Showing 63001 words to 66000 words out of 438336 words

Chapter 22 - Tsutsar Nama Book 1 Hausa Novel Complete

13 Dec 2024

2184

itama a basu bayani a kanta. Nan ma sunce sai washe gari. Hakan yasa d.c.o sakawa ai masa traicing number ɗin kafin su kawo bayananta. Sai dai me sam layin babu shi akan network kwata-kwata ma. Hakan na nufin shima mai shi ya karya shi ɗin kenan ko ya yarda ko ya sauke. Wani irin dukan ɓacin rai d.c.o ya kaima desk ɗinsa. Dan ya fahimci wannan al'amari gaba ɗaya akwai rainin wayo a cikinsa. Duk kuma wanda ya shirya ɗauke yarinyar nan yana da basira ƙwarai da gaske. Dan bai ɗauketan ba sai da ya gama tsara dukkan hanyoyin ɓullewarsa daki-daki ta yanda gano wanene shi zai yi matuƙar wahala. Amma babu komai, ai dole ne ko yaya yayi kuskure. Da kuma wannan ɗan ƙaramin kuskuren kaɗai zasu iya kama shi in sha ALLAH..
Ranar da kansa ya zo gidan Abba ba yaransa ba. Lokacin kuma anyi sa'a duk suna gida. Hatta Nabil yazo weekend bai koma ba dan shi a hostel yake zama. Hafizzullah dai ya koma bisa tirsasawar Yaya Musaddiq. Da farko kicin-kicin Mum tai da fuska. Dan ita fa magana ta gaskiya zancen Samraah ɗin nan ya fara isarta. Zirga-zirgan da ƴan sanda ke musu kullum a gida yanzu ta fara cimata rai. D.c.o dake ta binta da kallo cikin dakewa ya ce, “Ina ganin muna gab da ganin Samraah in sha ALLAHU”.
Mum data gama cika taf cikin ɓacin rai ta ce, “Yo dama kune ke wahalar da kanku, duk ma inda take ai itace takai kanta. Dan ni nasan abokan iskancinta tabi wani garin kawai suke zaman shashancinsu a wani wajen. Amma yallaɓai duk kunbi kun tadama kanku hankali muma kun gagara barinmu mu huta. Haba, Samraah dai Samraah dai kamar wata allura ko sarƙar gwal ko diamond”.
“To amma Hajiya duk kin san da haka miyyasa baki sanar mana ba tun farko?”.
“Ni! Rufamin asiri na mutu maza su kaini ba mata ba. Taya zan sanar muku kuwa yallaɓai. Ace kuma na laƙa mata sheri. Kadai san ɗan riƙo komi zaka masa ba tsira kake ba. Amma tun yaushe wannan yarinyar ke bin maza suna barin gari. Wane hotel ne bata san da zamansa a garin nan da wajen garin ba. Ai ni bana raba ɗayan biyu wannan yarinyar ta zubar da ciki sama da sau bakwai kuwa. Tunda nan zata dinga mana ihu da murƙususu wai mararta na ciwo, haka zakaga jini na binta, in ba zubda ciki ba kuwa mi tayi?”.
Kai kawai d.c.o ke faman jinjina wa. Yayinda Abba keta hararar Mum da mata alamar tai shiru amma matar nan sai da takai aya ta haɗiyi yawu bakinta kamar an ɓarka zani. Kallon Abba d.c.o yayi bayan ya gama ɗan rubuce-rubucen sa. “Amma Alhaji matsayinka na uba duk kasan da hakan baka taɓa ɗaukar wani mataki ba?”
Kafin Abba yay magana caraf Mum ta sake amshewa. “Matakin mi zai iya ɗauka a kanta yallaɓai. Bayan duk gidan nan babu wanda take shakka ko tsoro tafi ƙarfinmu. Sannan ɗan uwanta duk da saninsa take komai tunda shine kawalinta.....”
“Amma Hajiya ina magana da mijinki ne. Shi kuma nake son ya amsa min wannan tambayar.” kai Mum ta ɗauke gefe tana laɓe baki. D.c.o ya sake maida hankalinsa ga Abba da yanayinsa ya nuna sam baya jin daɗin abinda Mum ɗin keyi, amma ya gagara tsawatar mata. “Kai nake saurare Alhaji”.
“To yallaɓai ni mizance. Al'amarin ne gaba ɗaya akwai ruɗarwa. Amma ina yin iya bakin ƙoƙarina, sai dai kasan mu maza koda yaushe kana waje ba zaman gidan kake ba, shiyyasa ita ta fini sanin abubuwan”.
Shiru kawai d.c.o yay tare da zubama Abba dake ta ƴan kame-kame ido. Yaya Musaddiq da idanunsa suka cika da ƙwalla cikin sarƙewar murya ya ce, “Ranka ya daɗe Samraah bata taɓa aikata fasiƙanci ba. Sannan inba akan aikin nan nata ba zan iya rantse maka bata taɓa shiga hotel ba. Sannan ciwo da takeyi tana yinsa ne duk wata sakamakon al'adarsu ta mata. Amma inaga abar maganar nan, duk kuma inda take in sha ALLAHU addu'armu na biye da ita. ALLAH ya bayyanata, ya kuma bata kariya daga sharrin duk wani mai sharri”.
Maganganun Yaya Musaddiq sun sake saka Abba shiga wani yanayi, dan sai zufa yake kamar wanda ya haɗiyi kunama. Yayinda Mum keta ƙunƙuni ƙasa-ƙasa tana jin kamar ta rufe Musaddiq da duka. Sai dai babu damar hakan kodan d.c.o dake zaune. D.c.o ya gamsu da zancen Musaddiq, dan haka bai sake cewa komai ba ya miƙe. Miƙewar shima Musaddiq ɗin yayi batare da ya sake kallon inda su Abba suke ba ma, dan bai taɓa jin ɓacin rai mai tsanani akan abinda suke musu ba irin yau. Wani irin zafi yake ji a zuciyarsa game da su matuƙa....


