Showing 231001 words to 234000 words out of 355604 words

Chapter 78 - Triplets Book 2 Hausa Novel Complete

10 Dec 2024

2835

cewa dukka wannan shawara ta barshi sai bayan aure ba, kin ce haka zata rinƙa yi mashi kawai, ya kama arinƙa banbance mana, saurayin da za'a aura daban, miji daban atom)

Sosai ta nutsa cikin tunani tana tariyo zancen Aunty a kanta, can kuma sai ta ce "Daddy da farko dai kayi hakuri, In Sha Allah baby jellynmu zata dawo, na biyu kuma..." Bata karisa maganar ba sakamakon matsowa da ta yi ta riƙo hannayensa tare da ɗago kanta, ganin shi da ga shi sai Short da singlet ne yasa ta yanke maganar bata karisa shi ba, kwata-kwata bata yi zaton ba kaya masu ɗan girma a jikinsa ba.

Cikin sauri ta miƙe dan ta bar ɗakin, kankame hannunta ya yi a cikin nasa ya ki bari ta tafi.

KADA KU GA LAIFIN AYLA BATA DA ILIMI KUMA YANZU DA AUNTY KE WAYAR MATA DA KAI, SAI TANA NUNA MATA AKAN KOMAI ZATA IYA YIWA DADDYN JELLY DAN MIJINTA NE, A NATA TUNANIN AI SHI DADDYN JELLY BA ZAI YI MATA KOMAI BA, SHIYASA BATA WANI DAMU BA TAKE BATA WAYAN NAN SHAWARWARI, TO SHI DADDYN JELLY DUTSE NE? KU TAYA NI JI DA GANI, KADA KU MANCE SHEKARA SHA 16 YANA GWAURO🤣 AI SAI DAI MUCE ALLAH YA TSARE!.

"Ina zaki je baby?" Ya faɗa yana matse mata hannunta cikin nasa, wadda shi kansa ma, bai san yana yin hakan ba.

Cikin in'ina ta ce "Ba...ba... ko'ina daddy". Wani irin shauki yake ji a tattare da shi, shiru ya yi yana jin yadda zuciyarsa ke azalzalansa, (sheɗan na gefe😭 Allah ka rabumu da tsinanne🤲)

A hankali ya tsinci kansa da jawota jikinsa, kusan a tare suka sauke nauyayyar ajiyar zuciya, hannu yasa ya laluɓo wayarsa da ya saya jiya dake saman bedside drawer, idanuwansa har sun rikiɗe, yana jin matukar sha'awa ba na wasa ba, har wani rufewa idanun nasa suke yi.

Rungumeta ya yi a jikinsa tare da fito da number Abbi ya fara kira.

Bugu ɗaya Abbi ya ɗauka, muryarsa da kyar take fita ya fara magana "Yaya Deen ina kake?". A ɗan ruɗe Abbi ya ce "Maik lafiya? Ya naji ka haka? Ko dai baka da lafiya ne?" Nisawa ya yi tare da kara matseta a jikinsa, ita kuma bata wani damu ba, domin ba'a gaya mata harancin yin hakan ba, sai ma lafewa da ta yi a jikin nasa.

"Yaya Deen ina lafiya, dan Allah ina kake yanzu". "Gani nan tun da na fito daga masallaci sallar azahar na tsaya muke tattaunawa da malam liman akan ya ɗaura auren nan naka gobe Jumma'a dan ba zan iya bari wannan dama ta kubceba ato, Allah bashi idan aka ɗaura auren sai ta cigaba da zaman ta a Part ɗin namu tana zuwa school ɗin, amma dai da aure a kanta, dan ba zan lamunci wannan rike hannun ba".

Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya ce "Yaya Deen ka ce da liman tun da la'asar ya kawo kai idan an fito sallah kawai a ɗaura auren, daga baya za'ayi duk wani abin da ya rage". Cike da murna Abbi ya amsa da to, dan dama burinsu kenan, ya yi aure ko zai samu natsuwa sosai.

Ba tare da ya katse kiran ba ya ajiye wayar a saman bedside drawer, daga ɗayan ɓangaren Abbi ne ya katse kiran. Dawo da wayan nan rinannun idanun nasa ya yi a kan fuskarta.Ta lumshe ido tana shakar kamshin jikinsa.

