Showing 375001 words to 378000 words out of 438336 words

Chapter 126 - Tsutsar Nama Book 1 Hausa Novel Complete

13 Dec 2024

2218

bakin Azizat ɗin da ƙanwarta sukace su gaskiya mahaifinsu zasu bi. Dama tunda abin nan ya faru suka koma sashen Uncle Abdullahi. Damuwa da kukan da suke sha ya sakasu shiga kamar a halin depression. ALLAH sarki ɗan uwa rabin jiki, sai Malika ce ke ƙoƙarin kwantar musu da hankali ita da mahaifiyarta. Ganin yanda suka tubure zasu bi mahaifinsu yasa dole Hajiya Mammah ta sallama. Tana ji tana gani suka tattara kaf kayansu suka bisa zuwa ƙasarsu, ko kallonta basuyi ba sai itace ke famar kuka.

Bayan wucewarsu washe gari itama Maman Malika ta bama Uncle Abdullahi shawarar barin Mansion su koma nasu gida tunda aikinsa ya ƙare. Ta kuma bashi haƙuri bisa zargi data dinga masa da magana mara daɗi akan hakan. Dan sunsha tafka rigima akan dawowarsu Mansion batare da kowa ya sani ba. Saboda ita sam ba'a san ranta suka dawo ba a lokacin, sai dai da yake yafi ƙarfinta dole ta haƙura ta sallama ashe shi da tasa manufa.
ALLAH sarki rayuwa, duk abinda ya sakaka dariya watarana sai ya saka ka kuka. Hakama wanda ya sakaka kuka zai iya sakaka dariya watarana. Yau ga Hajiya Mammah dake so da burin mulkar Mansion ita kaɗai ƙwallin ƙwal a cikinsa. Sai securitys da aka bari da wasu tsirarun ma'aikata maza. Amma kaf masu aikin nan mata sai da Uncle Abdullahi ya sada kowa da iyayensa da alkairi mai tsoka daga Ummie. Kuka sosai Hajiya Mammah tayi a wannan rana, ta dinga zagaya gida tana sambatu da surkulle kamar wadda ta zare. Kwana biyu dai ta fahimci kanta na neman kwancewa ta tattara itama ta nufi tsohon gidansu na gado inda Baba prof yake rayuwa, tunda shi bai kai ko kaso ɗaya bisa goman girman Mansion ba. Nan ɗin ma dai ba daɗin take ji ba sam. Dan kowa ya watse babu masu aiki ko ɗaya a cikinsa hatta maigadi ma. Ga jami'an tsaro sunma gida kaca-kaca saboda bincike. Haka dai ta raɓa ta zauna dan babu yanda zatayi. Idan ma tace zata bar nan ɗin ina zata je? Ita dai ƴan kuɗaɗen da take samu dama kullum cikin fallasar dasu take da lissafin ai Azizat zata auri Awwab su mallake dukiya. Shiyyasa ɗan abinda take da shi yanzu bawani ya taka kara ya karya bane ba. Dukiyar dake tsakanin Mansion da nan kuwa karo na farko a rayuwarta taji ko tsinke bazata iya taɓawa ba dan ba nata bane ba. Tana matuƙar jin kunyar tace zata koma gidan Uncle Abdullahi kuma kodan cin kashin data dinga ma matarsa da shi kansa. Saboda ita dama ba kowa ta ƙyale ba ko sanda suna Mansion.
Tsanantar da jikin Paah yay ya saka Uncle Abdullahi zuwa ya sameta kan ko zataje tai jiyyarsa. Dan shi gaskiya yana matuƙar jin kunyar sanarma su Awwab halin da yake ciki. Balle ma shima Awwab ɗin yana can yana fama da jiyya. Ita kuma Ummue doctors na ƙara treatment ɗin ta yanda ya kamata. Batayi ko jayayya ba ta amsa masa. Haka ta shirya ya ɗauke ta ya kai asibiti batare da sun iya cema junansu komai ba. Dan su a karan kansu ma shakkar tada zancen abinda ya faru sukeyi. Sun fara shiga suka duba Hajiya Ƙarama da ɓarin jiki ke a shanye, sai Arwa da itama ke a kusa da ɗakinta yarinyar na cikin matsanancin depression abin tausayi. Sai Baba prof da komai baya motsi a jikinsa sai kai da idanu, ɗaki ɗaya suke shi da Commondo da Arwa ta tsinkema jijiya shima dai gashi nan ne kawai kwance sai idanun. A yanzu su duka huɗun suna a ƙarƙashin kulawar jami'an tsaro ne. Su asibiti ke kula da komai nasu shiyyasa ba'a buƙatar masu jiyya. Sai Paah ɗin ne kawai, amma duk da haka Uncle Abdullahi yana raba lokacinsa a tsakaninsu musamman Paah da Baba prof ɗin da suka zame masa dole...