★💫★💫★💫★💫★💫


Ciwo ne sosai yaci ƙarfina. Harma nake ganin ya ninka wanda nakeyi a baya. Ko hakan nada nasaba da yanda nasha magani wata na biyar kenan ma banyi ba. Sama-sama nake jin ana buɗe ƙofar. Daga haka ma nai ɗiff alamar hankalina ya gushe daga gangar jikina.

Da sauri wanda ya shigo ɗin ya koma baya ganin Samraah ta suma. Cikin tashin hakanli yake sanarma sauran ƴan uwansa, “Kai yarinyar nan fa kamar ta mutu”.
“Mutuwa fa?”.
Suka faɗa a tare suma cikin zaburowa. Komawa yay da gudu yana faɗin, “Kuzo to ku gani wlhy”. Duk binsa sukai cikin sassarfa suma. Wanda ke da ɗan yanayin hausawa a cikinsu ne ya ce, “Kamar suma tayi dai, Ayo ka kira oga Please, kasan dai irin gargaɗi da sharuɗɗan daya gindaya mana. Kar muce zamuyi shiru mu samu matsa”.
“Exertly maganarka gaskiya ne.” ya faɗa yana ƙoƙarin danna waya. Duk cikin harshen nasara suke maganar. Baifi mintuna biyu ba sai gashi ya dawo. Ya sanar musu oga yace duk su fita a ɗakin za'azo da doctor yanzu. Hakan kuwa akai duk suka fita, Ayo ya kulle ɗakin kamar yanda aka umarcesa. Bako a cika minti talatin cif ba sai ga driver ya kawo doctor. Ita kaɗai ta shiga ɗakin bayan Ayo ya buɗe mata. Sai da ta ƙarema fuskar Samraah kallo kafin ta kira Ayo ya taimaka mata suka maidata saman katifar. Duk taimakon daya dace tai ƙoƙarin bata, cikin ko ƙanƙanin lokaci ta farfaɗo. Sai dai tana buɗe ido ta dafe mararta da hannu bibbiyu tana kuka da murƙususu sosai. Da ƙyar ma take iya amsa tambayoyin doctor ɗin. Kasancewar likitar ƙwararriya ba'a wani ja da nisa ba ta fahimci matsalar Samraah. A take tai kiran wanda ya sakata aikin. Ta sanar masa zata turo sunayen magungunan da alluran da take buƙata yanzun nan a sayo a kawo mata. Yace okay ba damuwa ta tura. Rubutawa tai ta tura, sannan ta cigaba da bama Samraah taimakon daya dace kafin a kawo. Ba'a ɗauki lokaci ba Ayo yay knocking, izinin shigowa ta bashi. Ya shigo ɗauke da leda yace an kawone a bata. Amsa tai da godiya, shi kuma ya juya ya fita.
Duk zafin ciwo baya hanani shiga ruɗani a duk sanda za'amin allura. Yanzun ma hakane. Dan tunda na fahimci abinda take shirin mun na birkice mata. Duk yanda taso tankwarani kuwa ta kasa. Dan da gasken gaske na tsani allura harma da magani. Dole tai kiran wani wai yazo ya riƙeni. Nako tubure akan wlhy babu shegen gardin da zai taɓani. Ta ɗauka azabar ciwoce kawai ta sakani faɗin hakan. Sai da mutumin data kira ya shigo yana kawo hannu sukaga na rarumi handbag ɗinta zan kai masa duka sannan. Shiko yay baya da sauri yana yare da ɗaga hannaye sama. Ina kallonta tai murmushi da bashi umarnin fita. Ita kuma ta ɗauki waya, sai da ta daddana sannan takai kunne. Ina jinta sama-sama tana sanarma wanda ta kira cewar ina tsoron allura, na kuma ƙi yarda a riƙeni. Ban san mi aka gaya mata daga can ba na dai jita tana cewa okay. Daga haka ma ciwo yaci ƙarfina har tai allurar bamma sani ba saboda yanda marata kemin azaba har ina shiɗewa. Sai gani nai kawai ta haɗa kayan tafiya. Babu jimawa barci ya ɗaukeni, dama haka allurar kemin duk sanda akayita.
In dai aka min irin allurar nan cikin amincin ALLAH da nayi barci na farka shike nan. Amma abin mamaki yau saɓanin haka. Dan cikin dare na farka amma da sabon ciwon mara da yafi na farko ma. Ciwo sosai harna suma sau kusan biyu. Bamma san yaya akai ba naga doctor ɗin ɗazun a kaina. Tare da wata fuska dana taɓa sani sai dai na mance a ina nasan fuskar dan ciwo ya sakani galabaita dishi-dishi nake ɗan ganinsu, amma tabbas nasan fuskar wannan mutumin, kuma ya kamata na tuna ina ne na sanshi.......✍️


_🥱Ya kamata ki tuno dai kam, koma fita a ruɗani muma Samraatu🚴._



_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._


_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_

_BANK NAME:KEYSTONE_

_BANK ACC NO:6019473875_

_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_

_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_

__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_

_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_

*09033181070*

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*


_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*

*_Typing📲_*








*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*
_(Itama nama ce)_




_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_



_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒕𝒉𝒊𝒓𝒕𝒚 𝒔𝒆𝒗𝒆𝒏_



.......Yanzun ma dai barci ne mai nauyi sosai ya sake yin awon gaba dani batare dana gama tantance fuskar mutumin ba. Ban kuma farka ba sai washe gari da rana gatse-gatse. A yanzun ma dai ba farkawar daɗin rai bace ba. Dan still dai ciwon ne ya farkar dani ta yanda har sai da doctor ta sake dawowa. Yanzun kam naga alamun ruɗanin yanayin nawa a fuskarta itama. Dan bayan ta ɗan duddubani fita tayi tana danna waya, da alama magana take son yi da wani...
Bata wani jima sosai ba ta sake dawowa. Allurar dai ta sake fakar idona tamun, sai dai da alama tamafi ta jiya ƙarfi. Dan ko minti biyu cikakku banyi ba na sake komawa barci, daga haka ban san wainar da ake toyawa ba kuma...

