Showing 129001 words to 132000 words out of 355604 words
aka bashi da farko ya haddace, abin ya bawa Musharraf mamaki.
Yau dai cikin farinciki suka kwanta, kuma a tare suka yi barci ɗaki ɗaya, da Asuba Musharraf ya yi kokarin tashin shi domin su yi sallah amma ina yaki tashi, da Musharraf ya matsa mashi ma, sai ya ce cikin magagin barci idan Musharraf ya sake tashin shi sai ya harbe shi da gun idan ya tashi.
Haka Musharraf ya hakura ya kyale shi, amma wani hanzari ba gudu ba, gaba ɗaya daren jiya tun da karfe 2 ta cika Musharraf bai sake iyayin barcin ba, daya fara barci zai yi mummunar mafarki a kan Micheal da ya musulta, daya fara barci zai ga wata mata sanye da fareren kaya komai nata fari tas sai dai jini na zuba daga idanuwanta hannunta riƙe da katuwar wuka mai kaifi ta zo zata caka mashi, tana kuka a kan me zai cuce su, haka zai farka a birkice yana addua'o'i, wani lokaci kuma sai ya fara barci, sai ya kalli wata bakar mata, baka kirin kamar zunubi, tana rike da wuƙa, yana ji yana gani zata yankawa Michael wuya jini ya yi ta zuba. Haka har asuba bai samu barci ba. Hakan yasa yake tunain tabbas akwai wani abu a gidan nan nasu, ba lafiya ba, kuma shima ya dasa ayar tambaya a kan Micheal, kuma ya zamar masa dole ya kula da lafiyar Michael ɗin ta hanyar yi masa addua'o'i da sauransu tun da shi ya sanya shi ya musulta, komai ya faru da shi to shima yana da sa hannu.
(To fa me kuke tunain zai iya kasancewa a gidan William jacop? Me kuke tunanin ya jawo hakan? Me kuke tunanin ya samu Michael? Waye kuke tunanin ya ke aikata hakan? Me yasa sai Michael kawai? Ko dai sauran dan basu musulunta bane?)
Bayan ya yi sallar asuba sosai ya ɗaga hannu ya rinƙa zubawa Allah kirari yana rokonsa da ya kare Michael a duk in da yake. Bayan ya kammala ya dawo saman gadon ya dukufa wajen tofawa Michael ɗin addu'a domin abubuwan da ya gani a mafarki dan gane da Michael ɗin ba abubuwan wasa bane, sannan abin akwai rikitarwa da ɗaure kai.
After some hours👌
A ɓangaren Lion kuwa.
Tsaye suke a cikin ɗakin binciken su, yau daga shi sai Short da singlet, kakkarfar kuma kyakkyawar suran jikin nasa a bayyana, hakan yasa kwarjininsa ta kara bayyana sosai, soft skin nan nasa ba'a magana, yana kwance luf tamkar ka taɓa jini ya zuba, sai wani kyalli yake yi, ga bala'in laushi kamar bai taɓa fita waje ba, kamar fatar jariri, ya saki dark black curly hair nan nasa wadda ya zuba masa har bayan wuya, kyau iya kyau ba'a magana.
Daga gefensa Tyrone ne da Tga a tsaye kusa da shi, sun zubawa system dake gabansu idanuwa, suna ta kallon irin kisan da James yake yi, aiki suke yi sosai ba bu kama hannun yaro, domin Lion zai yi tafiya next week saboda ya samu abin da yake nema dan gane da binciken da yake yi a kan A.E.A shiyasa ya tarasu a ɗakin bincike suna duba wasu gunjiyoyin dake kewaye da A.E.A.
Tyrone ne ya ɗago kai cikin girmamawa murya kasa kasa a nutse yadda kasan wanda yake gaban mahaifinsa, wani ma ko mahaifinsa ba zai yi wa irin wannan biyayya ba, muryarsa har sarkewa take yi ya ce "Sir meyasa zaka tafi next week, why ba zaka bari sai nan da 3 weeks ɗin kamar yadda suka rubuta nan da 3 weeks za su yi gangami a wajen ba, kaga a lokacin zaka iya bamu umarni mu yi musu dirar mikiya mu kashe kowa mu ɗauko James".
