Showing 117001 words to 120000 words out of 438336 words

Chapter 40 - Tsutsar Nama Book 1 Hausa Novel Complete

13 Dec 2024

2194

ya janye tamkar wanda ba'ai komai ba ma. Ga fuskar tsamm babu alamun rahama ko sassauci balle ma kai tunanin ya taɓa sanin mai kama dani a rayuwarsa. Duk yanda naso janye nawa idanun daga kansa na gagara hakan saboda tsabagen shiga ƙololuwar baƙin ciki, ruɗani da mamakin makirci da mugun halin mutumin nan, kenan da gaske shi MAASH ɗin ake nufi da sunan gidan nan?. Tayaya ma to hakan ta kasance?, farkon labarin a kano, cigabansa a Abuja, ƙarashensa a Lagos. Duka a ƙarƙashin ikonsa, kenan da gaske yayi winning kamar yanda yake iƙirari da cika bakin shi ba'a game da shi baiyi winning ba. Kai impossible...
Mugun zagin da Azizat ta lailayo min da sake yo kaina ya maidoni a hayyacina, raina a dugunzume na janye idanuna a kansa na dawo da shi gareta, dan wlhy tana sake taɓani duk haushi da takaicin mugun nan saina juyesu a kanta yanzun nan. Tana gab da kai hannunta jikina aka kira sunanta da ɗan faɗa-faɗa. “Azizat minene haka wai?!”. Mu dukanmu kalon Aunty Mama da tayi maganar mukayi, yayinda itama ta dakata tana hararata da famar huci sai kace wata kububuwa. Cikin sake bada umarni daga inda take tsaye ta dubi Mama Balki. “Kuje inda na turaku”.
“Godiya muke ranki ya daɗe, ALLAH ya ƙara girma”. Mama Balki ta faɗa tana risinawa tare da kama hannuna. Tamkar wadda aka zarema illahirin lakar jiki na shiga binta zuciyata na wata kalar suya da raɗaɗi mai zafi. Yayinda idanuna ya kasa daina kallonsa, nama rasa wana kalar tunani kuma ya dace nayi. Muna gab da fita muka haɗa ido, wani irin lumshe nasa yay da yamutse fuska ya motsa lips ɗinsa a hankali, (First Game) sai kuma ya cije gefen lips ɗin da wani salo ya ɗauke kansa gaba ɗaya daga garemu.
Da ƙarfi na rumtse idanuna dake cikowa da ƙwalla. Cikin ɓacin rai na shiga ƙoƙarin son fisge hannuna daga na Mama Balki. Dan bazan iya haƙuri ba sai na maida masa murtani. Kai yau ma duk abinda za'ayi sai dai ayi wlhy. Sake damƙe min hannu Mama Balki tayi tare da jawoni gaba ɗaya daga cikin falon muka fito cikin main falo, sai da muka fito anan ma gaba ɗaya wajen compaund sannan. Cikin lallashi da ɗan faɗa ta furta, “Ya isa mana. Ki ƙyaleta. Banda abinki ina ke ina faɗa da ƴar masu gida. Kin san kuwa fitinar Azizat musamman akan bawan ALLAHn nan. Zuciya ba taki bace ba ɗiyata, anan a ƙarƙashinsu muke dole muyi haƙuri da koma mi zamu gani. Kima godema ALLAH Alhaji ƙarami yazo wajen da wlhy abinda zai faru ALLAH kaɗai ya sanshi. A hakan ma ALLAH ya taƙaita duk barci jama'ar gidan suke. Ita kuma Aunty Mama tana da sauƙi a cikinsu da ko gidan nan bazaki sake kwana ba. Kema dai na lura akwai ƙarfin hali, ki daure ki sauke wannan zuciyar taki kada ki sake kwatanta abinda kikayi yau”.
Zantukan Mama Balki sake ƙona min rai suke. Dan haka na sakar mata kuka kawai tare da faɗawa a jikinta na ƙanƙameta. Itama sai ta riƙeni hannu bibbiyu tana lallashi na.....

