Showing 216001 words to 219000 words out of 438336 words

Chapter 73 - Tsutsar Nama Book 1 Hausa Novel Complete

13 Dec 2024

2171

ta shirya kuwa za'a dinga koro mata su. Wannan magana tasa ta ƙona mata rai a ranar sai da suka tafka rigima sosai data kaisa da bata wan shika. Aiko dai tace babu inda zata. Kota kanta baibi ba yay ficewarsa.
Sam Halime bama tasan abinda ke faruwa ba ita. Dan kwanakin nan gaba ɗaya bata ganema kanta. Kullum bata da aiki sai barci, itama dai aikin gidan a ranar girkin nata ƙarfin hali kawai take yi wajen yinsa. Sai yamma taji zazzaɓi yace salamu alaikum. Bazata taɓa samun nutsuwa ba sai irin sha ɗayan nan na dare. A yau ɗin ma da aka tafka rigimar har ya bama Mom sakin tana barci bata san bikin da akeyi ba. Amma mi, Bibaa da Baby na ganin Abban ya fita suka afka ɗakin Halimen wai zasu daketa. Sun san itace ke ƙullama Mom ɗinsu munafunci. Miye-miye dai magana tsaff a bakunansu. Cikin barci kawai Halime taji an sauke mata uban dundu. A firgice ta farka tare da sakin ihu. Sai kuma ta tsaya cak ganin Bibaa da Baby tsaye kanta suna huci. Kallon mamaki ta bisu da shi, sai kuma ta tashi da ƙyau cikin dakewa ta tambayesu ko lafiya?.
“Uwarki zamu ci, shegiya annoba. Wlhy yau sai mun miki jina-jina a gidan nan dan ubanki”.
“Tofa babbar magana, wai kishiya taga abin cikin zanen kishiyarta”. Halime ta faɗa tana yayimar ɗan kwalinta ta aza bisa kai tare da sakkowa a gado. Waya ta ɗauka tana cigaba da faɗin, “Ai ku jira bani kaɗai ya kamata ku cima uwar ba, dole na kira Imamu kamar abin zaifi armashi. Kunga sai ku tuɓe ƙaton banza ku haɗamu ku lakaɗa mana dukan tsiya tunda shine ya kawoni gidan”.
Sororo Baby da Bibaa sukai suna kallonta. Kafin cikin ƙarfi hali da tsiwa Bibaa ta ce, “Badan Abbanmu ne ƙaton banza ba dan ubanki. Sai dai idan kece ƙatuwar banza. Kuma wlhy yau sai kin ban mana gidanmu”.
Dariya sosai Halime ta sheƙe da shi, kafin ta riƙe haɓa da faɗin, “Oh ni Halimatu. Gidanku dai gidanku dai. To ke banda abinki Habi wace sakarar mace ke alfahari da gidan tsohonta? Ai macen data kai mace gidan mijinta take ma fata da alfahari, dan acan ne idan ta tadda komai rigijif-jif-jif sai kiga ta gyara gidansu albarkar iyaye ta bata tsaro tako ina. Dan haka riƙe cika bakin nan naki wannan gidan Halime ne da Jalilah, Habi dai har yanzu bata da gida sai na raɓe-raɓe. Garama ita wannan galwalin ta kusa shiga daga ciki”. Tai maganar tana nuna Baby..
Cikin fusata Baby tace, “Waye Galwali? Aiko yau sai na tabbatar miki na fiki hauka da tashanci”. Fuuu tayo kan Halime.......✍️



_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._


_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_

_BANK NAME:KEYSTONE_

_BANK ACC NO:6019473875_

_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_

_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_

__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_

_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_

*09033181070*

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*


_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_




*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*

*_Typing📲_*








*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*
_(Itama nama ce)_




_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_



_𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_
_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒆𝒍𝒆𝒗𝒆𝒏_