Shiru Lion ya yi yana mamakin ma ya akayi mutun mai ƙaramin kwakwalwa irin Tyrone ya zama lieutenant General kwakwalwarsa sam bata da kaifin gudu na hangen nesa, ya zama dole ya rinƙa kara musu hangen nesa idan ba haka ba wata rana za su yi shirme.
Ya jima shiru bai yi magana ba, sai da ya kwashi good 15 mins san nan ya ce "Saboda C.I.A"
Kallon Tga Tyrone ya yi, yana son karin haske amma yana tsoron sake yin wata tambayar saboda ya san Lion baya son yawan surutu, idan ka cika saka shi magana sai ya jefaka ta window kowa ya huta.
Sarai Lion ya san suna sun karin haske, kuma yasan tambayar da za su yi mashi, hakan ya sa ya ce "Idan har C.I.A suka riga mu isa ga James to fa zasu har be shi ne lokaci guda ya mutu, ni kuma ba haka nake so ba, ina bukatar wasu amsoshin daga wajen shi kafin na hukunta shi". Tga ne ya yi karfin hali cewq "To why not ba zamu tafi tare ba? Please Lion ka taimaka ka bari mu bika, ina bukatar kama James da hannuna". Wucewa Lion ya yi ba tare da ya sake yi musu magana ba, dama kuma sun san hakan domin baya magana biyu. Shi dai Tyrone mutuwar tsaye ya yi yana zancen zuci "lallai James ya cika tantirin ɗan ta'adda, irin wannan kisa da yake yi kamar ba mutane yake kashe wa ba, shi kawai da sun ba shi aiki sai ya karɓa, baya duba waye zai kashe, kai anyama James jinin Romeo ne kuwa? Domin Romeo da Michael dai ba haka suke ba, sannan Romeo da yake The General of the Army ma ba ya yin irin kisan rashin imanin da James ke yi ba.
Wucewa Tga ya yi ya bi bayan Lion dan yau ko dukan shi Lion zai yi sai dai ya duke shi, amma sai ya roƙe shi akan su tafi tare.
Zaune saman bed ya isko shi ya yi shiru kamar mai tunanin wani abin. Gefen shi Tga ya zo ya zauna, shiru suka yi na tsawon mintuna ashirin.
Sannan Tga ya ce "Lion ka bari ku tafi tare mana, ina son kama James da hannuna".
Shiru Lion ya yi mashi kamar ba shi a wajen, zuba mashi ido Tga ya yi yana jiran amsa, tsawon mituna biyar sannan in a cool voice a nutse ya fara magana "Ba tare za mu tafi ba, amma dai ku zaku tarwatsa sansanin, sai dai ina son kasan wani abu ɗaya, James ba zai kamun maka ba, domin ya wuce yadda kake tunani, zata iya yiwu wa ku iya tarwatsa wayan da suka kama shi, amma fa ka sani daga lokacin da ku ka kuɓutar da shi daga hannunsu tofa kai kuma ba zaka iya kama shi ka dawo da shi gida ba".
Zaro ido Tga ya yi yana mamakin kalaman Romeo, cike da tsoro ya sake tambayarsa "Me yasa ba zan iya kama shi ba?". Nan ma dai shiru na ƴan mintoci Lion ya yi kafin ya ce "Bawai ba zaka iya kama shi ba ne, kunema zaku yaki kungiyar amma dai ina son ka sani James ya fi General training mai karfi, sannan ya fi General ƙwaƙwalwa saboda jinane shi, ba bu wata hukuma da zata iya kama shi cikin sauƙi, mutane biyu ne training na su yake gaba da James a yanzu, na farko The general of the army, ajiye muƙamina a gefe, na biyu Ni da kai na, bayan ni ba mai iya kama James cikin sauki". Kasa magana Tga ya yi domin Lion ya ɗaure mashi kai dayawa, shi dai ya san koda James yana kashe mutane shi da yake matsayin uncle nasa ba zai kashe shi ba, amma me yasa James ba zai kamun musu ba? Shine abin da ya tsaya mashi a rai.