🌿⭐🌿⭐🌿

A ɓangaren su Abba kam tunda suka isa gida Abba yayma Mom bayanin Maash ya amshi sunan mijin Baby yace zai bincika ta ɗan fara samuwa. Duk da dai a ƙasan ranta tana jin wani iri, dan koba komai dai Maash ɗin nan mijin Samraah ne. Yarinyar data ɗauka ba komai ba. Koda yake miye ma na ɓatama kanta rai, tasan dai matsayi irin na Maash da dukiyarsa mizaiyi da ita. Ƙilama ko ganinsa batayi balle ya mata kallon macen aurensa. Wannan batu na zuciyarta ta sata samun sassauci. A washe gari aka sallamosu asibiti. Suna zaune ita da Ummanta da Bibaa a falo Halime dake fama da ƙaton cikinta ta shigo tana ɗan hakki. Yanda cikin nata yay girma dole kayi mamakin kamar ba cikin fari ba. Da ga tsayen ta gaishesu da yima Mom ɗin yaya jiki dan bata iya zama sai da taimakon wani. Umma ce kawai ta amsa mata. Mom kam bama ta kalleta ba, yayinda Bibaa taja tsaki ta tashi ta bar falon. Ita kaɗai tasan zafi da raɗaɗin da take ji a zuciyarta a duk sanda ta kalla cikin yarinyar nan. Babu abinda basuyi dan ya zube ba amma ko gezau. Babu komai ai yanzu sun samo abinda zai musu maganinta. Dan teacher ɗinta ya tabbatar mata tayi ƙoƙari ta samo mahaifar Halimen a randa ta haihu. Shiyyasa yanzu ranar haihuwar kawai suke jira.
Halime da yanzu ita abinda ma ya isheta shine ya isheta tana gama gaishesu ta fito abinta. Ɗakinta ta koma inda Abba ke jiranta dan yana gidan shima. Yau kuma ranar girkinta ne. Kamata yay ta zauna yana mata sannu. Cike da shagwaɓa ta amsa masa tana miƙa masa ƙafarta da tayi fushi. Amsa yay yana danna mata a hankali suna ƴar hirarsu. Hirar data saka Abban kwasar dariya dan Halimen nata zuba masa shirmen turancinta ne data dage tana koyo. Duk da ma dai a tsakanin nan makarantar ta gagareta saboda bata jin daɗi...
Kullum sai Abba yayi waya dasu Samraah yanzu. Ƙoƙarin jawosu jikinsa yake yi domin ya kwaranye abinda ya cusa musu a baya. Su kuma sun saki jiki da shi da alama sun jima suna buƙatar hakan daga garesa amma ya gagara musu. Har dai ranar da su Samraah zasu wuce Spain Mom bata sani ba. Dan Abba ya daina sanar mata komai daya shafesu. Idan ma shawara yake nema Halime ce. Saboda zai iya cewa itace ta dawo dashi kan hanya akan batun su Samraah ɗin. Tunda ta fahimci komai kullum cikin masa nasiha take kamar ba yarinya ƙarama ba. Tun yana fushi da ganin ta shiga hurumin daba nata ba har ya fara fahimtarta. Sannu a hankali ya fahimci kuskuren da take ƙoƙarin nuna masa. Shiyyasa yanzu wani bala'in ƙara son yarinyar yake. Gata dai da ƙarancin shekaru sai hankali da sanin ya kamata. Fatansa dai ALLAH ya sauketa lafiya....