A ɓangaren Doctor bayan tama Samraah allurar barci ya ɗauketa babu jimawa wanda tai kira a waya ya iso. Kamar yanda ta shawarcesa da kai Samraah asibiti ya amince. Sai dai da kansa ya nuna zai kaisu asibitin data tabbatar masa akwai dukkan tsaron da suke buƙata. Dan ya sanar mata alaƙarsu da yarinyar ta yanda hankalinta zai ɗauka bawai ainahin gaskiyar sato ta ko kwatota ne ma oho musu ba. Ita kuma jin wanda ya saka aikin yasa bata wani damu ko ɗarsa zargi a ranta ba take bata duk wannan kulawar. Dan tun jiya da tasan yana a garin Abujar nan take jin wani farin ciki, tasan kuma a dalilin aikin yarinyar nan zata iya haɗuwa da shi, duk da dai yanayin ciwon yarinyar yana buƙatar aje da ita asibitin da gasken..
Sun isa asibiti batare da wata matsala ba. An kuma yima Samraah dukkan binciken daya dace. Dan har dare suna a asibitin, sai kusan goma suka gano matsalarta. A take suka haɗo duk abinda zai taimaka mata a matakin farko kafin ai mata abinda ya dace. Gidan suka sake maidota aka saka mata drip kamar yanda ya buƙata, daga haka suka fice aka barta da masu tsaronta.

