Showing 273001 words to 276000 words out of 438336 words

Chapter 92 - Tsutsar Nama Book 1 Hausa Novel Complete

13 Dec 2024

2209

ma abin ya bani kunya. Tuni na rissinar da kaina a cikin ƙirjinsa kawai dan banda abin cewa kuma. Shima kawai sai ya sake rungumeni tsaff. Tare da furta, “Shiyyasa nace miki you are tiger”.
“Ni ba damisa bace, kai ne dai Zaki da baya banbance na gida dana waje”.
Na faɗa cikin ƙunƙuni ina sake cusa kaina jikinsa hannayena duka biyu zagaye da shi. Ina jin alamun murmushinsa, nima sai na ɗan murmusa kaɗan. Dan a duk sanda yay murmushi wani irin nishaɗi nake ji a raina nima........✍️



_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._


_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_

_BANK NAME:KEYSTONE_

_BANK ACC NO:6019473875_

_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_

_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_

__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_

_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_

*09033181070*

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*


_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_




*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*


*_Typing📲_*








*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*
_(Itama nama ce)_




_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_



_𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_
_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒇𝒐𝒓𝒕𝒚-𝒐𝒏𝒆_


*_BILYN-ABDULL ONLINE SHOPPING_* _Duniyar cancaɗa ado da kwalliyar birgewa. Kar ku bari ayi babu ku😘😘😘._

*_My account on TikTok_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1

*_Instagram_*

I'm on Instagram as @balkissaibrahimmusa. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv


*_WhatsApp_*
https://chat.whatsapp.com/LkRMFFQZakP55c7xK0QaMG


https://chat.whatsapp.com/D1Ki9jt2lNkKVetOWNuFN5

.......Kamar ko yanda Hayatu yay alƙawari bayan sallar isha'i sai gasu niƙi-niƙi da kaya shi da Fahad da Hafizzullah. Lokacin shi ogan baima dawo massalaci ba. Da yake ina falo a lokacin sakamakon jini dana gani, dama dai ina ɗan jin alamunsa hakan tun safe. Alhamdullah tun maganin da yasa aka bani lokacin da yay kidnapping ɗin nan nawa bana azababben ciwon marar nan, sai kuma a wannan karon nafi samun sauƙi fiye da ko yaushe. Dan duk da na rage yin mai zafi idan lokaci yayi musamman randa zai zo nakanji ciwon. Amma yau alamarsa kawai naji sai ɗan karen ƙwaɗayi dake damuna, ashe zancen Ruƙayya gaskiyane data taɓa faɗa min idan kayi aure kakan daina duka. Kasancewar ta ƙofar baya ma'aikatan gidan ke shiga da kayayyakin yasa ban tashi a falon ba. Nayi mamakin yanda Fahad ya sake daya shigo. Dan zama sukai rashe-rashe suna bani labarin wuyar da suka ciwo. Niko ina musu sannu da kumshe dariya. A ɗan abinda na fahimta game da matsalar sa da ɗan uwansa a yanzun nan shine waje ɗaya ne kawai basa iya zama. Idan kuma har ɗaya na waje koda basa ganin juna suna jin zafin kansu. Amma idan babu ɗaya normal ne. Dan gashi dai Fahad kamar bashi ba anan duk da kuwa yasan a sashen wa yake. Munfi awa guda da shigowarsu dan har inata mamakin a ina ya tsaya shi tunda anyi salla dai tuni sai gashi ya shigo Hayatu biye da shi. Kamar amma Fahad allura zaram ya tashi tsaye. Tuni kuma murmushin dake fuskarsa ya ɓace ɓat. Hannun Hafizzullah ya kama da faɗin, “Dude lat's go”.
Kallonsa Hafizzullah yay zaiyi magana na girgiza masa kai. Sai kawai ya miƙe ɗin. Amma sai da ya gaida Maash da shima yay wani irin masifar kicin-kicin da fuska cikin girmamawa. Kai kawai ya ɗaga masa alamar amsawa, kafin ma ya fahimci a yanda ya amsa masan har Fahad ɗin ya ja hannun nasa sun fice. A hankali na sauke ajiyar zuciya, sai nima na miƙe jiki a sanyaye ina masa sannu da zuwa. Nima ɗin kai kawai ya jinjina min yana kaiwa cikin kujera. Ban damu ba na sake ma Hayatu sannu tare da godiya sannan na wuce ɗaki.