✨🌿✨🌿✨

“Wai yaushe ne batun tafiya Lagos ɗin nan Daddyn Attahiru. Tunda abubuwa sun lafa inaga ya kamata muje muyima bawan ALLAHn nan godiya. Na kuma sake neman gafararsa akan kuskuren dana tafka. Wlhy gaba ɗaya ko'a zuciyata na tuna kunyar kaina da kaina nake ji”.
Murmushi Dad dake zaune idonsa a television yayi, sai kuma ya ɗan kalla Mamyn tare da amsar kofin black tea ɗin da take miƙo masa. Sai da ya kai shayin bakinsa ya ɗan sha sannan ya sauke numfashi. “Karki damu zamuje, sai dai tama ƙara tsayi. Dan yau dana bincika ake sanar min shi da iyalinsa da mahaifiyar tasa duk sun wuce Spain. Dole muyi haƙuri har ALLAH yay musu dawowa.”
“Tofa, ba kwana biyu daya wuce kake cemin kun gama magana da PA ɗin nasa ba zamu je a satin nan ba. Yaya akai hakan to?”.
“Kin san manyan nan barin ƙasa tamkar zuwa bayi ne su fito suka maidashi. Balle shi Maash dake da jiragen kansa ma. Haka dai zamuyi haƙurin har ALLAH ya maidosu lafiya. Yanzu yaya batun shi Mansoor ɗin? Kin tuntuɓesa akan batun yarinyar nan ya amince? Dan so nake a haɗe bikin nan dana ɗan uwansa kawai a wuce wajen kowama ya huta naji da yarana mata suma”.
Murmushi mai ƙayatarwa Mamy tayi, muryarta a sanyaye ta ce, “Ni kasan har yanzu baya wani sakin jiki da ni. Daga gaisuwa dai shike nan. Amma Attahir yace min yaga suna waya sosai da ita. Har yana cemata a weekend ɗin nan zai sake shiga Maidugurin su gaisa. Kaga kuwa idan bai amsheta ba ai bazai ce zai koma gidansu ba bayan zuwan da mukayi muduka ko”.
“Eh gaskiya hakanne kam. ALLAH to ya ƙara daidaitasu. Haka zamu cigaba da masa addu'a ALLAH ya cire masa son ita waccan yarinyar. Dan ta masa nisa sosai sai dai haƙuri kawai. ALLAH kuma ya bamu ikon gyara kurakuranmu baki ɗaya”.
“Amin” Mamy ta amsa muryarta na sake rauni. A haka Attahir da Mansoor suka shigo falon. Da alama daga wani wajen suke a taren. Kowannensu ledar hannunsa ya ajiye. Kafin su gaida iyayen nasu. Da kulawa suka amsa musu, Attahir ya cigaba da faɗin, “ALLAH duk mun gaji. Yanzu ni da ɗan gata ne Mamy sai ki bani shayin nan na Dad mai zafi nasha na more. Amma nasan ba'a sha miki shayin miji”.
Dariya Dad da Mamy sukayi saboda yanda Attahir ɗin ya ƙare maganar abin tausayi. Yayinda Mansoor yay ɗan murmushi kawai dan yanzu ya koya miskilanci. Kofi Mamy ta ɗauka ta saka masa shayin tana faɗin, “A'a babana ai sai na baka. Nasan mika sayo min nima. Ai ba'a hana mai badawa. Man kaima zaka sha ko?”.
Ta maida hankalinta akan Mansoor. Kai kawai ya girgiza mata alamar a'a. Sai ma ya yunƙura zai tashi Attahir ya kamasa ya maida yana harararsa. Badan yaso ba ya koma ya zauna yana sauke ajiyar zuciya. Cikin tsaresa da ido Attahir ya ce, “Yaya mukai da kai ne?”.
Kai Mansoor ya ɗan sosa, sai kuma ya haɗe hannayensa biyu alamar ban haƙuri. Murya a karye ya ce, “In sha ALLAH zan gyara kayi haƙuri”.
Kai kawai Attahir ɗin ya jinjina masa, shi kuma ya maida hankalinsa ga Mamy murya a sanyaye ya ce, “Mamy zan sha”. Murmushi ta sakar masa idanunta na cika da ƙwalla. Haka ta zuba musu kowa ta bashi cike da kulawa. Daga haka suka cigaba da hira. Tun Mansoor na jefa ɗaɗɗaya har dai ya fara sakin jiki. Harma hirar ta koma fannin shirin auren Attahir, daga haka shima Dad ya takalo masa nasa batun da Salimah. Da farko ya ɗan nuna shi ba sonta yake ba, sai da suka dinga masa nasiha da lallashi sannan yace zai ƙara nazari. Abinda ya yanke zai sanarma Attahir. Sun jin daɗin hakan, suka kuma bisu da addu'a su duka........✍️



