Showing 180001 words to 183000 words out of 438336 words

Chapter 61 - Tsutsar Nama Book 1 Hausa Novel Complete

13 Dec 2024

2161

alkairin daya samu Musaddiq dan nan da sati biyu shi kuma zai wuce ƙasar Chaina. Yaso ayi bikin Baby da Musaddiq ɗin, sai dai hakan bazai yiwu ba saboda komai na tafiyarsa ya gama kammala. Wannan magana itace ta hargitsa Mom matuƙa har ta danne mata al'amarin Halime a kwanaki biyun nan.
Ummanta ce ta bazama wajen teachers ɗin su. Shine jiya da dare aka kawo abinda zatai amfani da shi akan Musaddiq dan daƙile wannan batun tafiya. Yau kuma ake son yaci a cikin abinci. Da rana baya gida, dan haka ta gama shiryama girkin dare gashi ba itace da girkin ba. Sai kuma ga Halime ta shiga domin ɗorawa saboda kowa yasan ita ya kamata tayi girkin daren. Ga kuma Abba yay kiranta da sake tabbatar mata dan har ma ya aiko yaro da cefane. Shine Mom tace bata isa ba itace zatai girkin. A lokacin makwafciyarsu da sukai magana da Mansoor na gidan. Shine ta raba gardamar ta sake tabbatarma Mom cewar Halime dai ya kamata tayi girkin daren. Kawai sai Mom ta fara tura mata ashariya. Shine ta fito tana Murmushi yayinda Halime ke dariya. Dan ita al'amarin Mom ɗin yanzu dariya ma ya koma bata. Mace kamar mai mutsukku a cikin kai. Murhun gawayi makwafciyar tasu ta kawo ma Halime tunda dama abin girkin kawai take buƙata komai na ma'aikaci itama tana da shi. Harda ƙullin gawayi biyu...

💕🌟💕

Bluetooth ɗin dake cikin kunnensa ya zare yana mai sakin wani kalar lalataccen murmushi. Sai kuma ya sake maida fuskarsa ya tsuke tamkar bashi ba. Tamkar ba wanda ake jira ba ya shiga zare kayan jikinsa a nutse dan babu alamar wani gaggawa a tare da shi. Dogon wandon jikinsa kawai ya bari batare da ya cire ba ya nufi closet ɗinsa. Daga can kusurwar bango Ya danna wani maɓalli, a take adon wutsiyar wadrobe ɗin dake ta dai-dai kona ɗin ya shiga naɗe kansa. Zallar gilashi garai-garai da haskensa kesa a iya ganin komai dake a cikin wajen ya bayyana. Nan ɗin ma dai wani abu ya danna, a take gilashin yaja kansa ya shige cikin wadrobe ɗin. Zallar adon golden ya bayyana da bindigu har guda uku da aka manna a bangon wajen tamkar an zana sune. Hannunsa duk biyu ya tura a cikin aljihun wandon, tare da gyara tsaiwarsa ya zubama bindugun ido. Biyu ƙananu ne, ɗaya ƴar babba hakannan daka ganta kasan zatai haɗari da tsada. Cike da wani salon taƙadaranci ya cije lips ɗinsa tare da zare hannunsa ɗaya ya maida gashinsa daya sakko masa a fuska kaɗan saboda salon gyaran dayay masa ɗazun da yamma. Sauke hannun yay a hankali ya kai yatsarsa ɗaya saman bindigar farko, tamkar mai zana abu sannu-sannu ya dinga sakkoshi ƙasa har ya dire akan ta tsakkiya, nanma bai tsaya ba yay ƙasa har sai da yaje ta ƙarshe. Zagaya kan bindigar ya cigaba dayi da yatsar tasa kusan sakan biyu sai kuma ya sake maidashi sama ya ɗora akan ta tsakkiyar. Nan ma yaja kusan sakanni biyar ma tamkar mai nazari sai kuma ya laɓe baki cike da salon ɗage kafaɗu ya ciro bindigar alamar zuciyarsa tafi aminta da ɗaukar tata. Sauran mahaɗanta dake gefenta suma kowanne a mahallinsa ya cicciro harda bullet kusan biyar sannan ya maida komai a yanda yake ya fito. Cikin bedroom ɗin nasa ya dawo, ya zauna a katafaren bakin gadonsa ya haɗa bindigar tsaff cike da ƙwarewa ya ajiye, sai dai bai saka bullets ɗin ba ya jawo side drawer ɗinsa ta gado ya zuba su ciki. Bathroom ɗin ya nufa abinsa cike da takunsa na mazantaka da nutsuwa.........✍️


