Showing 246001 words to 249000 words out of 438336 words
yau komai yana yinsa gently ne ni banga wannan gentle ɗin ba sam. Kuka na gidan duniya na shashi har ina jin idanuna kansu sun min wani uban nauyi. Roƙo magiya harda cizonsa nayi amma bawan ALLAHn nan sai da ya kai inda yake buƙata. A Bathroom ma wani sabon kukan na sha, amma sam baiji tausayina ba sai da ya tabbatar ruwan zafin ya ratsani sosai yanda ya kamata sannan ya taimaka min na tsaftace jikina. Yanda ya ɗaukeni da kansa ya kai haka ya sake ɗakkoni ya maido saman gadon. Da ƙyar na amshi magani daya bani, ina gama sha ya kwantar dani, bamma san barcin wahala yay awan gaba dani ba. Dan tun ina jinsa sama-sama yana salla har nayi barcin ban san ya dawo saman gadon ya kwanta ba sai asuba....
★★
Yanda Maash bai bari sunyi wani barcin kirki ba a wannan daren haka mafi yawan iyayensa basu runtsa ba. Hajiya Mammah dai na sake ƙulla abinda zata zo da shi gobe idan ALLAH ya kaimu. Paah na cikin tashin hankali da damuwa tare da nadamar abinda yake aikatawa. Dan shi kawai zuciyarsa na bashi TSUTSAR NAMA CE TA ZAMA NAMA. Ɓarnar da yake aikatawa ce tai naso wa gudan jininsa. Shiyyasa masu iya magana ke cewa ƊAN GADO HAR YA ZARTA. A wannan gaɓar kam ya yarda. Dama ance zina na bibiyar jini, idan kayi da ƴar wani sai anyi da taka. To shi bashi da ɗiya mace, shine ALLAH ya jarabci ɗansa babba da wannan ta'asar da ƙila zata zama sanadin tashi fallasar shima. Harga ALLAH bai taɓa fyaɗe ma kowa ba, amma fa tun yana secondary school ya fara neman mata. Saboda irin rayuwar da suka tashi, rayuwar turai. Uwa babu kwaɓa uba ba tsanani. Dan Ummansu nada faɗa, amma gasu ƴaƴanta soyayyace ziryan take musu. Garama mahaifinsu, yakan ɗan yi faɗan idan yaga abubuwan sunyi yawa. Shi kansa bai san adadin matan dayay mu'amala da su ba a rayuwarsa. Tun ma yanayin mai aji har gashi ya koma mu'amala da mai aiki. Dan da Siyama kawai yake mu'amala a gidan, hasalima ya santa ne tun kan ta fara aikin, koma yace saboda shi ta dawo aiki gidan, dan tace suyi aure yace a'a, shine ta zagaya ta samu aiki a gidan sai kawai ganinta yayi. Ya shiga matuƙar shock a lokacin, amma da yake ƴar duniya ce sai da ta maida shi ruwa a kanta duk da kuwa shi in har ya mu'amulanci mace ya rabu da ita da wahala ya koma. Amma akan Siyama sai tarihin ya canja, dan ta rantse masa in har yay sanadin data bar gidan sai ta tona masa asiri, shiyyasa ma ya barta saboda ya fahimci yarinyar hatsabibiya ce kwarai da gaske. Amma yau sai gashi ɗansa nayin yanda yaso a cikin gida batare da kunya ko shakkar wani ba.
Ita ko Hajiya ƙarama tashin hankalinta kada ace Maash ya sake haikema ƴar gaban goshinta Samraah ne. Har bayi ta shiga ta gwada kiran Mama Balki sai kuma ta fasa, saboda tunawa da Mama Balki nada miji fa. Ita dai damuwarta kawai kada Maash ya sake taɓa mata yarinya.
Acan Uncle Abdullahi da matarsa sun shiga wasi-wasi. Dan su zukatansu sun fara nusar da su anya kuwa ba magauta bane suka asirce Maash ɗin ke wannan irin ta'asar babu kunya babu tsoron ALLAH a cikin gida kamar wata rayuwar kafurci. Kai da sakal fa. Yaron nan na buƙatar manyan malaman ruƙuya a kansa. Ita dai Maman Malika ma harta fara batun maida Malika Niger sai abubuwa sun dai-daita. Idan har abinda Hajiya Mammah ta faɗa Awwab ɗin ya faɗa to lallai basuga ta zama ba kuwa. Dole abar gidan da ƴammatan yaran nan guda huɗu zankaɗa-zankaɗa. (😂Yayanmu kaga idi. Kowa zai fara killace ɗansa saboda kai🌚, wannan aiki yayi tsamari🤣).