"Baby kin ji shawarar da na yanke ko?" Gyaɗa mashi kai ta yi alamar e. "Idan hakan bai yi maki daɗi ba kiyi hakuri, ba zan iya cigaba da saɓawa Allah ba na taɓa ki da nake yi, na san cewa ba zan iya ganinki ban taɓa ki ba, shiyasa kawai gara a ɗaura mana auren in yaso ki zauna da su Sadiya har sai na tashi komawa Kano mu tafi, kinga idan akayi aure ko na taɓaki ba wata matsala".

Ɗago da kaita daga kirjinsa ta yi, a nutse ta ce "Daddy duk abin da ka yi daidai ne, dan Aunty ta gaya mani, ba zaka taɓa yin abin da zai cutar da ni ba".

Wani irn daɗi ya ji a hankali ya ɗago da hannunsa ya shafi face nata yana faɗin "Ban san yaushe, kuma a ina na kamu da azababben so da kuma kaunar ki ba, kina rikita ni dayawa".

"Daddy nima ai ina sonka sosai" "A'a nawa ya fi yawa, kawai ina zaman zamana kin zo kin rikitani" yar murmushin ta yi zata yi magana kenan suka ji muryar Hanan a palo tana doka sallama.

Ayla ce ta amsa mata daga cikin ɗakin.

"Ayla Aunty ta ce wai ba ta ce kada ki daɗe ba? To ki dawo hiran ya isa haka" shine abin da Hanan ta faɗa.

Ayla zata yi magana daddyn Jelly ya rigata da cewa "Ki je ki ce mai ita ya riƙe abarsa, dan haka Sadiya ta barmu mu sha iska" yana magana yana sha fuskarta.

To Hanan ta amsa da shi tare da ficewa ta koma cikin gida.

Shiru suka yi kamar wayan da aka cewa su yi shiru, ya zuba mata ido yana kallon kyakkyawar fuskar ta, yayin da ita kuma take kallon mirror dake a cikin ɗakin.

"Baby ta shi ki hauro gadon gaba ɗaya" ya yi maganar kasa kasa.

Da yake yana ta bakin gadon ne, kuma yadda ya jawota jikinsa kusan rabin jininta yana ta kasan gadon ne, kanta ne ke kwance a saman kirjinsa, shiyasa ya ce ta dawo saman bed ɗin gaba ɗaya.

Ba musu ta miƙe ta haye saman bed ɗin gaba ɗaya, tana hawa ya kara jawota jikinsa tare da cire hijabin jikin nata dan hijabin yana takura mashi, baya shafa face nata da kyau.

"Babyna baki ce komai ba akan auren da za'a ɗaura mana nan da minti goma zuwa Ashirin ba?" Ɗagowa ta yi tana kallon face nasa a sanyaye ta fara magana "Daddy Aunty ta gaya mani abin da ake nufi da aure, kuma na yarda saboda ina son yin rayuwa da kai ta har abada, kana da kirki sosai, kana son farincikina, dole nima zan so ka sosai daddyna".

Hannu yasa ya matse mata ɗan bakin nan nata, a hankali ya lumshe idanunsa tare da buɗesu a saman face nata, har lokacin yana ruke da lips ɗin tata. "Waye daddy?" Ya faɗa da wata iriyar murya wadda da ka jita ba sai an gaya maka ba kasan a kusa yake.

Shagwaɓe fuska ta yi zata yi mashi kuka dan ya matse mata lips sosai, shi kuma zafin da yake ji a jikinsa ne yasa ya ɗan matse mata lips ɗin tata da ɗan karfi, hasalima bai san ya matse da karfi ba, dan jikinsa ke azalzalarsa.

Sai da ya ga ta fara hawaye sannan ya sake lips ɗin tare da kara matseta sosai a jikinsa, ya matso da face nasa daf da tata har suna iya shakar numfashin juna, ya kasa kyafta ido daga kallonta, ita kuma wuyarsa take kallo.

"My baby ba zan ga ji da faɗe ba kina rikita ni sosai" ɗago da idonta ta yi izuwa cikin nasa idon, kamar ta kara ingiza zuciyarsa ne, har wani zirr yake ji a jikinsa.