_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._


_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_

_BANK NAME:KEYSTONE_

_BANK ACC NO:6019473875_

_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_

_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_

__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_

_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_

*09033181070*

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*


_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_




*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*


*_Typing📲_*








*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*
_(Itama nama ce)_




_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_



_𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒘𝒐_
_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒇𝒐𝒓𝒕𝒚 𝒔𝒆𝒗𝒆𝒏_

......Ina kitchen ina ƙoƙarin haɗama Ummie madara kamar yanda na saba a kowanne dare yanzu saboda naga tana sonta sosai Hajiya Mammah ta shigo. Kamar ko yaushe tsaff take cikin kwalliya mai ɗaukar ido da ke nuna ita ɗin wacece. Sosai take matuƙar bani mamaki matar nan. Itafa dare baya hanata kwalliya kamar jikanyar ifiritai, musamman idan akace tana da baƙuwa da zata kwana a gidan. Gaisheta nai a ɗarare da ƙoƙarin kauda kai daga kallon ƙurillar da take bina da shi daga sama har ƙasa. Kadaran kadahan ta amsa min sai dai fuskarta a sake. Juice ta ɗauka ta ɗaura a samar tray tare da glass cup, sai ƙaramin bowl da aka yanka fruit yay ƙyau sosai musamman yanda kalolinsu suka fito a farin glass bowl ɗin kamar an zana, sai kuma wani haɗaɗɗen kula shima mai ƙyau duk ta ɗora, har zata ɗauka sai kuma ta dakata. Kallona tai tare da tukunyar da nake dafa madarar.
“Kandala mi kike dafawa anan?”.
Fuskata a ɗan cinkushe, na ce, “Hajiya madarar Ummie ce”.
Kanta ta jinjina tare da faɗin, “Okay Masha ALLAH. Ta kusa kammaluwa ne?”.
“A'a yanzu na ɗora ai babu jimawa”.
“Okay! To kinga zonan kimin wani aiki sai na jire miki. Awwab zaki miƙama wannan part ɗinsa. Azizat ya saka Paah ɗinsu kuma ya sakata aiki, Awwab kuma baya son jira zai iya fasa sha kuma nasan ba wani abu yaci ba”.
Ji nai kamar na fasa ihu, sai dai nasan ban isa cewa bazanyi ba. Amma a cikin raina na ɗan yi mamaki, to amma ina ruwana ba yayar babansa bace. Cikin haɗiye yawu da ƙyar na amsa tray ɗin, ɗauke juice ɗin tayi da glass cup ɗin tana faɗin, “Banda wannan nawane. Kiyi maza zan koma sama ne”.
“Okay maa”. Na amsa mata cike da jin haushi. Acan ƙasan raina kuwa jinake kamar na haɗiyi zuciyata na huta. Amma dai ba komai, dan nima kai fruit salad ɗin zai min amfani, dan dama ina son ganinsa. Dan akwai bashina a kansa, bazan taɓa barin maganar daya gasamin ɗazun da safe ba sai na maida murtani, idan ba hakaba zan iya kasa barci ma wlhy. Kamar koyaushe a nutsena nake tafiyata. Jikina da hijjab iya gwiwa mai hannu kamar kullum. Duk fa amatsayin ƴar aiki nake gidan kamar yanda shaiɗanin ya ƙalabamin akoda yaushe zaka sameni cikin tsaftata, dan inada ƙyanƙyami, ga son wanka kamar ƴar agwagwa. Komai a gidan free ne har gamu masu aiki, banbancin kawai komai zakayi