......Kafinma ta kai hannu kanta ita ta ɗauke fuskar Baby da maruka. Ta shaƙo wuyan Bibaa dake bayanta itama ta bata nata. Basu gama dawowa a hayyacinsu ba ta shiga musu dukan kan mai uwa da wabi. Yo har a gayawa Halime iya danbe. Ita da ake kira giwar dambe a wajen ɗibar ruwa a garinsu. Kai hatta a islamiyya duk wanda ya sake ta haɗosu da Halime aka haɗu a lungun kaci uwaka bayan an tashi to ranar kuwa sai yaci uwar tasa. Cikin ƙanƙanin lokaci ta musu lis da duka. Sai gasu a ƙasa suna faman ribzar kuka. Itako ta ɗauki sabuwar wayarta da Abba ya siya mata kwanan nan tayi kiransa tana kuka wai yazo gasu Baby da taɓare zasu bigeta.
Bawan ALLAH sai gashi a haukace harda Alhaji Sadisu. Suka ko sameta kwance tana ɗan nishi ita adole ga wadda taci duka. Gashi ta kawo jan baki ta ɗan sassaka a wasu wurare na fuskarta da hannu wai duk sayin duka ne. Abinka da fara saika ɗauka haka ɗinne. Ido rufe Abba ya dinga sauke musu maruka abinda bai taɓa koda kwatanta yi ba. Sai dai ma idan Mom ta zugashi akan Samraah yana mata faɗa ita yana marinta suna dariya. Haukace masa Mom tayi da kuka da ihu, amma ada idan ta zuga aka mari Samraah daɗi take ji, ya kuma tabbatar mata idan har ta matso shi sai ya ƙara tsinke igiyar aurensu data rage. Dole taja birki tana kuka sai Alhaji Sadisu ne ya amshesu da ƙyar. Amma sai da yay musu lilis da duka ga wanda Halime tayi musu. Ya kuma tabbatar da ya matso da auren Baby nanda ranar juma'a ko daga shi sai mutanen anguwa ne za'a ɗaura ta tafi haka dan ta ishesa. Itama kuma Bibaan idan bata kama kanta ba zai aurar da ita ga duk wanda ya masa babu abinda ya shallesa da wani karatunta. Haka suka dinga kuka. Shiko ya kama Halimensa sukai ɗaki yana lallashi. Sai dai ita kuma duk jikinta yayi sanyi, dan harga ALLAH batayi zaton zai dakesu haka ba. Ita kawai tayi ne a tunaninta faɗa kawai zai musu a wuce wajen. Koda suka shiga ɗaki sai ta kasa haƙuri ta fito ta sanar masa gaskiyar abinda ya faru harda dukan datai musu. Tama nuna masa video data ɗauka dan sanda tace zata kirashi da farko bashi ɗin ta kiraba ashe video tajeyi.
Wannan halin nata shine abu na farko da yake sakashi jin ƙaunarta fiye da koda yaushe. Dan a ɗan zamansu sam ya fahimci Halime bata iya ƙarya ba. Sannan bata taɓa kawo masa ƙarar Mom ta mata wani abu a gidan ba idan baya nan kosu yaran sun mata. Sai dai ita Mom ɗin ta tonama kanta da kanta asiri ta hanyar gaya masa. Shiyyasa yau data kirashi ya taho a rikice. Amma Mom wani lokacin ma tun suna rigimar take kiransa ta sanar masa ƙarya da gaskiya cikin kunfar baki. Idan ya dawo gida yana jiran yaji Halime tace wani abu sai yaji shiru, ko yama samu tana firinfijimarta a gidan hankali kwance tamkar komai bai faru ba. Dan ita in har akwai wuta tv na kunne shikenan tace bata da sauran takaici a duniya. Balle ta haɗa uban shayinta cikin ƙaton kofi da burodi ta soya ƙwai ta zauna tana sha tana kallo ai ji take duniya babu ya ita. Har da rana da yamma shan shayi take saboda masifar ƙaunarsa da takeyi tun tana ƙaramarta. Abinci ma bai cika damunta ba in dai akwai shayi da burodi balle ga madara a ciki yaji da sauran kayan shayi ace kuma akwai soyayyen ƙwai wayyo jinta take kamar a aljanna. Yasha gwadata akan magana da Mom take sanar masa game da ita. Amma mutuniyar sai ta basar tama nuna ita yaushe akayi hakan, idan ma anyi to ta manta. Koda yake harga ALLAH bawai tanayi don makirci bane ko wani abu. Kawai ita har cikin ranta da halayenta da anyi abu ya wuce shikenan kawai sai wani ya taso kuma. Wannan dai ta gama da babinsa. Idan ko har kakaga Halime ta riƙe abu a rai ya dameta to lallai al'amarin babbane matuƙa. Dan wahalar data sha a hannun innarta da ace tana riƙewa a rai da tuni hawan jini da ciwon zuciya sun kai rayuwar yarinyar ƙasa....