Su Samraah na gama ficewa a falon Azizat tayo kansa. “Yaya Please kace afitar mana da ita a gida. ALLAH yarinyar nan mayya ce. Tun jiya da aka shigo da ita gidan nan naji na tsaneta, jinake kamar ma na kashe banza. Dan bazan taɓa yafe mata rungumar da tayi maka b.....”
Ko kallon inda take baiyi ba, sai ma motsa lips ɗinsa da yay a hankali cikin silent voice ɗin nan tasa ya furta, “Good Morning Aunt” yay wucewarsa. Wani irin tsayawa tayi cak jikinta na tsuma. Duk da ba yau ne farau ɗin hakan ba a tsakaninsu sai take jin na yau ɗin ya mata zafi. Da kallo ta bisa idanunta nayin narai-narai alamar gab take da sakin kuka. Murmushi Aunty Mama tayi da ɗan girgiza kanta tana binsa da kallo. Har sai da ya ɓacema ganinsu ta janye idanun, ganin Azizat ta zabura zata bisa ta sakko ta kama hannunta batare da tace komai ba ta jata suka koma saman dan tasan bin nasa bazai haifar da ɗa mai ido ba. Dama ga wata wutar dake neman tasowa akan matsalarsun....

★★★

Cike da nishaɗi Abba ya koma gida. Sai dai me, yana shiga ya samu Mom na jibgar Halime har Bibaa na tayata. Yayinda Baby ke kwance a kujera wanwar alamar tasha kayan nata. Tuni yay wata irin zabura batare daya sani ba ya hankaɗesu su duka. Sannan ya ɗauke fuskar Bibaa da mari. “Kinci gidanku Habiba. Dan uwarki wannan ɗin sa'arki ce?”.
Kafin Habiba dake kuka ta bada amsa Mom data sake shiga cikin matsanancin ɓacin rai ta hayayyaƙo masa. “Mitai maka zaka daketa. Akan ƴar aiki wulaƙantacciya da iyayenta ma suka sallama ma duniya saboda baƙin talauci”.
Wani irin ɓacin rai ne ya tasoma Abba. Cikin rufewar ido ya furta, “Jalilah! Halimatussa'adiyyar ce wulaƙantacciya?”.
“Kuturun ubancan! Imamu harma sunanta ka sani? Harda ƙara masa wani ƙaimi. To ko dai kana zagayowa ne ban sani ba ta zama karuwarka. No wander yanzu kullum sai ka dawo gida da rana. Idan ka zauna kuma kata waige-waige kenan...”
“You are vary stupid Jalilah! Ni kike dangantawa da fasiƙanci?”.
“Yo in ba fasiƙin ba minene kai? Taya akai kasan wannan tsinanniyar yariyar anan gidan ma? Bayan na mata gargaɗi kaima kuma nayi maka. To wlhy kuwa zaku mutu yau ku duka...” ta ƙare maganar da rarumo flower base tai kan Halime dake maƙure gefe tana kuka. Damƙota Abba yayi da masifar ƙarfi, aiko ta juyo gaba ɗayanta ta buga masa abin a kai. Lokaci ɗaya Bibaa da Halime da Baby da hayaniyarsu ta sakata buɗe ido suka ƙwalla wata irin masifaffiyar ƙara da duk maƙwaftansu sai da suka jiyo. Yayinda fuskar Abba ta gama wankewa da jini. A take ya faɗi wanwar ƙasa. Ai sai su Bibaa suka sake ƙwala wata ƙarar da tafi ta farko. Itama Mom ta yadda guntun flawer base ɗin daya rage a hannunta tayi wani uban tsalle gefe tana ware idanu. Halime kuwa tuni ta gigice tazura waje a guje.......


