Showing 234001 words to 237000 words out of 438336 words
falon. Binsu kawai yake da kallon ƙasan ido wani abu na masa motsi a zuciya. Daka gansu kaga waɗanda sukai matuƙar shaƙuwa da juna, suke kuma tsananin so da ƙaunar juna. Wani irin lumshe idanunsa yay murmushi na suɓuce masa a bazata. Hoton Fahad ne ya fara masa gizo a cikin idanunsa dake rufe, da sauri ya buɗesu yana cizar lips. Dan wani irin zafi zuciyarsa ta fara masa. Ƙoƙarin ture tunanin dake neman kutso masa a zuciya yayi ya sake maida dubansa kansu. Hakan sai yay dai-dai da Samraah ta juyo suka haɗa ido kuwa. A mamakinsa sai ta sakar masa murmushin da har ya bayyana haƙwaranta. Sai ya samu kansa da lumshe idanun da buɗewa. A hankali ya furta, “Dama haka ake tarban baƙi da surutu?”.
Murmushin ta sake sakar masa tana miƙewa daga durƙuson da tayi a gabansu. Muryarta kanta na nuna alamun farin ciki ta ce, “Ya Awwab ALLAH daɗine naji kamar ya kasheni. Ashe dama kasan yan gidanmu amma baka tafa faɗa min ba? Nagode, Nagode kaima ALLAH ya faranta maka fiye da yanda ka faranta min”.
Kansa ya ɗan girgiza yana sakin murmushin daya kasa riƙewa. Sai kuma ya maida kallonsa ga su Yaya Musaddiq da suma ke murmushin, muryarsa da alamun tausasawa ya furta, “Bara na ɗan je bazan jimaba zamu dawo. Please ku ƙara cin abinci sosai nan ɗin gidanku ne.”
Faɗaɗa murmushin yaya Musaddiq yayi, cike da girmamawa ya ce, “Mun gode sosai ranka ya daɗe. ALLAH ya saka da alkairi”.
“Don't say me thanks you or ranka ya daɗe ɗin nan. You are my brothers. By now we are family ne okay. Nine zan kiraka Yaya, sai kuma small kiddo Hafiz a gefe”.
“Yes babban Yaya”.
Cewar Hafizzullah cike da farin ciki. Yayinda Yaya Musaddiq keta murmushi dan shi sake ganin al'amarin yake kamar a mafarkinsa. Duk da bayanin da Hayatu yay masa tare da Maash ɗin kafin shigowar Samraah zuciyarsa ta kasa daina mamakin komai. Cikin jinjina kai ya furta, “Ni ne ya kamata na kiraka Yaya, kaga dama ni kaɗaine banda Yaya. Yanzu kuma na samu. I am so happy inada wanda idan nayi ba daidai ba zai tsawatar min, inada wanda nima zan yima kuka a jiki. Ka mana komai na rayuwa. Daba dan kai ba da yanzu ban san a wane hali muke ba, dan in har wani abu zai taɓa rayuwan Samraah mu dukanmu tamu rayuwar zata girgiza ne. Saboda mu duka biyun itace rauninmu. ALLAH ya faranta maka fiye da yanda kai mana”.
Hayatu da Maash ɗin suka amsa da Amin. Dan gaba ɗaya ma Maash ɗin ya rasa abin faɗa. Idanu suka haɗa da Samraah dake kallonsa tana murmushi. Cikin ɗan ƙanƙance cat eyes ɗin nashi ya ɗage gira sama da ɗan ɗage kai alamar kallon fa.
Samun kaina nayi da jin kunya, dan haka na duƙar da kan nawa kawai ina murmushi. Dan har ƙasan raina ban taɓa jin ya sakani a farin ciki irin na yau ba. Ji nake kamar naje na rungumesa. Amma ina jin kunya. Ɗagowa nayi na ɗan kalli Hayatu, shima a karo na farko na ce masa, “Thanks You”.