❤️‍🔥❤️‍🔥❤️‍🔥❤️‍🔥❤️‍🔥

Ƙarfe sha ɗaya da wasu mintuna suke shigowa gidan. Har gaban dashensa TJ ya faka motar, da sauri Shu'aibu ya fito ya buɗe masa. Koda ya fita maimakon shiga sashen nasa sai ya koma ainahin ƙofar shiga babban sashen gidan. Babu kowa a falon sai Azizat dake dakon jiran dawowarsa. Yana shigowa kuwa ta miƙe zambar. Fuskarta ɗauke da murmushi ta nufosa tana masa sannu da zuwa cike da shagwaɓa. Sai da tazo gab da shi ya wani watsa mata mummunan kallo yayi wucewarsa upstairs. Kai tsaye sashen Ummie ya nufa ya barta nan tsaye baki sake tana binsa da kallo ga hawaye na gudu a fuskarta. Sai kuma ta kwasa da gudu tai sashen Hajiya Mammah itama. Sai dai tana murɗa ƙofar bedroom ɗin ta tajita a rufe gamm. Jingina tayi jikin ƙofar tana sake fashewa da kuka. Sai kuma wani ɗan nishi-nishi da take juyowa kamar daga cikin bedroom ɗin ya sata fara sassauta kukan nata tai tsai alamar saurare. Tabbas daga ɗakin mahaifiyar tata ne. Knocking ƙofar ta farayi da kiran sunan ta amma babu alamar za'a buɗe, sai dai kamar anyi shiru an daina nishin. Sake fashewa tayi da kuka tare da barin jikin ƙofar da gudu tai ɗakinta.

Wata shegiyar dariya Arwa dake laɓe tun ɗazun tana kallonta dan komai akan idonta ya faru ta saki, sai kuma cike da farin ciki ta furta, “Iska na wahalar da mai kayan kara” ta juya cike da takun girgiza jiki ta koma nata ɗakin dake a sashen uwarta Hajiya ƙarama. Dan su dukansu kowanne a sashen mahaifiyarsa yake har suma su Malika....

★ A ɓangaren Maash kuwa bai wani jima ba a sashen Ummie ya fito, dan ya samu tana barci ne alamar sauki na samuwa. Baya buƙatar wata matsalar ta sake samuwa a dalilin shigowar tasa dan haka ya juya ya fita a kan lokaci. Har zai wuce sai kuma yay tunanin shiga sashen Paah dan akwai maganar da yake sun suyi. Gobe in ALLAH ya kaimu kuma ya sanar masa da baƙi da zaiyi da wuri zai fita a gidan ba lallai su haɗu ba. Sashen Paah ɗin ya nufa da tunanin shi kaɗaine dan yasan da wahala Hajiya ƙarama idan tana a gidan kasancewar ya ganta a asibiti ɗazun. Knocking yay har sau biyu amma baiji motsin komai ba. Yasan Paah da kallon labarai yanzu haka hankalinsa nacan baima jisa ba. Dan barci dai yanada tabbacin baiyisa ba zuwa yanzun kam. Kansa tsaye ya tura ƙofar ya shiga kawai, sai dai kuma da saurin tsiya ya tsaya cak dai-dai yana ɗaga kafarsa zaiyi taku kusan na biyar a cikin falon sakamakon furucin da Paah ɗin yayi waya a kunnensa. Da ƙarfi yaja numfashinsa da ke neman fisgewa daga cikin ƙirjinsa. A wani irin harzuƙe da kaushin harshe ya furta, “Paah!!”.
A bala'in rikice Paah ya juyo tare da sakin wayar ƙasa yan zazzaro idanunsa. Fuuuu Maash ya juya ya fice a falon tare da bugo masa ƙofar da masifar ƙarfi har sai da ya zabura. “ Innalillahi wa-inna ilaihiraji'un”. Ya shiga maimaitawa cikin tashin hankali. Shi ya haifi Awwab, amma wlhy zai iya rantsuwa da baya jin tsoron wani sama da yanda yake shakkar yaron nan. Kai hatta Baba prof daya haifesa baya jin yana shakkarsa kamar Muhammad. Koda wasa baya son Muhammad ya kamasa da wani laifi musamman akan abinda za'ace ya shafi mahaifiyarsa koda kuwa ɗan kaɗan ne...