💦❤️💦❤️

Komai na daina ganewa. Komai ya tsaya min cak. Ba brain kawai ba, hatta zuciyata da gangar jikina komai dake taimaka musu ya tsaya cak. har muka baro inda Alajah ta sakamu zuwa anan cikin gidan bana iya gane komai. Bin kowa kawai nake da kallo tankar wadda ke a duniyar mafarki. Koda muka koma can sashen Mama Balki bata shiga ba. Tace na shige ciki ita zata koma kan aikinta. Shiru sashen babu kowa, hatta tv a kashe take. Ban zauna a falon ba na shige ciki, saman gadon dana kwana na kai zaune, cikin gushewar tunani na dafe kaina tare da fasa wata irin ƙara illahirin jikina na rawa har ta kaini da faɗowa ƙasa....
Da gudu Bahijja data shigo sashen domin shiga toilet ta ƙaraso ɗakin, dan da farko ma ita tsorata tayi, sai da tajiyo ihun kamar daga ɗakinsu ne sannan cikin ɗari-ɗari ta nufi can. Sosai ta waro idanu, sai kuma ta zabura kan Samraah tana faɗin, “Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un!. Kandala! Kandala! Miya farune haka?...”
Ƙanƙameta Samraah tayi sosai tana cigaba da kuka mai tsuma rai da zuciya. Sai kawai itama Bahijjar ta sanya kuka. Dan yanzu su Sumayya ke bata labarin abinda ya faru tsakanin Samraah ɗin da Azizat. Sun kai kusan mintuna biyu a haka kafin su sassauta kukan nasu. Cikin lallashi Bahijja dake rungume da ita ta fara faɗin, “Kiyi haƙuri Kandala kinji. Haka take sam bata da mutunci. Bata ɗauki ɗan adam komai ba sai abin wulaƙantawarta. Sai kace itama ba cin arziƙi tazo yi gidan ba. Tunda ba gidan ubanta bane ba. Ai wlhy naji daɗin abinda Uncle Boss yay mata, azzaluma. Nima kullum sai ta mareni ga bautar gyara mata ɗaki da nake kamar jaka, hatta da pants ɗinta nike wankewa. Amma sam bata gani, komai akai mata ba'a iya ba, bayan ita ɗin ma babu abinda ta iya sai barcin tsiya da gantali. In sha ALLAHU Uncle Boss bazai aureta ba zamu gani”.
A hankali na ɗago ina kallon Bahijja, haka kawai kalamanta sukai wani irin tasiri a zuciyata. Har ban san sanda na furta kamar ya ba ƴar nan gidan bace Bahijja?”.........✍️


_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._


_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_

_BANK NAME:KEYSTONE_

_BANK ACC NO:6019473875_

_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_

_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_

__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_

_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_

*09033181070*

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*


_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_




*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*

*_Typing📲_*








*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*
_(Itama nama ce)_




_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_



_𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒘𝒐_
_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒇𝒊𝒇𝒕𝒆𝒆𝒏_


💫🔥💫🔥💫🔥💫🔥💫🔥💫🔥💫🔥

*_ALBISHINKU MATAN AFRICA DA KEWAYE, SHAHARARRA KUMA K'ASAITACIYAR MAI SAIDA KAYAN MATAN NAN WATO DR MAMAN YUSUF LIKITAR MATA SOKOTO TANA FARINCIKIN SANAR DAKU CEWA ZAKU IYA SAMUN KAYANTA ADUK INDA KUKE A FADIN NIGERIA DA NIGER HARMA DA WASU K'ASASHEN BAKI DAYA, KU SANI A DADE ANAYI SAI GASKIYA KUMA MACE MAI GYARA KANTA BATA BORANCI , INA MARABA DA MASU SIYAN DAYA KO SARI_* .http://wa.me/+2347069711327

*_munada zafafan kaya kamar haka ,_*👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻

*Hadin amarya budurwa ko zawara*

*Hadin uwar gida Mai taken (Maida tsohuwa yarinya)*

*Maijego package (virgin gain)* 📦

*Hadin sabon budurci ga yarinyar data rasa budurcinta ta hanyar fyade ko yaudarar da namiji*

*Sahihin maganin sanyi na Maza Dana Mata Wanda yake fatattakar sanyi cikin Dan lokaci*

*Maganin gyaran nono Wanda zai gyara maki nononki cikin Dan lokaci komai lalacewarsa*

*Maganin hips Wanda zaisa shape dinki ya fita kiyi kyau kema ki shiga jerin Mata masu aji*

*Maganin kiba Wanda zaisa ki ciko kiyi kiba yar dai dai misali kema adinga binki da kallo Idan kin juya Sam rama batayi ba yar uwa*

*Hadin mallaka ba boka ba malam , akwai taimakon da muke bayarwa ga Mai butsarin namiji Wanda cikin ruwan sanyi Zaki dinga juya abunki , haka akwai Hadi na musamman Wanda komai rowar namiji sai kin samu alkhairin a wajanshi,*