Murmushi shima ya sakar min yana yin ƙasa da kansa. Sai kuma ya jinjina kansa da faɗin, “Nine zan gode ai Aunty na”. Yanzu kam Harara na balla masa ina ɗauke kaina da murguɗa baki. Sai ko muka sake haɗa ido da ogan nasa. Ɗauke fuskata nayi gaba ɗaya daga sashensu. Sai da naji Hayatu nama su Yaya Musaddiq sallama akan sai sun dawo sannan...
🌿🌿🌿🌿
A hargitse Hajiya ƙarama ta koma office ɗinta. Kofar ta kulle dan bata buƙatar ganin kowa. Kai-kawo ta shiga yi cikin Safa da marwa. Kafin ta jawo waya ta shige cikin toilet. Sau uku tana kira amma ba'a ɗaga ba. Kanta ta dafe cike da takaici. Yanzu haka yana can yasha giyar tashi yana shaɓar barci. “Motsoww” taja tsaki tare da fitowa. Wayar ta wurga saman desk ɗinta, itama ta zube a kujera tana mai dafe kai. Ji take yana wani irin sara mata. So take tai magana da wani ko zataji daɗi. Amma dawa ɗin zata yi. Da sauri ta sake rarumo wayar ta danna ma Jannifer kira. Bugu ɗaya kuwa ta ɗauka. Jin muryarta wani iri ta sata jan tsaki. “Malama dalla koma dawa koke tare ta tashi taba mutane waje magana zamuyi.”
“Bara dai ni in tashi”.
Jannifer ta faɗa tana ƴar shaƙiyar dariya. Tsaki kawai Hajiya ƙarama tayi batace komai ba. Sai da Jannifer ta sanar mata ta fito tana jinta sannan ta sake jan tsaki da fara magana. “Jannifer wai ina kika samo yarinyar nan ne? Wlhy tunanina gaba ɗaya nan birkicewa yake a wannan gaɓar?”.
Da mamaki Jannifer ta ce, “Kamar ya? Wani abu ne ya sake faruwa?”.
“Miye ma bai faruba. Yanzu nan nazo asibiti na samu wai banzan yaron nan Awwab yazo ya ɗauke yarinyar nan sun wuce gida?”.
“Tofa babbar magana. Wai Maash kike nufi?”.
“To in ba shiba waye zaima mutane wannan gadaran”.
Dariya ce ta kufcema Jannifer, sai da tayi mai isarta kafin da ƙyar cikin dariyar ta ce, “Kai amma yaron nan ƙwallon shege ne wlhy. I like him style wlhy. Komansa yake baya tsoron uban kowa. Ya taka na waje kuma na gidan bai barku ba ciwon kan da gwale-gwale yake baku. To wai kodai son yarinyar nan yake ne? Abinfa da mamaki wlhy, dan ni bammaga wani damuwa a tattare da shi akan abinda ya aikata ɗin ba. Ka ɗirkama yarinya fyaɗe amma ka dinga abu It's like you don't care, I really like this boy's style.”
“Mtsowww!! Jannifer ban son shirme. Ina miki maganar serious kina mun wani soki burutsu.”
“Ehm sorry Maa. ALLAH abunne ya ban dariya ya kuma burgeni. Samun irin stubborn mazan nan ba ko inaba. A Abuja nasan yarinyar ni gaskiya......” ta kwashe komai data sani akan Samraah ɗin tun daga haɗuwarsu da abinda ya faru kuma duk ta gaya mata”.
Cikin damuwa Hajiya ƙarama ta ce, “Amma kema kinyi ganganci da baki san labarin nata ba”.
“To banda abinki Hajjaju mizai sa na damu da labarinta. Ni fa dama irinta na fita nema. Sai kuma na samu miya rage min. Kaiwa na ɗako nazo na samu kuɗaɗena ai.”
“Mtsoww!! Aikin kenan. To ita kuma Mashi'a ya akai ta zaɓi yarinyar? Bayan nasan idan kin kawo yara sai sunyi fin wata biyu ma kafin ki saida su. Musamman irinta ma ai baki badata a masu aiki?”.