Sashen Maash ɗin Paah ya nufa a ɗarare cikin kuma tashin hankali, dan Gara yaje suyita kawai baya son ya ɗauki fushin nan da shi. Kasancewar ta ainahin ƙofar shiga sashen ya fita yabi kansa tsaye ya shiga. Shu'aibu ya samu a falo da TJ. Cikin girmamawa suka shiga gaidashi. Da ƙyar ya iya danne yanayinsa ya amsa musu. Kafin ya ɗora da tambayar ogan nasu. Kai tsaye TJ ya amsa masa da, “Alhaji yana ciki”.
“Okay to bari na gansa ko?”.
Da girmamawa suka amsa masa da to. Shi kuma yay gaba kai tsaye sashen bedrooms ɗin Maash, suma sai suka fice dama abubuwan da suka dawo da shi a mota suka shigo da su ciki. A bedroom ɗin da yafi ƙyautata zaton samunsa yay knocking. Kusan mintuna biyu aka buɗe ƙofar. Ɗan zuba masa idanu Maash dake ɗaure da towel jikinsa na raɓar ruwa alamar daga wanka ya fito yayi. Sai kuma ya ɗauke kansa fuskarsa na sake zama kicin-kicin. Batare da ya ce komai ba ya saki ƙofar ya juya ciki. Bin bayansa Paah ɗin yay shima, a bakin katafaren gadonsa ya zauna, yayinda shi kuma yake daga ɗan lungun closet ɗin sa yana ƙoƙarin zira jallaniya fara tass mai gajeren hannu. Fuskarsa a tsananin ɗaure ya sake fitowa. Batare daya kalli Paah ɗin ba ya jingina da mirror daga tsaye yana kallon wani gefen. Kaɗan ya motsa lips ɗinsa wajen faɗin, “Good Evening”.
Karan farko Paah ya saki murmushin ƙarfin hali, sai kuma ya amsa da, “Evening dear, how are you?”.
Shiru Maash bai amsa masa ba. Sai ma ƙara ɗauke kansa da yay gefe. Shiru ɗakin shima Paah bai sake magana ba yana ƙulla ta inda zai fara. Kafin ya nisa a hankali ya sake furta. “Muhammad magana nazo muyi”.
“Ina jinka”.
Ya amsa masa a daƙile. Kai kawai Paah ya girgiza. Sai kuma ya cigaba da faɗin, “Kana fushi da ni ko? Akan abinda kaji ina faɗa. Haba Muhammad, kafa san yanda nake ƙaunar Ummu-Hidaya. Taya zan iya wofantar da ita saboda ta samu lalura”.
“Paah ka faɗi abinda ya kawoka kai tsaye Please”. Maash ya katsesa cikin zafin rai.........✍️



_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._


_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_

_BANK NAME:KEYSTONE_

_BANK ACC NO:6019473875_

_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_

_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_

__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_

_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_

*09033181070*

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*


_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_




*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*

*_Typing📲_*








*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*
_(Itama nama ce)_




_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_



_𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_
_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒕𝒘𝒆𝒍𝒗𝒆_