*Muna da kalolin gumbuna masu Saka ni'ima sha'awa da dandano*
*Kalolin garrika mash gyara gaban mace da jimawa ajiki*
*Kalolin Zuma masu saukar da ni'ima Nan take da gamsar da maigida*
*Kalolin tsumi Wanda cikin sauki zasu Baki ni'ima da dandano irin wadda akeso*
*Kalolin matsi Wanda suke ciko da gaban mace matse gaban mace da bata Wani irin dadi da dadano*
*Akwai set kala kala Wanda yawansh ya wuce na zayyanasu anan ga Mai bukatar kayana zata iya mun magana Kai tsaye ta hanyar danna wannan blue rubutun* 👉🏻 http://wa.me/+2347069711327

*Muna dahuwar zabo ,dahuwar kaza ,dahuwar kifi ,dahuwar zuciya ,dahuwar Yan shila ,dahuwar tsoka Tara ,dahuwar Kwan mallaka, dambun nama ko na kaza Wanda yake saukar da ni'ima da jimawa sosai ajikin mace*

*Idan nace zan rubuta komai da komai to wannan page din ba zai isheni ba ,Amma ga masu sha'awar siyan kayana Zaku iya mun magana Kai tsaye ta wannan number, haka masu sha'awa su dinga ganin kalolin kayana a status sumin magana ta wannan number sai nayi seving numbers dinki ta hakan ne Zaku dinga ganin kalolin kayana idan na daura*
http://wa.me/+2347069711327