Tunda suka shigo katafaren ginannen gidan take jin jina kai da sakin kurmushi. Duk da tasan wannan ba komai bane daga mamallakin gidan. Amma dai tayi mamakin yanda yaron nasa ya bata labarin an ginashi cikin ƙanƙanin lokaci tare da wani ma a Kano. Duk da kuwa tasan yana da gidaje sosai a Abujar nan da basu da adadi ma musamman ga ita da ba kowanne ta sani ba, amma tasan wannan ɗin na musamman ne gaskiya. Har kusan ƙofar falon ya kai kafin yay parking, cikin murmushi yay mata nuni da suje ciki. Babu musu ta ɓalle murfin motar ta fita, sai wani taku take cikin yauƙi da yanga. Tun a takun farko na shigowa falon wani sanyi da ƙamshi mai sauke gajiya suka ratsata. Ta wani shaƙi iska da dogon hancinta ta fesar a slowly. Ko makaho yasan falon ya haɗu tamkar mai shi. A hankali ta ɗan kai dubanta ta gefen damarta da take jin ƙamshinsa yafi yawaita a tanan. Shine kuwa zaune cikin kujera 1sitter da laptop a saman ƙafafunsa daya miƙe saman Centre table. Yanda keyboard ɗin laptop ɗin ke bada sautin ƙara zai tabbatar maka da typing abu yake. Da alama kuma mai matuƙar muhimmanci ne. Dan gaba ɗaya hankalinsa na kan screen ɗin, kuma yana dannawa ne da ɗan yanayin sauri na ƙwarewar sabo da hakan. Ƙananun kaya ne a jikinsa kamar ko yaushe. Dan sune suturar da yafi sakawa sai ko suit kamar dangin yahudu. Sai dai kasancewar wandon nasa kaɗan ya zarta gwiwa ya bama ƙafafunsa damar bayyana samɓal. Har suka kai zaune bai kallesu ba balle ya nuna yasan da shigowarsu. Sai da ya ɓata kusan mintuna shida curr sannan yay magana batare da ya kallesun ba yanzu ma.
“Any problems?”.
Ya faɗa a daƙile cikin silent voice ɗinsa. Hayatu ne ya jin jina kai yana mai sake sakama kansa nutsu da gyara tsaiwarsa cikin nuna girmamawa sosai. “Eh to Sir dama dai akan batun yarinyar can ne. Kasan tun jiya na sanar maka abinda ke faruwa na rashin lafiyar da take ciki, har kace Dr Rumaisa tazo ta dubata. To tun dai jiyan tayi duk abinda ya dace amma ba'a dace ba. Ɗazun dai dole tasa mukaje da ita asibiti domin a bincika matsalar ta shine dama muka zo sanar maka dan yan zun ne muke dawo wa...”
Shiru kamar bazai tanka ba, sai da ya mula dan kasa ya furta, “Uhum ina sauraren ku”.
Da sauri Doctor Rumaisa tai tsigil ta ce, “Ranka ya daɗe Good evening”.