“Hummm ki bari kawai, wlhy kuɗaɗe kawai na gani. Dan an samu kuskure ne dana aika a kira min su ta biyosu. Nace ta koma Alaja Mashi'a ta ganta ta nace ita take so harda ninka min kuɗi. Ni kuma kawai naga bazan iya ba na sallama. Dan nasan ko ƙasar waje na kaita ba lallai na samu abinda na samun ba a wajenta. Kuma ina ma jin nauyin Alaja Mashi'a wlhy. Kin san dai ba wannan karon ne na farko dana fara samo mata masu aiki ba. Tunda kusan yaran gidankun nan duk a wajena aka amshesu mafi yawanci kuma itace ke zuwa da ɗauka musamman ma masu kula da Hajiya Babba.”
Numfashi Hajiya ƙarama ta furzar, dan tasan gaskiyar zance Jannifer ke faɗa mata. Mashi'a tana kallon Jannifer ne kawai a mai kawo ƴan aiki. Kuma zama ta iya cewa itace ta nuna mata gidanta a lokacin da take neman masu aiki da zata wuce da su can Germany, shine take faɗa mata gidan Jannifer ɗin. Tunda ta ɗauka wancan yaran biyu ta wuce da su taji daɗin zama da yaran sai yazam duk sanda ta shigo Nigeria takan ɗaukama Hajiya Babba masu kula da ita. Ko idan taji wasu nason masu aiki takan musu hanya. Da yake itama halin Maash ne da ita yanzu haka yaran data ɗauka su biyu duk sunyi karatu a can. Ɗaya a cikinsu ma ta kusa aure da ƙanin mijin ita Mashi'a ɗin. Ƙaramin tsaki taja da ture batun Mashi'a ta koma wanda zai amfaneta. Amma ba komai, ita Awwab ɗin ma ya saukaƙa mata aiki, a gidan ma wasan zaifi armashi tunda yarinyar a sashen masu aiki take. Zata dakata ta dawo sashenta da kwana, ta nuna saboda abinda ya faru ta ƴanta yarinyar. Zata nema mata makaranta kawai a wata ƙasar daga haka shikenan ta gama samun cikar burina..........✍️
_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._
_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_
_BANK NAME:KEYSTONE_
_BANK ACC NO:6019473875_
_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_
_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_
__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_
_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_
*09033181070*
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*
_(Itama nama ce)_
_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_
_𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_
_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒕𝒘𝒆𝒏𝒕𝒚-𝒐𝒏𝒆_
.....Suna gama ficewa cike da zumuɗi na maido hankalina kansu Yaya Musaddiq. Ƙoƙarin zama nake Hafizzullah ya ce, “Wlhy ji nake kamar a mafarki. Wai aunty Samraah kece matar mutum kamar Maash. Ya ALLAH Maash fa. Wai dan ALLAH Adda yaya akai haka ta kasance? Kodai dama ke kin san wa kika aura? Dan wlhy duk da sun sanar mana komai yanzu kuma a gabana komai ta faru lokacin auren sai nake ganin kamar dama dai kuna son junan ku ne ke da shi.”
Harararsa na ɗan yi, sai kuma na koma kusa da Yaya Musaddiq na zauna ina sauke ajiyar zuciya. “Yaya dan ALLAH mi sukace muku? Sannan dama kaima baka san shi bane?”.