*Ina maraba da Mai siyan Daya ko sari Dr maman Yusuf likitar mata sokoto*

=============


.......Zama Bahijja ta gyara fuskarta cike da gulma. Sai kuma ta miƙe ta leƙa waje sannan ta dawo ta rufe ƙofar. Hannuna ta kama muka koma saman gadon A'i dake can ciki. Cikin sake sauke murya can ƙasa tace, “Eh mana ba ƴar gidan nan bace ba. Uncle Boss shi da ƙaninsa kawai aka haifa a gidan nan. Ita ɗin da ƙanwarta Hindu mahaifiyarsu yayar Baban su Uncle Boss ce. Ni na rasa gane musu, ko bata da mijine yanzu oho mata, dan nidai tunda nazo anan gidan nake ganinta zaune ita da ƴaƴan nata. Sai Ashna, ita kuma agola ce. Matar Baban Uncle Boss ta yanzu itace mahaifiyarta. Bata nan sunyi tafiya ne ita da Baban Uncle boss ɗin amma nasan yau zasu dawo. Itama wadda tazo dake Aunty Mama ƙanwar Baban Uncle Boss ce ba'a Nigeria take aure ba. Ƙanin baban dai da shima yake da nasa iyalan anan gidan basa nan sunje Niger biki suma yau zasu dawo yaransu uku. Suma duk basu da kirki musamman babbar su da suke takara da Azizat akan Uncle Boss dan itama sonshi take kamar zata mutu. Shiko ko kallo basu ishesa ba....”
“A'a, to shi ina mahaifiyar Boss ɗin ko ta rasu ne?”. Na faɗa cikin tare numfashinta. A take naga jikinta gaba ɗaya yayi sanyi, sai kuma idanunta suka ciko da ƙwalla. Cikin raunin murya irin ta tausayi ta ce, “Tana nan raye bata rasu ba. Amma bata da lafiya....”
Sagade nayi kawai ina kallonta. Sai kuma cikin ƙarfin hali na furta, “Tana asibiti kenan tana jiyya?”.
Nan ma idanunta ne suka sake cika da kwalla. Sai kuma ta girgiza kanta. “Tana a cikin gidan nan kulle a sashenta. Babu mai shiga inda take sai masu kula da ita, suma basa haɗa wata a gidan nan suke guduwa duk da ɗunbin kuɗin da ake biyansu na albashi, mun rasa miyasa basa zaman. Idan kinga masu gidan sun shiga su kuma to sai dai an ɗaureta ne ko an mata allurar barci mai ƙarfi”.
“Ɗaurewa kuma? Sai kace wata dabba?”.
Shiru tayi dan hawaye ne sosai ke ɓulɓulowa daga idanunta. Har tana jan ajiyar zuciya kamar zata shiɗe. Sosai hankalina ya sake tashi, sai dai ban iya cemata komai ba na dai riƙe mata hannu alamar lallashi. Kusan mintuna biyu ta haɗiye kukan da ƙyar. Sannan ta cigaba da faɗin, “Humm bazaki ganeba Aunty Kandala. Amma ni dai zuciyata na ayyana min abubuwa da yawa a gidan nan wlhy, sai dai bamu da wani ƙarfin iko ne shiyyasa kawai na zama cikin masu kallo. Mahaifiyar Uncle Boss tana da ciwon hauka ne, shiyyasa suka killaceta ba'a bari kowa ya shiga inda take sai masu kula da ita. Sai kuma likiticin dake dubata duk bayan sati biyu. Duk randa kikaga masu gidan sun shiga inda take to an ɗauretane, dan sunce duka take yi.....”
“Har su ƴaƴan nata?”.
Yanda nai maganar a ɗan tsawace yasa ta zabura. “I'm sorrry”. Nace mata dan na fahimci na fara rasa nutsuwata. Ajiyar zuciya ta sauke mai ƙarfi, alamar samun nutsuwa. “Ai Uncle Boss ne kawai. Shi ɗayan baya ƙasar, nima tunda nazo ban gansa ba sai a hoto kawai.....”
“Shi ɗin baya shiga kenan?!”.
“Yana shiga, sai dai ba koda yaushe ba. Saboda shigar tasa bata haifar da ɗa mai ido ne. Yau ma bakiga abu a gefen girarsa ba. Shekaran jiya ne daya shiga dubata bayan ya dawo ta jimasa wannan ciwon. Da ƙyar aka fiddosa a ɗakin ma”. Ta kare maganar tana hawaye. Cikin kukan ta cigaba da faɗin, “Wlhy yana bani tausayi aunty Kandala. Dan abubuwa da yawa idan yanayi zai tabbatar maka da yanda yake matuƙar son mahaifiyarsa. Itama kuma zakiji tana kuka duk dare tana kiran sunansa. Amma al'amarin nasu kamar wani abun sihiri basu isa haɗuwa a waje ɗaya ba kamar maƙiya. Wlhy da ace inada abinda zan taimaka masa koda da duk abinda na tara ne zanyi aunty Kandala. Ki duba fa kiga yanda ya inganta rayuwarmu a gidan nan tamkar ba ƴan aiki ba. Muhalli mai ƙyau, ilimin addini dana zamani kullum akwai malaman dake zuwa karantar damu. Ga albashi mai tsokar gaske. Rayuwarmu a killace ta yanda wani bazai taɓa ganinmu a ƙasƙance ya wulaƙantamu ba. Cimmu, shan mu, sutura, magani idan muna ciwo bai taɓa gazawa ba. Dan ALLAH dami zamu sakankama wannan bawan ALLAH?. Har sonake naga wace mai sa'a ce zata dace da samunsa matsayin mijin aure? ALLAH zan tayata murna harda azumin godiya ga UBANGIJI. Nasan bazaki gane duk abinda nake nufi ba. Amma nan da wata ɗaya kacal duk zaki maimaita abinda na faɗa, dan ma ba zama yake ba sosai saboda harkokin kasuwancinsa dana mahaifiyar tasa ance duk sun koma hannunsa, dan itace mai kuɗin fa. Ko wannan katafaren gidan ance ita ta fara gina shi sannan Uncle Boss ɗin yana ƙarami, sai da ya girma shi kuma ya ƙarasa saboda ita ciwo bai barta ba”. Tana kaiwa nan ta miƙe zaram idanunta akan agogon ɗakin. “Tabɗi na shiga tara, Aunty Kandala bari na koma wlhy minti biyar ta bani, nasan zansha mari”.
Kafin nace wani abu ta fice a guje. Shiru kawai nayi ina kallon ƙofa tamkar zan zuƙota da idanu. Akaf labarin data bani wanda ya shafi mahaifiyarsa ne kawai ya tsaya min a rai. To dama tana a haukan ta haifesu? Kokuwa daga baya ne haukan ya sameta? Bani da mai bani amsa dan haka na zabga tagumi kawai. A karo na farko naji ina kwaɗayin jin labarinsa. Ko shiyyasa baya son a tambayesa tarihinsa? Randa nai hira da shi ya shiga dawo min a rai. Tabbas a ranar bai amsa koda kalma ɗaya data shafi privet life ɗinsa ba. Na sake tuna ranar taron buɗe kamfaninsa. gargaɗinsa akan ƴan jarida baya buƙatar kowace

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login