Showing 414001 words to 417000 words out of 438336 words

Chapter 139 - Tsutsar Nama Book 1 Hausa Novel Complete

13 Dec 2024

2906

kwantar da hankalinki in sha ALLAHU muma zamuyi ta ɓangaren mu.”
“To ALLAH ya taimake mu Yaya. Amma mizai hana ka fara kaini naga Paah ɗin”.
“A'a kiyi haƙuri kada kije yanzu. Zan dai iya saka miki number sa ki kirashi a waya. Amma batun ku haɗu a wannan halin Yaya Awwab bai gama sakkowa ba akwai matsala.”
“Shike nan na fahimta, hakan ma yayi ka tura min number ɗin tashi.”

Koda muka iso gidan a falo muka sameshi zaune yana karatun Alkur'ani. Yaya hayatu baima shigo ba ya juya. Nima sai na samu waje na zauna ina sauraren muryarsa dake raira karatun cikin nutsuwa. Har ma barci ya fara rinjaye idanuna na zame na kwanta. Sai da naji ƙamshinsa gab da hancina sosai sannan na buɗe idon. Kallonsa nake kamar yanda take kallona. Baiyi magana ba ya ɗaukeni camak zuwa bedroom ya kwantar. Shima kwanciyar yayi ya sakani a jikinsa. Mu duka ajiyar zuciya kawai muke saukewa a jajjere har barci ya ɗauke ni, ashe shima barcin yayi sai da na farka na gansa....

