Showing 300001 words to 303000 words out of 355604 words

Chapter 101 - Triplets Book 2 Hausa Novel Complete

10 Dec 2024

2810

abin da zata faɗa sirri ce tsakaninta da ƴar uwarta Adivar.

"Adive i knew what am going kin gane? Ki kwantar da hankalin ki yanzu ai ba yakarsu za mu yi gaba da gaba ba, saboda ma ba ta yadda za'ayi mu yake su muna cikinsu, shiyasa kika ga duk wani hujjoji dana tara ban bari su A'isha sun gani ba saboda suma ban yarda da su ba, kuma kema ba wai na yarda dake ɗari bisa ɗari bane, no ban yarda dake ba, kuma abin da yasa ban yarda dake ba shine kin kwana biyu a nan kafin na zo mai yiwu wa sun canza maki wani abin daga tunaninki a yadda na sanki, shine kawai..... Juya harshe ta yi cikin harshen Hausa ta cigaba da cewa "Ina son ne yanzu mu nuna masu jan ido, mu nuna masu ba su isa suce zasu rinƙa bamu umarni son ransu ba, fitowa zamu yi mu nuna masu mu fa mun fi karfin su, yanzu muma idonmu ya buɗe, ba wai nace mu fito mu yaƙesu kai tsaye ba, a'a juyamu da suke yi suna mana abin da suka ga dama shi nake son mu dakatar da su first, idan muka yi faɗa da su sau ɗaya sau biyu wlh ko ba komai zasu fara jin shakkar tunkararmu da wani rainin hankalin, kuma ba komai ne zasu rinƙa kwasowa suna kawo mana ɗakin nan namu ba, sannan bugu da kari ba ko da yaushe bane zamu na kin yarda da maganarsu ba, wata sain mu yarda amma fa idan muka je wajen wadda yake bukatar mu to a nanne zamu nuna mashi asalin bariki, yanzu yakin zai fara ne daga kan masu zuwa nan wajen dan biyan buƙatarsu da mata, ba da su Zinariya zamu fara ba, zan gaya maku dabarun da zaku na bin dan tsira daga hannun azzaluman nan wato Alhazawan nan".

To suka amsa mata da shi tare da shirya yadda zasu ɓollowa lamarin, wannan ta kawo nata shawarar wannan ma ta kawo tata shawarar, haka suka rinƙa haɗawa Jehan tana tantance shawarar da za su ɗauka suyi amfani da ita, daga karshe dai suka yanke shawara ko wani dare misalin karfe ɗaya idan kowa ya yi barci za su fita su rabu izuwa sauran ɗakunan domin su sami damar da zasu tattauna da sauran waƴan da ke a cikin gidan, dan su haɗa kai su haɗa karfi da karfe su gudu tare su tsira tare, wannan kuma shawarar Jehan ce ta kawo, kuma dukka sun aminta da shawarar tata kuma sun ɗaura ɗamarar yakin ba kaɗan ba.

Da haka ko wance ta zauna jugum jugum a gefe da gefen baff ɗin wanka suka buga uban tagumi suna tunanin yadda za'ayi su fita daga cikin toilet nan, ga yunwa ya fara addabawa rayuwarsu, dukkansu fuskokinsu abun ban tausayi, sun yi wani wiki wiki da su, Jehan ce kawai mai ɗan kwari a cikinsu, Adiva kam da yake bata shiga tashin hankali sosai kamar na su Jehan ba sai ta shiga damuwa sosai, dan ma dai Jehan na kara kwantar mata da hankaki ko da yaushe ne, badan haka ba, da akwai matsala.

Idan muka koma ɓangaren gidan Abbi kuwa

Idan muka koma ɓangaren gidan Abbi kuwa zaune suke misalin karfe 9 na safe, Abbi ne da Aunty kawai a palon sai hiransu irin na masoya suke yi cike da girmama juna da kuma mutunta juna, sai zolayarta Abbi yake yi ita kuma tana biye mashi, abin gwanin ban sha'awa da burgewa.