_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._


_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_

_BANK NAME:KEYSTONE_

_BANK ACC NO:6019473875_

_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_

_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_

__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_

_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_

*09033181070*

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*


_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_




*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*

*_Typing📲_*








*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*
_(Itama nama ce)_




_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_



_𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_
_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒏𝒊𝒏𝒆𝒕𝒚-𝒇𝒊𝒗𝒆_



*_Wai ni Balki ina duk masoyan Bilyn Abdull ɗin nan dake a manhajar Instagram da TikTok ne?🤔? Kai jama'a gaskiya da kunya ace account na Bilyn Abdull a Instagram da TikTok iya kar fallowers ɗin kenan🥲😣. Ina masoyan facebook ɗin nan dana WhatsApp, Please a fito mana ai fallowing ɗina. Accounts ne na Bussines ko bazaki/zaka saya ba zakaga abinda ya burgeka ko kalarka ka nema a inda kake. Maza ku garzayo BILYN ABDULL ONLINE SHOPPING kodan kashe kwarkwatar idanunku ku more kallo iya kallonku da kaya ƴan yayi cikin farashi mai sauƙi da rahusa. Muna bada sari, muna adashen gata, muna sai da ɗai-ɗai. Ka gani su burgeka, ka saka ka birge mai kallonka sai Bilyn Abdull online shopping. Bari muga akwai ƙaunar kodai-kodai....😉🫣. Ga link nan naga accounts ɗin nan biyu kamar zasu fashe da fallowers 😘😘😘😍😍👍🏻👇🏻_*.

*_BILYN-ABDULL ONLINE SHOPPING_* _Duniyar cancaɗa ado da kwalliyar birgewa. Kar ku bari ayi babu ku😘😘😘._

*_My account on TikTok_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1

*_Instagram_*

I'm on Instagram as @balkissaibrahimmusa. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

_Ina masu son zuwa ganin likita ko yawon buɗe ido ƙasar Egypt?. To ku garzayo munada hanya mai sauƙi ta sama muku sauƙin tafiya cikin ƙa'ida da bin dokar ƙasa. Katafi anan cikin aminci, ka dawo kuma cikin aminci. Wajen kwananka a can zamu tanada, asibitin da zakaga likita duk zamu tsaya maka da tsayawar UBANGIJI. Hakama yawon hutawa zamu zame maka jagora. Kai ko hanyar zuwa domin sayo kaya duk muna da ita. Kai dai kawai kazo garemu kaga aiki da cikawa da iznin ALLAH. 09032345899. A nememu tanan ga masu buƙata, dan ALLAH serious bama son latsi ko wasa dan ba wasan muka fito ba 😂😍👍🏻._