Murmushi sosai Yaya Musaddiq yayi yana kallona. Sai kuma ya jinjina kansa. “Samraah wlhy har yanzu ni kaina ina a cikin yanayin da Hafizzullah ɗin yake ciki ne. Dan harga ALLAH ban taɓa sanin Maash ne mijinki ba, taya ma zan kawo hakan a raina to. Bama ni kaɗai ba, hatta su Abba babu wanda yasan wa kika aura. Koda aka ɗaukeni aiki a companynsa na amsa ne saboda dalilai uku. Na farko dai bazan iya bijirema umarnin ogana ba. Saboda yana treating ɗina like uba. Ko Abba dake ƙanin mahaifiyata muke a hannunsa tun bamu san kammu ba bana jin ya damu da tarbiyyata kamar yanda ogana ya tsaya a kaina. Hakan yasa babu abinda zai ce nayi a rayuwar nan naƙi yinsa sai dai ina na saɓama ALLAH ne ko cutar da wani. Wannan kam bazan masa biyayya ba. Na biyu maganar video ɗin nan. Na yarda zanyi aiki a companyn da tunanin ko zan fahimci wani abu dan na sanki da naci akan abu, komai tsahon lokaci da za'a ɗauka bazaki taɓa barin maganar video ɗin nan ba. Na uku amsar aikin kamar samun wata hanyar cigaban rayuwa ne yazo mana mu duka. Dan bamu da kowa sai junanmu. Dolene nayi aiki tuƙuru in har bana saɓama ALLAH bane domin cigaba da gina rayuwarmu. A lokacin da aka samu matsala game da aurenki, mahaifiyar Mansoor tazo har gida taci mutuncin su Abba akan ɗanta bazai taɓa ya aureki ba, su bazasu haɗa zuri'a da ke ba, idan kuma muka matsa zata iya ɗaukar kowane irin mataki dan ganin ta rabaki da ɗanta. Kin san Kawu Musa da zuciya, dan haka shima ya balbaleta, sai kawai ta ɗaga hannu ta maresa. Kafin ta sauke hannunta mukaji itama an sauke nata marin. Ta gigita sosai, haka muma da mamaki muke kallon bawan ALLAHn daya maretan. Mutum ne cikin shigar kamala harda gemunsa, maganganun daya gayama mahaifiyar Mansoor a lokacin sun matuƙar birgemu. Sai muka ji sauƙin yanda kalamanta suka ƙona mana rai dama kowa na wajen a take muma mukace ko Mansoor ne autan maza kin barsa har abada. An gama duk wannan rikici Maman Mansoor ta wuce bawan ALLAHn nan shima zai wuce Kawu Musa ya dakatar da shi. Godiya ya masa muma haka. A mamakin mu sai kawai muka ji ya fara jera masa tambaya. (Yaro munene sunanka?) Yace masa Muhammad. Anan kake? Yace masa eh to yana aiki anan amma asalinsa ba mazaunin nan ɗin bane. Kana da aure? Sai da yay jim kamar mai tunani kafin yace masa a'a. Kana shirin yi ne? Nan ma ya amsa masa da a'a. Iyayenka fa? Yace suna nan a raye. Sai mukaga kawai Kawu Musa yayi murmushi. Batare da wani tunani ba kawai ya ce (kowa ya shaida. Ni Musa a matsayin yayan Abdul-wahab na bama wannan bawan ALLAHn Muhammad auren ɗiyata Samraah. Ina fatan bazaka taɓa watsa min ƙasa a ido ba. Ina fatan zaka tabbatar min da ƙyautata maka zato da nake yi. Ina fatan zaka riƙeta amana bazaka taɓa cin amanata ba. Idan kuma har akwai matsala ka fito ka sanar min wlhy zan fahimceka. Nima kuma badan bana son Samraah na baka ita ba. Ba kuma dan na zubar mata da darajanta nayi hakan ba. Yarinyata mai ilimin addini ce dana zamani. Sannan ƙyaƙyƙyawace mai tarbiyya. Kaga dai ban sanka ba, ban san daga inda ka fito ba. Komai daya faru daga UBANGIJI ne ba daga mu ba. Dan abinda kayi yanzu yasa nake ji a raina ko daga ina ka fito kai ɗin mutumin kirki ne, dan ɗan halak shike kare martabar tsoho a duk inda yaga za'a yaga masa rigar mutunci.”