Miƙewa Lion ya yi ya nufi Balcony yana faɗin "General kada ka rikita kanta dayawa, James ba zai kamun muku cikin sauki yadda ka ke tunanin nan ba, domin kuwa kungiya daban daban ne suke neman shi ruwa a jallo, sannan ni ma yanzu idan na fita kasar nan bawai kai tsaye kama James zan je yi ba, no bam ma tabbatar a wani waje takamaimai yake ba, saina natsu". Ya kai karshen maganar tare da shigewa cikin balcony ɗin ya shige cikin karamar pool nasa dake wajen, ya lumar da jikinsa gaba ɗaya a cikin ruwan, ya bar iya kai kawai a wajen, sannan ya lumshe idanuwansa kamar mai yin barci.
Shi kuma Tga tashi ya yi, jiki ba kwari zuciya cike fal da tunani ya wuce ya koma wajen Tyrone dan su ci-gaba da aikin da ya sanya su.
Shi kuma John yana word room dan ya ci kwakwa wajen Tga, ba karamin horashi ya yi ba, hakan yasa daddy yake bashi kulawa a word room.
Shikuma Michael sai karfe takwas bayan ya gama gym ya dawo ne ya gabatar da sallar asuban shi, Musharraf na zaune yana kula da shi yadda yake Sallah har ya idar, sannan Musharraf ya gaya masa ba'a tsallake lokacin yin Sallah, da lokacin ya yi to dole ne ayi, dan haka ya koyi tashi da asuba, kasan cewar yana son abin sai ya ce da Musharraf ya yi masa alwarin zai rinƙa tashi da asuba, sosai Musharraf ya ji daɗi, kuma yasan wannan nasara da yake samu akan Michael ba komai bane face addu'ar da yake yawan yi ne Allah yake ɗaura shi a kan Micheal ɗin. Daga jiya da daddare da Michael ya karɓi musulunci zuwa yanzu, har wani haske fuskarsa ta kara, sai kyalli yake yi, har gashin kansa sai da ta san ya shiga addini kai tsarki, domin gashin nasa har wani kwanciya ta karayi tana wani curly kamar me, idanuwansa duk sun sauya, wasu sihirtattun kyau suka kara yi, idan ka gan shi kai kace ba shi ba ne, ya kara wani sihirtaccen kyau sosai abin shi, lokaci guda haiba ta bayyana a tattare da shi, ga kwarjini na addinin musulunci ya bayyana, ya ƙara natsuwa, ga shi ƙwaƙwalwar tasa tana ta kara buɗuwa saboda karatun Alkur'ani mai girma da suka yi da Musharraf jiya da daddare, Suratul Fadiha Musharraf ya koya masa jiya, bawan Allah da yake babu wata hayaniya a ƙwaƙwalwar tasa, har ya haddace surar, yanzu ba shi da damuwar komai, ya dai na fita Palo ma, yau tun safe suna tare da Musharraf ya dage a kan sai Musharraf ya kara koya masa wata surar, haka suka wuni yana koyar nasi da falaki, sai farinciki yake yi abinsa bawan Allah.......
Nima sai farinciki nake yi na tattara kayana na wuce sai mun haɗu gobe a sabon gidan Abbi idan Allah ya kai mu da rai da lafiya
💖💖TRIPLET'S💖💖
39-49
💖After 2days👌💖
(Bari mu fara da restaurant kafin mu yi wani wajen kuma)
Acikin yan kwanaki biyun nan Rimsha ta saba sosai da aikin restaurant ɗin, dama kun san ta da son koyar girki, dan haka sai ta tare wajen girkin hotel ɗin, saɓanin Jehan da ko leƙa wajen bata yi, sai dai idan ta zo ɗaban abinci zata kai wa masu saya.
A yanzu Rimsha fa ta iya abinci sosai, kuma akalla zai kala girki kala 15 ta iya, bata da kiwuyar aiki, haka zalika bata jin nauyin jikinta, sake jiki take yi ta murji aikin ta, idan ta koma gida ta yi wanka ta yi ta barcin ga ji ya, sannan a yan kwana biyun nan kafin ta tafi restaurant ɗin sai ta yi wa maman Sadiq shara da wanke-wanke sannan ta tafi.