......Zuru Paah yay masa yana kallo, sai kuma ya haɗiye yawu masu kauri yana jinjina kansa. “Muhammad wai sai yaushe zaka yarda dani akan mahaifiyarka ne? Ƙarshen maganata da kawai kaji baka san akan mi nakeyi ba, ba kuma kasan dawa nake yi ba”.
Fuska sosai Maash ya yamutse ransa na ƙara masa suya akan halin mahaifin nasa. Duk yanda yaso danne kar ya biye masa bazai iya ba, a fusace ya bashi amsa da, “Sai randa ka canja Paah. Sai randa ka ajiye son zuciya ka tuna da halacci. Bazan hanaka yin dukkan abinda kai niyya ba. Sai dai wlhy ina gab da ɗaukar mummunan mataki. Sannan yaronka na bashi nan da kwana uku ya sallami waɗan nan ƴan iskan yaran daya tara min a company, idan ba hakaba duk wani mai alaƙa dasu ya kuka da kansa. Kuma shima ya ajiye aiki da hannunsa kar ya bari na ziyarci Company yana ciki”
Cikin ɓacin rai da tsarguwa Paah ya ce, “Muhammad kana zargina ne?”.
Shiru yay yaƙi tankawa. Sai da Paah ya miƙe zuwa gabansa. Cikin sauke murya ya sake furta, “Muhammad miyyasa kai baka yafiya ne? Miyyasa kake da riƙo? Sai yaushe zaka yarda dani? Dan kawai kaji ina waya sai ka fasaarata da wata siga daban har kana tunanin sallamar waɗanda basu ji ba basu gani ba daga aiki”.
“Sai randa ka daina saka wannan ɗan iskan yaron na maka kawalcin yara ana kawosu da sunan wai ma'aikata. Paah na sanka fiye da yanda nasan kaina. Dama na jima ina zargin waɗan nan yaran zaman iskanci suke min a company. To wlhy na basu daga daren yau zuwa gobe su koma inda suka fito, in ma gidan karuwai zaka buɗe musu bai shafeni ba rayuwarka ce”.
Rumtse idanu Paah yayi da ƙarfi. Sosai kalaman ɗan nasa ke masa amsa kuwwa a cikin kunne. Yasan wanene Awwab idan yay fushi. Sam baya tauna magana yayin faɗarta balle shakka. Jin alamar zai bar wajen ya sashi buɗe idanunsa. Cikin ɓacin rai ya dakatar da shi da faɗin, “Miyasa baka tauna magana yayin furtata? Ina matsayin mahaifinka amma baka shakkar tauna magana yayin furta min ita. Komai ya zo maka a rai saika yaɓosa waje”
A daƙile da yanayin zafin rai shima Maash ya furta, “Ni ɗankane bani da hurimin hanaka duk abinda ka tsarama rayuwarka kam. Amma ka sani bazan iya cigaba da jurar ganin kana kana takamin mahaifiya a ƙarƙashin takalman ƙafarka ba Paah. Abinda na ɗauka kafin yanzu bazan iya ɗaukarsaba a yanzu. Idan da kace rashin mace ke saka aikata abinda kake aikatawa yanzu minene hujjarka kuma tunda kana da wata matar? Kai da kanka kamin alƙawarin dainawa, ashe baka fasa ɗin ba. Idan mace ɗaya ta maka kaɗan ka ƙara auren mana. Ka ƙaro uku su zama huɗu yafi min wannan mummunar ɗabi'ar taka mai zubar da mutunci ga zunubi wajen UBANGIJI.....” ya ƙare maganar cikin ƙaraji dasa hannu ya watso kayan saman mirror ɗinsa gaba ɗaya. Sai kuma ya kaima mirror ɗin naushi, a take kuwa ya shiga tsatstsagewa. Sake kai masa wani naushin yayi, ya kuma tsagewa tare da

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login