Dawo da kallonsa ya yi kan laɓɓanta, a hankali ta fara motsasu ta ce "Daddy ni ban san ma taya nake rikita ka ba, ni wlh ban ma san me rikitawan ba, amma dai tom ka gaya mani menene?".

Kasa jurewa ya yi, lokaci guda ya haɗe bakinsa da tata ya fara bata hot kiss, mutuwar kwance ta yi, domin bata taɓa jin wani abu makama mancin hakan ba, kuma bata taɓa gani ba, ita dai tasan Rimsha ta taɓa gaya mata mafarkin Lion da ta yi na zai yi kissing nata, to bata ma san me kiss ɗin yake nufi ba, sosai ta shiga duniyar tunani tare da mutuwar kwance.

Shi kuma sosai yake kissing nata, ya kankameta a jikinsa yana fitar da wani irin numfashi, sai wasa yake da harshensa a bakinta cike da kwarewa. Kiran sallar la'asar ne ya dawo da su cikin hayyacin su.

A hankali ya zame bakinsa daga tata, sai kuma me, wani irin kunyarta ne ya kama shi, ita ma duk da bata san me hakan yake nufi ba, ta ji matsanancin kunyarsa ya kamata,

Ayla bata san kiss ba, duba da yadda ta ta so, ba abinci a gidansu ma bare kuma Tv kallo da zata kalla ko a Film ne, bata da kawa ko yar uwa, daga mamanta dake kwance ba kafiya sai ita ɗin, rayuwarta rabi a wajen bara, rabi kuma a Daular Mutuwa ta kare, baiwar Allah bata san komai ba sai wanda Rimsha da Aunty suka koya mata, dan ma Allah yasa tana sa natsuwa da sanyin hali, ba dan haka ba ai da shikenan kuma sai dai muce Allah ya tsare.

Shiru ta lafe a jikinsa tana tunanin menene daddy ya yi mata, shi kuma yana kankame da ita yana lumshe da idanunsa, dan baya son buɗewa bare su yi ido huɗu.

Suna zaune a wajen ya kasa motsawa, yana ji har aka idar da Sallar la'asar, ba shi ya tashi motsawa ba har sai da wayarsa ta fara kara alamar shigowar kira.

Da kyar ya iya kai hannu ya ɗauki wayar, tamkar wadda aka zarewa laka, haka ya dawo. Picking na call ɗin ya yi tare da kara wayar a kunnensa, ya kasa magana ya yi shiru yana jiran wanda ya kira ya yi magana.

Daga ɗayan ɓangaren Abbi ya ce "Hello Maik an ɗaura fa, yanzu muka gama, saura na kira su Irfan na sanar da su".

Jinjina kai kawai ya yi tamkar Abbi na a gabansa, daga nan ya maida wayar saman bedside drawer ya ajiye, jin bai yi magana ba yasa Abbi ya yi tunanin ko ba lafiya yake ba kawai yana ɓoye masu ne, cikin sauri ya kamo hanyar gida, dan ya zo ya duba ɗan uwansa lafiya ko yaya ake ciki.

Shi kuma bayan ya ajiye wayar, sai ya sa hannunsa ha ɗago da fuskarta suna fuskantar juna, idonta a lumshe ta kasa buɗe wa dan tana matsanancin jin kunyarsa.

Kamar mai raɗa haka ya furta sunan ta babyna, kasa-kasa ita ma ta amsa mashi, da murya ciki ciki, da alama dai ita ma jikinta ya karɓi saƙo yadda ya kamata.

"Yanzu fa kin zama matata, halak na, ni kaɗai" yana magana yana jingina kansa da jinin headboard na gadon tare da ɗaga kan nasa sama kamar mai tunanin wani abin.

Hannunta dukka biyu ta zura ta bayansa ta kankameshi da kyau, a shagwaɓe ta ce "Daddy shikenan dama haka kawai akeyin aure? Ni na zaci da ake cewa igiya uku akan mutun, na zaci sai an ɗaure shi da igiya uku ai kafin nan ya zama matar aure". Tana magana idanuwanta a lumshe ya yin da hannayenta ke a saman bayansa ta ɗaura su, tana ɗan yawo da su a wuraren.

Nisawa ya yi tare da ɗago kansa daga jikin headboard ɗin, da kyar ya waro idanunsa gaba ɗaya a kan face nata.