Bai amsa mata ba, illa ɗan jinjina kansa da yay kawai alamar amsawar kenan batare da ya kalleta ba kuma. Taji ba daɗi, dan ba haka taso ba. Amma sai ta daure ko za'a dace ta cigaba da faɗin, “Gaskiya yarinyar akwai babbar matsala a tare da ita. Da alama tun kafin yanzu tana fama da pain a duk sanda zatayi prioud, kuma yana mata tsanani. Maybe hakan ne ya jata ta dinga shan maganin hana zuwan prioud ɗin a duk sanda lokacinsa yayi, shine ya haifar da matsalar wannan karon ɗin. Dan sai wahala kawai take sha amma jinin yaƙi ya fita, yanzu dai in sha ALLAHU na mata dukkan abinda ya dace akoda yaushe zai iya fita ɗin, sai kuma ta kiyaye cigaba da shan wancan magungunan inba haka ba zatama kanta illa. Dan a yanzu hakan ma sai an ɗorata akan magunguna masu ƙarfi sosai da zai dai-daita mata komai, sai dai sunada wahalar samu maganin dan sunada tsada gaskiya, ba kowanne pharmacy zaka iya ganinsu anan ba ma”.
A yanzu ɗin ma dai babu alamar zai amsa dan kamar ma bashi takema bayanin ba. Hakan yasa Hayatu bata amsar dan yasan Maash bazai sake magana ba kuma. “Sir zan ƙarasa komai in sha ALLAH. Dama dai na kawota ne kawai ta maka bayani yanda zakafi fahimta.” daga haka yayma Dr Rumaisa nunin ta miƙe shima yana tashi. Sam ba haka taso ba, dan fuskarta ma ta nuna. Ta kafe Maash da kallo tana mai fatan ya sake cewa wani abu koda bazai ɗago ɗin ya kalleta ba, dan dama ita ta matsama Hayatu akan ya kawota ta masa bayani da kanta. Amma sai bai ko kallonsu ba aikinsa ma ya cigaba dayi kamar yanda suka shigo suka samesa. Sai ka ɗauka ma ya manta da su a falon ne tsabar halin yarfin mutumin nan.
Suna fita ta kalli Hayatu rai ɓace. “Amma ba haka mukai da kai ba Hayatu?”.
“To yaya kike so nayi doctor. Kin san dai halin Boss ba sai na sake tisa miki ba. Ba yau ne kika fara masa aiki ba kuma. Shiyyasa naso ma ki bari muyi komai mu gama iya mu kaɗai tunda ba gagara zai yi ba. Tunda kuma shine yasa kizo zai buƙaci ku haɗu kafin mubar garin. Yanzu dai kiyi haƙuri a madadinsa. Kiyi kuma magana da pharmacy ɗin da kikace zasu turo maganungunan nata. Sannan ki bada account number da za'a saka kuɗin.”
Gaba ɗaya fuskarta ta sauya da tsantsar damuwa da ɓacin rai. Duk da dai tasan zata shaƙi kuɗi a aikin nan, dan ko Hayatu hannunsa a buɗe yake tamkar boss ɗin nashi a wajen ƙyautatawa. Kamar zatayi magana sai kuma dai ta shanye da ƙyar, gaba tai idanunta na cika da hawaye ta buɗe motar da suka zo ta shiga. Murmushi Hayatu dake binta da kallo yayi, acan ƙasan ransa kuma yana jin tausayinta. Dan yasan tamkar ta ɗebo ruwan dafa kanta ne dakon soyayyar wanda soyayyar uwa kawai da familynsa ya sani sama data wata ɗiya mace a wannan rayuwar. Shi kansa har mamaki yake anya ogan nasa nada lafiya kuwa, dan shi

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login