Kwanaki biyu kenan muna tare da ga ni sai shi a gidan. Babu dai yawan magana dan ya koma min Maash ɗin dana sani a baya. Sai dai dukkan kulawa yana bani dan sai nima na kasance duk bana jin daɗin jikina abinka da mai ciki. Abinci safe, rana, dare Mama Balki na ƙoƙarin aiko mana da shi. Yaya Hayat ne mai kawowa. Abinda yake burgeni da shi ya matuƙar maida al'amarin sa ga UBANGIJI. dan a zaman nan ibada ce kawai sai kuma kasancewa da ni. Duk wasu harkokin Bussines ya ajiyesu gefe guda kawai. Hatta phones ɗin duk ya kashe. Tsahon kwana huɗu sannan mukayi shirin komawa gida. Bayan sallar magrib ya shigo yana min maganar na shirya muje sai ga Hayatu yay kiransa, ban san miya ce masa ba naji kawai ya kama faɗa. Sai kuma ya yanke wayar. A fusace ya nufi ƙofa zai fita. Nai saurin tafiya na rungumesa ta baya nima. Kaina kwance a faffaɗan bayansa, na zagayo hannayena ta saman shafaffen cikinsa. A hankali na ce, “Miya faru Zaki na? Ban sanka da faɗa cikin hayaniya haka ba, Please cool down”.
Shiru yay sai ajiyar zuciya da yake faman saukewa a jajjere. Cikin sake tausasa harshe na ce, “Please ka faɗa min miya faru? Maybe na iya baka shawara”.
Nan ma shirun yayi a binsa, sai da ya mula dan kansa ya furta, “Miyasa zai kawoshi nan. Nace na haƙura, mi kuma ya rage”.
“Wanene?”.
“Mijin Ummie”.
Ni dariya ma maganar tasa ta bani, wai mijin Ummie. Yau Paah ɗin ma baza'a kirashi ba kenan. Amma sai na danne tare da sake tausasa harshe na zagayo ta gabansa. Hannayena duk biyu na ɗora akan kafaɗunsa duk da ya mun tsaho ina kallon cikin shakkiyar idanunsa da gaba ɗaya sun jirkice. Na ce, “Haba my Hot, kenan baka hakura ba? Ba kaji nasihar Malam ba. Yanzu kana son kayi min wani kuskure wataran abinda ke cikina ya dinga maka yanda kakema Paah a yanzu. Kai ma fa yanzu uba ne, sannan bamu san mi yau da gobe zatazo mana da shi ba. Kasan kuwa matuƙar wahalar da mukasha a rayuwa saboda rashin iyaye? Amma ku kuna son raba naku dake a tare. Yaya a mafi yawan lokuta nike girka abincin da za'aci a gidanmu, amma ni bazan cisa ba. Wani daga cikin ƴan uwana bazai cisa ba. Badan bama so ba fa ko babu wadatar abincin. Ka gaya min da Baba na darai ko Ummyn mu zasu barmu da yunwa ne? Government school mukayi, amma yaran gidanmu private masu tsada. Ana musu ɗinki sau biyar mu ba'a mana sau ɗaya ba. Shin da ace iyayenmu na raye ko guda ɗaya ne zamuga wannan rayuwar ne. Duk inda zasu faɗi su tashi zasuyi domin mu. Ku godema ALLAH naku duk suna raye, har gamu muma muna jingine jikinsu suna mana gatan da muka rasa a baya. Paah yayi kuskure, ya kuma yarda yayi kuskure, muma kuma bamu wuce kuskuren ba. Shi da Ummie suna son junansu, kada ku ƙi basu haɗin kan cigaba da zama a ƙarƙashin inuwa ɗaya. Ku tausaya mata kodan bayanin likita, yanzu kunfi son ta rabu da Paah ta auri wani banza can da maybe ma dan dukiyarta zai aureta ne kawai? Kai ne babba, idan har kayi mubaya'a Fahad shima zaiyi wlhy. Please ka saki ranka komai ya wuce”. Na ƙare maganar cikin sanyin murya da marairaicewa kamar zanyi kuka. Ganin ya zuba min idanu kawai na sake faɗin, “Please mana”. Naja kumatunsa. Hararata yayi, niko na sanya dariya da sake ja masa hanci. Sai ya dungure min kai shima yana ɗan lumshe idanunsa a slowly.
Cikin farin ciki naja hannunsa muka fito. Ganin Paah a falo zaune nai saurin sakin hannun nasa na koma bayansa na laɓe. Ƙaramar dariya Paah ɗin yayi mai ɗan sauti da faɗin, “Oh oh my daughter please fito mana.”
Fitowar nai kaina a ƙasa ina wasa da yatsun hannuna. Sum-sum nazo gabansa na durƙusa cikin girmamawa na gaishesa. Ya amsa min da kulawa tare da sanya albarka. Cikin jin daɗin addu'ar da yay ma iyayena na miƙe zuwa kitchen. Ruwa na ɗakko masa da yogurt, sai snacks dan bamu da wani abinci. Yanzu kam zaune na sami Yaya Awwab ɗin kansa a ƙasa. A gaban Paah na ajiye tray ɗin zan bar wajen ya ce dani “Daughter dawo”. Dole dawowar nayi, ya nuna min gefen Yaya Awwab ɗin ya ce, “Zauna kusa da mijinki”. Ban musa ba na zauna kaina a ƙasa. Sai da ya ɗauka ruwan dana kawo masa ya sha tare da sanya min albarka sannan yay gyaran murya da gyara zama.
“Muhammad! Kayi haƙuri ka sake yin hakuri kaji. Ni dai koda bazaka yarda na cigaba da zama da mahaifiyar ku ba, ka yafe min. Namaka alƙawarin zanyin nesa da ku na har abada dan nafi so da fatan kuyi farin ciki a rayuwarku, hakan shine ƙaddarar mu...”
Shiru babu alamar zai ce komai. Ganin haka yasa ni na magantu. Murya a sanyaye na ce, “A'a Dady duk ma ba'aje can ba. Babu inda zaka tafi in sha ALLAHU kana tare damu har abadan. Na tabbata shima kansa yana jin nauyin abinda ya farune shiyayasa kaga haka”. Na ƙare maganar ina mintsinin yaya Awwab ɗin dan so nake yace wani abu. Ganin na damesa ya nisa. Muryarsa acan ƙasa ya furta, “ALLAH ya yafe mana baki ɗaya. Kamar yanda ta faɗa kuma ni banga amfanin tafiyar ba. Tunda kun daidaita kanku mu miye kuma namu face mu muku fatan alheri. Kawai dai magana ta gaskiya ya kamata kaje asibiti a tabbatar mata da lafiyark.....”
Da sauri na zaro idanu waje, tare da kai hannuna saman bakinsa na rufe. Cikin rawar baki data murya na ce, “Yaya Please kada kai magana haka”.
Katseni Paah ɗin yay cikin murmushi ya furta, “Daughter gaskiya mijinki ya faɗa, kuma hakan shawarace me ƙyau shine kuma abinda ya dace nayi. Naji daɗi kuma da amincewarsu akan cigaba da zama da mahaifiyarsu, ALLAH yay muku albarka Muhammad”.
Murya a sanyaye na amsa da Amin. Yayinda shi kuma ya amsa a saman lips kawai........✍️




