Showing 27001 words to 30000 words out of 438336 words
da ita da suit kala uku a ciki. Yasan kayan dake a shiryen duk aikin Hayatu ne. Batare da yace komai ba ya ciri farin pyjamas mai shegen ƙyau da laushi, sai boxer shima dai sabo. Tsaf yay shirinsa tare da sake komawa gaban mirrorn yay sabon wankan tsadaddun turarurrukansa na barci da ƙamshinsu ba'a magana kamar ba dare ba. Tsaki yaja a hankali yana hararar wayarsa da ke cigaba da tsuwwa babu ko ƙaƙƙautawa. Ya san mai kiran nasa, dan ita kaɗaice take karya dokarsa akan hakan. Duk wanda ya sanshi yasan yanada doka a akan kira, dokar kuwa itace in har kamasa kira 1 bai ɗaga ba ka bada mintuna kamar biyar sannan ka sake. Idan nan ma aka samu akasi bai ɗaga ɗin ba to ka haƙura kawai, idan shi ya samu lokaci zai iya ya kiraka, idan bai biyo ba kuma ka ɗauka kiran naka baida muhimmanci ne. Wayoyinsa duk a hannun Hayatu suke. Wannan ce kawai yake riƙewa saboda Ummien sa. Gaban gadon ya ƙarasa in da ya yasar da wayar, cikin ƙara ɗaure fuska ya ɗauka dan yana son ta barsa. A daƙile ya kai wayar kunensa sai dai yaƙi cewa komai. Sai da yaja kusan sakan hamsin ya ce, “Thanks”. Kawai yaja bakinsa yay shiru. Kasancewar bai sauke wayar ba zai tabbatar ma da har yanzu magana ake daga can, dan sai wani yamutsa fuska yake da sake tsuketa kamar mai jin warin mai maganar. Kusan minti biyu ya sake furta, “Zanyi barci”. Daga haka ya yanke kiran gaba ɗaya. Wayar ya wurga a saman gadon tare da jan tsaki mai ƙarfi ya haye gadon yay kwanciyarsa. Kai kace ma baida wata damuwa a rayuwa. Sai da yay addu'oi barci sannan ya lumshe idanunsa. Kafin wani dogon lokaci ya fara sauke numfashi a hankali alamar yayi barcin.....
●´⌓`●●´⌓`●●´⌓`●
Duk yanda nagaji na kasa barci. Sai faman juye-juye nake abubuwa na dawo min tamkar yanzu suke faruwa, dan ma ƴar wayar da mukai da Mansoor ta ɗan sani ƴar nutsuwa. Ganin ƙwaƙwalwata na neman tarwatsewa na tashi na ɗaura alwala. Salla na farayi, sai da na kwashe kusan awa ɗaya da rabi sannan na zauna ina istigifari. Kamar a mafarki naji wayata na verbration. A gogo na kalla, ƙarfe biyu da kwata. Mamaki ya kamani, dan ko Mansoor baya kirana a wannan irin lokacin, kuma ma ai munyi waya duk da dai yace zai sake kira video call amma bai kira ba, ganin lokaci haja yasa ban damu ba. Dan duk tsawon wayarmu baya wuce daga tara zuwa goma. Jin an sake kira bayan ta katse na yunƙura na ɗauka. Abin mamaki Mansoor ne. Ɗagawa nai hankali a tashe, a tunanina ko wani abu ya samesa. Amma sai naji yaymin sallama cikin taushin murya. Ajiyar zuciya na sauke a hankali, sannan na amsa masa.
“Dama naji a jikina zaki iya kasa barci, kiyi haƙuri Yaya ne ya ɗauke hankalina shiyyasa ban sake kiran ba. Haba Babie dan ALLAH ki cirema kanki damuwar nan. Ai ko ke kika aikata laifin nan sai haka”.
Numfashi na sauke a hankali. Cikin sanyin murya na ce, “Ni ban kasa barci ba fa, na farka ne kawai”.
“Uhhm yau kuma halin daba naki ba kika aro, to ai bai miki ƙyau ba dan baki iya ƙaryarba tunda ga harshenki yana rawa”.