A ɓangaren Baba prof shima ba barcin daɗin ran yayi ba. Dan ya jima ma bai runtsa ba bayan ajiye wayar da yayi. Har gwada kiran wayar Maash yay amma ba'a ɗauka ba (😂ina zai ɗauka kuwa kandala ta kanainayesa, danginta na murna an kwace mana Yayanmu🥶). Haka ya dinga kai-kawo kamar mai Safa da marwa, sai da yaji ƙafafunsa na neman sagewa ya haƙura ya kwanta. Aiko asubar fari ya miƙe dan ko'a barcin nasa mafarkin Maash ɗin kawai yake yi ya haikema yarinyar mutane (kuji masifa🥱. Yo banda sa kai a uku kai tsoho ina ruwanka😝).
🩸🌟🩸🌟🩸
Saukar iska mai sanyi akan idanuna ya sani buɗesu a hankali dan sun min nauyi jingim saboda kukan dana sha. Ga barci da nake ji matuƙa dan sam ɗan wanda nayi bai wadaceni ba. Dishi-dishi nake ganin abinda ke gab da ni, cigaba da huramin iskar ya sani ƙarasa buɗe idanun sosai. Fes suka shige cikin nasa da sukai wani irin fitowa blue sosai, hakama golden ɗin daya ratsasu ya sake yin garai-garai tamkar zinare na ƙyalli a cikin glass. A hankali na ƙoƙarin sake maida nawa zan kulle saboda wani irin kunya ne ya baibayeni.
Cike da karsashi ya ɗaura soft hannunsa saman fuskata yana sake matso da tasa fuskar gab da tawa, har hancinmu na gogar juna. Da silent muryar nan tashi mai fita acan ƙasan maƙoshi kamar abin dole ya furta, “No! Baby. Open your eyes”.
Baki na taɓe kamar zanyi kuka. Cikin shagwaɓa da ban san ni kaina nayi ba na ce, “I'm not baby”.
Sake manne fuskarsa da tawa yayi, tare da sake maida muryarsa can ƙasa ya ce, “Yes you are not ni shaida ne”. Yanda yay maganar yana kai hannunsa saman jikina da sauri na saka nawa na ɗan buge nasan ina sake ɓata fuska zan saki kukan. Na kuma janye fuskata da ga jikin tasa na juya baya. Zafin da naji ya sani sakin ƴar ƙaramar ƙara. A hankali ya kwanto ta bayana duk da ma ya rufeni gaba ɗaya ƴar tsitt dani a jikin nasa. A cikin kunnena ya furta, “Still Pain?”.
Maimakon amsa kuka na sakar masa. Sautin murmushinsa naji a cikin kunnena, sai kuma ya saka hannunsa a saman fuskar tawa ya shafo hawayen. Hannuna nasa na ture nashin in ƙara ƙarfin kukan. Baice komai ba ya miƙe, har nayi tunanin ya barni ne sai naga ya zagayo ta gabana. Duvet ɗin da nake ciki ya yaye, tare da duƙowa ya ɗagani gaba ɗaya. Luff na kwanta a jikinsa tare da lumshe idanuna. Sai da muka shiga bayin na buɗe ganin yana ƙoƙarin cewa zai min wankan ma. Da sauri cikin shagwaɓa na ce, “Ni ka fita zan iya”.
“Kin tabbatar?”.
