi, irin abin nan da ake cewa fitar ruhi na yan mintuna, shi Rimsha ta yi, kamar wadda ta suma haka ta kasance, bata ji kuma bata gani, sai da Akila ta zaunar da ita saman bed tare da kawo mata ruwan sanyi dan tasha zuciyarta ya yi sanyi, kafa mata robar ruwan ta yi a bakinta bayan ta buɗe, tanayi yana yi mata dariya, cike da zolaya ta ce "Rimsha dama ba za ki iya ba kika fara? Tab ai kuwa tom da sauran suma a gabanki, Allah ya nuna mani ranar da zai ga zanen nan kuma in ga ta tsiya, wata kila mutuwa zaki yi ranar ko? In Sha Allah sai ya ga zanen nan zaki yabawa aya zakinta kuwa, ke ba yar soyayya ba" tana magana tana dariya.

Rimsha kuwa sai da ta ɗauki good 20mins kafin ta iya dawowa daidai ta watsake, da taimakon Akilar, bayan ta watsake ma ta jima zaune a wajen, ita wannan fusataccen fuskar tasa ce ke matukar razana ta, idan ta kalli wannan fuska sai ta ji kamar ita ya zo kashewa, bayan fuskar kullun a fusace ga kuma bala'in kwarjini a tattare da shi, sannan ga dara-dara idanunsa masu wani irin yanayi na rikitar da wanda ya kalla, abin sun haɗu da dama ne akan fuskar tasa.

Bayan ta tawo daidai ne suka lallaɓa zuwa palo, Akila ce ta dawo ta ɗauki wayar suka wuce Palo.

Suna zama Akila ta fara dube dube a wayar, sai taga hotuna da videos nasa kusan guda 20 Imran ya turawa Rimsha, wata hoton ma tun suna school.

Ba karamin rikicewa suka yi ba, kuma bin da ya kara rikita su shine hoton TRIPLETS da Imran ya toro, James ne ya ɗauke su hoton suna kwance a saman katafaren bed ɗin Lion ɗin , har ma da wani shot video da James ɗin ya ɗauke su suna a bedroom na Lion, Michael yana kwance saman bed yana zancen yana son kuɗi, shi kuma Lion yana zaune a befen bed ɗin a lokacin yana latsa laptop, James ɗin kuma yana faman serving na Lion abincin, bayan ya ɗauke su su biyu, sai ya juyo da camerar ya ɗauki kansa.

Wannan hoto da video na TRIPLETS ba karamin tashin kan su Rimsha ya yi ba, dama su uku ne, shine abin da suka iya faɗa kawai, ga su da yake jini ba wasa ba sai su ka yi masu kallon kama ɗaya, sun razana sosai.

Wunin yau dai abin da suka yi ta kallo kenan, kuma ganin videos ɗin da pics ɗin yasa Rimsha ta rage tsoron fuskarsa, saboda ta yi ta gani sosai, ta wuni tana gani.

(Yau fa Rimsha duniya ta samu, an samu sabon Film, Imran nata kara hura mata wuta, zaki yi bayani, ki biye mashi ke dai ya kai ki ya baro, ki zama ba tsuntsu kuma ba tarko, dan ina da tabbacin daga ke har Imran ɗin naushi ɗaya ya isa Lion ya tura ku in da ba'a dawowa🤣)

Bari mu waiwaye gidan ABBI tun da ita dai Rimsha yau duniya ta samu.

Wani uban kwalliya ta ci, da yake ita mace ce mai gyran jikinta sosai, tana shan kunun larabawa, wato alkama da farar shinkafa, sai hakan yasa ba zaka taɓa cewa ta haifi su Irfan ba, ga shi ba laifi tana da kyanta daidai gwargwado kuma ya haɗu da gyara, dan gaskiya Hajiya Hadiza tana kashewa jikinta kuɗi ba wasa, shiyasa take bala'in shiri da Hajiya Batula wadda ta kasance kanwar su Abbi ce, ita ce autar su, tana aure ne a Maiduguri, duk wata macen da take gyaran jiki a kusa da su, zaka tarar da wuya idan bata san Hajiya Hadiza ba, gata da son kunshi, makirci, kistsa, ba abin da bata iya ba.

Yau wasu shegun riga da sket ta saka, sai ta dawo kamar yarinya yar 25 years, tayi kyau ba karya, akwai ta kuma da son cin chewing gum, haka ta zuba wasu shegun chewing gum nan a bakinta masu bala'in kamshi, sai wani kas-kas-kas take abinta, kayan nata sun bi shap ɗin ta sun zauna, da yake akwai shape ɗin, ita Umaisha ta gado akwai sss sosai, saboda tsabar gyara har surgery na tumbi ta biya aka yi mata, sai cikin nata ya koma plat kamar na budurwa yarinya karama, hakan ya bata daman sanya duk irin ɗinkin da take so kuma ya zauna mata daidai, sai tashin wani shu'umin kamshin perfume na Hajiya Batula da ta haɗa nata take yi, tana kwance saman bed nata tana ɗaura kafa ɗaya bisa ɗaya tana wani shan kamshi, sai da ta ji fitowar Abbi sannan ta sanya wani shegen flat shoe a kafarta mai shegen kyau ta fito waje.

Tana fitowa suka haɗu da shi da aunty zai wuce Aunty zata raka shi, tsabar iya kirsa da makirci har kasa ta tsugunna irin ladabin nan ta ce "Ina wuni sahibina?" Kamshin perfume ya daki hancin Abbi, tsabar kyan da ta yi ma da farko bai gane wace ce ba ce, ya ɗauka wata baby yar cakwai ce, sai da ya ji Muryarta ya gane.

Bata barshi ya yi dogon tunani ba ta miƙe tare da karɓar jakar hannun Aunty tana faɗin "Kai kanwata bari na hutasheki, kinga kin jima kina yi mashi rakiya, yau bari na karɓa maki, ki huta kema, amma sahibina gaskiya wannan kanwar tawa akwai ta da kirki, baka ga da na dawo gidan nan yadda ta rinƙa ɗawainiya da ni ba, har da ce mani fa


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login