Ɗan murmushin ƙarfin hali nayi, sai kuma nakai kwance ina faɗin, “To amin afuwa gashi na kwanta. Amma kaima miya hanaka barci?”.
“Saboda mahaɗin zuciyata batayi ba”.
“Humm”. Na faɗa kawai ina murmushi. Shima ina jiyo sautin nasa murmushin. Mun ɗan yi shiru na wasu sakannin kowannemu na sauraren saukar numfashin ɗan uwansa. Kafin ya katse shirun da cewa, “Kin sanarma Yaya Musaddiq abinda ya faru ko?”.
“A'a”.
“Miyasa?”.
“Kawai dai”.
“Aiko Babie ya kamata ya sani. Dan ko zamu iya ɓoyema kowa shi banda shi. Maybe ma ya ƙaremu da shawara ai. Dan wlhy har yanzu ni kaina duk a kulle yake”.
“Hakane zan sanar masa gobe in sha ALLAHU. Amma ni dai dan kaƙi ta nawane. Hukuma kawai ya kamata mu miƙawa ai”.
“Baƙi naiba Samraah. Ina son ki fahimci wani abu. Mutumin nan fa ya wuce duk inda kike tunani a ƙasar nan. Yanzu koda mun miƙa video ɗin nan ga hukuma kina ganin zasu hukuntashi ne. Ko kin manta yanzu a ƙasar nan tamu KUƊI ne ke magana ba GASKIYA ba. Shi kuma ALLAH ya bashi su, Samraah Maash fa zai iya juya Africa a tafin hannunsa ta yanda yaso bama Nigeria ba. Ke hatta da ƙasashen masu jajayen kunnuwan yanada ƙarfin faɗa aji sosai fiye da yanda kike tunani ta wasu fannoni. Sai dai su banbancinsu damu zasu iya hukunta duk wani mai laifi koda shi wanene? Amma a ƙasarmu ba haka bane. Ko wanda bai kama ƙafar Maash ba zai iya shallakewa in har da kuɗi. Kiyi haƙuri dai mu nema mafita mai ɓullewa. Mu kuma samu jajirtaccen ɗan sandan da zai iya yin duk abinda ya dace batare da kuɗi sun iya tankwarashi ba saboda gaskiyarsa. In dai Maash ne bazamu ƙyalesa ba sai an ƙwatoma mutumin nan hakkinsa”.
“ALLAH ya tabbatar to. Na kuma gamsu da bayaninka.”
“Masha ALLAH dear, yanzu dai zan shigo gobe in ALLAH ya kaimu ki biyo Yaya Musaddiq gareji mu haɗu acan dan ina so mu tattauna da gaggawa mu nemo mafita kafin Maash ya farga. Saboda babu yanda za'ai ace babu camaras a wajen nan duk da Companyn bai fara aiki ba sai Monday”.
Sosai zancensa ta ratsani dan har sai da na tashi zaune dingangan. Amma na gagara cemasa komai saboda yanda zuciyata ke bugawa da sauri-sauri........✍️
_Tofa masu karatu yanzunne fa ainahin wasan zai fara. Dan da alama mun gama sharar fage zamu tafi mataki na biyu a labarin. Wa kuke tunanin ya rubuta saƙon nan? Sannan karku manta a cctv footage fa Samraah za'a gani. Shin ko itace dai ta rubuta saƙon? Ko kuma wani yaji sanda take faɗama Mansoor yay amfani da damar? Ko kuwa ba ita kaɗaice ta gani ba? Shin minene dalilin Maash nayin kisan nan ma wai? Wanene aka kashe?..... Kai kai kai cakwakiya ce fa iya cakwakiya a labarin nan. Amma dai ina son jin amsoshinku a comment section. Yau har masu laɓe su fito inba haka ba gobe babu posting sai bayan salla🚴🚴🚴._
_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._
_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_
_BANK NAME:KEYSTONE_
_BANK ACC NO:6019473875_
_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_
_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_
__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_
_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_
*09033181070*
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*
_(Itama nama ce)_
_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_
_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝑺𝒆𝒗𝒆𝒏𝒕𝒆𝒆𝒏_
.......*_WASHE GARI_* kamar yanda na saba na tashi nai ayyukana da sauri-sauri. Ana idar da sallar asuba nai wanka. Breakfast ɗin Yaya Musaddiq na ɗauka na nufi kai masa kusan bakwai da rabi. Nako samu har ya kammala shiryawa. Tunda na shigo yake bina da kallo, basai nace komai ba nasan ya gama fahimtar yanayina ne. Amma sai na dake. Sai dai ina gaishesa maimakon amsa min tambaya ya jeho min. Baki na buɗe zance babu komai yay saurin ɗaga min hannu da faɗin, “Karma kimun ƙarya. Faɗamin mike damunki?”.