Da akan yau za su je gidan su Hanan wato Katsina, amma da yake daddyn Jelly baya cikin natsuwarsa yau sai Abbi ya ce su bari sai ranar Monday, hakan yasa aka ɗaga tafiyar domin dama da shi da daddyn Jelly da Irfan da Imran sai Akil za su tafi da Hanan ɗin.

Hanan kuwa tana ɗaki a kwance saman gadonta tana kallo a wayar Aunty, yanzu damuwarta ya ragu sosai da sosai.

Wani irin fitinannen kamshi perfume ne ya daki hancin su Abbi, cikin sauri ya ɗago kansa kusan a tare da Aunty suka kai kallonsu saman benen dan daga nan kamshin yake fita.

A hankali take sauƙowa, kafarta na sanye da bedroom slippers jikinta na sanye da wasu shegun riga da wando, wandon jeans ne ya natseta sosai ta yadda ya fito mata da ainahin surar jikinta, while shikuma rigar ya kasance irin t-shirt ɗin nan ne masu kananan hannun wadda ba su wuce kafaɗarta ba, skin na matar nan sai wani sheki yake yi, ya ji gyara iya gyara kamar wata ƴar 25 years, ta fito a cikakkiyar macenta, hajiya Hadiza ba dai ɗaukar wanka ba, ga jikinta kuma mai shegen kyau kamar ita ta tsarawa kanta, gata gwana wajen cin chewing gum, yanzu ma tana taku tama wani kas kas kas da chewing gum, aunty kuwa kullun sai iya kwalliya da lace da atamfa or shadda, ko irin kananan kaya masu ɗan fasalin nan bata sawa, ita gata malama ta sha sunnah ta ƙoshi sai iya saka manyan hijabai kamar wata matar liman, a gida ma zumbula hijabi take yi abinta.

Tuni Abbi ya kafe Ommu da ido ya kasa ɗaukewa, yadda take taunar wannan chewing gum ɗin ya ilahi ya lillihi ba'a magana dan taunar ma da salo da rangwaɗa ake yi.

Ta gaban Abbi ta zo ta wuce sannan ta koma hefensa saman hannun sofa ta zauna tare da rankwafo da kanta daidai da tasa, cikin salo da rangwaɗa ta ɗan hura mashi chewing gum ɗin a fuska.

Wani dogon numfashi ya ja tare da sauƙewa a hankali, har lokacin ya kasa ɗauke idanunsa daga kanta, gata bata yawan yin make up irin na haukarnan wadda idan miji ya zo ma zata ɓata mashi jiki, no ita simple make up take yi wadda zai kara tsatso mata da kyanta kuma ba zai ɓata wa mijinta jiki ba, ya kalla ya ji daɗi ya shafa face ɗin tata ya ji sanyi a ransa, ya rungumeta ya ji nishaɗi ba wai ya rungumeta Foundation ko powder ta ɓata mashi riga ba.

Kas kas ta kara kyasta mashi chewing gum a kan fuska tare da sanya hannunta a saman idanunsa ta rufe mashi ido tare da kashe murya cike da kirsa da kisisina ta ce "Kai Sahibina irin wannan kallo haka ai sai ka kwashe mani kayan nawa gaba ɗaya, to ni dai gaskiya ban yarda ba Allah kuwa".

Aunty kam sake baki ta yi tana kallon ikon Allah, ta kasa koda motsawa daga in da take, yadda kasan Tv haka ta mayar da Ommu da kallo, yau ga ɗanyen karuwanci tsagwaransa.

Murmushi Abbi ya yi tare da cire hannun nata daga saman face ɗin nasa ya ce "Kai Hadiza ki kyaleni na kalli kayana". A zahirin gaskiya Abbi bai san time ɗin da ya furta hakan ba, kawai dai ya ji maganar ce ta fito mashi daga bakinsa.

Matso da bakinta ta yi kusa da kunnansa kasa kasa ta ce "Tashi muje ɗaki sai ka kalli kayan naka da kyau da kyau zai fi ko?".

Wani irin daɗi ya ji tana ratsa shi da sauri ya dawo da kallonsa kanta, kashe mashi ido ɗaya ta yi tare da sake hura mashi chewing gum ɗinta mai shegen kamshin nan akan face nasa tana sakin wani makirin murmushi, gaba ɗaya Abbi ya susuce ya birkice tare da rasa tunaninsa.