Yau ma kamar kullun da sassafe ta tashi ta yi wanke-wanke da shara, sannan ta yi wanka, ta shirya, ta ɗauko wayarta, tun da ta zo sai yau ta ɗauki wayar, kokarin kunnawa ta yi amma ina battery ya kare wayar ta mutu ba charji, turo ɗan bakin nan nata tayi sannan ta yi wa mamam Sadiq sallama ta wuce sauri sauri domin Sadiq yana tsaye a waje yana jiranta.
Tare suka jera zuwa bakin titi, a yanzu saura mata 4k a cikin 20k da Ahmad ya bata, gaba ɗaya ta kashe kuɗin a sayawa maman Sadiq irin su omon wanke-wanke da sabulun wanki da wanka, bata damuwa idan ta zo zata yi abu idan taga babu sai ta ciro kuɗi ta saya, harta tsintsiya ita ta saya musu guda uku, Yusuf mai rakata sayowa, dan shine babban abokinta.
Karfe 8 daidai ta shiga restaurant ɗin nasu, kai tsaye wajen girki ta nufa, masu shara har sun yi sun goge koina, wajen ya yi fes,
Rismha akwai goshi kamar me, tana shigowa suka fara samun baki, har Ibraheem ya campa abun, kullun cewa yake yi idan Rimsha bata zo ba basu samun ciniki, amma idan ta zo kuma, tana shigowa restaurant ɗin yake fara cika da jama'a, amma fa wa su ba abinci suke zuwa saya ba, kallonta suke zuwa yi sai su ɓige da sayar abinci, idan ta kawo musu abinci sai suyi ta rokarta akan ta basu number wayarta, amma ko kula su bata yi, suna yi mata kallon babba saboda tana da tsawo kuma tana zuba hijabi har kasa, a cikin hijabi sai ka yi mata kallon babba, amma idan ta fito yar firitu zaka ganta.
Bata taɓa kula kowa ba, fuskar nan nata kullun a ɗaure kamar hadari. Sanya wayar ta ta yi a charji kusa da Ibraheem sannan ta fara karɓar oder kowa tana kawo masa abin da yake buƙata, ita da Faiz suke wannan aiki, shi kan shi Faiz ɗin daurewa kawai yake yi yana aiki tare da ita, amma magana ta gaskiya ya gama faɗawa da ita, haka zalika shima Ibraheem ya faɗa da ita sosai daurewa kawai yake yi saboda bata ba shi fuska ba.
Bayan ta kammala kaiwa duk wayan da suka zo a lokacin abincin ne, sai ta koma saman wani kujera da suke zama idan sun kammala aiki, shiru ta yi tana tunanun rayuwa, tunanin ina zata sake ganin su mum ɗin ta kawai take yi, tunanin Ayla ne ya faɗo mata a ranta, cikin sauri ta miƙe ta nufi wajen Ibraheem.
Tana zuwa ta ciro wayarta daga charji ta shiga neman layin Ayla, abin haushi gaba ɗaya wayar number Ahmad ne kawai a ciki, shiru ta yi tana tunanin a ina zata samu number Ayla.
Tana tsaka da tunani wayar tata ta fara ringing, kallon screen ɗin ta yi, Yaya Ahmad shine sunan da ya bayyana a kan screen ɗin wayar.
Picking call ɗin ta yi tare da kara wayar a kunanta. Daga ta cikin wayar ta ji wani nauyayyar ajiyar zuciya da ya sauƙe, muryarsa can kasa-kasa ya ce "Hello Queen of beauty" dogon numfashi ta ja tare da sauƙewa a hankali.