Ya faɗa cikin tsatstsareni da idanu. Kaina kawai na jinjina masa. Shima sai baice komai ba ya juya ya fita, yana gab da ƙarasa ficewar ya ce, “Ki tabbatar kin shiga ruwan nan”. Daga haka ya ficewarsa. Ajiyar zuciya na sauke mai ƙarfi, ni ba haushinsa nake ji ba. Tausayin kaina kawai nake ji, in dai haka zata cigaba da faruwa wlhy na kaɗe har ganye na. Dan al'amarin sam bashi da sauƙi. Ban cuci kaina ba na nutsu na gyara jikina yanda ya kamata, kamar kuma yanda Mama Balki ta koya min hakama Doctor. Sai kuma naji na ƙara jin nutsuwa. Wanka nayi na ɗauro alwala. Cikin sanɗa da jan ƙafa na fito. Naji daɗin ganin babu kowa a ɗakin, sai doguwar riga mara nauyi da hijjab dana samu a saman sofa. Ɗauka nayi cikin sauke ajiyar zuciya na saka dan har shida da wasu mintuna. Sallar asuba nayi, koda na idar duk yanda naso yin karatun Alqur'ani kasawa nai, anan inda nai sallar na ɓingire barci. Bamma san ya shigo ya ɗagani ya maida a saman gadon ba..........✍️
*_Typing📲_*
*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*
_(Itama nama ce)_
_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_
_𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_
𝑷𝒂𝒈𝒆twenty- seven
.......Kamar yanda Baba prof yay alƙawari ƙarfe shida da kusan rabi a Maash Mansion ta masa. Sosai ma'aikatan gidan sukayi mamakin ganinsa da wannan uban safiya. A ƙasan rai kuma kowa na tunanin ko jikin Hajiya Babba ne ya sake motsawa. Dan in har ba ciwon Hajiya Babba ba baka ganin Baba prof ɗin a gidan sai dai wani babban dalili. Fitowarsa a mota dai-dai da fitowar Maash daga sashensa sanye cikin farare ɗin tas sports wear. Gefensa Laalah ne sai baƙin bluetooth daya manna a kunnesa ƙafarsa da sport shoes na kamfanin adidas. Kallon kallo aka tsaya tsakanin shi da Baba. Kafin shi Maash ɗin ya fara rissinar da nasa idon a yanayin nan nasa mai ban haushi. Inda Baban yake ya ƙarasa, ƙasa-ƙasa ya ce, “Good morning grandpa”.
Danne komai Baba prof yayi, cike da kulawa ya amsa masa da, “Morning dear, how was your night?”.
A takaice ya ce masa, “So good”.
“Hummm Masha ALLAH haka ake so ai. Amma inaga zaka bar fita Jogging ɗin nan kamar?”.
Cikin wani irin tsare kakan nasa da ido ya furta, “But why?”.
Haɗe fuska Baba prof yay dan karma ya masa gardama. Kai tsaye ya amsa masa da, “Nazo ne muyi magana mai muhimmanci”.
Shima fuska Maash ɗin ya ƙara tsukewa, tare da kallon agogon dake ɗaure a tsintsiyar hannunsa baƙi mai ƙyau. Kansa ya ɗan girgiza fuskar na sake komawa tamau. “No grandpa am sorry. Ka shiga ciki, jus 30minutes am come back”. Baima jira mi Baba prof ɗin zai ce ba ya raɓashi ya wuce. Matuƙar sosuwa ran Baba prof yayi, dan ko iya cewa komai baiyi ba ya bisa da kallo kawai shi da karen nasa. Sai guards ɗinsa da suka take masa baya. Gefen lips ɗinsa ya ɗan cija kawai yana nufar hanyar babban sashen. Duk ta inda ya gitta masu aiki zubewa suke suna gaishesa. Ɗaya bayan ɗaya masu gidan suka fara fitowa suna gaishesa suma tunda duk sun san da zuwansa. Su dai yaran basu san mike faruwa ba dan ko barci ba tashi sukai ba balle ai batun yin sallar asuba. Hajiya Mammah tayi zaram zata wuce kiran Maash Baba ya dakatar da ita. Sanar musu Maash ɗin ya fita yayi, amma yanzu zai dawo. Sai a lokacin Paah ya ɗan sauke ajiyar zuciya. Tashi yay ya haura sama ya duba Ummie. Barcinta ma take hankali kwance. Sai mama Balki dake ɗan siɗaɗowa da tayi sallar asuba ta gyara sashen ta mata wanka ta bata abinci. Cikin girmamawa ta gaida Baban. Shiko yanata faman saka mata albarka da wannan ƙoƙarin nata. Murmushi dai ta dinga yi ita dai kawai.