Banfi mintuna goma da shigar ba ina ƙoƙarin canja channel a tv sai gashi ya shigo. Kallo ɗaya na masa na ɗauke kaina. Shiko ma bana zaton ya kallan ɗin. Sai da ya gittani na ɗan bisa da kallon ƙasan ido. Mutum dai gashi nan sundum-sundum😎 kamar wani kurma. Kai ina zan iya ƙuntata kaina haka. Duk da nima sai naso dai nake magana amma nashi yayi yawa wlhy. Shifa a rana zaka ma iya lissafa furucin bakinsa tsaff.....
“Oya zo nan”.
Silent muryansa ya katse min tunani. Ɗagowa nai na kallesa. Ganinsa tsaye tacan bakin closet ya canja kaya yasa na miƙe ina ajiye remote ɗin hannuna. Koda na karasa garesan bai yi magana ba ya dai kama hannuna muka shige ciki. Babu wani bayani ya hau zame min kayan jikina. Koda na kallesa zanyi magana sai ya girgiza min kansa yana wani lumshe ido. A zuciyata na fassara abin nasa da (bansan surutu. Koba haka ɗan uwan naku ke faɗa ba Bliy😎?). Oho shi dai bai fasa abinda yake ba. Ga kunya kamar na nutse. A bazata matuƙar bazata naji kawai a cikin kunnena ya furta, “Time for Menstrual pain ba”. Da sauri na ɗago cikin waro idanun waje sai ya wani ɗage min gira. Cike da salon iya shege ya furta, “Duk zufan nan da nasha ashe ban farauto baby ba. Ba komai thanks you my ALLAH. Ina addu'a da roƙon samun little Ummu-Hidaya a next”.
Gaba ɗaya jina nai a rikice. Dan haka nai ƙoƙarin janye jikina a nasa, amma sai naci karo da kunyar da tafi ta farko dan babu kaya a jikina. Sai kawai na sake komawa na ƙanƙamesa. Yunƙurin murmushinsa kawai naji a ƙirji, amma ina da tabbacin a zahiri babu alamarsa a kan fuskarsa. Bai sake cewa komai ba shima sai ƙoƙarin saka min wasu kayan da ban san daga ina ya samosu ba. Wani shegen ƙyaƙyƙyawan abaya ne mai azabar ƙyau milk da kwalliyan golden a jikinsa. Ƙamshin ma da take kawai abin ɗaukar hankali ne. Kasa haƙuri nayi sai da na kallesa fuskata da murmushi na ce, “Woow Yaya ina ka samo a bayar nan ta haɗu wlhy”.
Banyi tunanin zai amsa min ma, amma sai kawai ya ɗan ranƙwafo ya lakace min hanci kaɗan, cikin raɗa-raɗa ya ce, “Ƙanwata BILYN ABDULL ONLINE SHOPPING mana. Indai kina son Abayoyi ƴan yayi da fidda kwalliyar kece raini jeki can kawai My Tiger, har masu sari suna kawoma kaya tun daga ƙasar Egypt akan farashi mai sauƙi da kai ma zaka sayar ka samu taka riban 09032345899”.
“Woow, gaskiya madalla da Bilyn Abdull online shopping da ya sauƙaƙa mana wahal halun neman abayoyi muna a gidajenmu kwance. Jiba dai yanda rigar nan ke wani wal-wal na fito kamar jinin sarauniya Aminar zazzau.”
A hankali ya saki murmushi da kanne ido ɗaya ya ce, “Bilyn Abdull online shopping ai duniya ne”.
Jikinsa na faɗa na rungumesa. Na ce, “Tabbas na shaida hakan”.....