kai da kanka ne masu gidan kuwa mune ke musu. A hankalin ƙamshin turaren da Ummie ta fesamin ɗazun har a cikin gashina ke tashi, sosai turaren ya kwanta min a zuciya. dan yana fidda wani sihirtaccen ƙamshi mai ratsa zuciyar mai shaƙa harma da kai daka saka. Na ɗakko ne zan saka mata ta fisge ta hau min feshi da shi a jikina tana dariya, bata kuwa barsa ba sai da nayi dabarar amshewa. Koba'a faɗa ba nasan an sayesa ne da kuɗaɗe masu nauyi. Murmushi na saki mai sanyi, dan yanda yake bama Ummien kulawa a gidan da kowanne nau'in abubuwan more rayuwa duk da lalurar dake tare da ita na ƙayatar dani. Sau kusan uku ina knocking amma babu alamar za'a buɗe min. “Ɗan wulaƙanci fitinanne mai girman kai”. Na faɗa a hankali ina murguɗa baki da hararar ƙofar. Cikin jin zafi na murɗa handle ɗin ƙofar na shiga falon. Kamar kullum babu yawaitar haske. Sai uban sanyin ac da mayataccen ƙamshinsa daya gama mamaye komai. Hatta kusa da mutum idan ya tsaya ko wani dalili yasa ya taɓaka koya zauna guri ya tashi ka zauna sai ka ɗeba mayen ƙamshin nan nashi. Narasa da wane shegen turare yake amfani haka. Koda yake ya wuce na tsafi. Na bama kaina amsa ina murguɗa baki. Ƙoƙarin ajiyewa nake a Centre table ɗin falon aka shigo da sallama bayan anyi knocking. Bakowa bane face Hayatu, dan haka na amsa sallamar tasa a zuciyata kawai batare dana kallesa ba na ƙarasa ajiye tray ɗin.
“Barka da dare Maa”.
Ya faɗa cikin girmamawa kamar yanda yake min yanzu musamman idan babu kowa a waje. Harara na ɗago na balla masa ina mai jan sirrin tsaki. Shiko yay ƙasa da kansa. Ƙafa na ɗaga zan bar wajen da sauri ya ce, “Dan ALLAH kiyi haƙuri. Ki kai masa bedroom inba hakaba bazai shasa anan ba. Dan muna uzirin fitane, Ummie kuma bata ƙaunar zamansa da yunwa duk yau babu abinda yaci kuma sai chocolate.”
Wata hararar na sake balla masa. Shiko ya sake marairaicewa da faɗin, “Dan ALLAH dan ƙaunar da kike ma Ummie”.
Idanuna na rumtse da ƙarfi. Kamar kar nayin sai kuma dai na ɗauka dan ni shaidace, duk randa Ummie ta cika fitina a gidan to dan gudan jinin nata ne. Sai dai kuma daya raɓeta babu sauran zaman lafiya musamman ace ya shiga ɗakin da take ko yazo kusa da ita sosai. Sai dai ya kasance a nesa da itane yanzu zata fa zuba masa ido kamar mai son tuna wani abu a kansa kosan sanin wanene shi har hotonsa haka take masa. Cikin ƴar fusatar da Hayatun ya sake saka min nai knocking ƙofar bedroom ɗin nasa da ƙaddara tasa zan masa shiga ta biyu. Nasan latsin rainin wayonsa. Zai ma iya kasancewa yana jina yay shiru, niko ina son komawa na kaima Ummie madararta tasha magani. Agadarance na murɗa ƙofar na shiga ina mai sake tsuke fuskasta da haɗa baƙar maganar dazan gasa masa da nake fatan ta hanashi barci. Wayam babu kowa a ɗakin, sai dai anan ɗin ma hasken akwai ƙaranci, sai dai yafi na falon dan anan ana iya ganin komai. Kayansa daya watsar a kan lallausan milk carpet ɗin dake a gaban gadon na ballama harara da taɓe baki. A bayyane na furta, “Ƙazami kawai sai iyayi da feleƙe, amma ba'a iya yima kai komai.” a saman bed side drawer na nufi ajiye tray ɗin, sai idona ya sauka akan bindiga. Sosai na waro idanu, jikina