"Yaya Ahmad baka da lafiya ne?" Nisawa ya yi sannan ya ce "Bani da lafiya my princess" zaro dara-daran sleeping eyes nata ta yi tare da marairace murya cike da tausayi ta ce "Allah sarki sannu ka ji? Allah ya baka lafiya, ka ga ma ko sallama ban yi ba bare mu gaisa, saboda yadda na ji muryar ka" "Allah sarki Queen of beauty ai kece silar rashin lafiyar tawa". Zaro idanuwanta waje ta yi, tana ƙokarin yin magana Ibraheem ya ce mata ga baƙi fa sun zo tun minti biyar da suke wuce, kuma sune masu wannan restaurant ɗin, jin haka yasa ta sallami Ahmad a kan anjuma zata kirashi, bata jira amsar shi ba ta katse kiran, sauri sauri ta nufi bakin dan tambayar me suke buƙata.
Sallama ta yi musu, Dr Nawid ne da Imran, Imran ne ya amsa mata sallamar nata shi kuma Dr Nawid cewa ya yi "Ina Jehan? Ki je ki ce ta kawo mana abinci".
Tana kokarin yin magana muryar Imran ya katse ta da cewa "Rimsha Nawazudden right?" Ya yi maganar yana zaro idanuwansa waje.
Dawo da kallonta kan shi ta yi, zaro idanunsa waje ya yi sosai yana kare mata kallo, tabbas ita ce, abin da kawai yake faɗi a zuciyarsa, ita kuma kokarin gane wanene shi ai na kuma ya santa kawai take yi, shi kuma Nawid ya zuba mu su ido yana kallon ikon Allah.
Sake maimaita mata tambayar Imran ya yi "Rimsha Nawazudden ko?" Gyaɗa mashi kai ta yi alamar E.
A zabure ya miƙe tsaye yana binta da kallo, ganin ya miƙe tsaye ne yasa Nawid ya ce "Imran lafiya? Ai na kasan ta? Wace ce kuma ita ɗin?" Dawo da kallonsa kan Nawid ɗin ya yi, sannan ya fara magana "Nawid baka san Nawazudden ba? Ɗan takarar shugaban kasa wadda ya yi ɓatar lokaci guda shida familynsa, daga baya aka kawo gawarsa ya yi haɗari ya mutu?".
A zabure shima Nawid ɗin ya miƙe suna kallonta, ganin yadda take jujjuya idanuwanta ne yasa suka kai kallonsu wajen, gaba ɗaya jama'ar dake restaurant ɗin ne suka zuba musu ido suna kallon su.
Ganin hakan yasa Imran ya koma ya zauna yana faɗin "Ranki ya daɗe dan Allah ki zauna mu yi magana". Ba musu ta zauna domin ta jima tana addu'ar Allah yasa ta haɗu da wanda ta sani, mai kuma mutunci.
Shima Nawid komawa ya yi ya zauna yana faɗin "Yanzu kai Imran kana da tabbacin wannan yar Nawazudden ce?" Gyaɗa mashi kai Imran ya yi kafin ya ce "Har cikin gidan su na taɓa zuwa sau uku, a nan ne ma na santa, dan ita bata wani yin media sosai, account nata ma bata da wani abu da take posting da ya wuce abubuwan addini da tunatarwa, su kawai take posting, shiyasa ma kai baka santa ba, amma ni har cikin gidan su naje sau uku shiyasa na santa".
Ita dai Rimsha kasa kawai ta yi da kai tana jiran ta ji da me ya zo shi kuma. "Rimsha ina iyayen ki, ina His Excellency? Ina su mummy? Ina Jehan? Ina following nata a Instagram, lolacin da kuka yi ɓatar lokaci gudan nan, na je har gidan ku, amma gidan a rufe da kwaɗo na yi wa Jehan magana a Instagram amma shiru ba amsa, na nemeku shiru ban same ku ba, ni dai nasan kuna nan da ranku ake ta ce wa wai kun mutu a lokacin" ya kai karshen maganar kamar zai yi kuka.
Kasa ta yi da kanta, wasu siraran hawayene suka fara bin kuncinta, ganim haka ya sa Imran ya ce "Ya isa yanzu ta shi muje ki kai ni wajen su Madam". Murya can kasa kasa ta ce "Ni kaɗai na rage, su mum sun ɓata ban san in da suke ba, ban san ina suka je ba, nima shekaran jiya na