Ran kwafo da kansa ya yi izuwa daidai saitin face nata, kasa-kasa ya kira sunanta, tana ɗagowa ya zura harshensa cikin bakinta tare da kankame ta sosai a jikinsa, wannan ya wo da hannun nata da take yi a bayansa, ba ƙaramin kara rikita shi take yi ba.

Shima zura hannayensa ta bayanta ya yi, ya hauro da hannunsa ɗaya ta daidai kanta, a hankali ya ɗan ja kan nata baya ta yadda zai sami damar yi mata kiss sosai, while ɗayar hannunsa kuma, yana ta kugunta ta bayan, ya tallaɓo ta da kyau.

Ita dai idonta a lumshe sai karɓar saƙo kawai take yi. Almost 5mins suna a haka kafin ya saketa, suna sauke numfashi a hankali hankali kusan a tare kuma.

Sun ɗauki 10mins a haka kafin ya ce "Baby ki yi wa daddy afuwa kin ji?" "Daddy afuwar me kuma?". Ta yi maganar tana ƙoƙarin zame hannunta daga bayan nasa.

Riƙo hannunta ɗaya ya yi cikin nasa, ɗayar hannun nasa kuma, ya yi amfani da shi yana shafa kanta zuwa wuyarta da ta kwantar masa a saman kirjinsa.

Yana ƙoƙarin yin magana, suka ji sallamar Abbi a bakin kofa. Kallon face nata ya yi, ko ajikinta bata wani damu ba, ɗagowa ya yi ya amsawa Abbi sallamar.

Bai gama rufe baki ba, Abbi ya shigo a ruɗe yana faɗin "Maik me yake damunka? Ya na ji muryanka can kasa? Baka da lafiya........" Bai kai ga karisa maganar ba idonsa ya sauka akansu gaba ɗaya, kasa da kai daddy'n jelly ya yi dan ya rasa bakin magana, kuma har ga Allah bai so barin Abbi ya shigo ɗakin ba, kawai dai ya kasa yin magana sosai ne, kuma shima Abbin yana ruɗe ne, burinsa kawai ya shigo ya ga wani hali ɗan uwansa ke a ciki da yake magana kasa kasa haka, da kyar ma ya iya tsayawa har sai da Maik ɗin ya amsa mashi sallamar, amma jikinsa har tsuma yake yi, akan ya zo ya ga ɗan uwansa.

Ganin haka yasa Abbi juyawa da sauri har kamar zai faɗi, ya fice daga ɗakin, yana fita kuma a tare suka sauke nauyayyar ajiyar zuciya shi da daddyn Jelly ɗin.

"My baby jeki kiyi wanka ki yi Sallah time na kurewa, idan kin yi sallah sai ki kawo mani abinci na kin ji? Amma fa daga yau idan zaki zo nan, kada ki saka mani manyan kaya bana so, kisa kanana sai ki ɗaura hijabi a sama, anjuma da daddare ma dole muje shopping dan na saya maki kananan kaya sosai, dan ina son su, suna kuma birgeni" ya kai karshen maganar tare da manna mata kiss a goshi.

Murmushin ta yi tare da miƙewa daga jikin nasa ta sauƙo kasan gadon, zuba mata ido ya yi yana kare mata kallo, yau ba hijabi a jininta, dan ya cire mata, kalle kayarsa yake yi sosai.

Hannayensa dukka biyu ya ɗaura a saman hips nata ta gefe dukka biyun, ya riƙosu yana faɗin "Baby ke fa zaki yi kiba kaɗan idan kika huta kika samu kula da abubuwan da suka dace" yana magana yana kare ma breast nata kallo, masha Allah da su, dan duk tafi su Rimsha shekaru, kuma ta fisu cika, barema yanzu da ta fara samun kulawa da kwanciyar hankali, sai kara cika take yi abinta, abin sai dai Masha Allah.

"Baby baki ce komai ba?" Murmushin ta yi kafin ta ce "Daddy ai bansan me zan ce bane" "Yau shawarar Sadiya ya kare kenan?"