har tsuma yake wajen ajiye tray ɗin hannuna kaɗan ya rage ban zubar da shi ba na dai gyara masa zama ina ɗaukar bindigar. (Ta tabbata dai guy ɗin nan ɗan ta'addane. Yo anya ma ba ɗan fashi da makami bane? Kambu aiko yau zan tona asiri, zai ko tabbatar ya kawo ƴar jarida gidan nan) na ƙare zancen a zuciyata ina sakin ƙwafa a fili. Ƙofa na zabura zan nufa ina ƙoƙarin soke bindigar a cikin jikina. Dai-dai nan aka buɗe ƙofar bathroom. Naji firgici, dan yanayina ma ya nuna hakan sakamakon a yanda na jiyo na kalla wajen. Ganin shine ɗaure da towel iya ƙugu zuwa gwiwa yana riƙe da ƙarami a hannunsa zai kai shi fuskarsa amma ya tsaya yana kallona nai saurin ɗauke idanun nawa tare da zaburar son nabar ɗakin kafin ya farga da abinda na ɗauka. Sai dai me ina isa jikin ƙofar naji ta bada ƙitt alamar rufewa, duk da kuwa a rufen take dama. Ban fasa kai hannuna jikin handle ɗin ba, na murɗa na murɗa amma ko gezau tabbacin dai an kulle. (To ta yaya?) Zuciyata ta tambaya, rashin amsa da makama ya sani juyowa, sai ko idanunsu suka sauka akan ƙaramin black & golden remote dake hannunsa alamar da shi ya kulle ƙofar. Dan yanda ya ɗauke kansa tamkar baiyi komai ba ya sake tabbatar min da hakan. A ɗan zamana gidan na fara haddace mugayen halayensa a cikin kaina. Dan babu ubanda yake ragamawa da wannan murɗaɗɗen halin nasa na rashin mutunci. Ko kallona bai sake yi ba ya nufi gaban mirror ɗinsa hankali kwance. Saurin kauda idona nayi daga kansa dan dama dai a gaba ɗaya cikin sakanni da baifi goma bane komai ya faru, ban kuma iya masa ko kallon sakan ɗaya cikakke ba saboda yanayin da yake ciki, dan ma babu yawaitar haske a ɗakin ne shiyyasa.
A bazata cikin dakewarsa da daƙilallen yanayi irin na mugayen muskilan mutane a silent voice ɗin nan nashi ya furta, “K idonki bazai daina gane-gane ba ko?”.
Sam da farko bammayi zaton shine yay maganar ba. Sai da nai ɗan jimmm sannan na fahimta. Baki na murguɗa batare dana kallesa ba cike da tsiwa nima na furta, “In dai masu mugun halin ta'addanci na a inda nake gane-gane ma yanzu ya fara ai. Kuma in kere na yawo zabo na yawo wataran za'a gamu. Adai juri zuwa rafi. Saboda wataran tulu zai fashe a tsakkiyar kasuwa. Dan in ma an binne wani abun wani bazai binnu ba. Musamman ma Samraah Abdul-wahab Gwarzo”.
Shiru bai tanka min ba. Ni kuma na kasa iya ɗaga ido na kallesa saboda a yanda yake samandagari guda babu riga ƙaton kawai. A bazata matuƙar bazata naji tsaiwar mutum a kaina daf, ai bamma san sanda na ɗago ba a harmutse. Ƙamshin turarensa ne yay mugun rige-rigen shiga min hanci saboda iskar razana dana shaƙa da ƙarfi. Kusancin namu yayi yawa dan haka nai matuƙar zabura baya ina ƙyaƙyƙyafta idanu uwa ya na namijin biranya. Hannu ya miƙomin alamar na bashi. Nasan bindigarsa yake nufi, amma sai na balla masa harara na ɗauke kaina. Dan ya kafeni da muggan idanunsan nan na maguna. Sai dai yanda nake a tsorace yasa a ankare nake karya shammaceni. Ina kuwa ganin ya motsa na sake zabura baya. Ganin kaina yayo na ɗage zan falla da gudu koda cikin bathroom ɗinsa ne tunda ya kulle nan mugun yasa ƙafa ya taɗoni, sai gani zube a saman gadonsa.......✍️