Bayan ya dawo ƙasan suka ɗan fara tattaunawa akan al'amarin Maash ɗin. Hajiya Mammah nata sakko batun Azizat, acewarta hakan shine kawai maganin wannan matsala data kunno musu kai. Uncle Abdullahi ya bata goyon baya, shi dai Paah da farko shiru yayi, sai da Hajiya Mammah ta balbalesa da masifa ne ya ce shifa bawai baya so bane. Kawai yana tunanin ta yanda za'a sake tadawa Awwab ɗin maganar ne baya kuma anyita a watannin baya sai dai rai ya ɓaci kawai a banza. Kowa ya fahimci uzirin Paah ɗin, dan taurin kan Maash a bayyane yake ga kowa na gidan. Dan in fa har bashi yace zai yi abuba babu ubanda ya isa ya sanya shi ya yisa. Hajiya Mammah dai ta nuna musu wannan karon za'a masa zagir-zagir ne, dolene su nuna masa su suka haifesa ba shine ya haifesu ba. Domin kafa hujja aka aika Maman Malika wai taje sashen Maash ɗin ta duba wace yarinya ce ya kai. Taso noƙewa, amma girman suruki ya hanata dole ta miƙe ta tafi, babu jimawa ta dawo ta sanar musu yafa kulle ƙafarsa.
“Tunda yasan miya ajiye ba dole ya kulle ƙofa ba. Ai mudai Ummu-Hidaya ta haifa mana bala'i cikin zuri'a”.
Duk da furucin Hajiya Mammah ɗin baima kowa daɗi a wajen ba babu wanda ya tanka mata. Kusan a dai-dai lokacin ne kuma Maash ɗin yake dawowa gidan. Yayi zufa sosai sai furzar da huci yake. Dan yayi amfani da ƙarancin lokacin ne yay gudu sosai. Kai tsaye ƙofar babban sashen ya nufa, bayan ya amshi bottle water ɗin sa da towel a hannun Shu'aibu, Laalah biye da shi ya shiga da sallama ciki-ciki. Tuni su Afrah dake gyaran sashen sun fara zubewa suna gaishesa da girmamawa. Sau ɗaya ya amsa musu kawai yana ƙarasawa ƙaramin falon da iyayen nasa suke, wanda in ba irin meeting ɗin nan ba da wahala ma kaga wani a cikinsa. Kasancewar an rabashi da glass ne da babban yasa ko damuwa da kai-kawon masu aikin basu yi ba. Dan ba'a jiyo magana, na waje kuma baya ganin na ciki, na ciki ne ke hango ma waje.
Kowa bai kalla a cikinsu ba ya kai zaune a kujerar farkon shiga falon da babu kowa a kai. Ruwansa ya ɗaga sama yana tsiyayawa a baki kamar daya shigo bai ga kowa ba. Sai da ya sha sosai ya ajiye a gabansa, karensa nata gefen ƙafafunsa ya kwanta shima yana huttan gudun da suka sha yau ɗin. Sai lokacin ya ɗan kalla iyayen nasa da duk suka zuba masa ido. A taƙaice ya janye yana cigaba da goge wuyansa zuwa ƙeyarsa ya furta, “Good Morning”
Paah ɗin ne kawai ya iya ƙarfin halin amsa masa da Uncle Abdullahi da Maman Malika. Amma Hajiya ƙarama da Hajiya Mammah wani shegen kallo suke binsa da shi. Na Hajiya ƙarama ba'a bayyane ba, amma ita Hajiya Mammah kamar idanunta zasu faɗo kansa. A masife ta ce, “Eh ai ba sai ka nuna mana kai tarbiyanka bai cikaba Awwab. Mune kakema gaisuwa like wasu sa'anninka ko. Kaje ai duniya ce zaka gani, wanda baima zo ba jiransa take”.
Ko kallon inda take baiyi ba ma. Sai zamansa ya gyara cike da ƙasaita yay crossing ƙafafunsa ya jingina kansa da kujera ya wani lumshe idanu. Takaici, baƙin ciki, haushi. Babu wanda bai kumesu ba. Sai dai babu wanda ya tanka sai Baba prof ne ya ce, “Awwab!”.
Batare da ya ɗago ba ko gyara zamansa ya ce, “Na'am”.
