Showing 429001 words to 432000 words out of 438336 words

Chapter 144 - Tsutsar Nama Book 1 Hausa Novel Complete

13 Dec 2024

2147

muna da ita. Kai dai kawai kazo garemu kaga aiki da cikawa da iznin ALLAH. 09032345899. A nememu tanan ga masu buƙata, dan ALLAH serious bama son latsi ko wasa dan ba wasan muka fito ba 😂😍👍🏻._



......Anan aka bar min Gwaggo Gudidi da auta, sai yarinyar Uncle Sulaiman ɗaya mai suna Fatima. Sai Mammi da zata ɗan kwana mana biyu itama dan zataga likita akan ciwon ƙashi dake damunta. Haka suka wuce suka barmu da kewa ana fatan kuma sai Bahijja ko Ruƙayya wani ya haihuwa a haɗu a Nigeria. Harda kukana dan nazata Ummie zatace tunda anyi suna muje can na ƙarasa wanka. Amma saita lallasheni nayi haƙuri uban tutsun ya hana. Dan itama taso hakan amma Paah yace ta barshi da matarsa tunda baya son na taho. Shine aka yanke shawarar bar min su Gwaggo Gudidi ɗin. Kasancewar Auta ya gama primary sai kawai na yanke shawarar sakashi makaranta anan. Dan in sha ALLAHU yazo kenan. Gara koshi Abba ya mora a cikin yaƴan Mom dai.
Ban sha wahala ga Yaya Awwab ba. Dan ina sanar masa manufata akan auta ya bani goyon baya ɗari bisa ɗari, tare da sake min albishir ɗin suna gab da sanin inda mijin Baby yake. Dan tunda ya amsa sunansa a wajen su Abba yake ta bincike ta ƙarƙashin ƙasa. Saboda al'amarin sai da taka tsantsan, ƙungiyar da mutum yake babbar ƙungiyace ta ƴan luwaɗi, sannan sunada ƙarfi matuƙa da fito-na-fito da su ba ƙaramin abu bane. Wannan bayani nasa ya tayar min da hankali matuƙa, dan sai da nai kuka sosai ina mai taya ƴar Uwata da addu'ar ALLAH ya ƙwatota daga wannan makaunuyar ƙaddara da kwaɗayin abin duniya da son wuce wani ya jawo mata.
Rayuwa ta cigaba da tafiya bisa ƙaddarorin dake rubuce a cikin littafin mu da alƙalaminsa baya ƙarya ko kuskure. Sosai Gwaggo Gudidi da Mammi ke kulawa da ni da Heedaya. Gyara suke min na haƙiƙa irin na tsoffi, nima kuma ina nawa dabarun a gefe da aunty Halime tazo min da su. A haka cikin amincin ALLAH mukayi arba'in. Yaya Awwab dai yayi haƙuri sosai a wannan gaɓar. Irin haƙurin da banyi zato ko tsammanin zai yi ba. Kodan aikin da yake ne ya ɗauke hankalinsa oho. Sannan yayi ƴan tafiye-tafiye dan har wajen su Yaya Musaddiq yaje yay kusan one week. Sannan yaje Nigeria ma. A dawowar ne ma nake jin batun mutuwar Hajiya ƙarama. Dan su Ummie duk da muna waya babu wanda ya taɓa sanar min. Ko basu sani bane oho. Washe garin da mukai arba'in ya dawo daga tafiyar kwana biyu da yayi, ranar dai kam ban tsallake ba a hannunsa. Dan murje idanu yay yama sauka a ɗakina ta yanda dole Gwaggo Gudidi ta janye jikinta. Aikam nako ji a jikina sosai. Dan sai da na dawo ina wayyo-wayyo na wahala.
Ko tausayi babu ya ce ai yana kan sani yay duk abinda yayi, nima banji tausayinsa ba ai duk da nasan yana cikin wani hali na biyema su Mammi. Gobe ma na sake masa makamancin wannan horon. Baki kawai na tura masa bance komai ba. Ya fita yana dariya. Sati biyu da yin arba'in ɗina Bahijja tai ɓari. Tsabar Fahad baya ji haka ya kiramu yana rusar kuka wai ya rasa Babynsa. Kai al'amarin Fahad sai shi. Mudai mun jajanta tare da kwantar masa da hankalin ALLAH zai bada wani rayayye. Wannan ɓari sai da suka saka Ummie zuwa Spain dole. Satinta biyu acan ta biyo tanan wajenmu ganin takwararta. Kwana huɗu tai mana tai shirin wucewa. Aiko su Gwaggo sukace ƙafarta ƙafarsu. Babu kalar lallaɓawar da bamu musu ba musamman Mammi amma sukace ina su wannan zaman takura bada su ba. A gida sun saba shiga maƙwafta, barkar haihuwa, gaisuwar mutuwa da bakin aure da ziyarar dangi. Amma anan saika sati ma bakaga rana ba sai idan an fita damune sannan. Ya muka iya, haka Ummie ta wuce da su bayan Yaya Awwab ya haɗa musu shatara ta arziƙi. Aka barmu da Fateema da Auta. Wucewar tasu babu jimawa Fahad da Hafizzullah da Bahijja suka zo mana hutu. Zuwan nasu ya mana daɗi, nan fa Hafizzullah da Fateema aka ɗin ke. Tun bamu fahimta ba Bahijja ta tona. Nayi murna da hakan, dan al'amarin nasu zaiyi dai-dai insha ALLAHU. Itama dai Fateeman ba wata babba bace, yanzu ne ma ake nema mata makaranta anan dan ta kammala secondary a Nigeria. Shima Yaya Awwab da yaji yayi murna matuƙa, sai dai ya kiransu ya musu nasiha da tabbatar musu da ba yanzu ba sai shi Hafizzullah ya gama school sannan. Ita ko bata kammala ba ta idasa a gidansa. Hakan yama kowa, na kuma bisu da fatan alkairi. Suma satinsu uku suka koma inda suka fito. Haka rayuwar ta cigaba da gangarawa har ga Baby Heedaya da watanni takwas a duniya. Tayi ƙyau abinta kamanninta da mahaifinta da kakarta sun sake bayyana. Idan ka ganta sai ka ɗauka ma bani na haifeta ba. Dan sam bamu kamanni tako ina sai dai kawai ace dan jini. Tana rarrafenta ko ina, idan ma ta kama wani abu takan miƙe tana tafiya a haka. Amma ita kaɗai dai kota miƙe takan koma ta zube ne.