Ita kuma Aunty mamaki take yi akan Ommu ta ci matsu da riga da wando, gani take yi ai Ommu ta yi girma ta sanya riga da wando, wannan sai yara irinsu Ayla, a tunanin Aunty fa kenan, amma kuma ga shi nan da idanunta ta ga yadda riga da wandon ya tafi da imanin mijinta, tana ganin yadda ya susuce lokaci guda har da wani zuba kamalan da bai san yana yi ba, GASKIYA DRESSING WA MIJI KANANAN KAYA DUNIYA NE, MACE DAI BATA TSUFA, IDAN TANA GYARA KANTA IRIN HAJIYA HADIZATU WATO OMMU TO LAFIYA LOU ZATA KARA DA KOMA WACE IRIYAR MACE CE!!.

Miƙewa Abbi ya yi tare da niƙo hannunta yana faɗi "To muje ki nuna mani". Make kafaɗa ta yi kamar karamar yarinya, cikin yanga da kisisina ta ce "Ni aa kafin mu shiga daga ciki sai ka fara ɗaukata munje sayan sire, sai na ci sire tukun nan".

"Haba Hadiza baga nama a gidan nan ba, kuma ga kanwarki Halima ta iya gasa nama sosai zata yi maki ai, yanzu dai ki zo mu tafi".

Halima kuma Aunty ta maimaita a cikin zuciyarta tana tunanin wato ita ce ma zata yi masu tsiren dan cin mutuncin da cin fuska, ita kuwa Ommu abun nema ya samu sai ta sake kashe murya ta ce "Kuma fa hakane sahibina, ni da nake da kanwa ƴar albarka mai kaunata ai na manta ne, Halima ki gasa mani ya gasu sosai, kuma dan Allah ki cika mashi yaji sosai dan abin ya haɗu mani biyu ya ji ta sama ya ji ta kasa abin sai ya fi yi mani yadda nake so".

(Waye ya gane bakar maganar da Ommu ta gayawa aunty a nan?)

Tana kai karshen maganar bata tsaya ta jira amsar Auntyn ba ta wuce sama Abbi ya bi bayanta, wani irin dukukun bakin cikine ya tasowa aunty, da gudu ta miƙe ta yi sama.

Tana zuwa ta faɗa ɗakinta tare da nufar gaban mirror tana kallon kanta dan ta ga dame Ommu ta fita. Tabbas babu abin da Ommu ta fita sai ma wadda ita ta fi Ommu, matsalar shine wayewarsu ita da Ommu daban daban, Ommu ta san duniya sosai da sosai, duk wani makirci ta iya shi sinka sinka, Aunty kuma ta kwankwaɗi hadda ta ƙoshi, banda jawo aya da hadisi ba wani abin da ta iya, da zarar ka taɓota zata faɗa maka suratul Maryam or Yusuf irin su Aaraf, an'am, sai kuma ta koma maka ɓangaren hadisai, Shikenan bata iya soyayya ba bare kula da miji bayan kiss da runguma sai girki, idan tana yi wa su Ayla nasiha kullun nasihar ɗaya ce shine kada su cewa miji a'a, komai ya ce matukar bai saɓawa Allah ba to kada suce a'a, kullun aikin kenan, shiyasa Ayla banda to ba wani abin da ta iya cewa daddyn Jelly, Allah ma yasa shima daddyn ba baya ba a fagen zuba love da shikenan Ayla ma tabi sahun Aunty.

Tsab ta karewa kanta kallo, tafi Ommu hips, ga shi ita ma breast nata a tsaitsaye suke dan bata taɓa shayarwa ba, bugu da kari breast nata na ainahine Ommu kuma nata sai da akayi shaye shayen magunguna tare da wasu shafe shafe sannan suka ciko, nata breast ɗin ya fi na Ommu kyau da ɗaukar hankali, sannan ta fi Ommu kyau, kawai dai Ommu ta fi ta hasken fata ne, kuma shima kaɗan ne.

Kuka ta sa tare da faɗawa saman gadonta tana tsinewa Ommu akan abin da ta yi mata na rikita mata miji da ta yi.