Koda muka kammala shiryawa tsaff hannunsa riƙe da nawa muka fito. Babu abinda kake ji sai mayataccen ƙamshin turarensa. Dan ni kam sam ba'a jin nawa. Da kansa ya kulle ƙofar ya saka mata security. Ko'ina na gidan akwai haske sai kace a turai. Kasancewar ba dare ne yay ba tako ina ma'aikatan da basa barcin wuri nata kai kawo. Sosai nake jin kunyar yanda ya riƙe hannuna ram kamar zan gudu masa. Suko duk wanda ya mana kallo ɗaya baya sakewa sai yay ƙasa da kansa yana gaishe mu kawai. Muna gab da isa parking space mukaci karo da Hajiya ƙarama dake fitowa a mota. Da alama shigowarta gidan kenan dai itama. Yanda ta ke kallonmu kamar wata gunki ya sani ɗan risinawa na gaisheta. Lips ɗinta na rawa ta amsa min. Shiko gogan ko kallon inda take banga yayi ba muka gittata muka wuce. A gaban wata motar dake rufe da tempol muka isa. Sai ga TJ kuwa da ɗan gudinsa ya iso. Yaye tempol ɗin yay. Wata arniyar farar dunƙulalliyar mota da ban san yaya zan siffanta muku ƙyawunta ku gane ba. Gashi naci kai ban san sunayen motoci ba. (Su o'e ƴar uwarku bata san mota ba fa😝) ta bayyana. Kasa daurewa nayi sai da nace, “Woow” a hankali ina sake damƙe hannunsa dake riƙe da nawa. TJ na gama yaye tempol ɗin yabar wajen, ɗan kallonsa nayi, dai-dai da ya ciro key ɗin motar ya ɗan ɗaga min shi sai tin fuskata. Murmushi na sakar masa har haƙwarana na bayyana. Dan na fahimci dai da kansa zai yi driving ɗin kenan abinda ban taɓa gani ba. Hannuna kuwa ya ja har gaban motar yana mai danna key ɗin tai ƴar ƙara. Sai ko ga murafanta sun wani shiga ɗagewa sama kamar fukafukai. Tofa yau naga jalalar rayuwa. Mota dai dana sani buɗe mata murfi ake kamar ƙofar ɗaki. Amma wannan al'amari haka tab ɗin. Ina kallon yana murmushi, nasan kuma bai wuce yanda yaga na saki baki ba ina zuba ƙauyanci. Da kansa ya sakani a motar, sannan ya zagaya ɗaya side ɗin ya zauna. Wani abu ya danna a hankali murafan suka shiga komawa yanda suke. Wani irin ƙamshin motar da sanyin ac daya kunna suka fara ratsani. Juyowa yay ya kallan cikin wani irin shanye cat eyes ɗinsa.
“Are you like it?”.
Yanda yay maganar cikin motsa lips ɗinsa a wani kalar hankali yasa tsigar jikina tashi, nima a hankali idanun nawa a cikin nasa na furta, “Fiye ma da yanda kake tunani Yaya”.
“I'm not your Yaya, change this name for me. I no like it”.
Fuska na ɗan shagwaɓe kamar zan yi kuka nace, “Yaya Musaddiq ƙaninka, Aunty Falaq ƙanwarka. Hafizzullah ƙanwar ka. Hayatu ƙaninka, Fahad ƙaninaka, sai ni ce kaɗai za'a ware a dangi. To ALLAH ma nayi yaji da ga yau zan koma wajen Ummiena”. Na ɗauke kaina.