Alhamdullah tana da wata goma ta miƙe, babanta daɗi kamar ya cija kansa. Ni harma mamakinsa nake akan soyayyar da yakema yarinyar nan. Idan yana mata wani abun nakan zauna ne kawai ina kallonsu. Sai na dinga jin kewar namu iyayen muma. Har kuka nakanyi watarana. Ai tunda ta cika wata na goma sha ɗaya ya fara tsirar yawo damu ƙasashe. Mune nan yau, mune can gobe kamar ƴan sama jannati. Idan nai magana yace gwara muyi yanzu dan da Heedaya ta isa shiga makaranta yawo ya ƙare. Amma yanzu muna da damar da zai zagaya da ni naga duniya nima. Da wannan sharhin nashi dole nake jan bakina nayi shiru. A wannan tsakanin ne Rukyn Yaya Musaddiq ta haihu, sai dai su sun koma Nigeria ne. Dole muma muka shirya muka nufi Nigeria. Tarba muka samu ta musamman a wajen Ummie da Mama Balki. Tuni an gyara mana sashenmu tsaf. Paah na maƙale da ƴar jikarsa. Sosai yake nunama Heedaya soyayya, dan yakance kama take da matarsa Ummie komai nata kamar ƙuruciyarta. Dan haka son da yake mata na musamman ne. Ummie dai takanyi dariya muma hakan. Kwanan mu biyu a Lagos muka wuce Kano. Nan kuma fa aka haɗu da ƴan uwa da abokan arziki. Rayuwa kenan, a yanzu kowa so yake mana bana wasa ba. Kowa so yake ma ace yana mu'amula da mu daga cikin ƴan uwa har ƙawaye. Babyn Yaya Musaddiq yaci sunan Babanmu, wato Abdul-wahab. Ban tsaya sanya ba a wannan suna na kishi kuɗi matuƙa. Dan bikin suna mukayi na nunama sa'a da ya sake birkice Mom da komai ya lalace mata. Ga Bibaa ta zame mata ƙarfen ƙafa yarinya bata jin magana sam. Dan washe garin sunan Abdull sai da Hafizzullah ya zaneta saboda yanda take zagin Mom dan ta mata faɗan yawo. Mukam sai abun ma ya girmemu. Yaya Abbas shaye-shaye har baya gane kansa. Dan haka mukai meeting akan kaisa Rihab ko za'a dace. Abba yay ta kuka yana sake neman gafararmu da sanya albarka. Muko mukace dan ALLAH ya daina bamu haƙurin nan haka mu komai fa ya wuce a garemu in sha ALLAHU. Kwana biyu da sunan mukai ziyarar dangi, mune har Gwarzo. Dole badan Yaya Awwab yaso ba yabar Ummie ta cika mana alƙawarinmu. Dan kuwa sati guda yace miyo. Farin ciki mukai sosai musamman ma Aunty Falaq da dama babban birinta kenan.
Wannan ɗan hutu a gwarzo ya saka mu farin ciki matuƙa, dan mun zagaya dangi har cikin wasu ƙauyukan dake ƙasanmu da dangi ke rayuwa a can. Mun baza alkairi sosai inda muke ta samun sambarka da albarka da addu'oi wa mahaifanmu. Dan hatta abokan mahaifinmu na ƙuruciya bamu bari ba. Kowa ya samu alkairi daga garemu gwargwadon iko. Muma kuma da zamu taho sun haɗa mana tsaraba taban mamaki. Dan motocin da akaje ɗaukarmu banda biyun da aka barmu dasu dama saboda zuwa yanzu daga ni har Aunty Falaq kowa na murza tasa. Koda yake dama ita tana da mota, nice dai sai yanzu ALLAH yayi. Mun dawo Gwarzo da kwanaki uku muka sake komawa Lagos. Daga can kuma muka fara shirye-shiryen komawa inda muka fito. Amma sai Ummie tace ko zamuyi haƙuri kawai tunda ga bikin su Azizat ɗin Hajiya Mammah na tunkarowa. Dan baifi saura sati biyu ba. Kuma dai ya kamata ace mun halarta ai. Duk mun gamsu da hakan, amma mun roƙeta taima su Yaya Awwab ɗin magana da kanta. Musamman ma ni da nasan halin tutsun nawa. Ashe dai a hakan ma ba tsira nayi ba. Dan da daddare kamar yanda muka saba naga har zan kwanta bai kirani ba. Sai na sauke nawa jin kan ni na ɗaga wayar na kirashi. Kira biyu bai ɗaga ba. Sai nai tunanin ko yana wani uzirin ne idan ya kammala zai kirani. Amma mi har barci ya ɗaukeni shiru kake ji. Ina farkawa da asuba wayata na fara dubawa. Sai dai babu ko text message balle miss call. Haka nayi salla sukuku, bayan na idar nai azkar. Kasancewar mu muke haɗa break fast tunda mukazo muka hutar da su Ummie sai na tashi na fita zuwa kitchen.......✍️