.........Isowar mu ƙasar Spain bata zame mana cikin daɗin rai ba. Dan daga airport ma asibiti aka wuce da Maash. Abu kamar wasa ashe dai ciwo ke cinsa sosai yana dannewa. Sai ɗan jigatar tafiyar nan ta sake ruɓu-ruɓu da shi. Koni mai fama da ciki ban kaisa takwarkwashewa ba. Duk da nima dai sai da suka bani gado ba wasu awwani. Bayan komai ya dai-daita muka wuce gida aka barsa nan dan dokarsu babu mai jiyya. Dan nima ina buƙatar nutsuwar. Gida ne a cikin estate da ya amsa sunansa gida. Gida na farko muka shiga, hakan ya sakani sauke ajiyar zuciya, dan in ba haka ba wannan ai sai ka rikice saboda ginin duk iri ɗaya ne ya tafi reras abin sha'awa. Yay min ƙyau da tsari sosai. Ƙaton falone a farko sai gefen haggu da dama daya zama gidan kamar wani sashe biyu. Sai upstairs. Mun sami masu aiki biyu, mace da namiji, cikin girmamawa suke mana sannu da zuwa. Kafin su mana bayanin tsarin gidan. A take Hayatu yace ni na wuce sama, dan nan ne ɗakin Maash yake. Sai Ummie da dama tana da ɗakinta itama dan sun ɗan taɓa zaman jiyyarta anan ama lokacin ne Maash ɗin ya sai gidan. Itama ya rakata nata a side na hannun dama dake dauke da bedrooms huɗu, sama biyu, ƙasa biyu. Ita zata zauna a saman ne, ɗayan ɗakin kusa da ita tace Falaq ta zauna nan ita da Bahijja, dan tace cikakken wankan jego zata fara mata ta gaji da wannan gantallen jego nata kadama Ya Hayat ya saka ran zata bashi yanzu. Dariya muka saka sosai yayinda Hayat ke faman shafa ƙeya. Ɗakunan ƙasa kuma Mama Balki da Baba suma aka basu. Sai Fahad da Hafizzullah suma a side na haggun aka basu sama. Hayat kuma ɗakunan ƙasa koda dai Ummie ta bashi ƴar matarsa ga inda zai fake nan. Hakan yayi sosai. Dan haka babu wanda yaja zancen kowa ya tafi inda aka bashi.
Sosai saman yay min ƙyau da ƙyatar da ni. Falo ne madaidaici sai bedroom guda ɗaya tal. Babu kuma ta inda muke da alaƙa da side ɗin bedrooms ɗin su Ummie da nasu Fahad. Komai tsaf yake kuma fari tas kamar kaci. Na dai samu nayi wanka na kwanta dan barci ne a idona sosai. Dama kuma likitocin sun ce a barni na huta sosai. Ban samu nutsuwar fahimtar gidan yanda ya kamata ba sai washe gari. Alhamdullah na tashi jikina yay daɗi ba kamar jiya ba. Sai kuma kewar mijina da son zuwa na ganshi amma ina jin kunya. Haka dai na daure a munafunce na tambayi Yaya Hayat. Shine yace na kwantar da hankalina zuwa anjima zai kaimu mu gansa. Naji daɗin hakan. Haka kuwa akai zuwa yamma muka je muka dubashi, yanama barci. Haka muka sakance kullum muna zuwa mu dubashi, wataran yana ido biyu wataran barci. Randa yake ido biyu ya dage nice zan masa komai, babu yanda na iya haka nake yi ina jin kunya har mu taho. Satinsa ɗaya aka sallamesa ya taho gida shima, dan ya matsa likitocin su sallamesa kin san ya tsani zaman asibiti. Murmushi kawai na ɗanyi lokacin da Hayatu ke sanarma Ummie ina mai jin daɗi a raina. Nima nafi son ya dawo gidan na bashi kulawa da kaina ai. Kamar ko yanda Hayatu ya faɗa da yamma sai gasu da shi. Kowa ya nuna farin cikin ganinsa. Bayan sun gaisa da su Ummie muma muka gaisheshi da masa yaya jiki. Da kai kawai yake amsa mana kafin ya tashi ya haura sama. Kasa tashi nayi dan kunyar idon su Ummie sai da Mama Balki tamin wayon maya tace na tashi ga abincinsa can an shirya na kai masa.
A bakin gado na samesa zaune ya zubama ƙofar ido kamar dama ni yake dakon shigowa. Ina shigowar ya wani ɗan lumshe idanunsa da sake buɗesu a kaina. Hannu ya miƙa min alamar nazo garesa. Banyi musu ba kuwa. Saman cinyarsa ya ɗaurani tare da rungumeni muka dinga sakin ajiyar zuciya. Mun jima a haka sannan cikin raɗa nace masa, “Yaya jikin?”.
Maimakon amsa min sai ya ɗagoni yana kallon fuskata. Tare da kai babban yatsarsa saman lips ɗina ya ɗan shafa. Idanuna na lumshe a hankali, dan yanda yake zagaya yatsar tashi sai nake jin tsigar jikina na tashi. Saukar hannunsa saman cikina ya sani buɗe idon.

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login