“Ai nasan bama zaki iya ba, yin nesa da ɗan santalelen mijin nan naki tab. Asibiti mafa matsawa kikai a sallameki dan ki dawo kusa da ni”.
Da wani masifar sauri na juyi na kallesa. Ya wani tsatstsareni da idanu hannayensa harɗe a ƙirjinsa, sai wani ƙara shanye idanun yake ƙasa-ƙasa. Kafin ma nace wani abu, a saman lips ya furta, “Ki rantse ba haka bane Kandala”.
“Ni ALLAH bance ba. Kuma ni ba Kandala ba, in ba haka ba ALLAH kaima Yaya to”.
Karan farko naga yayi murmushi mai wahalar gani akan fuskarsa. Dan haƙoransa har sai da suka bayyana. Ya dunguremin kai da faɗin, “Kema Yaya to”.
Dariya na ƙyalƙyale da ita. Shima sai ya wani shafa kansa yana mai ma motar key. Sosai mamaki ya kamani ganin har lokacin Hajiya ƙarama na tsaye a inda muka barta ɗazun idonta a kammu. Kaina na ɗauke abina kawai har lokacin fuskata da murmushi.
Yanda yake juya steering cike da gwaninta ya sani kasa haƙuri sai da na furta, “Dama ka iya mota amma kullum ake tuƙaka”.
Baice komai ba sai ɗan murmushi kawai ya cigaba da tuƙinsa. Nima sai nayi shiru kawai na sake maida hankalina a kallon gari. Dan yau itace rana ta farko da nake ganin birnin Lagos da ƙyau duk da ma dare ne. Tabbas Lagos ta cancanci zama cikin citys na duniya. Dan adai ta inda muke zaka ɗauka ma a turai kake ba Nigeria ɗinmu ba. Jinai na sake so da ƙaunar ƙasata sosai. Isowarmu bakin katafaren ruwan nan na Lagos da muke ta jin labari ya sa kaina sake susucewa. Duk da darene akwai mutane sosai anata harkokin arziƙi. Kai da ka gani kasan duk wanda ke'a wajen yaci ya tada kai. Yo wannan irin holewa haka ina talaka yaga lokacin yinta. Sosai mamaki ya kamani ganin mu anzo an taremu cikin tsaro da matuƙar girmamawa. Sannan maimakon wajen taron mutanen nan mu can ta gefe aka mana rakkiya mu kaɗai a wajen ƙwallin ƙwal. Sai dai akwai haske sosai da zaka iya ma yarda allurarka a cikin yashin nan ka ɗauki abinka. Sai ƙarar ruwa dake wani irin ambulowa na hanƙoro a gaɓa, sai kuma ya janye ya koma. Na zata nan kawai zamu tsaya mu kalla ruwan mu koma, sai kawai ga wani ɗan madaidaicin jirgi fari tass mai masifar ƙyau ko'a kallonsa ya iso gaɓar ruwan. A hankali ya juyo ya kallan ta re da motsa lips ɗinsa kaɗan ya ce, “Les't go”.
Idanu na ɗan waro waje da faɗin, “Cikin jirgin?”.
“Yerhhh”.
Ya bani amsa a taƙaice yana jan hannuna.......✍️