_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._


_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_

_BANK NAME:KEYSTONE_

_BANK ACC NO:6019473875_

_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_

_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_

__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_

_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_

*09033181070*

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*


_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_




*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*


*_Typing📲_*








*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*
_(Itama nama ce)_




_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_



_𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒘𝒐_
_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒇𝒐𝒓𝒕𝒚 𝒆𝒊𝒈𝒉𝒕_


......Da wani kalar sauri da rawar jiki na motsa zan tashi, zuciyata na wani kalar masifaffen gudu a cikin ƙirjina tamkar zata fito ta baki ya hana hakan ta hanyar ɗora ƙafarsa ɗaya a saman gadon ɗaya a ƙasa ya ranƙwafo yay mun rumfa. Hakan ya saka kammu gwaruwa waje ɗaya saboda na riga na ɗago. Wani azabane ya ratsa min goshina, da sauri na koma tare da dafewa da hannayena duka biyun ina faɗin “Wayyo ALLAH mai kan rodi ya fasan kai na”. Nayi kusan minti ɗaya a haka raɗaɗi na ratsani dan da gaske naji zafi kafin na janye hannun ina ƙoƙarin hana hawayen da suka cika min ido zubowa, bindigar na ciro daga hijjab ɗin na nunasa da ita, cike da masifa na buɗe baki zanyi magana amma a mamakina sai naji bakin ya gagara motsawa, sai rawa lips ɗina kemun kar-kar da motsi a hankali. Dan wani irin masifar jinai ya cika min ko'ina. Hatta ɗakin jina nake a matse matuƙa a cikinsa. Idanuna na rumtse da ƙarfi ina sake wayancewa na maida hannuna saman goshin na dafe, ɗayan kuma dai na nunasa da bindigar. A cikin zuciyata nake jera masa ALLAH ya isa. Jin kamar ana ƙoƙarin saka min abu a jikin tsintsiyar hannuna ya sani saurin ƙoƙarin janye hannun. Bamma san sanda na sake zaburowar ba ganin ya saka min handcuffs. Hannun nai ƙoƙarin fisga shi kuma ya cire key ɗin daya kulle handcuffs ɗin dai-dai nan. Bindigar hannuna ce ta faɗi.
“Malam minene haka kayi?”.
Na faɗa cikin gigita da ruɗewa. Bai tanka min ba, sai ma ƙoƙarin sauke ƙafarsa yake yi, cikin ƙunar rai da rufewar ido na sake buɗe baki zan yi magana tare da kai ɗayan hannuna zan damƙoshi batare dana san mi nake shirin yi ba ya wani kalar juyowa. Farin yatsarsa mai ɗauke da dogon farin farce ƙal-ƙal masu sheƙi ya ɗaura saman pink ɗan ƙaramin lips ɗinsa. “Shiii!!!” ya faɗa yana wani waro min cat eyes ɗinsa masu girma da cikar gashi. A take tsigar jikina tai bala'in tashi. Bamma san sanda nai saurin kauda kaina ba bakin nawa na rufewa bamm batare dana iya furta ko a ba. Ga hannuna da nakai zan riƙosa na tsaye ƙyam, ban sauke ba ban kuma ƙarasa kaisa jikinsa ba, dan sai yanzu nama fahimci taɓargazar da naso yi...
Maash dake bin fuskarta da wani ɗan iskan kallo zuciyarsa na wani masifar hanƙoron mamakinta a cikin ƙirjinsa ya janye idanun ya saukesu akan hannunta. Sake tsuke fuskar yayi, a kausashe ya furta, “Idan wannan small hand ɗin ya sauka jikina You will regret it har wayewar garin yau”. Ya ƙare maganar yana kaɓar da hannun tare da ƙoƙarin ɗaukar bindigar nai saurin ɗaukewa kafin ya kai nasa hannun na tura cikin skirt ɗina.
“Humm” ya faɗa yana wani shanye girman idanunsa da jan sirrin tsaki da yay matukar zafata. Sake rumtse idanuna nayi ina mai sake tsuke

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login