A hankali hawayen da nake riƙewa suka silalo. Nima babu shiri na silale ƙasa ina mai fashewa da kuka. Duk abinda ke a raina tun jiya ne ya samu damar fitowa. Kafin ma ya sake cewa da ni komai na shiga faɗin, “Yaya kisan kai yayi. Da idona na gansa yana zare wuƙa a jikin mutumin ga jini face-face. A kunnena naji yana faɗin akai gawar wani anguwa a ajiyeta.....”
A cikin matuƙar tashin hankali ya katseni jikinsa na rawa. “Waye wai? Ki min magana a buɗe Samraah Please wa aka kashe waye kuma yay kisan?”.
Maimakon bashi amsa sai na miƙa masa wayata kawai. Amsa yay da rawar jiki. Yana ko dannawa da video ɗin ya fara cin karo dan ni bana sakama waya password sam. A matuƙar birkice ya ɗago yana kallona tun a fara kallon video ɗin. Idanunsa a warwaje na shiga razana ya furta, “Samraah Maash fa?”.
Kaina na jinjina masa da sauri ina faɗin, “Shi yaya! shi! Mutumin nan azzalumi ne bana kirki bane kamar yanda duniya ke kallonsa. Zata iya yiwuwa ma kuɗin nasa bana ALLAH bane na jinin mutane ne”.
Tuni zufa ta wanke Yaya Musaddiq. Cikin tashin hankali ya ce, “Bayan ni wa kika faɗamawa?”.
“Mansoor ne kawai Yaya. Tun jiya nace mu kai ma hukuma video ɗin amma ya hana. Shine ma yace na baka ka gani dan mu haɗu da shi a gareji mu tattauna”.
“Gara daya hanaki Samraah. Dan dole wannan al'amarin na buƙatar nazari. Maash ba anyhow mutum bane da dokar hukuma zatayi tasiri akansa cikin sauri. Inaga yanzu ba zama zamuyi ba tashi mu wuce. Bara na kira Mansoor ɗin ya fito shima gara muyi abinda ya dace da wuri tun kafin ya bar garin nan. Dan bai zama lallai a sake samun irin wannan damar ba duk da naji ya amsa miki wai kiyi hira da shi. Ga gari nan duk ya ɗauki zance harda masu faɗin ba haka kawai kikaje masa ba akwai asiri saboda yanda ya amsa ɗin babu musu a gaban duniya. Amma ni zuwa yanzu na fara zargin akwai wata a ƙasa kam, bana raba ɗayan biyu ya ganki sanda kike ɗaukar video ɗin nan, ko kuma ta cctv, dan Company kamar nasa dole asamu camaras tako ina”.
Idanu na waro sosai na matuƙar mamaki, Yaya Musaddiq ya jinjina min kai alamar tabbatarwa. “Samraah duk mai hankali dolene ya gane akwai dalilin Maash na amsa miki gayyatar da kikai masa cikin sauƙi. Dan bazai taɓa zama ya amsa miki bane kawai saboda kin jera masa tambayoyi. Kai ina dolene ma ya ganki fa, ya barki ne kawai bisa dalilinsa, sannan yazo a bainar jama'a ya amsa zaiyi hira dake, hakan na nufin akwai wani abu da yake ƙullawa”.