A ɓangaren daddyn Jelly da babynsa kuwa, barcine mai daɗi ya kwashe babyn tasa saboda wahalar da kuma gajiyar dake a tattare da jikinta. Zuba mata idanun nan nasa ya yi yana ta kare mata kallo, wani irin azababben sha'awar tane yake taso mashi, ji yake yi kamar ya sake shigarta a yanzu, sai dai kuma yana tausaya mata, yana son ya barta koda na kwana ɗaya ne ta ɗan huta dan tasha bakar wahala, dan ma dai tana da tawakkali da haukuri ga kuma kaunar shi ne har yasa ta hakura haka, sannan kuma akwai yarinta sosai akanta shiyasa.

Ya jima yana kallonta kafin ya sanya hannunsa ya kara jawota jikinsa sosai tare da lumshe idanunsa yana mai jim tsantsar kaunarta na ratsa ilahirin gangar jikinsa. A hankali ya fara shafa breast nata yana ɗan burza kan nipple ɗin tata a hankaki hankali, wani irin sauƙi na musamman yake ji tana ratsa shi, cikin natsuwa ya matso da bakinsa kusa da tata tare da capko lips nata ya fara tsotsa yana jan numfashi.

A hankali ta fara motsawa alamar tana son tashi, cikin sauri ya kyaleta dan baya son ya tasheta daga barcin da take yi, sai ya hakura ya lumshe idanunsa yana ɗan shafa bayanta har shima barci ya ɗauke sa.

Idan muka koma ɓangaren su Jelly kuwa wato gidan Abbo, Nawid dai wani sabon kula da tattalin so yake bawa Jelly, amma kuma ita ko kallo bai isheta ba, A ɓangaren Abbo kuwa sai shirya ta yadda zai ɗauketa ana gobe ɗaurin aure yake yi, yau saura kwana uku a ɗaura auren, komai ya kankama Ummi uwar biki uwar amarya kuma Uwar ango abin ba'a magana busy kamar network, duk wani tsumi dake karawa mace ni'ima sai da ta sanya hajiya Batula ta bawa Jelly, sannan kuma ga maganin karin girmar breast da aka haɗa mata da kuma fito da shape abin ba'a magana duk wanda ya kalli Jelly sai ya waiga ya kara kallonta breast ɗin nan nata sun cika kamar an hura balo balo, dama hips kam ba baya take ba akwai shi sosai, amma da aka kara fitar mata da shape ɗin ta sai ta kara wani mugun kyau abin ba'a cewa komai, ta zama wata ƴar cas caras da ita, mutanen Maiduguri sun fito da ita, Nawid fa duk ya bi ya susucewa da ruɗewa sosai, kullun cikin lafazata da kuma lallaɓata yake yi, amma duk na banza bata kula shi kuma bata zama inuwa ɗaya da shi, akwaita da riƙo a zuciyarta, tun da ta ruƙe ya ce baya sonta shikenan.

Yauma dai kamar kullun misalin karfe 5 na yamma tana zaune ita kaɗai a ɗakin Ummi tana buga game a wayar Umm, yayin da ƴan biki keta faman hidima na jeka ka dawo, anata girke girke soye soye da sauransu.

Tana kwance ta baje a saman bed na Ummi, sanye take da wani haɗaɗe doguwar riga launin sky blue ta yi kyau sosai, kanta ba ɗankwali gashin kan nan nata ya sha gyara sosai sai kyalli yake yi, kai idan ba ka yi wa Jelly farin sani sosai ba to bazaka taɓa gane cewa ita ɗin bace, saboda wani ruwan kyau da ta kara, komai ya ciko zamzam.

Ta yi nisa cikin game da take yi, bata ji sallamar kowa ba bata ji motsi ba sai gani ta yi an kwace mata wayar tata, cikin sauri ta ɗago kanta dan ganin wanene.

Yana tsaye sanye da suit baki ya ɗaura kayan aikinsa a jikinsa sai wani kayatatcen murmushi yake sakar mata.

Wani mugun kallo ta bishi da shi tare da miƙewa zaune tana faɗin "Ka bani wayata yaya Nawid".