_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._


_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_

_BANK NAME:KEYSTONE_

_BANK ACC NO:6019473875_

_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_

_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_

__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_

_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_

*09033181070*

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*


_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_




*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*



*_Typing📲_*








*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*
_(Itama nama ce)_




_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_



_𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_
_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒉𝒖𝒏𝒅𝒓𝒆𝒅 & 𝒕𝒘𝒆𝒏𝒕𝒚-𝒕𝒘𝒐_


Follow this link to join my WhatsApp group:

https://chat.whatsapp.com/JJkSofA4Hto57YwEu2Z8Xq


*_Wai ni Balki ina duk masoyan Bilyn Abdull ɗin nan dake a manhajar Instagram da TikTok ne?🤔? Kai jama'a gaskiya da kunya ace account na Bilyn Abdull a Instagram da TikTok iya kar fallowers ɗin kenan🥲😣. Ina masoyan facebook ɗin nan dana WhatsApp, Please a fito mana ai fallowing ɗina. Accounts ne na Bussines ko bazaki/zaka saya ba zakaga abinda ya burgeka ko kalarka ka nema a inda kake. Maza ku garzayo BILYN ABDULL ONLINE SHOPPING kodan kashe kwarkwatar idanunku ku more kallo iya kallonku da kaya ƴan yayi cikin farashi mai sauƙi da rahusa. Muna bada sari, muna adashen gata, muna sai da ɗai-ɗai. Ka gani su burgeka, ka saka ka birge mai kallonka sai Bilyn Abdull online shopping. Bari muga akwai ƙaunar kodai-kodai....😉🫣. Ga link nan naga accounts ɗin nan biyu kamar zasu fashe da fallowers 😘😘😘😍😍👍🏻👇🏻_*.