Sosai na zubama Yaya Musaddiq ido, dan tabbas zancensa yasa na fara dawowa cikin hankalina yanda ya kamata. (Humm you are vary smart girl) kalmar daya fara ambata a kaina kenan. Tabbas wannan mutumin terror ne na gasken-gaske. Shin mi yake ƙullawa? Dan dolen dole akwai abinda ke ransa kamar yanda Yaya Musaddiq ya faɗa. Kai ina buƙatar ganin ma program ɗin jiya gaskiya.....
“Kinga tashi muje, ba lokacin tunani bane yanzun”. Yaya Musaddiq ya faɗa cikin katse mun tunani. Miƙewa nai babu musu, dan basai na koma cikin gida ba dama....
🤙❤️🤙❤️🤙❤️
A ɓangaren Maash asubar fari ya farka, da ƙyar ya iya tashi saboda gaɓɓansa duk ciwo suke masa. Ruwa ya fara watsawa ya fito a gurguje ya kimtsa cikin wando da rigar polo. Koda ya fito su Hayatu suma har sun fito zasu wuce massalacin. A tare suka fita, bayan an idar da salla bai koma cikin gidan ba yace ma Tijjani ya fito da mota zasu je wani waje. Da sauri Tijjani ya shiga ciki, babu jimawa ya fito da mota, suma guards ɗinsa suka fito. Komai baice ba Hayatu ya buɗe masa baya ga shiga, shi kuma ya shiga gaba kusa da Tijjani. Jihar Jigawa suka nufa, a wani ƙauye dan akwai business ɗin da zai yi a wajen. Duk da dai da farko bai wani ɗauki abin da muhimmanci ba, sai da zasu je massalacin nan ne Hayatu ke sanar masa mutumin da zasuyi kasuwancin ya kira, kuma yana son suje da wuri ne.
Yinin ranar guda a Jigawa suka cinyesa. Ko abinci bai sakama cikinsa ba garama su su Hayatun. Sai Black tea kawai yake faman sha kasancewar duk inda yake yana tare da flaks ɗin ruwan zafinsa a mota, sai kuma chocolate dan mayenta ne da haɗaɗɗun biscuits. Sai bayan la'asar suka dawo cikin Kano a matuƙar gajiye. Musamman ma shi duk da dai yaci chocolate sosai amma yana buƙatar dafaffen abinci, dan rabonsa da dafaffen abinci sosai tun shekaran jiya a Lagos. Ko zama a falon baiyi ba ya wuce bedroom, suma dai su Hayatun duk a gajiye suke, dan haka kowa ya nufi sashensa danya watsa ruwa. Bathtub ya cika ra ruwan ɗumi sosai sannan ya shiga ciki, sai da yaji ko inansa ya miƙe sannan ya ɗauraye jikinsa ya fita. Duk yau sau ɗaya kawai yay waya da Ummien sa. Ji yake duk kewarta ta damesa. Sai dai yanzu yasan koya kira bazai samu ba dan ba lokacin kira bane dan sallar magrib aketa kira. Shiri yay tsaf cikin kaya marasa nauyi. Ya baɗe jikinsa da turare sannan ya saka slippers da ke ajiye yay ficewarsa.
Tun kafin ya ƙarasa fitowa cikin falon Hayatu dake zaune yana jiran fitowarsa ya miƙe da sauri. Dan tun ɗazun ya dawo daga wanka da yaje yayo shima a sashensa. Ya dawo ne da wuri akan batun cctv footage na jiya, dan yana ganin ya kamata su duba issue ɗin kar a samu matsala. Kallo ɗaya ya masa ya ɗauke kansa, sai kuma ya nufi ƙofa a taƙaice ya ce, “Kayi alwala”.