Sake danne zuciya Baba prof yayi ya cigaba da faɗin, magana ce mai muhimmanci ta taramu anan, kuma amsa muke buƙata daga bakinka, ba wannan shirun naka ba. Wancan karon kata mana zame-zame, na barka ne kawai dan na tabbatar da abinda akace kayin, ashe kuwa bazaka fasa ba tunda gashi ka maimaita. Kana ganin wannan rayuwar ta dace da kai kuwa Awwab, kaifa muka dinga fama da kai yin aure watannin baya amma ka nuna baka buƙata, why kuma yanzu ka zaɓi wannan rayuwar? Bayan tako ina ALLAH bai tauyeka ga yin auren ba? Na farko ya faru, anyi na biyu, to baza'a sake na uku ba, dan haka mun yanke shawarar daga nan zuwa next month za'a ɗaura maka aure da ƴar uwarka tunda a wata kusan tara ka kasa samo matar sai ka fara shiri”.
Wani shegen murmushi Maash ya saki a bazata. Dukansu sai da murmushin ya basu mamaki, hakan yasa duk suka zuba masa ido cikin ɓacin rai. Kasa haƙuri baba prof yayi yanzu kam cikin ɓacin rai ya furta, “Oh dariya ma na baka ko?”.
Murmushin ya sake saki yana mai buɗe manyan idanunsa a kansu. Yanda sukai wani tar-tar blue ɗin ya fito sosai zai tabbatar maka da baya tare da kowace irin damuwa. Cikin halin ko'in kula ya ɗan lumshe idanun ya buɗe, tare da motsa lips ɗinsa a nutsensa ya furta, “Shike nan zan iya tafiya?”.
Yanzun kam hatta Paah sai da ya zuba masa ido. Yayinda cikin masifa Hajiya Mammah ta shiga tafa hannaye da jera salati. Ta ce, “Ni Nafisa ALLAH kana gani, Awwab wai anya kuwa kai kam ba shaiɗani bane? Gaba ɗaya neman maida mu watsatstsu kakeyi ma dai na kula. Yanzu nan a duk zantukan nan da baba yay maka saboda sheɗanci da raini baka da abin cewa. Magana ta ALLAH Mu'azz ka haifa mana jaraba a family”.
Ko motsi baiyi ba balle yama nuna yasan mi take cewa, sai da yaja fin mintuna biyu sannan ya wani irin buɗe idanunsa, kai tsaye a kanta ya sauke su, cikin wani irin salon kallon raini, gaba ɗaya sai ta daburce ta fara kame-kame da zaginsa. Ɗauke kansa yay daga gareta ya maida kan Baba prof, cikin motsa lips a daƙile ya furta, “Daga farkon fara wasan har zuwa yau ai duk itace Director, ni ina amsa sunan actor ne kawai. Dukan amsoshin da kuke son ji a gareni ita ke da su.”
Wani irin kuka Hajiya Mammah ta fashe da shi tana zagin Maash da yaɓo maganar da duk tazo bakinta. Ko kallo bata sake isarshi ba ya miƙe abinsa yana mai ɗaukar bottle water ɗin sa. Da sauri Laalah ya miƙe shima. Cike da takun nan nasa na ƙasaita ya nufi ƙofa sai da ya kama ƙofa zai buɗe sai kuma ya ɗan dakata, kamar wanda yay mantuwa ya juyo, “Oh nace ba. Zan baki first and last warning. Idan kikace zaki cigaba da bin sawuna, wlhy wataran sai taɓo mai danƙo ya riƙe miki ƙafa ta yanda har sai naje na dawo daga inda zanje na sake dilmiyaki a ciki, kona datse ƙafafun kowa ya huta.” ya kare maganar cikin karkaɗa yatsarsa, daga haka yay ficewarsa kamar baiga kallon da suke binsa da shi ba.........✍️
*_Typing📲_*
*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*
_(Itama nama ce)_
_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_
_𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_
_𝑷𝒂𝒈𝒆 twenty-eight
.......Tsuru-tsuru kawai sukayi suna bin ƙofar da kallo, sai Hajiya Mammah ce ke zazzaga masifa cikin borin kunya. Dan sosai maganarsa ta ƙarshe ta wani irin shigarta. Ganin kallon da Baba prof ke mata yasa ta miƙe. Murya a ɗan zafafe ya ce, “Koma ki zauna Nafisa”.