_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._


_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_

_BANK NAME:KEYSTONE_

_BANK ACC NO:6019473875_

_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_

_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_

__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_

_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_

*09033181070*

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*


_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_




*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*


*_Typing📲_*








*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*
_(Itama nama ce)_




_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_



_𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_
_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒉𝒖𝒏𝒅𝒓𝒆𝒅 & 𝒇𝒐𝒖𝒓𝒕𝒆𝒆𝒏_


Follow this link to join my WhatsApp group:

https://chat.whatsapp.com/JJkSofA4Hto57YwEu2Z8Xq


*_Wai ni Balki ina duk masoyan Bilyn Abdull ɗin nan dake a manhajar Instagram da TikTok ne?🤔? Kai jama'a gaskiya da kunya ace account na Bilyn Abdull a Instagram da TikTok iya kar fallowers ɗin kenan🥲😣. Ina masoyan facebook ɗin nan dana WhatsApp, Please a fito mana ai fallowing ɗina. Accounts ne na Bussines ko bazaki/zaka saya ba zakaga abinda ya burgeka ko kalarka ka nema a inda kake. Maza ku garzayo BILYN ABDULL ONLINE SHOPPING kodan kashe kwarkwatar idanunku ku more kallo iya kallonku da kaya ƴan yayi cikin farashi mai sauƙi da rahusa. Muna bada sari, muna adashen gata, muna sai da ɗai-ɗai. Ka gani su burgeka, ka saka ka birge mai kallonka sai Bilyn Abdull online shopping. Bari muga akwai ƙaunar kodai-kodai....😉🫣. Ga link nan naga accounts ɗin nan biyu kamar zasu fashe da fallowers 😘😘😘😍😍👍🏻👇🏻_*.

*_BILYN-ABDULL ONLINE SHOPPING_* _Duniyar cancaɗa ado da kwalliyar birgewa. Kar ku bari ayi babu ku😘😘😘._

*_My account on TikTok_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1

*_Instagram_*

I'm on Instagram as @balkissaibrahimmusa. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

_Ina masu son zuwa ganin likita ko yawon buɗe ido ƙasar Egypt?. To ku garzayo munada hanya mai sauƙi ta sama muku sauƙin tafiya cikin ƙa'ida da bin dokar ƙasa. Katafi anan cikin aminci, ka dawo kuma cikin aminci. Wajen kwananka a can zamu tanada, asibitin da zakaga likita duk zamu tsaya maka da tsayawar UBANGIJI. Hakama yawon hutawa zamu zame maka jagora. Kai ko hanyar zuwa domin sayo kaya duk muna da ita. Kai dai kawai kazo garemu kaga aiki da cikawa da iznin ALLAH. 09032345899. A nememu tanan ga masu buƙata, dan ALLAH serious bama son latsi ko wasa dan ba wasan muka fito ba 😂😍👍🏻._