Cikin girmamawa Hayatu ya amsa da “Okay Sir”. Sai kuma ya saki murmushi yana mai binsa da kallo. A duniya boss ɗinsa da banne. Mutum ne mai abubuwan ban mamaki daban-daban. Ba kuma zaka tabbatar da hakan ba sai ka kasance a makusancinsa. ALLAH ya azurtashi da ni'imomi da yawa a rayuwa. Gadai ƙyawu kamar shine ya zana kansa. Ga dukiya, ga ilimin addini dana zamani. Yanada ƙyauta ga duk wanda ke tare da shi. Sai dai kuma hatsabibin kansa ne baifa mutunci a wasu fannin. Dan wani irin mutum ne a hagungunce da zaka iya ɗaukar lokaci baka fahimci alƙiblarsa ba. Ga taurin kam masifa da baƙar zuciya. Baya ragi ko ragowa ga duk ubanda yace masa kule. Yakan karya yatsar duk wanda ya nunashi dan baya ƙaunar raini. Shifa ko'akan business ana lallaɓa abokan harƙalla dan su dawo shi a garesa bai san wannan ba. Kana kawo masa hauka zai cireka a sabgarsa kawai. Sai dai baka isa tabbatar da waɗan nan halayyar tasa ba kai tsaye sai ka shigo gonarsa. Dan sumumu kasaune shi _*MACIJIN SARI KA NOƘE_*. A zahirinsa zaka ɗauka mutum ne mai sanyi da nuna halin ko'in kula, sai dai a kowanne motsi na cikin rayuwarsa a ankare yake. Domin indai brain ce ALLAH ya bashi. Irinsu ne ke juya akalar abubuwa a ƙanƙanin lokaci da kwanyarsu.....
Firgigit ya dawo hayyacinsa jin kiran sallah. Da sauri ya shiga toilet ɗin falon ya ɗauro alwala ya wuce masallacin shima...
Bayan idar da sallar isha'i suka shigo gidan. Sai dai Hayatu da Tijjani drivern sa sun rigashi shigowa. Dan su duka suna a gidan har baturiyar nan. Sai dai kowannensu yana a mabanbancin masauki da sai in shine ya buƙaci ganinsu zasu ganshin. Kusan mintuna goma suna a ƙaton compound ɗin gidan da ga jikin motoci suna hira sai gashi ya shigo shima. Ya ɗan dakata yay magana da masu gadi da suka kasance ƴan sanda har su uku sannan ya ƙaraso inda suke. Duk nutsuwa sukai kawunansu a ƙasa, baice da su komai ba ya wuce inda lafiyayyar ƙofar shiga sashensa take. Dan ta gilashi ce mai tsananin ƙyau da ɗaukar idon mai kallo. Gata golden daga waje sai walwali take kamar wani zinaren gaskiya. Da sauri Hayatu dake biye da shi ya buɗe masa ƙofar. Harararsa ya ɗan yi, Hayatu ɗin ya duƙar da kai ƙasa yana murmushi dan yasan laifinsa akan buɗe ƙofar ne tunda yana hanasu. Har ya shiga ya ɗan waiwayo. Driver dake ƙoƙarin komawa da baya ya dakatar ta hanyar faɗin, “Tijjani!”.
Da sauri Tijjani ya amsa masa da “Na'am ranka ya daɗe”.
Komai bai sake cewa ba ya cigaba da tafiyarsa ciki. Dan haka duk suka bisa. Duk da garin ba zafi ake ba, ba kuma sanyi ne mai tsanani ba dan ya fara bankwana falon a ƙanƙare yake da sanyin raɓar ac. Ga wani ƙamshi na musamman daya gaurayu da turarensa tamkar ba a jiya ne ya fara rayuwar cikin gidan ba. Zaune ya kai saman 3sitter. Kamar yanda ya saba zaman ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya yanzun ma hakan yayi. Shiru kamar mai nazarin wani abu sai kuma ya ɗago yana ma Hayatu nuni da remote dake a Centre table. Remote ɗin Hayatu ya ɗauka da sauri, dan ko ogansa bai magana ba yana saurin gane karatun shirunsa saboda da hakan ya horesu tun farko. Dan shi bamai yawan magana bane sai idan shine yaso hakan da kansa. Sai kuma idan yana a gaban mahaifiyarsa ko mahaifinsa, shima a wasu lokutan