_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._


_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_

_BANK NAME:KEYSTONE_

_BANK ACC NO:6019473875_

_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_

_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_

__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_

_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_

*09033181070*

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*


_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_




*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*


*_Typing📲_*








*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*
_(Itama nama ce)_




_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_



_𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_
_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒇𝒐𝒓𝒕𝒚-𝒕𝒘𝒐_


.......Tamkar wata shasha haka na koma wajen kallo har muka shige ciki. Jinai har numfashina na sama da ƙasa saboda haɗuwar cikin jirgin da kayan alatun da aka shirya masa. Zaune ya kai cikin lallausan wajen da aka shirya tamkar falo, tare da kamo hannuna a hankali ya jawoni saman cinyarsa ya zaunar. Ajiyar zuciya na sauke nima a hankali, tare da juyawa na kallesa. Sai kawai ya saka soft hannunsa cikin nawa ya ajiye min key ɗin motar nan. Hannun nawa na kalla na ɗago shima na kallesa. Ya wani irin kashe min ido ɗaya da ɗage gira sama.
Tashi tsigar jikina tayi, dan haka nai ƙasa da kaina ina jujjuya key ɗin, muryata na ɗan rawa na ce, “Key! Karfa na yarda”.
Sake rungumoni yayi jikinsa tare da ɗaura kansa a kan wuyana yana wani shinshinawa sannu-sannu har ya kai saman kunnena. A hankali ya kama kunnen da haƙori ya ɗan ciza. Jikina na ƙanƙame lips ɗina na rawa alamar son yin magana amma na kasa. Sai ƙoƙarin ɗaura hannuna da nai akan nashi da yake yawo a saman cikina. Raɗar da yake min akan kunnen ta sani ƙanƙame hannun nasa da masifar ƙarfin da ban san daga ina yazo ba.
“It's yours”.
Kasa magana nayi tsabar yanda yake neman haukata min jiki da salon sa. Sai kawai na saki hawayen da suka cika idona na, lips ɗina na rawa na ce, “Mota fa?”.
“Uhhmm!”.
Ya faɗa yana ƙara cusa hancinsa cikin wuyana. Kasa jurewa nayi, dan jikina ya fara rawa. Sai kawai na birkito na faɗa jikinsa na ƙanƙamesa kawai tsam-tsam ina sauke numfashi a gwame...

Wani irin shegen murmushin mugunta Maash ya sake yana sake turata a cikin jikinsa da ƙyau. Shi kaɗai yasan mi yake ji akan wannan ƴar ficilar yarinyar mai wayon tsiya....

😎Humm su Yayanmu fa to🥱Bara dai nayi ciluuu.

💦💦💦💦💦

Sosai jikinta yay sauƙi a ɗan tsakanin nan, sai ma wata irin murjewa da ƙyawu da cikin ya ƙara mata. Ga haskenta ya sake fitowa bazaka taɓa cewa Halimen ƴan tumaki bace ba. Yawan kwaɗaita mata karatu da Aunty Zakiyya keyi ya fara jan hankalinta. Aiko Abba na zuwa yau da dare ta ce masa tana son komawa makaranta. Kallonta yake da mamaki, itako ta shagwaɓe masa fuska kamar zatai kuka. Dole ya saki murmushi da faɗin, “Haba Halimatussa'adiyya, karatu kuma? Keda ke fama da jikinki wane karatu”.
“Ni dai naji sauƙi, ina son komawa na samu ƙarin ilimin addini dana zamani kodan nasan ta yanda zan cigaba da bautama UBANGIJINA na kuma shiga duk inda nake so a duniya. Yanzu dan ALLAH ina daɗi kamarka ace matarka bata iya ko karanta sunanta ba balle ta rubuta. Dan ALLAH ka duba dai Dalin”.
Murmushin ya sake saki yana ƙumshe dariya, dan yasan idan yayita a waje to za'a samu matsala shi da ita. Saboda cikin nan fushi yake sakata sosai ga masifar tsiya. Gwaggo Gudidi dake saurarensu daga waje ce ta shigo, zama tayi itama ta saka baki akan maganar komawar Halimen makaranta. Dan in ta koma ɗin ko abinda zata zauna da Mom ta samu ai anci riba. Saboda ita kanta ta fahimci Halimen na buƙatar ilimin zamani sosai kodan zama da irin su Mom. Shiyyasa ma da Zakiyya na zugata bata ce musu komai ba. Cikin hikima duk tama Abba bayani sai ya fahimta...

Yin maganar nan da kwana baifi uku ba kuwa sai ga Abba da form ɗin wata makaranta. Suna boko da safe islamiyya da yamma. Sosai Halime ta shiga murna. Hakama Gwaggo Gudidi. Nan dai Abba ya cike mata Form ɗin ya maida, tare da ɗan yin duk abinda ya dace. Randa suka bukaci a kaita su mata interview ya zo ya ɗauketa ya kaita. Tsabar yanda ya matsu da son kasancewa da ita sai ya wuce da ita gida. To ita kanta dai tana buƙatar, dan haka ko musa masa batai ba. Sun samu Mom bata gidan, sai Aunta kawai da sabuwar mai aikin da Mom ta kawo. Haka Abba ya saka mai aikin ta gyara ma Halimen

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login