*_BILYN-ABDULL ONLINE SHOPPING_* _Duniyar cancaɗa ado da kwalliyar birgewa. Kar ku bari ayi babu ku😘😘😘._

*_My account on TikTok_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1

*_Instagram_*

I'm on Instagram as @balkissaibrahimmusa. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

_Ina masu son zuwa ganin likita ko yawon buɗe ido ƙasar Egypt?. To ku garzayo munada hanya mai sauƙi ta sama muku sauƙin tafiya cikin ƙa'ida da bin dokar ƙasa. Katafi anan cikin aminci, ka dawo kuma cikin aminci. Wajen kwananka a can zamu tanada, asibitin da zakaga likita duk zamu tsaya maka da tsayawar UBANGIJI. Hakama yawon hutawa zamu zame maka jagora. Kai ko hanyar zuwa domin sayo kaya duk muna da ita. Kai dai kawai kazo garemu kaga aiki da cikawa da iznin ALLAH. 09032345899. A nememu tanan ga masu buƙata, dan ALLAH serious bama son latsi ko wasa dan ba wasan muka fito ba 😂😍👍🏻._


.......Muna aiki ina yawan kallon waya. Har dai Aunty Falaq ta kasa haƙuri ta magantu. Shine nace mata babu komai. Da ga ita dai har Bahijja basu gamsu ba. Sai da aikin namu yay nisa ne Bahijja ke cemana mu bata shawara. Tun jiya Fahad ke mata masifa akan zaman yin bikin nan. Yace shi bikin suna kawai ya turota ba zuwa biki ba. Iya haƙuri ta bashi da masa bayanin muma fa har damu amma yaƙi saurarenta daga ƙarshe ma ya kashe mata waya. Tuni hankalina ya tashi, dan tabbas nima kuwa inaga akan wannan matsalar ce nawa gwaskan ke shareni. To amma mu manya ne ai, sai na danne komai a raina muka shiga bata shawarar data nema. Gashi baiwar ALLAH tana fama da ɗan laulayin cikinta. Kai maza dai duk sai a barsu halinsu ɗaya wlhy. Harna koma sashenmu nai wanka na kimtsa dan a babban kitchen muke aikin na dawo bai kira ba. Heedaya dama tana wajen Mama Balki ne da Ummie ko Mammi, idan kin ganta a wajena tofa feeding ɗinta zanyi, da yake ma ta gado uban nata rashin damuwa da abinci sai na yini bata damu ba. Amma a hakan nace a yayata ya hauni da tujara wai karma ma nayi koda kwatance. Sai yarinyarsa tayi two years cif sannan. Ranar dan takaicinsu shi da ƴar har jinai hawaye sun cikan ido.
Har muka gama break fast babu Yaya Awwab babu dalilinsa. Dole na zare jikina na koma sashenmu kamar zanyi wani aiki na sake kiransa. Yanzun ma ƙin ɗagawa yay, dan haka nai alƙawarin zanyi kiran ƙarshe. Idan yaƙi ya ɗaga ALLAH na barsa kenan. Yo ina dalili, naga dai bikin danginsa ne. Sannan Ummie tace mu tsaya ai bamu muka nema ba. Amma yake neman ɗaura min jakar tsaba. To na dai yi sa'a ya ɗaga, amma sai wani faman shashashan ƙamshi yake da tsuke fuska da yake video call na masa. Dan shi yafi son kira haka. Gaisuwar ma ciki-ciki ya amsa min daga haka yaja bakinsa yay shiru. Sai na daure na tambayesa ko baida lafiya ne. A gadarance ya ce, kin damu da hakan ne? Look Samrh kin san bana san raunin wayo, bikin suna na turoki yi, aka tilastani kikai tafiyar da ban niyya ba nai haƙuri na barki. Shine yanzu kuka sake tsarama Ummie magana ko. To ni bazance komai ba. Amma zaɓi ya rage naki, jibi Hafizzullah zai taho min da yarinyata, idan kin gadama kiyita zama ke kuma. Fateema da Mahaboob zasu dawo suma na barki lafiya”. Ya yanke kiran ƙitt.