“Wlhy Kandala ya matuƙar jimawa tsaye bai motsa ba a wajen. Har sai da Kawu Musa ya dafa shi da faɗin. Idan fa har kaga akwai matsala kada ka saka kanka a cikin damuwa. Mu duka dake nan babu wanda zai zargeka da rashin ƙyautawa har abada. Kuma mun ƙulla zumunci da kai kenan har abada. Murmushi yayi, sai kuma ya ɗan jinjina kai da roƙon a bashi wasu mintuna zaiyi waya. Kai tsaye Kawu Musa ya bashi dama. Tafiyarsa waya muka samu damar tattaunawa muma, Kawu Musa ya fahimtar damu dalilinsa na yanke hukuncin nan. Ni dai dan banda yanda zanyi ne bazan iya jayayya da su ba na amince. Hakama Hafizzullah atake yace shi dai dan ALLAH a barki. Amma sai Kawu Musa ya mana nasiha da nuna mana illar barinki ba'a ɗaura auren a ranar ba. Ya kuma ce mu cigaba da miki addu'a in sha ALLAHU sai kinci ribar wannan auren. Dawowarsa ta katse zancen mu. Ya tabbatar ma su Kawu ya amshi aure, sannan waliyyinsa na tafe in sha ALLAHU kafin lokaci yayi. Shima kuma zai je ya dawo. Badan muna da hope ɗin dawowar tasa ba muka barshi, amma abin mamaki na takaice miki sai gashi muna ƙoƙarin wucewa masallaci. Sunzo tare da babban malamin nan Sheikh Muhammad bin Khalipha Al-Hussain a matsayin waliyyinsa. Sai wannan Hayatu da suke tare yace ƙaninsa ne. Sheikh Muhammad dai ba ɓoyayyen mutum bane a garin Kano dama Nigeria baki ɗaya, dan haka duka damuwarmu da wani wasiwasi ya kau. Sheikh Muhammad ya tabbatar mana Muhammad tamkar ɗa yake a wajensa, kuma in sha ALLAHU bazamuyi kukan haɗa jini da shi ba. Idan ma muna tunanin wani abu mu cire, dan wata hikima ce ta UBANGIJI shigowarsa rayuwarmu. Bai kuma ɓoye masa komai game da abinda ya farun ba. Kawu Musa yafi kowa shiga a farin ciki. Dan haka a take aka ɗaura aurenku bayan idar da sallar juma'a, aka kuma kwaso kayanki da aka kai gidan Mansoor aka maida gidan daya bada matsayin nasa. Bayan an kaiki kuma sai aka samu akasin ciwo da kika shiga har ya taho dake Abuja, daga baya ya sanar mana kuna Lagos wajen iyayensa. Koda yaushe muna waya da shi, amma bai taɓa gaya min komai da ya shafeshi ba. Sai a yau da muka iso an kaimu masauki kawai naci karo da fuskarsa matsayin mijinki. Bayan kuma ni sai a gobe zan gansa matsayin ogana bayan munzo wajenki. Kin san kuwa ruɗanin dana shiga Samraah. Har kusan faduwa nayi sai da Hayatu ya rikeni. Bayan sun bani ruwa nasha mun zauna a ɗarare Hayatu ya min bayani komai tun daga batun ɗaukar video har zuwa kidnapping ɗinki da mahaifiyar Mansoor tasa akayi, da karɓarki da yayi a hannunta sanadin bincike da yayi saboda kuɗi da aka nema a hannunsa da sunanki har 500m. Bayan ya gano bake bace amfani kawai ake son yi da sunanki ya kuma gano anyi kidnapping ɗinki shine ya kubutar dake. Yaso amsar video ɗin a hannunki lokacin kodan gudun kada ki sake shiga wata matsalar sai kikaƙi bashi. Sai kawai ya haƙura ya sake ki akan zai cigaba da bibiyarki har sai ya amsa dan in ba haka ba yasan wataran wani zai iya sake yunkurin cutar dake a kansa in har akasan da shi. Ya tabbatar mana shi ya kubutar dake daga auren Mansoor ne saboda kawai yasan bazaki taɓa samun farin ciki ba dan mahaifiyarsa da ƙanwarta ya tabbatar da zasu iya aikata komai akanki, yanda kuma basu samu kudin nan ba kema bazaki samu yanda kike so ba. Ko ran daurin auren da yazo ya biyo mahaifiyar Mansoor ne cikin ɓadda kama dan ya tabbatar tayi abinda auren zai fasu amma sai kawai tai abinda ya sashi tilas bayyana kansa garemu alhalin shi beyi niyyar hakan ba. Sai kuma kawai