.......Daga ƙarshe dai tare da shi muka fito bayan mun kashe komai. Da kansa ya buɗe mun mota ya taimaka min na shiga, Paah na kallonmu da murmushi. Sai da ya maida ya rufe sannan ya buɗema Paah ɗin shima. Ya shiga ya zagaya mazaunin driver. Yanda Paah ɗin ke janmu da hira yana ɗan amsa masa yasa naji sanyi a raina. Nima yana sakani a hirar cike da kulawa. Murmushi kawai nake iyayi da bashi amsa a kunyace. Dawowarmu gidan tare da Paah ya saka kowa farin ciki, musamman Ummie data kamani ta rungume tana sanya min albarka. Shima Yaya Awwab ta rungumesa. Fahad na tura baki zai wuce Paah ya jawosa ya rungume shi shima yana murmushi. Alhamdullah ita rayuwa komai akai haƙuri sai ya zama mai sauƙi cikin rahamar UBANGIJI. Ranar kowa zaka samesa cikin cikakkiyar walwala da rabonmu da ita tun a hidimar bikin nan. Duk da haka Paah bai kwana a gidan ba. Ya koma can gidan ya kwana. Sai dai ya sanarma Ummie duk yanda mukayi. Ya kuma mata alƙawarin zaije ya binciki lafiyarsa. Idan har akwai matsala zai sawwaƙe mata. Idan kuma babu shike nan. Amma dan ALLAH kada ta sanar ma su Awwab.
ALLAH sarki Ummie haka kuwa tai gum fa bakinta duk da tana a cikin fargaba da damuwa. Haka shima Paah ɗin yana cikin tashin hankali. Washe gari suka haɗu a asibiti, Yaya Hayat tasa ya kaita. A gabanta akaima Paah komai aka basu kwanaki uku zuwa amsar result. Daga nan ne suka dawo gida. Suun samu baƙi daga Kano, Attahir yayan Mansoor da Mansoor ɗin, sai Mahaifinsu ne suka kawo ma Yaya Awwab invition ɗin aurensu takanas domin girmamawa. Tare da zuwa su masa godiya akan abinda yay game da Mansoor a dubai. Ni bamma sani ba sai da ya shigo yake sanar min akwai baƙi a gidan naje na sanarma su Ummie zai shirya sannan. Ban tambayesa su waye ba naje na sanarma su Ummie ɗin. Kasancewar a falon baƙi aka saukesu dan danan na shiga kitchen da kaina ina tsaye masu aiki suka haɗa komai suka tafi kai musu. Dan naga yanda ya ɗauki batun baƙin da muhimmaci. Kusan mintuna talatin da kai musu abinda na aika ɗin ya shigo ya samemu a babban falo yake sanar mana gasu zasu shigo. Magana Ummie ke son yi amma bai bata dama ba ya fita. Sai mukaita kallon kallo. Waɗan nan waɗanne irin baƙine haka masu muhimmanci a wajen Yaya Awwab. Shigowarsu ya katse mana tunaninmu, ina ɗaga kai wazan gani. Mansoor da fa babansa da yayansa. Sunan ALLAH na ambata zuciyata na rawa, dan na rasa ma ina zan kamo al'amarin nikam. Ashe bani kaɗai ba, ta ɓangaren Ummie ma ta daskare a tsaye ta zubama Dad ɗin su Mansoor ɗin ido. Yayinda shi kuma Dad ɗin ya kafe ƙaton black & white ɗin hoton Kakar Ummie da Mahaifiyarta kakar su Yaya Awwab kenan da kallo. Shi kuma Mansoor ya ƙure ni da ido. Gyaran Muryar da Yaya Awwab yayi ne ya dawo damu hayyacinmu mu duka. Cikin rawar baki data jiki Dad ke nuna hoton da yake kallo. Kamar wanda ke koyon magana idonsa akan Yaya Awwab ya furta, “Son ina kasan wannan matar?”. Yay nuni da kakar Ummie. Kallon Ummie Yaya Awwab yayi, sannan ya kalla Dad ɗin cikin nutsuwarsa ya furta, “Uwa take a wajena, domin ɗiyarta gata nan a kusa da ita itace ta haifi Ummie na”.
“What!? Kakar tawa? kasan mi kake faɗa kuwa?”. Ya faɗa a matuƙar birkice yana kallon Ummie da itama jikinta ke rawa sosai. Matsawa Yaya Awwab yay jikin hoton sosai ya kamashi ya sauke. Tare da takowa gaban Dad yana mai jinjina kansa. Ya furta, “Tabbas Maimoonatu itace ta haifi Rabi'ah, Rabi'ah ta haifi Ummie na tare da wannan” ya ƙare zancen da juyawa ya nuna kakansa Abie. Birkicewa Dad yay gaba ɗaya. Yayinda Attahir ya furta Dad wlhy kamar Mammi, dan ALLAH Mansoor kalla da ƙyau basa kama da Mammi? Ni sai nagama kamar akwai irin hoton nan a cikin hotunan Mammi da muka taɓa ɗauka ta kwace har tana kuka”.