Shiru kawai nayi ina kallon wayar kamar mai son ganin ainahin cikinta. Kafin naji wasu hawaye masu zafi sun gangaro min. Dan ALLAH minene laifinmu anan Bily, wlhy halin maza na ban takaici. Su dai kawai abinda suka so shine dai-dai. Ga kuma gaskiya sai su taketa kai a ɗora maka laifi. Miyyasa da Ummien ta kirasu duk basu nuna mata basu amince ba. Sai su komo ta bayan fage mu suna ƙuntata ma. Dan dai mune kuka masu daɗin hawa. Cikin ɓacin rai na tashi na hau haɗa kaya. Sai da na gama tsaf na fita zuwa wajen Ummie. Cikin danne ɓacin raina nai mata bayanin abinda ya faru harma na Fahad da Bahijja. Ai bama ta bari nakai ƙarshe ba tai kiransu ta haɗa har Yaya Hayatu da bai ce komai ba ta zage tas. Ta kuma ce ba zamu koma ɗin ba sai anyi bikin, suma tana buƙatar gannin kowannensu a Niger ranar ɗaurin aure. Idan ba hakaba ransu zai fi haka ɓaci.
Tofa Ummie ta ɓaro aiki. Dan daga wannan faɗa mu duka ukun suka ɗauke mana wuta. Muma sai muka haɗe namu kan kamar yanda Ummien ta bamu shawara muka tattarasu muka watsar. Haka muka cigaba da hutawarmu a Nigeria. Tun biki na sauran sati ɗaya Aunty Mama ta iso. Sai kawai Ummie tace mu shirya mu bita kawai suma zasu same mu. Haka kuwa akayi muka shirya mukabi Aunty Mama. Kasancewar jirgin dare muka bi mun isa batare da mun ƙaras da komai ba. An dai zo an ɗauke mu. Hajiya Mammah dama tana can one week kenan.
Duk da saukar dare mukai na fahimci mahaifin su Azizat shima na da ɗan halinsa gwargwadon iko. Dan mai rufin asiri ne ba talaka tiɓis ba. Matansa biyu yanzu da ƴaƴa kusan goma sha uku harda su Azizat ɗin. Gidansu nada girma babu laifi. Azizat dai nata ɗan nuna kamar jin nauyin mu, da alama har yanzu wancan abun daya faru na a ranta. Mudai duk muka basar kamar bamu fahimceta ba harta gaji ta saki jikinta. Kwanan mu biyu su Malika suka iso suma da su Ummie. Kasancewar Ummie ta saka hannu sosai a bikin ita da su Aunty Mama bikin an masa shiri na musamman gaskiya fiye da ƙarfin mahaifinsu. Gashi kuma mijin da Azizat ɗin zata aura ɗan gidan sarauta ne. Sai kuma kasancewarmu ya sake kambama komai da armashi. Tun ana saura kwanaki uku ɗaurin aure aka fara bikin al'adunsu na buzaye daban-daban da suka matuƙar ƙayatar damu. Aiko Malika itama ta samo nata. Tana dojewa tana dojewa muka sakata a layi. Tuni ta bi suka ɗinke kuwa. Ranar ɗaurin aure babu zato babu tsammani sai ga Yaya Awwab, Fahad, Yaya Hayatu, yaya Musaddiq, harda su Mansoor da Dad ɗin su da Uncle Sulaiman sai Abba da Uncle Abdullahi. Tofa nan aka fara kallon kallo, musamman mu masu laifi a wajen mazan namu. Bahijja nata ɓakyatun tsoro muka dakar da ita. Muka ciskule muma kamar bamu san ina suka dosa ba. Dama ni rabona da waya da nawa gogan tun ranar da yace zai aiko a ɗauki su Heedaya. Yau kam sai yay kamar bai ganni ba. Yana manne dai da ƴarsa yana mata murmushi da wasa. Itako tana faman ɓangale baki dan akwai sabo a tsakaninsu kam da shaƙuwa mai inganci. A yanzu haka bata iya cewa komai ba sai Dadaa. Dadaa dai Dadaa dai iya maganar

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login