Dariya ta yi har sai da fararen hakwaranta suka bayyana, tana ƙoƙarin yin magana ya rigata da cewa "Tom kullun idan kika yi sallar isha ki zo na fara koya maki soyayya sai karfe 10 zamu tashi ki je ki kwanta, amma fa kada ki ce da sadiya soyayya zan koya maki, kice kawai karatu zan fara koya maki, idan ta ce na me, ki ce mata na Alqur'ani mai girma, daga nan sai ki zo mu koyi soyayya ko?" To ta amsa mashi da shi, tana ƙoƙarin ɗaukar hijabinta, sunkuyawa da zata yi, wuyar abayar jikinta ya yi kasa, zubawa kyawawan breast naya ido ya yi yana kare masu kallo.
Duk sun cukuikuye hijabin nata, kamar anyi yaki akan shi.

Haka ta ɗauka ta miƙe ta zura a jininta, ji yake yi kamar ya jawota jikinsa ya yi wasa da breast ɗin nata kaɗan, amma kuma sai ya share kawai dan lokacin yana yi masu nisa basu yi Sallah ba.

"Daddy na tafi" shine Abin da ta faɗa tana ƙoƙarin nufar waje. "Baby haka zaki tafi babu yiwa mijinki kiss na bye-bye?" Ju yo wa ta yi ta ce "To ai daddy ban iya ba" Alama ya yi mata da hannu akan ta zo.

Matsowa gabansa ta yi, zata duƙa ya yi saurin nuna mata saman cinyarsa akan ta zauna. Ba musu ta zauna tana kallon kyakkyawar kwantacen gashin dake a gefe da gefen fuskarsa, ga kuma wani dake kewaye da ɗan bakin nan nasa, ya yi round.

Matso da bakinsa ya yi saitin saman tata tare da ɗan kamo lips nata na kasa ya fara sha cikin salo. Kaɗan ya sha ya sake ta yana faɗin "Wannan shine kiss, kuma shi zaki rinƙa yi mani kullun idan kika zo, shine gaisuwata kin ji ko?" Gyaɗa mashi kai ta yi alamar ta ji.

"To shikenan ta shi ki je ko?" Miƙewa ta yi da sauri ya nufi kofar kita. Har zata fita sai kuma ya kira sunanta a hankali, juyowa ta yi tana kallonsa.

"Baby kada ki gayawa wani abin da muka yi fa, wannan sirrin mijin ki ne kin ji ko?" To ta amsa mashi da shi sannan ta fice, abin da ya sa ya yi mata wannan magana kuma, saboda yasan duk mutumin da zai zo ya gaya maka ga yadda suka yi da wani makusancinsa, to ba makawa haka kaima yake ɗaukar yadda kuka yi ya gayawa wani, to dik abin da Aunty ta gaya mata, haka take gaya mashi ba ɓoye ɓoye, ya san cewa tsab zata iya gayawa Aunty ga yadda suka yi, kuma ya san Aunty da shegen tambaya kamar me, shiyasa ya yi saurin dakatar da abin ma da wuri.

Da kyar ya iya miƙewa ya shiga toilet dan yin wanka, yana wanka yana tunanin wai yau shine da mata, Allah mai yin yadda ya so da bawansa.

A ɓangaren ita kuma Ayla, tana shiga palo ta sami Aunty da Hahan har ma da Abbi, suna zaune suna hira, haka kawai ta tsinci kanta da jin kunyarsu, kasa ta yi da kanta tare da tsugunnawa ta ce "Abbi ina wuni"

Ɗan murmushin ya yi kafin ya ce "Sai yanzu kika ga Abbin ko?" Shiru ta yi tana tunanin lokacin da ya shigo ɗakin daddyn Jelly, daddy'n Jelly ɗin ne ya rufe mata baki da hannunsa, dan yasan zata yi mashi magana, shine yasa ya rufe mata baki, dan bai son ta yi magana a wannan lokaci.

"Ayla tashi ki je ki yi alwala ki yi sallah, kyale Abbin kin nan hai" cewar Aunty.

Ɗan ɗago kai ta yi karaf suka haɗa ido da Abbi, murmushi ya yi kafin ya ce "Amarya je ki ki yi alwala ki yi sallah lokaci na kurewa".

Da sauri ta miƙe zuwa sama. Tana shiga ta zauna a bakin bed nata ta fara hawaye tana faɗin "Ina kewarki yar uwata, ina kewarki Rimsha, yau ga shi


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login