Amsa Masoor ya bashi da, “Tabbas Yaya wannan hoton Mammi na da shi, kuma ta faɗa mana sunan ta jikin hoton Maimoonatu Addarta ce. Har alƙawari tama akan zata bamu tarihinta wataran ka manta. amma sai bamu samu zama ba saboda abubuwa”.
Kamar zancen su Mansoor ya ƙara zaburar da Dad tuni ya lalubo wayarsa a cikin aljihu. Danne-danne yayi ya kai kunnensa. Baima ko amsa sallamar da ake masa daga can ba ya furta, “Kawu, dan ALLAH zan tura maka wani hoto yanzu ɗan nunama Mammi, duk amsar data baka akan hoton ka kirani yanzun nan”. Bamu san mi akace masa daga can ba ya dai yanke kiran. Hoton ya ɗauka a waya ya tura, muna nan tsaye kusan mintuna biyar sai gashi an kirashi. Ɗagawa yay da rawar hannu ya saka a hansfree. Raɗau muryar ƴar tsohuwa ta fito sai dai cikin kamar mai son fashewa da kuka ta furta, “Abubakar ina ka samo wannan hoton? Da ga ina ka samo min hoton Adda Maimoona? Waya baka shi? Dan duk duniya daga ni sai ita keda shi a yanzu, kuma na duba nawa na tare da ni. Ban taɓa nunama kowa ba kuma sai Mansoor da Attahiru naka. Suma a jaye-jayensu na tsiya suka ɗakko kuma a take na ƙwace balle nace sune suka sata suka kai maka....” kuka ya sarƙeta. Cikin tashin hankali da kulawa Dad ya tareta da faɗin, “Kinga yi haƙuri Mammi, in sha ALLAHU duk zan miki bayani. Bari nayi magana da Kawu Sulaiman daga yanzu zuwa ko yaushe zai kawoki inda nake”.
“Ba ita ya kamata ta zo ba. Nice zanje Muhammad. Dan ALLAH ku kaini inda suke ina son naga tsohuwar nan”. Ummie ce ta faɗa cikin kuka. Rungumeta Yaya Awwab yay yana lallashi. A take ya juya ga Hayatu yace ya bincika musu airport akwai jirgi mai tashi yanzu ne zuwa Kano. Da girmamawa Hayatun ya amsa. Bai kuma ko gusa a wajen ba yay kira. Ankoyi sa'ar samu. Sai dai sai nan da awa uku zai tashi. Sam Ummie tace sai dai fa a tafi airport a jira jirgi. Amma ko minti goma bazata sake yi a Mansion ba. Haka dole kowa ya shiga shiri muka fice a gidan aka bar masu aiki kawai. Harda Paah da Yaya Awwab yay kira ya sanar mawa. Zama mukai na awa biyu ciff a airport kafin jirgi ya tashi, cikin ƙanƙanin lokaci kuma muka iso. Mun samu motoci ma na jiranmu. Dan haka babu ɓata lokaci muka dunguma.
Gidane madaidaici mai ƙyau. Mota uku ce kawai ta iya shiga ciki, ukun sai a waje suka tsaya. Sai da muka firfitone na tuna tabbas mun taɓa zuwa gidan ni da Mansoor. Kuma lallai anan ne nake tuno nasan mai kamannin Kakar su Yaya Awwab ɗin. Haba nayi-nayi na tuna, har shan zaman bincike da hasashe nake da zuciyata amma sam na gagara tunawa saboda abin yamun nisa ne sosai ashe. Kafinma mu gama fita a mota tsohuwar ta fito wani mutum mai tsananin kama da kakar su Ya Awwab ɗin riƙe da hannunta. A tun sanin danai mata dama tsohuwa ce, sai dai yanzu ta ƙara tsufa fiye da da. Duk kuma da kasancewarta a hakan tana tafiya da ƙafafunta, dan irin tsoffin nan ne da ALLAH ya bama ƙaramin jiki sannan bata da tsaho sosai kuma ALLAH ya bata lafiya. ALLAH sarki Ummie jikinta har rawa yake ta ƙarasa gare su. Bata san kakarta ba sai a hoto, hakama mahaifiyarta. Amma ko makaho ya kalla hoton Mama Rabi'ah da mahaifiyarta ya kalla na tsohuwa Mammi da wanda ke riƙe da ita yasan sun haɗa jini. Dan kamace sosai a bayyane dan ma tsufa ya cinye wani abun na iya

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login