Zama ya yi a gefen gadon yana ƙoƙarin riƙo hannunta, cikin sauri ta zuro kafafunta kasa tare da miƙawa ta nufi waje abinta ta kyale shi nan wurin zaune ruƙe da wuya a hannunsa yana binta da kallo yana haɗiyar yawu.

Tana fita sai kuma ya ji ihunta, da sauri ya miƙe ya bi bayanta dan yaga menene. Kwance ya iskota a tsakiyar palo tana kuka dafe da cikinta, da sauri ya kariso wajen tare da tallabota yana faɗin me ya sameta bayan yanzu ta fito daga ɗakin Ummi lafiya.

Hakan kuma ya yi daidai da shigowar Abbo cikin palon shima ya dawo daga wajen nasa aikin. Da sauri ya kariso cikin palon yana tambayar me yake faruwa ne, me ya sameta.

Jin hayaniya yasa Ummi ta fito daga kitchen ta zo palon, itama tana ganin abin da yake faruwa ta yi maza ta kariso wajen tana ambatar me yake fatuwa ne? Me ya sami baby.

Kuka take yi sosai hawaye bibbiyu, duk Nawid ya birkice sai faman dubata yake yi ko zai game me matsalar tata, shima Abbo ya ruɗe sosai, Ummi kam ba'a magana da yake ta fi su sonta, ita tun ainahi tsakani da Allah take sonta, amma daga Abbo har Nawid akwai dalilin da ya sanya suke son nata.

Nawid yana ƙoƙarin ɗaukarta dan su shiga daga cikin ɗakinsa kada ƴan biki su taru masu a kai, bai kai ga ɗaga ta ba sai suka ga jini a jikin kayan ta, da yake kayan tata sky blue ne kalar mai haske hakan yasa jinin ya fito ɓaro ɓaro.

Kallon Ummi Nawid ya yi kafin ya ce "Ummi girma ne ya zo mata fa, period ta fara yi, zan kaita ɗakina na dubata tare da yi mata allura In sha Allah nan da minti biyar zuwa goma zata ware ta koma daidai".

Da ɗan karfi Abbo ya furta "Period kuma?!!". Ba ƙaramin mamaki jin yadda ya maimaita kalmar Ummi da Nawid suka yi ba, kamar ba lafiya ba. Jaddada mashi period Nawid ya yi, nan take wani zufa ya fara tsastsafo mashi daga gefe da gefen fuskarsa kamar ba lafiya ba, cikin lokaci ƙanƙani ya sauya ya fita hanyyacinsa, zuba mashi ido Ummi da Nawid suka yi suna kallon ikon Allah, daga jin sunan period ya canza haka, to anya kuwa lafiya? Tambayar da ko wannansu yake yi a cikin zuciyarsa kenan.

Da dai Nawid ya ga matarsa tana ƙoƙarin sume masu a wajen sai ya fita batun Abbo ya saɓi kayarsa a kafaɗa suka wuce da ita cikin bedroom nasa, saman gado ya shimfiɗeta tare da ɗauko A box ya fara duba ta dan ta sami saukin wannan ciwon.

A ɓangaren Ummi da Abbo kuwa, tambayarsa Ummi ta yi akan ko lafiya ya sauya daga jin baby ta fara period, ya kasa amsa mata tambayar tata sai ma wucewa da ya yi izuwa cikin ɗakinsa ya rufo kofa har da murza key, cike da mamaki Ummi ta wuce ta koma Kitchen dan ta cigaba da abin da take yi, abin da yasa kuma bata bi bayan Abbo ba saboda ƴan biki, bata son wata hayaniya ga jama'a cike a gidan, shiyasa kawai ta kyale Abbon ta wuce abinta, amma ta kuduri niyar bayan biki sai ta ji dalilin daya sanya ya shiga damuwa dagajin baby ta fara period.

Shi kuwa Abbo yana faɗawa ɗakinsa ya fara safa da marwa yana zarya tare da tunanin ta yadda zai ɓullowa wannan lamari, a fili kasa kasa ya fara magana shi kaɗai kamar zautatce "No banso kiyi mani haka ba wannan yarinya, bamso yin amfani dake a cikin gidan nan ba, na fi son sai na mayar dake gidana na Abuja idan yaso ki fara


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login